Jump to content

Bikin Mauludin Annabi

Daga wikishia
Wannan maƙala tana magana ne a kan bikin Maulidin Annabi. Don ƙarin bayani game da Maulidin Annabi, duba Haihuwar Annabi (S.A.W).

Bikin mauludin Annabi (Larabci: الاحتفال بالمولد النبوي) wani taro ne da ake yi duk shekara domin tunawa da ranar da ake haifi Annabin Muslunci (S.A.W), Shi'a da Ahlus-Sunna suna shirya wannan taro na murna da haihuwar Annabi, amma Su kuma Wahabiyawa suna la'akari da wannan maulidi ko biki a matsayin bidi'a, da hujjar cewa irin wannan biki da taro ba a yi shi ba a lokacin Annabi (S.A.W) da sahabbanshi.

Amma malamn Musulmi sun mayarwa da Wahabiyawa martani cewa, duk da wannan biki na mauludi ba a aikata shi ba a lokacin Annabi (S.A.W) da sahabbanshi ba, duk da haka wannan abu ba haramun ba ne a shari'ar Muslunci. Wannan malamai sun dogara da ƙur'ani wajan nuna halaccin yin Mauludin Annabi (S.A.W) da ayoyi da ma'anonin Kur'ani da suka yi umarrni kan girmama Annabi (S.A.W) da son shi.

Kazalika bisa wasu ruwayoyi na tarihi a ƙarni na huɗu hijira da bayanshi suna cewa, Musulmi sun yi bikin Mauludi Annabi (S.A.W), kuma mutanen Makka a ranar haihuwar Annabi (S.A.W) sun kasance suna taruwa a gurin, suna tabarruki da addu'a da sallah, har zuwa lokacin hukumar Alu Sa'ud suka rusa wannan gurin.

Ƴanshi'a suna ganin ranar 17 ga wata Rabi'ul Awwal ita ce ranar da aka haifi Manzon Allah (S.A.W), amma Ahlus-Sunna suna ganin 12 ga wata Rabi'u Awwal ita ce ranar mauludi ranar da aka haifi manzon Allah (S.A.W), a wannan rana ne malaman Shi'a suna yin wasiyya ga mutane kan mustahabbacin ba da sadaka a wannan ranar da yin aiki na gari da farantawa muminai da abubuwa kamar haka, kamar yadda suma Ahlus-Sunna suna yin umarni da ba da sadaka a ranar haihuwar ta Annabi (S.A.W) da ciyar da talakawa domin girmama Annabin Musulinci(S.A.W). saboda haka Musulmi suna gudanar da taron mauludi a duniya, kuma ana la'akarin wannan rana rana ce ta hutu a Iraƙ da Iran da Afganistan da Indiya da Fakistan da Indunusiya da Misra.

Gwamnatin tarayyar ƙasar Najeriya ma ba a barta a baya ba, kusan duk shekara tana bayar da hutu a ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal domin bawa al'ummar musulmi ƴanƙasar damar shagulgulan murnar mauludi.

Muhimmacin Mauludi Da Tarihinshi

Taron Bikin Mauludi A Najeriya 2022M

Tarurrukan da ake yi a ranar haihuwar Annabi (S.A.W) a ko wace shekara ana kiranshi da mauludi, akwai saɓani a tsakanin Shi'a da Ahlus-Sunna, da kuma Wahabiyawa a hannu guda kan shin ya halatta a yi mauludi ko a a? dukkan ƙungiyoyin Musulinci suna hallata yin mauludi, inda suke girmamawa da yin wannan mauludi a ranar haihuwarshi.[1] haka abun da ya ke a wasu ƙasashe kamar Iraƙ, da Iran.[2], Indiya[Akwai buƙatar kawo madogara] da Fakistan da Misra،[3] duk suna yin taron mauludin Annabi (S.A.W) ta hanyar yin abubuwa da suka shafi addini[4] da kuma taruka kazalika suna la'akarin wannan rana a matsayin ranar hutu. Amma Wahabiyawa suna ganin Mauludi a matsayin bidi'a da abin da ya haramta.[5]

A ƙasar Najeriya a duk shekara a ranar zagayowar haihuwa Annabi gwamnatin ƙasar tana ba da hutu, Musulmi suna shirya bukukuwan mauludi musamman ma a jihohin Arewacin ƙasar misalin Kano, Kaduna kai harma da jihohin Kudu kamar Lagos.[6]

Tarihin fara mauludi yana komawa zuwa ƙarni na huɗu da na biyar. Malamin tarihin ƙarni na 9 Ahmad Bin Ali Muƙrizi ya faɗi cewa, mauludin Annabi (S.A.W) ya yaɗu ne a lokacin mulkin Faɗimiyyun daga shekara ta( 297-567H) a Misra.[7] bisa abin da ya zo cikin litattafan tarihi Muzaffarud-din Alkaukabari (Rasuwa: 530H) da shugaba Salahud-dini Ayyubi da shugaban Arbil duk sun yi mauludin Annabi (S.A.W)a watan Rabi'ul Awwal[8]

Shin Bikin Mauludi Bida'a Ne?

Wahabiyawa suna la'akari da yin mauludi Annabi (S,A.W) a matsayin bidi'a kuma haramun ne.[9] Abdul-Aziz Bin Baz ɗaya daga cikin malaman Wahabiyawa yana ganin cewa yin mauludin Annabin Musulinci bidi'a ne.[10] Kamar yadda malaman Salafiyya suke haramta yin taruka ko halartasu a yayin bukokuwan mauludi, da zama a gurin irin wannan tarukan shima haramun ne,[11] kamar yadda wasu marubuta na Wahabiyya suke jingina fasiƙanci da rashin addini da abin da ya yi kama da haka ga mutanen da suke shirya mauludin Annabi (S.A.W).[12] Dalilin Wahabiyawa kan bidi'antar da mauludi, shi ne cewa ba yi ba a zamanin Annabi (S.A.W) ko lokacin sahabbai.[13]

Amsar Malaman Ƴanshi'a Da Ahlus-Sunna

Duk da babu daga shari'a da ya zo kan mauludin Annabi (S.A.W), sai dai cewa akwai ayoyi da yawa da suke ƙarfafa yin mauludi.[14] Haƙika malamai sun yi amfani da gamagarin ma'anonin ayoyin Alƙur'ani a dunƙuƙule, kamar larurar son Annabi (S.A.W)[15] da larurar girmama shi.[16] kan halasci da shar'anci yin mauludin mai girma.[17] Bisa abin da malamin Shi'a Jafar Subhani ya ce, shi yin mauludi wani abu ne da musulmi suke bayyana da nuna so da ƙaunar Manzon (S.A.W). shi wannan so ƙur'ani ya yi nuni kan kansa.[Akwai buƙatar kawo madogara]

mauludi wanda Musulmi da Kiristoci suka yi a Jihar Kaduna Arewacin Najeriya

Bisa dogaro kan ayoyin ƙarshe a cikin suratul Ma'ida waɗanda suke dalili ne da ya nuna cewa Annabi Isa (A.S) ya yi mauludi a ranar da ma'ida (Kaɓaki) ta sauka gare shi da mutanenshi Alhawariyyi daga sama, kuma har yanzu Kiristoci suna yin bikin tinawa da wannan rana, Saboda haka ana ɗauka wajibi ne a yi bikin haihuwar Annabi na Musulunci (S.A.W), saboda shi ne wanda ya ceci duniya daga jahilci da bautar gumaka, kuma wannan ni'ima tafi kaɓakin da aka saukarwa mutanen Annabi Isa (A.S).[Akwai buƙatar kawo madogara]

Yusuf Alƙardawi ɗaya daga cikin malaman Ahlus-Sunna ya kafa hujja kan yin maulidin Annabi (S.A.W) da halaccinshi, inda ya yi imani cewa yin mauludin Annabi (S.A.W) da tinawa da abubuwa da suka faro na Musulinci kamar tini ne kan ni'imar Allah da ya yiwa Musulmi, wannan tinatarwar ba bidi'a ce kuma ba haramun ba, wannan al'amari ne da yake mustahabbi[18] malamin Ahlus-Sunna Ɗahir Alƙadiri yana cewa, babu wata matsala wajan aikata wani abu na halas wanda shari'a ba ta hana ba, ya ƙara da cewa wannan abu ya zama al'ada ga mutane, kuma shi yin Mauludi hadafinshi shi ne, nuna rabauta da dacewa da Akayi sakamakon haihuwar Annabin Musulinci (S.A.W).[19]

Kamar yadda wata ruwaya ta zo cikin littafin Iƙbalul A'amal tana cewa yin azumi a ranar haihuwar Annabi (S.A.W) yana da ladan da ya kai azumin shekara ɗaya[20] Kamar yadda malaman Shi'a suka tafi kan cewa mustahabbi ne yin sadaka da ziyarar gurare masu tsarki da yin aikin alheri da farantawa muminai a ranar da aka haifi Annabi (S.A.W)[21] kuma a litattafan Shi'a an rawaito yin wata sallah ta masamman a ranar da aka haifi annabi (S.A.W)[22] kamar yadda malaman Ahlus-Sunna suna yiwa mutane wasiyya da yin huɗuba da lacca kan Annabi (S.A.W) da kuma karanta ƙur'ani da tausayawa mutane da ba da kyauta da ciyar da mutane.[23]

Lokacin Da Gurin Da Aka Haifi Annabi (S.A.W)

Akwai saɓani kan tarihin da aka haifi Annabi[24] Amma abin da ya shahara gun malaman shi'a shi ne an haifi manzon Allah (S.A.W) a 17 ga wata Rabi'ul Awwal, amma a gurin Ahlus-Sunna abin da ya fi shahara shi ne an haifi Manzon Allah (S.A.W) a 12 ga wata Rabi'u Awwal,[25] saboda haka ne ƴanshi'a suka sanya tazarar da take tsakanin wannan tarihi guda biyu ta zama satin haɗin kai a tsakanin Shi'a da Ahlus-Sunna.[26]

An haifi Annabi (S.A.W) a wani gida a unguwar Shi'ibi Abi Ɗalib, a Makka a tsakanin dutsen Abil Ƙaisi da dutsen Alkandama.[27] Bisa maganar wani malami na Shafi'iyya Muhammad ɗan Umar Barraƙ wanda ya rasu a shekara ta 930H, ya ce mutanen Makka sun taru a gurin da aka haifi Annabi (S.A.W) a daren da aka haife shi, suka dinga ambaton Allah da yin Sallah da sami shi albarka.[28]

Kamar yadda Allama Majlisi malamin Hadisi a ƙarni na goma sha ɗaya ya naƙalto cewa gurin da aka haifi manzon Allah, wuri ne da mutane suke zuwa ziyara tun yana raye har zuwa zamanin hukumar Alu Sa'ud a Hijaz[29] amma sakamakon aƙidar Wahabiyawa ta hana neman albarka daga duk wani abu na Annabawa da guraren da aka binne su da inda aka binne mutanen kirki, sai aka rushe gurin.[30]

Bayanin kula

  1. كيف تحتفل الدول العربية بالمولد النبوي الشريف؟، Kamfanin labarai Iqna.
  2. Time.ir.
  3. Public Holidays in Pakistan 2018..
  4. عيد المولد النبوي الشريف..
  5. Duwish, Fatawi Allujna Da'ima, juzu'i. 3, shafi. 299.
  6. https://hausa.legit.ng/news/1671883-gwamnatin-tarayya-za-ta-ba-yan-najeriya-hutu-a-watan-satumbar-2025-ji-dalili.
  7. Maƙrizi, Al-Mawa'iz wal-I'tibar bi Zikr al-Khiɗaɗ wal-Asar, Juzu'i na 2, Shafi na 436.
  8. Maƙrizi, Al-Mawa'iz wal-I'tibar bi Zikr al-Khiɗaɗ wal-Asar, Juzu'i na 2, Shafi na 436.
  9. Duwish, Fatawi Allujna Da'ima, juzu'i. 3, shafi. 299.
  10. [1] .
  11. Shahata, Al-Mawlid an-Nabawi... Hal Nahtafil?, Shafi na 116
  12. Dabiri, Al-Ihtifal bi Milad ar-Rasulullah salla Allahu alaihi wa alihi wa sallam, Shafi na 9.
  13. «رأي الإمام ابن تيمية بالاحتفال بالمولد النبوي.
  14. Karimi,«Al-Ihtifal wal-Farah bi Milad ar-Rasul al-Karim salla Allahu alaihi wa sallam min Manzur al-Kitab was-Sunna, » Shafuka na 127-132 .
  15. Suratut Tauba: 23
  16. Suratul A'araf: 157
  17. Karimi, Muhammad Mahdi, «Al-Ihtifal wal-Farah bi Milad ar-Rasul al-Karim salla Allahu alaihi wa sallam min Manzur al-Kitab was-Sunna,» Shafi na 126.
  18. Yusuf Alƙardawi, الاحتفال بمولد النبي والمناسبات الإسلامية.
  19. Ƙadiri, Milad an-Nabi, Shafuka na 15 da 17.
  20. Ibn Ɗawus, Iƙbalul A'amal, Juzu'i na 2, Shafi na 603.
  21. Ɗusi, Misbah al-Mutahajjid, Juzu'i na 2, Shafi na 791.
  22. Majlisi, Bihar al-Anwar, Juzu'i na 95, Shafi na 359.
  23. IbnƊawus, Iƙbalul A'amal, Juzu'i na 2, Shafuka na 611-612.
  24. Mas'udi, Murujuz Zahab, Juzu'i na 1, Shafi na 362.
  25. Subhani, Ila al-Abad, Juzu'i na 1, Shafi na 151.
  26. Khomaini, Sahifat al-Imam, Juzu'i na 15, Shafuka na 440 da 455.
  27. Maƙrizi, Imta' al-Asma', Juzu'i na 1, Shafi na 6.
  28. Bahraƙ, Hada'iƙ al-Anwar, Shafi na 150.
  29. Majlisi, Mir'at al-Uƙul, Juzu'i na 5, Shafi na 174.
  30. Amili, As-Sahih min Sirat an-Nabi, Juzu'i na 2, Shafi na 147.

Nassoshi

  • Dabiri, Al-Ihtifal bi Milad ar-Rasulullah salla Allahu alaihi wa alihi wa sallam, Maktabatul Aƙida, 1437H.
  • Mas'udi, Ali Bin Husain, Murujuz Zahab wa Ma'adin al-Juwhar, Bincike: As'ad Dagher, Qom, Dar al-Hijrah, bugu na 2, 1409H.
  • Amili, Jafar Murtaḍa, As-Sahih min Sirat an-Nabi al-A'azam, Cibiyar al-'Ilm wa al-Thaƙafah, Dar al-Hadith, 1426H.
  • Bahraƙ, Muhammad Bin Umar, Hada'iƙ al-Anwar wa Matali' al-Asrar fi Sirat al-Nabi al-Mukhtar, Bincike: Muhammad Ghassaƙ Nasuḥ 'Azqul, Jeddah, Dar al-Minhaj, 1419H.
  • IbnKasir, Isma'il Bin Umar, Al-Bidaya wan-Nihaya, Beirut, Mawallafar Gidan Fikr, 1407H.
  • Ibn Ɗawus, Ali Bin Musa, Iƙbal Bi A'amalil Hassana, Tehran, Gidan Littattafan Musulunci, bugu na 2, 1409H.
  • Karimi, Muhammad Mahdi, «Al-Ihtifal wal-Farah bi Milad ar-Rasul al-Karim salla Allahu alaihi wa sallam min Manzur al-Kitab was-Sunna, » (Bikin murna da farin ciki da haihuwar Manzon Allah Mai Girma (Sallallahu alaihi wa Sallam) bisa fahimtar Alƙur'ani da Sunna) Mujallar Fiƙihun Musulunci, lamba 69, Rabi' 2009M.
  • Khomaini, Ruhullah, Sahifat al-Imam, Tehran, Cibiyar Shirya da Buga Ayyukan Imam Khomaini, 1378Sh.
  • Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya' al-Turath al-'Arabi, bugu na 2, 1403H.
  • Majlisi, Muhammad Baƙir, Mir'at al-Uƙul fi Sharh Akhbar Al al-Rasul, bincike: Sayyid Hashim, Tehran, Gidan Littattafan Musulunci, bugu na 2, 1404ƙ.
  • Maƙrizi, Ahmad Bin Ali, Al-Suluk li Ma'rifat Duwal al-Muluk, Beirut, Dar al-Kutub al-'Ilmiyyah, 1418H.
  • Maƙrizi, Ahmad Bin Ali, Imta' al-Asma' bima li al-Nabi min al-Ahwal wa al-Amwal wa al-Hafadah wa al-Mata, Bincike: Muhammad Abdul-Hamid, Beirut, Dar al-Kutub al-'Ilmiyyah, bugu na 1, 1420H.
  • Maƙrizi, Ahmad Bin Ali, Al-Mawa'iz wal-I'tibar bi Zikr al-Khiɗaɗ wal-Asar, hawashi: Khalil al-Mansur, Beirut, Dar al-Kutub al-'Ilmiyyah, 1419H.
  • Shahata, Muhammad Saqr, "Maulidin Annabi... Hal Nahtafil?", Iskandariyya, Gidan Halifofin Shiryayyu, babu bayanin bugu, babu kwanan wata.
  • Shahata, Muhammad Saƙr, Al-Mawlid al-Nabawi… Hal Nahtafil?, Alexandria, Darul Khulaf'ir Rashidin, bugu ba a sani ba, lokaci ba a sani ba
  • Subhani, Jafar, Ila al-Abad, Qom, Bustan al-Kitab, 1380Sh.
  • Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, Misbah al-Mutahajjid wa Silah al-Muta'abbid, Tehran, Gidan Littattafan Musulunci bugu ba a sani ba, lokaci ba a sani ba.
  • "كيف تحتفل الدول العربية بالمولد النبوي الشريف؟"، (Yaya ƙasashen Larabawa suke yin bikin Maulidin Annabi Mai Tsarki?) Kamfanin dillancin labarai na Iqna.
  • Yusuf Alƙardawi:https://www.al-qaradawi.net/node/3604 yanar gizo na hukuma na Yusuf Al-Qaradawi. Tarihin wallafawa: Talata, 9 Fabrairu 2025M. ziyara: 27 Yuli 2026M.

الاحتفال بمولد النبي والمناسبات الإسلامية, ranar ziyara: 13 Agusta 2026M