Jump to content

Daƙiƙa:Allah

Daga wikishia
Wannan maƙala ce game da keɓantaccen sunan Allah. Domin sanin Allah da bahasosin sanin Allah ku duba shafin Khoda da Sanin Allah.

Allah (Larabci: الله) suna ne na musamman kuma shi ne sunan Allah mafi shahara a addinin Muslunci. A imanin malaman Muslunci, Allah suna ne da ya tattaro dukkanin siffofin kamala na Allah kuma ismul a'azam. Haka kuma suna cewa wannan suna yana da mafi ɗaukakar matsayi cikin Kurani da addu'a kuma ya kasance ginshiƙi na tauhidi, shahadataini da ayoyin Kur'ani. Kalmar Allahu ta keɓantu da Allah kuma ba a amfani da ita a kan waninsa. Wannan kalma an ambace ta a Kur'ani fiye da karo dubu biyu.

A cewar Jafar Subhani, mafi yawan malamin tafsirin Kur'ani, mafi yawan malaman hadisi da tafsiri sun tafi kan cewa an ciro kalmar Allahu daga "Alaha""da take da ma'anar wanda ya cancanci a bauta masa. Tare da haka akwai wasu ra'ayoyin daban da ake tsammani da aka yi bayaninsu daga jumla akwai cewa tana da ma'anar ruɗewa, firgici da dogaro da kuma kwanciyar hankali.

Cikin irfanin Muslunci, sunan Allah ya kasance a cikin salsalar ginshiƙan sunayen Allah kuma sauran sunayen sun samo asali ne daga wannan suna. Kalmar Allahu cikin al'adu da al'ummun Muslunci, an yi amfani da ita sosai. Alal misali an sanya wannan kalma jikin sulallan daurorin daulolin Muslunci da wurare masu tsarki kamar haramai da masallatai da tutoci da alamomi na ba'arin ƙasashen Muslunci kamar Iran, jamhuriyar Azerbaijan da Iraƙ.

Haka kuma jikin tambarin sojojin ƙasar Najeriya akwai rubutun "Nasara Daga Allah Take".

Matsayin Sunan Allah A Al'adun Muslunci

"Allah"suna ne na musamman[1] kuma mafi shaharar sunan Allah a Muslunci.[2] Malaman Muslunci suna la'akari da wannan suna matsayin jigo da ginshiƙi na tauhidi da Ikhlasi da yake tare da mafi ɗaukakar matsayi a Kur'ani da addu'a.[3] Haka kuma suna cewa kalmar Allahu kaɗai tana da misali guda ɗaya rak, kuma suna ne da ya tattaro dukkanin siffofi na kamala kuma ba a amfani da shi kan wanin Allah.[4] Saboda haka, Allahu ginshiƙi tattaunawa da bahasosi game da Allah a cikin littafin sama na Musulmi da kuma Nahajul Balaga, kuma an ce cikin Kur'ani ana tabbatar dukkanin siffofin kamala ga Allah.[5]

Kalmar Allahu ginshiƙi ne na take guda biyu na asali a Muslunci, ma'ana shahadataini, cikin shahada ta farko, an kore samuwar duk wani abin bautawa da gaskiya koma bayan Allah, cikin shahada ta biyu, an gabatar da Sayyidina Muhammad (S.A.W) a matsayin ɗan'aiken Allah.[6]

Kalmar Allahu, tare da sunaye kamar "Rabbu" da "Ilahu" sune mafi yawan sunayen Allah da aka fi amfani da su a cikin Kur'ani.[7] an ƙidaice adadin maimaicin kalmar Allahu a cikin Kur'an sau 2699[8]2707[9] da 2807.[10]

Da yawa-yawan malaman Muslunci suna ɗauƙar Allahu matsayin Ismul A'azam.[11] Daga jumlar dalilin kasancewar wannan kalma Ismul A'azam, ita ce tushe da asasin tauhidi, kuma tare da furta wannan kalma kafiri yana cirata zuwa ga imani, idan wani maimakon "La ilaha illallhu"sai ya furta "La ilaha Illar Rahman" hakan ba zai fitar da shi daga da'irar kafirci ba zuwa Muslunci.[12]

Cikin harshen Farsi kalmar Khoda ita take matsayin kalmar Allahu.[13] Cikin tarjamomi na baya-bayan nan na littafi mai tsarki na Yahudu da Nasara da Zartush, kalmomin "Yahuwa”, "Ta'us" da Ahuramazda da suke nuni zuwa ga Allah, an tarjama su zuwa kalmar Allah.[14] Tun kafin zuwan Muslunci an yi amfani da ita kuma a cikin aya ta 87 suratul Zukhruf da aya ta 25 suratul Luƙman an yi ishara da amfani da wannan kalma tun kafin saukar da Kur'ani.[15]

Asali Da Kuma Nazarin Ma'ana

Wasu suna ganin Allahu kalma ce ta Larabci[16] Wasu kuma suna cewa asalin wannan kalma daga harshen Ibraniya ko Suryaniyya take.[17] A imanin wasu malamai, kalmar "Allahu" a asali ta kasance "Al-Ilah" harafin alhamza na biyu sakamakon yawan amfani sai aka shafe shi kalma ta juya zuwa "Allahu".[18] A ra'ayin wasu kalmar Allahu ta samo asali daga "Lahu" sai alif da lamun suka gangara kanta ta zama Allahu.[19] Dangane da ciro kalmar Allah daga wata kalma daban ko kuma ba a ciro aka yi ba, malamai sun yi saɓani.[20] A cewar Fakhrur Razi, mafi yawan malaman fiƙihu da usul suna ganin wannan kalma ba a ciro ta daga wata kalma daban ba.[21] Waɗanda suka tafi kan cewa suna ne da aka ciro daga wata kalma daban, sun ambaci ra'ayoyi daban-daban game da asali da tushen ta[22] ba'ari daga wannan ra'ayoyi sun kasance kamar haka:

  • Allahu an ciro daga Alaha ma'ana wanda ya cancanci a bauta masa.[23] A cewar Jafar Subhani, malamin tafsirin Kur'ani, da yawa-wayan malaman hadisi da tafsiri sun yarda da wannan mahanga.[24] Haka zalika an naƙalto wannan ma'ana cikin riwayoyi.[25]
  • An ciro daga Aliha ko Waliha da ma'anar ruɗewa, saboda hankula suna ruɗewa cikin sanin zatin Allah.[26]
  • An ciro daga Ilahu da ma'ana firgici da dogara; saboda mutane a lokacin wahalhalu suna fakewa da Allah[27] kuma suna dogara da shi.[28]
  • An ciro daga Ilahu da ma'anar kwanciyar hankali da nutsuwa, saboda ambaton Allah yana samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.[29]
  • An ciro daga "Laha" da ma'anar kasancewa cikin ɓuya; saboda Allah ya ɓuya daga barin hankula da wahami da hiyali.[30]

Allahu A Cikin Irfanin Muslunci

A faɗin malaman irfani, a cikin irfanin Muslunci sunayen Allah suna da wani keɓantaccen tsari, sunan Allah da ya tattaro komai, shi ne ginshiƙin salsalar jerin sunayen Allah, bayansa ne sunaye huɗu (Ma'ana Farko, ƙarshe, bayyane, asirce) da sunaye bakwai duka suna ɓuɓɓugowa ne daga sunan Allahu, kuma haka har a kai ga sunaye ƙanana, saboda haka a cikin irafnin Muslunci baki ɗayan sunayen Allah suna komawa zuwa ga Allahu.[31]

Amfani Da Kalmar Allahu

An rubuta kalmar Allahu a jikin tuta da tambarin ƙasar Iran[32] da tambarin jamhuriyar Azerbaijan.[33] da tuta da tambarin ƙasar Iraƙ cikin shakali da tsari na Allahu Akbar.[34] Kalmar Allahu, ita kaɗai ko tare da wata kalmar ta kasance kan sulallan da ake bugawa a daulolin Muslunci da suka gabata.[35] Wannan kalma an rubutu ta a wurare masu tsarki daban-daban kamar haramai da masallatai. Haka kuma wannan kalma ta Allahu ta kasance take na sojojin ƙasar Najeriya da ke jikin tambarinsu.[36] Masu rubutun kwalliya da daman gaske sun yi aiki kan rubutu da kyakkyawan salo na wannan kalma cikin hanyoyi da salo daban-daban.

Bayanin kula

  1. Fakhri Razi, Tafsir al-Kabir, 1420 AH, Jild 1, Shafi 143. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur’an, 1390 AH, Jild 1, Shafi 18. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 119.
  2. Kaf’ami, Al-Maqam al-Asna, 1412 AH, Shafi 25.
  3. Kaf’ami, Al-Maqam al-Asna, 1412 AH, Shafuka 25 da 26.
  4. Safi Golpaygani, Ilahiyyat dar Nahj al-Balagha, 1386 SH, Shafi 36.
  5. Safi Golpaygani, Ilahiyyat dar Nahj al-Balagha, 1386 SH, Shafuka 33–36.
  6. Pakatchi, «Allah», Shafi 73.
  7. Misbah Yazdi, Khudashnasi, 1396 SH, Shafi 58.
  8. Ruhani, Al-Mu’jam al-Ihsai li-Alfaz al-Qur’an al-Karim, 1372 SH, Jild 2, Shafuka 244–262.
  9. Safi Golpaygani, Ilahiyyat dar Nahj al-Balagha, 1386 SH, Shafi 34.
  10. Kashfi, Jawahirin Tafsir, 1379 SH, Shafi 357..Ashtiani, Tafsir Surah Fatiha al-Kitab, 1377 SH, Shafi 63
  11. Kashfi, Jawahirin Tafsir, 1379 SH, Shafuka 357 da 361. Kaf’ami, Al-Maqam al-Asna, 1412 AH, Shafi 26. Khomeini, Misbah al-Hidayah, 1392 SH, Shafuka 12 da 13. Ashtiani, Tafsir Surah Fatiha al-Kitab, 1377 SH, Shafi 64.
  12. Kashfi, Jawahirin Tafsir, 1379 SH, Shafi 361.Ashtiani, Tafsir Surah Fatiha al-Kitab, 1377 SH, Shafi 64.
  13. Javadi Amoli, Tawhid dar Qur’an, 1395 SH, Shafi 228.
  14. Pakatchi, «Allah», Shafi 73
  15. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur’an, 1390 AH, Jild 1, Shafi 18. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafuka 116 da 117.
  16. Ku duba: Fakhri Razi, Tafsir al-Kabir, 1420 AH, Jild 1, Shafi 148. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 116
  17. Fakhri Razi, Tafsir al-Kabir, 1420 AH, Jild 1, Shafi 148. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 116
  18. Sheikh Saduq, Al-Tawhid, 1398 AH, Shafuka 195 da 196.. Sheikh Tusi, Al-Tibyan fi Tafsir al-Qur’an, Beirut, Jild 1, Shafi 27. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur’an, 1390 AH, Jild 1, Shafi 18. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 118
  19. Sheikh Tusi, Al-Tibyan fi Tafsir al-Qur’an, Beirut, Jild 1, Shafi 27. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372 SH, Jild 1, Shafi 91.
  20. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 117.
  21. Fakhri Razi, Tafsir al-Kabir, 1420 AH, Jild 1, Shafi 143.
  22. Abu al-Futuh Razi, Rawz al-Jinan, 1408 AH, Jild 1, Shafuka 55–57.
  23. Sheikh Saduq, Al-Tawhid, 1398 AH, Shafi 195.. Sheikh Tusi, Al-Tibyan fi Tafsir al-Qur’an, Beirut, Jild 1, Shafi 27. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372 SH, Jild 1, Shafi 91. Abu al-Futuh Razi, Rawz al-Jinan, 1408 AH, Jild 1, Shafi 57. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur’an, 1390 AH, Jild 1, Shafi 18
  24. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 117.
  25. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, Jild 1, Shafi 87. Sheikh Saduq, Al-Tawhid, 1398 AH, Shafi 221.
  26. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372 SH, Jild 1, Shafi 91. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur’an, 1390 AH, Jild 1, Shafi 18.
  27. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372 SH, Jild 1, Shafi 91. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 118.
  28. Abu al-Futuh Razi, Rawz al-Jinan, 1408 AH, Jild 1, Shafuka 55 da 56.
  29. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372 SH, Jild 1, Shafi 91. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 118.
  30. abarsi, Majma’ al-Bayan, 1372 SH, Jild 1, Shafi 91. Abu al-Futuh Razi, Rawz al-Jinan, 1408 AH, Jild 1, Shafuka 55 da 56. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 118
  31. Yazdanpanah, Mabani wa Usool-e ‘Irfan-e Nazari, 1389 SH, Shafuka 455–460. Amini-Nejad da wasu, Mabani wa Falsafe-ye ‘Irfan-e Nazari, 1390 SH, Shafuka 237–240.
  32. «طرح پرچم ایران؛ بازتاب گفتمان انقلابی و اسلامی»،‌ Kafamin Labarai ta Jamhuriyar Muslunci.
  33. «لفظ مقدس الله در مرکز آرم حکومتی جمهوری آذربایجان»، Kafamin Labarai ta Aran
  34. «پرچم عراق و سیر تحول آن»Shafin yanar gizo na Iraq Yar.
  35. Sarafrazi, «Sha’air Shia bar Sikkah-haye Islami ta Shakl-giri Hukumat Safaviyan», Shafuka 9–11, 19, 22 da 23
  36. Nigerian Army logo:https://nigerianfinder.com/nigerian-army-logo-description-and-meaning/?utm_source=chatgpt.com

Nassoshi

  • Ashtiyani, Jalaluddin, Tafsir Suratul Fatiha al-Kitab, Qom, Daftar Talibaat Islami, 1377 HS.
  • Fakhr Raaziy, Muhammad bin Umar, At-Tafsiirul Kabiir (Mafaatiihul Ghaib), Beirut, Daar Ihyaa’ut-Turaathil ‘Arabiy, bugun uku, 1420 h / 1999 m.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Umar, al-Tafsir al-Kabir (Mafatih al-Ghayb), Beirut, Dar Ihya’ al-Turath al-‘Arabi, Chap Uku, 1420 Q / 1999 M.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tasnim, Qom, Markaz Nashr Isra, Chap Uku, 1381 HS.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tawhid dar Qur’an (az Silsilah Tafasir Mawzu’i Jild Doma), ba Koshish Haidar Ali Ayubi, Qom, Markaz Bainal-‘Alami Nashr Isra, 1395 HS.
  • Jawadiy Amuliy, Abdullahi, Tasniim, Qum, Markazin Nashar Israa, bugun uku, 1381 sh.
  • Jawadiy Amuliy, Abdullahi, Tauhiidi a cikin Al-Kur’ani (daga jerin tafsirin maudu’i, juzu’i na biyu), da kokarin Haidar Aliy Ayyubiy, Qum, Markazin Duniya na Nashar Israa, 1395 sh.
  • Kaashifiy, Mullah Husain, Jawahirut-Tafsiir, Tehran, Markazin Bincike na Miraas Maktoob, 1379 sh.
  • Kafa‘amiy, Ibraahiim bin Aliy, Al-Maqaamul Asnaa fii Tafsiiril Asmaa’il Husnaa, tahqiq Faaris Al-Husun, Qum, Mu’assasar Qaa’im Aal-Muhammad (aj), 1412 h / 1370 sh.
  • Kaf’ami, Ibrahim bin Ali, al-Maqam al-Asna fi Tafsir al-Asma’ al-Hasna, Tahqiq Fars al-Huson, Qom, Mu’assasah Qa’im Al-Muhammad (AJ), 1412 Q / 1370 HS.
  • Kashfi, Mulla Husayn, Jawahir al-Tafsir, Tehran, Markaz Pazhuhishi Mirath Maktub, 1379 HS.
  • Khomeini, Sayyid Ruhullah, Misbah al-Hidayah ila al-Khilafah wa al-Wilayah, Tehran, Mu’assasah Tanzim wa Nashr Asar Imam Khomeini, 1392 HS.
  • Khumainiy, Sayyid Ruhullahi, Misbaahul Hidaayah ilal Khilaafah wal Wilaayah, Tehran, Mu’assasar Tsarawa da Buga Ayyukan Imam Khumainiy, 1392 sh.
  • Kulayni, Muhammad bin Ya’qub, al-Kafi, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, 1407Q.
  • Kashfi, Mulla Husain, Jawahirin Tafsiri, Tehran, Cibiyar Bincike na Gado na Rubuce-rubuce, 1379 SH.
  • Kaf’ami, Ibrahim bin Ali, Matsayin Mafi Girma a Tafsirin Sunayen Kyawawa, Gyara: Faris al-Hassoun, Qom, Cibiyar Qa’im Aal Muhammad (AJ), 1412 AH / 1370 SH.
  • Misbaah Yazdiy, Muhammad Taqiy, Khudaa-shinaasiy, Qum, Intisharaat Mu’assasar Ilimi da Bincike ta Imam Khumainiy, 1396 sh.
  • Najafiy, Muhammad Hasan, Jawahirul Kalaam fii Sharhi Sharaa’i‘il Islaam, Beirut, Daar Ihyaa’ut-Turaathil ‘Arabiy, bugun bakwai, 1362 sh.
  • Pakatchi, Ahmad *«الله»A cikin Dayrah al-Ma’arif al-Buzurg Islami, Jild 10, Tehran, Markaz Dayrah al-Ma’arif al-Buzurg Islami, Chap Awwal, 1380 HS
  • Nigerian Army logo:https://nigerianfinder.com/nigerian-army-logo-description-and-meaning/?utm_source=chatgpt.com
  • Rouhani, Mahmoud, al-Mu’jam al-Ihsai li Alfaz al-Qur’an al-Karim (Farhang Amari Kalimat al-Qur’an al-Karim), Mashhad, Astān Quds Razavi, 1372 HS / 1414 Q.
  • Ruhaniy, Mahmud, Al-Mu’ujamul Ihsaa’iy li Alfaazil Kur’aanil Kariim (Farhang Aamariy Kalimomin Al-Kur’ani Mai Girma), Mashhad, Aastan Quds Razawiy, 1372 sh / 1414 h.
  • Saafiy Gulpaaygaaniy, Lutfullah, Ilaahiyaat dar Nahjul Balaaghah, Qum, Bustaan Kitaab, 1386 sh.
  • Safi Golpayegani, Lutfullah, al-Ilahiyat dar Nahj al-Balagha, Qom, Bustan Kitab, 1386 HS.
  • Sarafaraaziy, Abbas,«شعائر شیعی بر سکه‌های اسلامی تا شکل‌گیری حکومت صفویان»، Mujallar Shi’a-Shinasi (Nazarin Shi’a), lamba ta 51, watan Aban shekara ta 1394 (Hijirar Shamsiyya)
  • Shaikh Saduuq, Muhammad bin Ali bin Baabawaih, At-Tauhiid, Qum, Jaami‘atul Mudarrisiin Hauzar Ilmin Qum, bugun farko, 1398 h.
  • Shaikh Tuusiy, Muhammad bin Hasan, At-Tibyaan fii Tafsiiril Qur’aan, Beirut, Daar Ihyaa’ut-Turaathil ‘Arabiy, ba tare da shekara ba.
  • Sheikh Saduq, Muhammad bin Ali bin Babawayh, al-Tawhid, Qom, Jami’at Madarisin Hawzah ‘Ilmiyyah Qom, Chap Awwal, 1398 Q.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, al-Tibyan fi Tafsir al-Qur’an, Beirut, Dar Ihya’ al-Turath al-‘Arabi, Bi-ta.
  • Sobhani, Ja’far, Manshur Javid, Qom, Mu’assasah Imam Sadiq (A), 1390 HS.
  • Subhaaniy, Ja’afar, Manshur Jaawid, Qum, Mu’assasar Imam Sadiq (a), 1390 sh.
  • Tabaatabaa’iy, Sayyid Muhammad Husain, Al-Miizaan fii Tafsiiril Qur’aan, Beirut, Mu’assasatul A‘lamiy lil Matbuu‘aat, 1390 h.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma’ al-Bayan fi Tafsir al-Qur’an, Tehran, Nasir Khosrow, bugu na Uku, 1372 HS.
  • Tabarsiy, Fadlu bin Hasan, Majma‘ul Bayaan fii Tafsiiril Qur’aan, Tehran, Naasir Khusraw, bugun uku, 1372 sh.
  • Tabatabai, Sayyid Muhammad Husayn, al-Mizan fi Tafsir al-Qur’an, Beirut, Mu’assasah al-A’lami lil-Matbu’at, 1390 Q.
  • Yazdaan-Panaah, Sayyid Yadullah, Mabaani wa Usul ‘Irfaan Nazariy, rubutu na Sayyid ‘Ataa Anzaliy, Qum, Mu’assasar Ilimi da Bincike ta Imam Khumainiy, bugun biyu, 1389 sh
  • Yazdiy, Muhammad Kaazim, Al-‘Urwatul Wuthqaa ma‘at-Ta‘liqaat, Qum, Madrasa Aliy bin Abiy Taalib (a), 1428 h / 1326 sh.
  • «لفظ مقدس الله در مرکز آرم حکومتی جمهوری آذربایجان»Kamfanin Dillancin Labarai na Aran, ranar wallafa labarin: 29 Mordad 1396 (Hijirar Shamsiyya), ranar duba/ziyara: 28 Ordibehesht 1404 (Hijirar Shamsiyya).
  • «پرچم عراق و سیر تحول آن»،Shafin yanar gizo na Iraq-Yar, Tarihin shigarwa: 24 ga watwan 9, shekara ta 1399 HS, Tarihin ziyara: 28 ga watan 2 shekara ta 1404 HS.
  • Sarafaraazi, Abbas«شعائر شیعی بر سکه‌های اسلامی تا شکل‌گیری حکومت صفویان»،Majallar Kwata-kwata ta Nazarin Shia, Lamba 51, Aban 1394 HS.
  • «لفظ مقدس الله در مرکز آرم حکومتی جمهوری آذربایجان»Kamfanin Dillancin Labarai na Aran, ranar wallafa labarin: 29 Mordad 1396 (Hijirar Shamsiyya), ranar dubawa/ziyara: 28 Ordibehesht 1404 (Hijirar Shamsiyya).
  • «طرح پرچم ایران؛ بازتاب گفتمان انقلابی و اسلامی»،‌Hedikwatar Labarai ta Jamhuriyar Islama, Ranar Rubuta Labari: 25 Tir 1399 HS, Ranar Ziyara: 27 Ordibehesht 1404 HS.
  • Abulfatuhu Razi, Husain bin Ali, Rawd al-Jinan wa Ruh al-Jinan fi Tafsir al-Qur’an, Tashih Muhammad Mahdi Nasih wa Muhammad Ja’far Yahqi, Mashhad, Astan Quds Razavi, 1408 Q.
  • Amininejad, Ali wa Digiran, Mabani wa Falsafa Irfan Nazari, Qom, Muassasa Amuzishi wa Pazhuhishi Imam Khomeini, Chap Awwal, 1390 HS.