Babu Abin da Na Gani Sai Alheri
Babu abin da na gani sai alheri (Larabaci: ما رأيتُ إلّا جميلاً) wannan wata jumla ce da ta shara daga Sayyida Zainab (A.S) bayan waƙi'ar karbala ita wannan jumla raddi ce ga Ubaidullahi Bin Ziyad, wannan ya faru ne a lokacin da aka shigar da fursunonin karbala cikin fada a Kufa, shi wannan abu da ya faru a Karbala ya faru ne da nufin Allah. To a cikin fadar ne Ubaidallahi ɗan Ziyad ya tambayi Sayyida Zainab (A.S) cewa mai za ki ce kan abin da Allah ya hukunta kan ɗan uwanki da iyalanshi? Sai ta ba shi amsa da wanzazziyar wannan jumla ta har aabda, ta kuma ƙara da cewa haƙiƙa Allah ne ya nufi Imam Husaini (A.S) da sahabbanshi da yin shahada, kuma ranar gobe ƙiyama Allah zai tara su domin yi musu hisabu.
Wannan jumla ta Sayyida Zainab ta na nuni ga ƙarfin imani da iklasi da miƙa wuya na Sayyida Zainab (A.S) ga jarrabawar Allah. Amma masu bincike suny i saɓani kan abin da Sayyida Zainab (A.S) take nufi da alheri da kyau, ga wasu daga cikin ma'anoni; kyan aikin Imam Husaini (A.S) da sahabbanshi, kyan gudanarwa ta Allah. Daga jumlar abin da Sayyida Zainab take nufi da wannan jumla akwai kunyata Ibn Ziyad da tabbatar da gaskiyar Imam Husaini (A.S).
Asalin Wannan Jumla A Tarihi
Ana la'akari da wannan jumla «مَا رَأَيْتُ إِلَّا جَمِيلاً» ta Sayyida Zainab (A.S) ɗaya daga cikin nasosshi sanannu kuma wace ta wanzu bayan waƙi'ar Ashura.،[1] Wannan jumla ta zo a cikin tarihi a yayin da birsununin yaƙi suka shiga fadar Ubaidullahi Ibini Ziyad a Kufa, inda Ubaidullahi mai yana halin farin ciki da muranar kashe Imam Husaini (A.S) da sahabbanshi ya tambayi Sayyida Zainab (A.S) cewa ya ya kika ga abin da Allah ya yi da ɗan uwanki da iyalanshi? Sai Sayyida ta bashi amsa da wannan jumla.[2]kuma taƙara da cewa mutane ne da Allah ya rubutawa shahada kuma sun yi shahada kuma da sannu Allah zai taraku domin yin hukunci, to a wannan ranar ka jira ka ga wane ne zai yi nasara, a wannan ranar mahaifiyarka za ta rasa ka (Wannan addu'a ce ta neman Allah ya hallaka shi)[3] ya kai ɗan Marjana, yana jin haka kawai ya yi fusata, ya yi ƙoƙarin kashe Sayyida Zainab (A.S) amma daga ƙarshe sai ya fasa sakamakon maganar ɗaya daga cikin sahabbansa.[4]
Masanin tarihi Muhammad Hadi Yusufi Algarawi yana ganin cewa wannan nassi an same shi ne a ƙarni na bakwai hijirar Annabi (S.A.W) ta hanyar Sayyid Ibn Ɗawus wanda ya yi wafati a shekara ta 664 a cikin littafinshi mai suna Alluhuf Ala Ƙatala Aɗ-ɗufufi.[5] Sai dai kuma cewa wannan jumlar «مَا رَأَيْتُ إِلَّا جَمِيلاً» ta zo ne a cikin littafin Al-Futuhu na Ibn A'asam Alkufi (314 hijira)[6] shi kuma Ali Shiri wanda ya gyara littafin Al-Futuhu ya ce Kalmar "Hamalan" wadda ta zo a cikin wannan nassi ba ta dace da siyaƙin ba, to sai ya canza ta da Kalmar (Jamila)[7][Tsokaci 1]
Bayanan Hikima Na Adabi Game da Jumlar (Babu Abin da Na Gani Sai Kyau)
Suyuɗi (Rasuwa: 911 hijira) malamin tafsiri da hadisi da tarihi kuma masanin harshan Larabci kuma sannanen malamin addini, a cikin littafinshi mai suna Bahjatul Mardiyya Fi Sharhi Alfiya, ya ce idan aka ciro sifa mushabbaha daga wani fi'ili akan sikelin fa'ula, to ita siffa mushabbaha tana zuwa a kan sikeli guda biyu na ɗaya fu'ul da kuma fa'il, kamar Dhukam da Jamil, saboda haka jamil siffa ce mushabbaha, ita siffa mushabbaha[Tsokaci 2] tana kama da fi'ili, abin nufi tana ƙunshe da damiri a cikinta kamar fi'ili.[8] Saboda haka ita wannan jumla«ما رأيت إلا جمالًا», Jamal zai zamo suna ne na masdari, shi kuma suna na masdari babu damiri a cikinshi, amma Kalmar Jamil ta cikin wannan jumla ta Sayyida Zainab (A.S) «ما رأيت إلا جميلا» Sifa ce mushabbaha wacce take ƙunshe da damiri a cikinta, saboda haka ya kamata a yi bayaninta bisa damirin da take ƙunshe da shi, to sai ta zamo kamar haka, (Banga komai ba sai ma'abocin kyau) ita wannan jumla tana bayyana ma'anar wani hadisi da ya zo daga Imam Ali (A.S) wanda yake cewa shi Allah mai kyau ne saboda haka yana son kyau..[9]
Bayyana Halayyar Sayyida Zainab (A.S)
Wannan jumla «ما رأيت إلا جميلا» tana nuni kan ƙarfin imani da iklasi da miƙa wuya na Sayyida Zainab (A.S) ga al'amarin Allah da jarrabawarshi.[10] Wasu kuma sun tafi kan cewa wannan jumla tana nuna wani ɓangare na Irfani a gun Sayyida Zainab.[11] Har ila yai, wasu suna ganin wannan jumla tana nuna wani ɓangare na tauhidi da take shiryarwa zuwa imani da ƙada'u da ƙadar.[12]Ana cewa Sayyida Zainab (A.S) a ranar Ashura ta ga abubuwa guda biyu masu kyau, saboda imaninta mai zurfi a tauhidi, abu na ɗaya shi ne kaɗaitakar ubangiji, abu na biyu kuma shi ne kyau na bauta a gurin Imam Husaini (A.S) to wannan abu yana ƙololuwar matsayin son Allah da yarda da shi.[13]
Abin da Ake Nufi Da Kyau
Wasu sun faɗi cewa wannan jumla ta «ما رأيت إلا جميلا» tana ba da ma'anar ban ga komai ba sai wanda yake da kyau.[14]Amma wasu masu bincike sun ce a zahiri babu wani abu mai kyau a waƙi'ar Ashura, amma Sayyida Zainab (A.S) ta kasance tana nuni ga wata haƙiƙa daban wacce babu ita a zahiri..[15]
Kyawuntar Manufa Da Hadafi
Wasu suna ganin kyau a waƙi'ar Ashura cikin kalaman Sayyida Zainab (A.S) ya kama ta a bincika ne kan hadafin da ya sa aka yi Ashura, wannan hadafi yana bayyana ne wajan shiriyar da ɗan'adam da fitar da shi daga duhu na jahilci, da raya musulunci da Sunnar Annabi (S.A.W) da iyalan gidanshi da bayyana rashin cancantar Banu Umayya da gusar da bidi'a da ɓata da raya gaskiya da kuma kawar da ɓata da yin umarni da kyakykyawa da hani da mummuna.[16]
Kyawun Aiki
An faɗi cewa abin da Sayyida Zainab (A.S) take nufi shi ne kyaun aikin da Imam Husaini (A.S) da sahabbanshi suka yi, da kyaun shahada da kashe mutum a kan hanyar Allah.[17] tabbas Imam Husaini (A.S) da sahabbanshi sun yi nasara kuma sun tsira da hanyar bin umarnin Allah da sauke nauyin da ya hau kansu ta fuska mafi kyau, saboda haka ya zamo babu wani abu da yafi daɗi gare su face sauke nauyin da Allah ya ɗoa musu, babu bambanci wajan sauke wannan nauyi ya zamo yana da sauƙi ko yana da wahala,[18] saboda haka Sayyida Zainab (A.S) take ganin duk abin da ya faru mai kyau ne..[19]
Kyawun Gudanarwa Irin Ta Allah
Wasu suna ganin abin da Sayyida Zainab take nufi da kyau shi ne kyau wajan gudanarwar a gun Allah, ta wannan mahangar ne ta ga kyawun musibar abin da ya gudana a Ashura.[20] wasu masu bincike sun tafi kan cewa faɗar wasu mutane Sayyida Zainab (A.S) tana ganin kyawun duk abin da ya faru a Karbala ba ingantacce magana ba ce, kawai dai suna ganin cewa ta ba da amsa ne kan tambayar da aka yi mata cewa mai ta gani kan abin da Allah ya yi da ɗan uwanta? Saboda haka abin da maganarta take nufi shi ne babu abin da ta gani sai abin da Allah ya yi shi kuma duk abin da Allah ya yi mai kyau ne.[21]
Manufar Wannan Jumla
Wannan jumla ta Sayyida Zainab (A.S) «ما رأيت إلا جميلا» da abin da Sayyida take nufi da ita, ya zama wani abu da masu bincike suke bawa muhimmanci kuma sun ambaci tasiri daban-daban[22] na wannan jumla ga wasu kaɗan daga ciki:
Tona Asirin Ibn Ziyad
Wasu masu bincike suna ganin cewa Ubaidullahi ɗan Ziyad ya ksance yana ƙoƙarin rufe laifinshi a ranar Ashura ta hanyar alaƙanta abin da ya faru da abin da Allah ya hukunta wato ƙaddara, da kawar da ido kan kuskuren da ɗan'adam ya aikata da kuma san ya rufe batun shahadar da Imam Husaini (A.S) da sahabbanshi suka yi amma sai ta bayyana haƙiƙa da maganarta, Sayyida ta mayarwa da Ibn Ziyad raddi da abin da yake tinani da cewa abin da ya faru da Imam Husain (A.S) ya faru ne da izinin Allah,[23]Sai dai kuma Sayyida Zainab (A.S) ta karyata da'awar Ibn Ziyad ta cewa rashin nasarar Imam Husaini (A.S) da da sahabbansa a Karbala ya faru ne da nufin Allah[24] saboda haka Sayyida Zainab (A.S) ta kunyata ɗan Ziyad da wannan magana tata kuma ta bayyanawa mahalarta wannan guri haƙiƙanin gwagwarmaya da abin da Imam Husaini (A.S) ya yi.[25]
Tabbatar Da Gaskiyar Imam Husaini (A.S)
An faɗi cewa duk wata magana da za ta nuna rauni ko baƙin ciki da ya gangaro daga Sayyida Zainab (A.S), tana iya nuna cewa maƙiyin Imam Husain (A.S) shi ne ya yi nasara, amma maganar Sayyida Zainab (A.S) sai ta raunata maƙiyan Imam Husaini (A.S) kuma ta tabbatar da gaskiyar Imam Husaini (A.S),[26] kuma ta hana jirkita haƙiƙanin waƙi'ar Ashura da gwamnatin Umayyawa ta yi niyyar yi, kuma wannan maganar tata ta sa mutane sun ji cewa wajibi ne sai sun ɗauki fansar kashe Imam Husaini (A.S).[27]
Bayanin kula
- ↑ «مَا رَأَيْتُ إِلَّا جَمِيلاً» الجانب الفني للنصِّ»، Al-Atba Al-husainiyya Al-muqaddasa
- ↑ Ibn A'tham al-Kufi, Al-Futuh, juzu’i na 5, shafi na 122; Al-Muqarram, Maqtal al-Husayn, shafi na 431; Ibn Tawus, Al-Luhuf ala Qatla al-Tufuf, shafi na 160
- ↑ Al-Ṭabarī, Tarikh Al-Umama Wal Muluk, juzu’i na 5, shafi na 457. Ibn Kathīr, Al-bidaya Wan Nihaya, juzu’i na 8, shafi na 193; Ibn al-Athīr, Al-kamil Fit Tarikh, juzu’i na 4, shafi na 82. Ibn Aʿtham al-Kūfī, Al-Futūḥ, juzu’i na 5, shafi na 122.
- ↑ Al-Ṭabarī, Tarikh Al-Umama Wal Muluk, juzu’i na 5, shafi na 457. Ibn Kathīr, Al-bidaya Wan Nihaya, juzu’i na 8, shafi na 193
- ↑ «عدم تایید منابع تاریخی در نسبت دادن"ما رایت الا جمیلا" به حضرت زینب(س)»، "Kamfanin Labarai na Shabestan.
- ↑ Ibnu Aʿatham al-Kufī, al-Futūḥ, juzu’i na 5, shafi na 122.
- ↑ Aʿatham al-Kūfī, al-Futūḥ, juzu’i na 5, shafi na 122, hamashin (hamish) 6:
- ↑ al-Bahja al-Mardiyya na al-Suyūṭī, shafi na 306
- ↑ https://qasedoon.blog.ir/1392/11/25/al-Kāfī na al-Kulaynī, juzu’i na 6, shafi na 438ما-رایت-الا-جمیلا-را-درست-معنا-کنیم؛ .
- ↑ Fāṭima Sādāt ʿAlavī-ʿAlī Ābādī ta rubuta game da “ما رأيتُ إلا جميلاً”:
- ↑ Majmu'atu Minal Muallifin“Maʿa al-Rukb al-Ḥusaynī” juzu’i na 5, shafi na 131:
- ↑ Majmu'atu Minal Muallifin“Maʿa al-Rukb al-Ḥusaynī” juzu’i na 5, shafi na 131:
- ↑ «حضرت زینب(س) چگونه به مقام «مارایت الا جمیلا» رسید»، (Kebna News).
- ↑ «ما رأیت الا جمیلا را درست معنا کنیم»، Shafin Qasidun.
- ↑ «چرا حضرت زینب(س) فرمودند ما رایت الا جمیلا؟»، Tibyan؛ «منظور از «ما رأیت الا جمیلا»»، Tushen Bayani na Masu Taimakon Imam Mahdi (A.S..
- ↑ «معنا و تفسیر دقیق جمله حضرت زینب(س) مارایت الا جمیلا چیست؟»، Shahre Jawab.
- ↑ «مَا رَأَیتُ إِلَّا جَمِیلًا؛ جواب دندان شکن «حضرت زینبSamfuri:اختصار/ع به ابن زیاد»، Kamfanin Labarai na Mīzān.
- ↑ «معنای «ما رأیت الا جمیلاً»، Kamfanin Labarai na Hawzah «سرّ تولد «ما رأیتُ الّا جمیلاً» از دل مصائب کربلا، Kamfanin Labarai na Shabestan
- ↑ «معنای «ما رأیت الا جمیلاً»، Kamfanin Labarai na Hawzah.
- ↑ Ali Alawi آبادي، فاطمة سادات، «مارأیت الا جمیلا»؛ «شرح عبارت "ما رأیت الا جمیلا" (بخش اول) - سید محمد مهدی میرباقری»، Cibiyar Bincike da Yaɗa Ilimin Ahlul Bayt (A.S)..
- ↑ «معنای صحیح ما رأیت الا جمیلا»،Tushen Bayani na Ƙungiyar Masu Jihadi na Musulunci"
- ↑ مشاهری فرد، «تأملی زیباییشناختی بر ما رأیت الا جمیلا».
- ↑ Hāshimī Nezhād, "Darsi keh Imam Ḥusayn beh Insanha Amukht shafi na 208«معنا و تفسیر دقیق جمله حضرت زینب(س) مارایت الا جمیلا چیست؟»، Shahre Jawab.
- ↑ Hāshimī Nezhād, "Darsi keh Imam Ḥusayn beh Insanha Amukht shafi na 208
- ↑ Hāshimī Nezhād, "Darsi keh Imam Ḥusayn beh Insanha Amukht shafi na 208
- ↑ Alawi Aliabadi, Fatima Sadat, "Mara'aitu Illa -Jamila".
- ↑ Hāshimī Nezhād, "Darsi keh Imam Ḥusayn beh Insanha Amukht shafi na 208
Tsokaci
- ↑ A cikin wasu bugu-bugu da salo daban-daban na littafin "al-Futūḥ" na Ibn Aʿtham al-Kūfī, musamman wacce Suhayl Zakkār ya gyara (juzu’i na 2, shafi na 175), an kawo fitacciyar magana ta Sayyida Zainab bayan yakin Karbala:"ما رأيتُ إلّا جميلاً "Ban ga komai ba sai kyawun (abinda Allah ya tsara)"
- ↑ Kalmar "الصفة المشبهة" tana nufin ṣifa mushabbaha, wato irin siffa da ke nuna ɗabi’a mai ɗorewa ko halayyar da ke cikin mai aikatawa.
Nassoshi
- Ibn Atham al-Kufi, Ahmad, "Kitab al-Futuh", Bincike: Ali Shiri, Beirut, Darul Al-Awtah, juzu'i na 1, 1411 AH/ 1991 Miladiyya.
- Ibn al-Athir, Ali bin Muhammad, "Al-Kamal fi al-Tarheekh", Beirut, Dar Sadir, 1385 AH/1965 miladiyya.
- Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, "Allahuf Ali Qatali Al-Tufuf", Tehran, Jahan Publications, Juzu'i na 1, 1348.
- Ibn Kathir, Ismail Ibn Omar, "Albidaya Wan Nihaya", Beirut, Darul Fakr, 1407H/ 1986 Miladiyya.
- Al-Syuti, Abd al-Rahman bin Abi Bakr, "Al-Bahja Al-Mardiya Ali Alfiyya Ibn Malik", Qom, Ismailian, juzu'i. 19, d.t.
- Al-Tabari, Muhammad Bin Jarir, "'Tarikh Al-Umam Wal-Muluk (Tarikh al-Tabari), Bincike: Muhammad Abu Al-Fazl Ibrahim, Beirut, Dar Al-Tarath Al-Arabi, Mujalladi 2, 1387 Hijira/ 1967 Miladiyya.
- Al-Kulaini, Muhammad bin Yaqoob, “Al-Kafi”, gyara: Ali Akbar Al-Ghafari da Muhammad Al-Akhundi, Tehran, Darul Kutub al-Islamiyya, Juzu’i na 4, 1407H.
- Al-Muqarram, Abd al-Razzaq, "Maqtal al-Hussein", Beirut, Al-Khorsan Press Agency, D.T.
- «حضرت زینب(س) چگونه به مقام «مارایت الا جمیلا» رسید»،Labaran Kabna, ranar bugawa: 09/12/1399, kwanan duba: 04/07/1403.
- «چرا حضرت زینب(س) فرمودند ما رایت الا جمیلا؟»،Tabian, bugawa: 06/06/1396, kwanan duba: 07/04/1403.
- «سرّ تولد «ما رأیتُ الّا جمیلاً» از دل مصائب کربلا, Kamfanin Dillancin Labarai na Hawza, ranar shigowa: 29/06/1397, kwanan wata: 04/07/1403.
- «شرح عبارت "ما رأیت الا جمیلا" (بخش اول) - سید محمد مهدی میرباقری», Cibiyar Bincike da Buga Ilimi ta Ahlul-Baiti , ranar bugawa: 06/14/1396, kwanan duba: 07/04/1403.
- «عدم تایید منابع تاریخی در نسبت دادن"ما رایت الا جمیلا" به حضرت زینب(س)»، Kamfanin dillancin labarai na Shabestan, ranar bugawa: 02/11/1396, kwanan watan: 04/07/1403.
Fāṭima Sādāt ʿAlavī ʿAlī Ābādī, ما رأيتُ إلا جميلاًMujallar Maʿārif al-Ḥusaynī, zagaye na 4, lamba ta 14, shekara ta 1398 Hijira Shamsiyya (2019)
- «ما رأیت الا جمیلا را درست معنا کنیم»،Shafin yanar gizo na Qasidun, ranar bugawa: 25/11/1392, kwanan duba: 04/07/1403.
- «مَا رَأَیتُ إِلَّا جَمِیلًا؛ جواب دندان شکن «حضرت زینبSamfuri:اختصار/ع به ابن زیاد»، Kamfanin dillancin labarai na Mizan, kwanan wata: 05/06/1399, kwanan wata: 04/07/1403.
- «مَا رَأَيْتُ إِلَّا جَمِيلاً» الجانب الفني للنصِّ»، Al-Utbah al-Husseiniyah al-Maqdisa, ranar bugawa: 25/11/2018 miladiyya, kwanan wata: 25/09/2024 م.
- Majmu'atu Minal Muallifin, “Ma’ al-Rukb al-Husaini”, Qum, bugun farko, 1386.
- مشاهري فرد، عطیة، «تأملی زیباییشناختی بر ما رأیت الا جمیلا», Cibiyar Al'adu da Fasaha ta Salis, ranar kallo: 04/07/1403 AH.
- «معنا و تفسیر دقیق جمله حضرت زینب(س) مارایت الا جمیلا چیست؟»،Birnin Juab, ranar bugawa: 23/08/1396, kwanan duba: 04/07/1403.
- «معنای «ما رأیت الا جمیلاً»، Kamfanin Dillancin Labarai na Hawza, ranar shigowa: 30/06/1399, ranar kallo: 04/07/1403.
- «معنای صحیح ما رأیت الا جمیلا», Shafin bayani na Majalisar Jaruman Musulunci, ranar ziyarar: 04/07/1403H.
- «منظور از «ما رأیت الا جمیلا»»،Shafin yanar gizo na mataimakan Imam Mahdi (a.s.), ranar ziyarar: 04/07/1403H.
- Hashminejad, Abdul Karim, "Darsi Keh Hussaini Be Insanha Amukt", Mashhad, Al-Utaba al-Razaviya al-Maqaddasa, 1382.