Batula

Daga wikishia
(an turo daga Batul)

Batula (arabic: البتول) daya daga cikin lakubban Hazrat Fatima (S) ne, ana mata lakabi da Batula sakamakon fifitar da ta yi kan sauran mata a cikin magana, dabi’a, da Ilimi, hakika shima Imam Ali (A.S) ana masa Lakabi da Mijin Batula sakamakon aurenta da ya yi, Hazrat Maryam (A.S) ita ma ana mata lakabi da Batuka.


Kalmar Batula a Mahangar Lugga

Batala a cikin harshen larabci tana bada ma’anar: cire wani abu daga jikin wani abu, ko kuma dai yanke shi daga jikinsa, sannan Batul ana amfani da Kalmar kan Kamammiyar Budurwa da ta tsare kanta daga Maza ta ki aure, sannan kuma ba ta da wata sha’awa zuwa ga Maza[1] Hazrat Maryam Mahaifiyar Isa (A.S) ita ma ana mata lakabi da Batula saboda ta nesanci Maza,[2] haka kuma ana amfani da Kalmar kan Matar da ta ke yankewa zuwa ga Allah tare da baki dayan zuciyarta.[3]

Annabi Akram (S.A.W) ya ce:

«انما سمیت فاطمه البتول لانها بتلت من الحیض و النفاس؛

Kadai an kira Fatima da Batula saboda ta yanke daga barin yin jinin Haila da Nifasi.

Kandusi cikin littafinsa, Yanabi’ul Al-Muwadda, shekara ta 1416 j 2 sh 322.

Dalilin Sanya Mata Wannan Lakabi

Dalili da illar sanyawa Fatima (S) lakabin Batula, an nakalto maganganun da za su zo a kasa kan bayanin dalilin sanya mata wannan lakabi: Kan asasin adadin wasu riwayoyi, an kira yi Fatima (S) da Batula saboda bata ganin Jinin Al’ada,[4] [Tsokaci 1] Hakika ta banbanta da kuma fifita kan Matan zamaninta daga mahangar aiki, halaye, da saninta da iliminta kuma ta kasance ta yanke zuwa ga Allah.[5] Banbantuwarta daga sauran Mata cikin Kamun kai, Addini, Falala da matsayi.[6]

Auren Batula

Asalin Makala: Auren Batula. Bayan Sarkin Muminai Ali (A.S) ya auri Fatima (S) sai ya zama ana masa lakabi da Mijin Batula, hakika Hazrat bayan ya dawo daga Yakin Naharawan cikin wata huduba da ya yi ya kira kansa da Mijinta Batula.[7]

Bayanin kula

  1. Johri, Al-Sahah, 1410 AH, Juzu'i na 4, shafi na 1630; Al-Ain, Al-Nasher: Dar da Al-Hilal Library, Juzu'i na 8, shafi na 124
  2. Ibn Manzoor, Lasan al-Arab, juzu'i na 11, shafi na 43; Rajeb Esfahani, Al Fardat, 1375, juzu'i na 1, shafi na 240.
  3. Johri, Al-Sahah, 1410 AH, Juzu'i na 4, shafi na 1630; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 25, shafi na 179.
  4. Sheikh Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403 AH, shafi na 64; Tabari Amoli, Dala'il al-Imamah, 1413 AH, shafi na 54; Erbali, Kashf al-Gahma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi.464; Kundozi, Yanabi Al-Moudah, 1416 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 322.
  5. Mazandarani, Bayanin Usul Kafi, 1421 AH, juzu'i na 5, shafi na 228; Tareehi, Majma Al-Baharin, 1375, juzu'i na 5, shafi na 316; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 25, shafi na 179.
  6. Al-Ahmadi al-Mianji, Makatyib Rasul (SAW), mawallafi: Darul Hadith, juzu'i na 2, shafi na 435.
  7. Sheikh Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403H, shafi na 58.

Tsokaci

  1. Wani lokaci ana ɗaukar fasalin da ba na al'ada ba kuma na ban mamaki a matsayin babban darajar. Kamar jawabin da Annabi Isa ya yi a cikin shimfiɗar jariri, wanda ya kasance wani abu da ba a saba da shi ba, Amma da iznin Allah wannan magana da ya yi ta wanke mahaifiyarsa daga tuhumar zina

Nassoshi

  • Ahmadi Mianji, Ali, Makatib Al-Rasoul, Al-Nasher, Dar al-Hadith, Bi Ta, Bi Ja.
  • Alameh Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, bincike na Mohammad Baqer Behboodi, Beirut, Al-Wafa Institute, 1403 AH/1983 AD.
  • Erbali, Ali bin Isa, Kashf al-Gahma, Tabriz, Bani Hashemi, bugu na farko, 1381H.
  • Johari, Al-Sahah, Dar Al-Alam Lal-Mulayin, Beirut, 1410H.
  • Kulaini, Kafi, Dar al-Kutb al-Islamiya, Tehran, 1365.
  • Kundoozi, Yanabi Al-Mowaddeh Lazvi al-Qorabi, bincike: Seyyed Ali Jamal Ashraf Hosseini, Dar al-Aswa na bugawa da bugawa, 1416H.
  • Makarem Shirazi Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyeh, 1374.
  • Mazandarani, Mohammad Saleh, sharh Usulul Al-Kafi, bincike na Mirza Abulhasan Shearani, gyara daga Seyyed Ali Ashour, Beirut, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, 1421 AH/2000 AD.
  • Muhaddith Nouri, Mirza Hossein, Mostadrak Al-Wasail, Qom, Al-Bait Institute, 1408 AH.
  • Qomi, Sheikh Abbas, Bayt Al-Ahzan, wanda Eshtredi ya fassara, Qum.
  • Ragheb Esfahani,Mufradat Alfaz Alkur'an, wanda Seyyed Gholamreza Khosravi Hosseini ya fassara, gidan buga littattafai na Mortazavi, Tehran, 1375.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Dokokin Dokoki, Bincike na Sayyid Mohammad Sadiq Bahrul Uloom, Manuscripts na Al-Maktaba Al-Haydriya, Najaf, 1966/1385.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Ma'ani al-Akhbar, Kum, Jamia Madrasin, 1403H.
  • Tabari Amoli Saghir, Mohammad Bin Jarir, Dala'il al-Imamah, Qom, Dar al-Zhakhar na manema labarai.
  • Tarihi, Fakhreddin, Majma Al-Bahrin, bincike na Sayyid Ahmad Hosseini, Tehran, kantin sayar da littattafai na Mortazavi, bugu na uku, 1375.