Jump to content

Daƙiƙa:Bikin Mauludin Annabi

Daga wikishia

Bikin mauludin Annabi (Larabci: الاحتفال بالمولد النبوي) wani taro ne da ake yi duk shekara domin tunawa da ranar da ake haifi Annabin Muslunci (S.A.W), Shi'a da Ahlus-Sunna suna shirya wannan taro na murna da haihuwar Annabi, amma Su kuma Wahabiyawa suna la'akari da wannan maulidi ko biki a matsayin bidi'a, da hujjar cewa irin wannan biki da taro ba a yi shi ba a lokacin Annabi (S.A.W) da sahabbanshi.

Amma malamn Musulmi sun mayarwa da Wahabiyawa martani cewa, duk da wannan biki na mauludi ba a aikata shi ba a lokacin Annabi (S.A.W) da sahabbanshi ba, duk da haka wannan abu ba haramun ba ne a shari'ar Muslunci. Wannan malamai sun dogara da ƙur'ani wajan nuna halaccin yin Mauludin Annabi (S.A.W) da ayoyi da ma'anonin Kur'ani da suka yi umarrni kan girmama Annabi (S.A.W) da son shi.

Kazalika bisa wasu ruwayoyi na tarihi a ƙarni na huɗu hijira da bayanshi suna cewa, Musulmi sun yi bikin Mauludi Annabi (S.A.W), kuma mutanen Makka a ranar haihuwar Annabi (S.A.W) sun kasance suna taruwa a gurin, suna tabarruki da addu'a da sallah, har zuwa lokacin hukumar Alu Sa'ud suka rusa wannan gurin.

Ƴanshi'a suna ganin ranar 17 ga wata Rabi'ul Awwal ita ce ranar da aka haifi Manzon Allah (S.A.W), amma Ahlus-Sunna suna ganin 12 ga wata Rabi'u Awwal ita ce ranar mauludi ranar da aka haifi manzon Allah (S.A.W), a wannan rana ne malaman Shi'a suna yin wasiyya ga mutane kan mustahabbacin ba da sadaka a wannan ranar da yin aiki na gari da farantawa muminai da abubuwa kamar haka, kamar yadda suma Ahlus-Sunna suna yin umarni da ba da sadaka a ranar haihuwar ta Annabi (S.A.W) da ciyar da talakawa domin girmama Annabin Musulinci(S.A.W). saboda haka Musulmi suna gudanar da taron mauludi a duniya, kuma ana la'akarin wannan rana rana ce ta hutu a Iraƙ da Iran da Afganistan da Indiya da Fakistan da Indunusiya da Misra.

Gwamnatin tarayyar ƙasar Najeriya ma ba a barta a baya ba, kusan duk shekara tana bayar da hutu a ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal domin bawa al'ummar musulmi ƴanƙasar damar shagulgulan murnar mauludi.

Muhimmacin Mauludi Da Tarihinshi

Taron mauludi a ƙasar Najeriya

Tarurrukan da ake yi a ranar haihuwar Annabi (S.A.W) a ko wace shekara ana kiranshi da mauludi, akwai saɓani a tsakanin Shi'a da Ahlus-Sunna, da kuma Wahabiyawa a hannu guda kan shin ya halatta a yi mauludi ko a a? dukkan ƙungiyoyin Musulinci suna hallata yin mauludi, inda suke girmamawa da yin wannan mauludi a ranar haihuwarshi.[1] haka abun da ya ke a wasu ƙasashe kamar Iraƙ, da Iran[2], Indiya,[3] da Fakistan da Misra،[4] duk suna yin taron mauludin Annabi (S.A.W) ta hanyar yin abubuwa da suka shafi addini[5] da kuma taruka kazalika suna la'akarin wannan rana a matsayin ranar hutu. Amma Wahabiyawa suna ganin Mauludi a matsayin bidi'a da abin da ya haramta.[6]

A ƙasar Najeriya a duk shekara a ranar zagayowar haihuwa Annabi gwamnatin ƙasar tana ba da hutu, Musulmi suna shirya bukukuwan mauludi musamman ma a jihohin Arewacin ƙasar misalin Kano, Kaduna kai harma da jihohin Kudu kamar Lagos.[7]

Tarihin fara mauludi yana komawa zuwa ƙarni na huɗu da na biyar. Malamin tarihin ƙarni na 9 Ahmad Bin Ali Muƙrizi ya faɗi cewa, mauludin Annabi (S.A.W) ya yaɗu ne a lokacin mulkin Faɗimiyyun daga shekara ta( 297-567) a Misra.[8] bisa abin da ya zo cikin litattafan tarihi Muzaffarud-din Alkaukabari (Rasuwa: 530 h) da shugaba Salahud-dini Ayyubi da shugaban Arbil duk sun yi mauludin Annabi (S.A.W)a watan Rabi'ul Awwal[9]

Shin Bikin Mauludi Bida'a Ne?

Wahabiyawa suna la'akari da yin mauludi Annabi (S,A.W) a matsayin bidi'a kuma haramun ne.[10] Abdul-Aziz Bin Baz ɗaya daga cikin malaman Wahabiyawa yana ganin cewa yin mauludin Annabin Musulinci bidi'a ne.[11] Kamar yadda malaman Salafiyya suke haramta yin taruka ko halartasu a yayin bukokuwan mauludi, da zama a gurin irin wannan tarukan shima haramun ne,[12] kamar yadda wasu marubuta na Wahabiyya suke jingina fasiƙanci da rashin addini da abin da ya yi kama da haka ga mutanen da suke shirya mauludin Annabi (S.A.W).[13] Dalilin Wahabiyawa kan bidi'antar da mauludi, shi ne cewa ba yi ba a zamanin Annabi (S.A.W) ko lokacin sahabbai.[14]

Amsar Ƴanshi'a Da Ahlus-Sunna

Duk da babu daga shari'a da ya zo kan mauludin Annabi (S.A.W), sai dai cewa akwai ayoyi da yawa da suke ƙarfafa yin mauludi.[15] Haƙika malamai sun yi amfani da gamagarin ma'anonin ayoyin Alƙur'ani a dunƙuƙule, kamar larurar son Annabi (S.A.W)[16] da larurar girmama shi[17] kan halasci da shar'anci yin mauludin mai girma.[18] Bisa abin da malamin Shi'a Jafar Subhani ya ce, shi yin mauludi wani abu ne da musulmi suke bayyana da nuna so da ƙaunar Manzon (S.A.W). shi wannan so ƙur'ani ya yi nuni kan kansa.[19]

Bikin murnar ranar haihuwar Annabi da Musulmi da Kirista suka shirya a Kaduna Najeriya

Bisa dogaro kan ayoyin ƙarshe a cikin suratul Ma'ida waɗanda suke dalili ne da ya nuna cewa Annabi Isa (A.S) ya yi mauludi a ranar da ma'ida (Kaɓaki) ta sauka gare shi da mutanenshi Alhawariyyi daga sama, kuma har yanzu Kiristoci suna yin bikin tinawa da wannan rana, Saboda haka ana ɗauka wajibi ne a yi bikin haihuwar Annabi na Musulunci (SAW), saboda shi ne wanda ya ceci duniya daga jahilci da bautar gumaka, kuma wannan ni'ima tafi kaɓakin da aka saukarwa mutanen Annabi Isa (A.S).[20]

Yusuf Alƙardawi ɗaya daga cikin malaman Ahlus-Sunna ya kafa hujja kan yin maulidin Annabi (S.A.W) da halaccinshi, inda ya yi imani cewa yin mauludin Annabi (S.A.W) da tinawa da abubuwa da suka faro na Musulinci kamar tini ne kan ni'imar Allah da ya yiwa Musulmi, wannan tinatarwar ba bidi'a ce kuma ba haramun ba, wannan al'amari ne da yake mustahabbi[21] malamin Ahlus-Sunna Ɗahir Alƙadiri yana cewa, babu wata matsala wajan aikata wani abu na halas wanda shari'a ba ta hana ba, ya ƙara da cewa wannan abu ya zama al'ada ga mutane, kuma shi yin Mauludi hadafinshi shi ne, nuna rabauta da dacewa da Akayi sakamakon haihuwar Annabin Musulinci (S.A.W).[22]

Kamar yadda wata ruwaya ta zo cikin littafin Iƙbalul A'amal tana cewa yin azumi a ranar haihuwar Annabi (S.A.W) yana da ladan da ya kai azumin shekara ɗaya[23] Kamar yadda malaman Shi'a suka tafi kan cewa mustahabbi ne yin sadaka da ziyarar gurare masu tsarki da yin aikin alheri da farantawa muminai a ranar da aka haifi Annabi (S.A.W)[24] kuma a litattafan Shi'a an rawaito yin wata sallah ta masamman a ranar da aka haifi annabi (S.A.W)[25] kamar yadda malaman Ahlus-Sunna suna yiwa mutane wasiyya da yin huɗuba da lacca kan Annabi (S.A.W) da kuma karanta ƙur'ani da tausayawa mutane da ba da kyauta da ciyar da mutane.[26]

Lokacin Da Gurin Da Aka Haifi Annabi (S.A.W)

Akwai saɓani kan tarihin da aka haifi Annabi[27] Amma abin da ya shahara gun malaman shi'a shi ne an haifi manzon Allah (S.A.W)a 17 ga wata Rabi'ul Awwal, amma a gurin Ahlus-Sunna abin da ya fi shahara shi ne an haifi Manzon Allah (S.A.W) a 12 ga wata Rabi'u Awwal,[28] saboda haka ne ƴanshi'a suka sanya tazarar da take tsakanin wannan tarihi guda biyu ta zama satin haɗin kai a tsakanin Shi'a da Ahlus-Sunna.[29]

An haifi Annabi (S.A.W) a wani gida a unguwar Shi'ibi Abi Ɗalib, a Makka a tsakanin dutsen Abil Ƙaisi da dutsen Alkandama.[30] Bisa maganar wani malami na Shafi'iyya Muhammad ɗan Umar Barraƙ wanda ya rasu a shekara ta 930 hijira, ya ce mutanen Makka sun taru a gurin da aka haifi Annabi (S.A.W) a daren da aka haife shi, suka dinga ambaton Allah da yin Sallah da sami shi albarka.[31]

Kamar yadda Allama Majlisi malamin Hadisi a ƙarni na goma sha ɗaya ya naƙalto cewa gurin da aka haifi manzon Allah, wuri ne da mutane suke zuwa ziyara tun yana raye har zuwa zamanin hukumar Alu Sa'ud a Hijaz[32] amma sakamakon aƙidar Wahabiyawa ta hana neman albarka daga duk wani abu na Annabawa da guraren da aka binne su da inda aka binne mutanen kirki, sai aka rushe gurin.[33]

Bayanin kula

  1. "كيف تحتفل الدول العربية بالمولد النبوي الشريف؟"، Kamfanin labarai Iqna.
  2. Time.ir.
  3. Holidays.
  4. Public Holidays in Pakistan 2018.
  5. عيد المولد النبوي الشريف.
  6. Al-Daweish, Fatawi Allujna Da'ima, juzu'i. 3, shafi. 299
  7. https://hausa.legit.ng/news/1671883-gwamnatin-tarayya-za-ta-ba-yan-najeriya-hutu-a-watan-satumbar-2025-ji-dalili/
  8. Al-Maqrizi, Al-Mawa'iz wal-I'tibar bi Dhikr al-Khitat wal-Athar, Juzu'i na 2, Shafi na 436
  9. Al-Maqrizi, Al-Mawa'iz wal-I'tibar bi Dhikr al-Khitat wal-Athar, Juzu'i na 2, Shafi na 436
  10. Al-Daweish, Fatawi Allujna Da'ima, juzu'i. 3, shafi. 299
  11. «الإمام ابن تيمية لم يستحسن الاحتفال بالمولد النبوي»، الموقع الرسمي لـ (بن باز).
  12. Shahata, Al-Mawlid an-Nabawi... Hal Nuhtafil?, Shafi na 116
  13. Ad-Dubayri, Al-Ihtifal bi Milad ar-Rasulullah salla Allahu alayhi wa alihi wa sallam, Shafi na 9
  14. «الإمام ابن تيمية لم يستحسن الاحتفال بالمولد النبوي»، الموقع الرسمي لـ (بن باز).
  15. Al-Karimi, Muhammad Mahdi, Al-Ihtifal wal-Farah bi Milad ar-Rasul al-Karim salla Allahu alayhi wa sallam min Manzur al-Kitab was-Sunnah, Shafuka na 127-132
  16. Surat at-Tawba: 23
  17. Surat al-A‘raf: 157
  18. Al-Karimi, Muhammad Mahdi, Al-Ihtifal wal-Farah bi Milad ar-Rasul al-Karim salla Allahu alayhi wa sallam min Manzur al-Kitab was-Sunnah, Shafi na 126
  19. «الاحتفال بالمولد النبوي الشريف هو حب عملي له واتباع تعليمات القرآن الكريم»، موقع شفقنا.
  20. «الاحتفال بالمولد النبوي الشريف هو حب عملي له واتباع تعليمات القرآن الكريم»، موقع شفقنا.
  21. «الاحتفال بمولد النبي والمناسبات الإسلامية»، الموقع الرسمي ليوسف القرضاوي.
  22. Al-Qadiri, Milad an-Nabi, Shafuka na 15 da 17
  23. Ibn Tawus, Iqbal al-A'mal, Juzu'i na 2, Shafi na 603
  24. At-Tusi, Misbah al-Mutahajjid, Juzu'i na 2, Shafi na 791
  25. Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, Juzu'i na 95, Shafi na 359
  26. Ibn Tawus, Iqbal al-A'mal, Juzu'i na 2, Shafuka na 611-612
  27. Al-Mas'udi, Muruj adh-Dhahab, Juzu'i na 1, Shafi na 362
  28. As-Subhani, Ila al-Abad, Juzu'i na 1, Shafi na 151
  29. Al-Khomeini, Sahifat al-Imam, Juzu'i na 15, Shafuka na 440 da 455
  30. Al-Maqrizi, Imta' al-Asma', Juzu'i na 1, Shafi na 6
  31. Bahraq, Hada'iq al-Anwar, Shafi na 150
  32. Al-Majlisi, Mir'at al-‘Uqul, Juzu'i na 5, Shafi na 174
  33. اAl-‘Amili, As-Sahih min Sirat an-Nabi, Juzu'i na 2, Shafi na 147

Nassoshi

  • Ibn Ṭāwūs, Ali bn Musa, Al-Iqbal bi al-A‘mal al-Hasanah, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, bugu na 2, 1409 H.
  • Ibn Kathir, Isma’il bn Umar, Al-Bidayah wa al-Nihayah, Beirut, Dar al-Fikr, 1407 H.
  • Khomeini, Ruhullah, Ṣaḥīfat al-Imam, Tehran, Mu’assasat Tanzim wa Nashr Āthār al-Imam al-Khomeini, 1378 Sh.
  • Al-Dabiri, Al-Iḥtifal bi Mawlid al-Rasul Allah, Maktabat al-‘Aqidah, 1437 H.
  • Al-Duwish, Ahmad bn Abd al-Razzaq, Fatawa al-Lajnah al-Da’imah, Riyadh, Ri’asat Idarat al-Buḥuth al-‘Ilmiyyah wa al-Ifta’, bugu ba a sani ba, lokaci ba a sani ba.
  • Al-Subḥani, Ja‘far, Ila al-Abad, Qom, Bustan al-Kitab, 1380 Sh.
  • Al-Ṭusi, Muhammad bn Hasan, Miṣbah al-Mutahajjid wa Silah al-Muta‘abbid, Tehran, al-Maktabah al-Islamiyyah, bugu ba a sani ba, lokaci ba a sani ba.
  • Al-‘Amili, Ja‘far Murtaḍa, Al-Ṣaḥiḥ min Sirat al-Nabi al-A‘ẓam, Mu’assasat al-‘Ilm wa al-Thaqafah, Dar al-Ḥadith, 1426 H.
  • Al-Qadiri, Muhammad Tahir, Mawlid al-Nabi, Minhaj al-Qur’an, 2008 M.
  • Al-Karimi, Muhammad Mahdi, Al-Iḥtifal wa al-Faraḥ bi Mawlid al-Rasul al-Karim min Manẓur al-Kitab wa al-Sunnah, Majallat al-Fiqh al-Islami, lamba 69, Rabi‘ 2009 M.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Biḥar al-Anwar, Beirut, Dar Iḥya’ al-Turath al-‘Arabi, bugu na 2, 1403 H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Mir’at al-‘Uqul fi Sharḥ Akhbar Āl al-Rasul, tahqiq: Sayyid Hashim, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, bugu na 2, 1404 H.
  • Al-Mas‘udi, Ali bn Husayn, Muruj al-Dhahab wa Ma‘adin al-Jawhar, tahqiq: As‘ad Dagher, Qom, Dar al-Hijrah, bugu na 2, 1409 H.
  • Al-Maqrizi, Ahmad bn Ali, Al-Suluk li Ma‘rifat Duwal al-Muluk, Beirut, Dar al-Kutub al-‘Ilmiyyah, 1418 H.
  • Al-Maqrizi, Ahmad bn Ali, Al-Mawa‘iẓ wa al-I‘tibar bi Dhikr al-Khuṭaṭ wa al-Āthar, hawashi: Khalil al-Mansur, Beirut, Dar al-Kutub al-‘Ilmiyyah, 1419 H.
  • Al-Maqrizi, Ahmad bn Ali, Imta‘ al-Asma‘ bima li al-Nabi min al-Aḥwal wa al-Amwal wa al-Ḥafadah wa al-Mata‘, tahqiq: Muhammad Abd al-Hamid, Beirut, Dar al-Kutub al-‘Ilmiyyah, bugu na 1, 1420 H.
  • Baḥraq, Muhammad bn Umar, Ḥada’iq al-Anwar wa Maṭali‘ al-Asrar fi Sirat al-Nabi al-Mukhtar, tahqiq: Muhammad Ghassaq Naṣuḥ ‘Azqul, Jeddah, Dar al-Minhaj, 1419 Hijira qamari.
  • Shaḥatah, Muhammad Ṣaqr, Al-Mawlid al-Nabawi… Hal Naḥtafil?, Alexandria, Dar al-Khulafa’ al-Rashidin, bugu ba a sani ba, lokaci ba a sani ba
  • شحاتة، محمد صقر، المولد النبوي... هل نحتفل؟، الإسكندرية، دار الخلفاء الراشدين، د.ط، د.ت.
  • "كيف تحتفل الدول العربية بالمولد النبوي الشريف؟"، Kamfanin dillancin labarai na Ikna.
  • «الاحتفال بالمولد النبوي الشريف هو حب عملي له واتباع تعليمات القرآن الكريم»، موقع شفقنا.
  • «الاحتفال بمولد النبي والمناسبات الإسلامية»، الموقع الرسمي ليوسف القرضاوي.
  • «الإمام ابن تيمية لم يستحسن الاحتفال بالمولد النبوي»، الموقع الرسمي لـ (بن باز).
  • عيد المولد النبوي الشريف.
  • Public Holidays in Pakistan 2018.
  • Holidays.
  • Time.ir.
  • Legit,Hausa[1]