Ranakun Fatima

Daga wikishia
(an turo daga Ayyamu Fatima)

Ranakun Fatima (Larabci: الأيام الفاطمية) wasu kwanaki ne da `yan Shi’a ke raya su da zaman Makoki sakamakon shahadar Hazrat Fatima (S) bisa la’akari da tarihi da ya tafi kan cewa ta yi shahada 13 ga watan Jimada Awwal sai dai cewa abin da yafi shahara shine tayi shahada ne a 3 ga watan Jimada Sani, daga ranar 11 har zuwa 13 ga watan Jimada Awwal ana kiransu da ranakun Fatimiyya na farko,sannan daga uku ga wata har zuwa biyar ga watan Jimada Sani ana kiransu da Fatimiyya na biyu.

A wasu Kasashen musulmi misalin Iran, Iraki Pakistan da Azerbaijan suna zaman makokin juyayin shahadar ta, haka zalika 3 ga watan Jimada Sani ana bada hutu hukumance a Kasar Iran don samun damar zaman Makoki, sannan wasu ba’ari suna hallara a wuraren zaman makoki, hakika zaman makokin ranaku na watan jimada Sani a Iran tun daga shekarar 1379 hijiri shamsi tafiyar rana wacce rana ce ta uku ga watan Jimada Sani an ayyana ta ranar hutun zaman makokin shahadar Fatima (A.S) hakan ya sa zaman makokin ya samu bunkasa ta musammam.

Wane Ranaku ne ake Kiransu da Ranakun Fatima?

Ranakun Fatimiyya wasu kwanaki ne da `yan Shi’a su ke yin zaman makokin da juyayin shahadar Sayyada Fatima (A.S) [1] abinda ya fi shahara shine 13 ga watan Jimada Awwal da 3 ga watan Jimada Sani cikin dayansu tayi shahada, ana kiran watan farko da ranakun Fatimiyya na farko na biyu kuma da ranakun Fatimiyya na bjyu, ranakun 11 da 12 da 13 ga watan Jimada Awwal sune Fatimiyya ta farko, sannan 2 da 3 da 4 da biyar ga watan Jimada Sani sune ake kira da Fatimiyya ta biyu,[2] na’am wasu suna ganin daga 10 zuwa 20 ga watan Jimada Awwal Matsayin Fatimiya ta farko sannan daga 1 har 10 ga Jimada Sani Fatimiyya ta biyu,[3] bayyanannen ranar Shahadar Hazarat Fatima (S) bai samu ayyanuwa ba a kan wannan batu akwai sabanin Malamai daga littafin Mausu'atul Alkubra an Fatimati Azzahra (S) talifin Isma’il Ansari Zanjani wanda ya yi wafati a shekara 1388 hijiri shamsi ya bayyana cewa akwai ra’ayi kusan 21 kan ayyana ranar shahadarta, a fadin Assayid Muhammad Jawad Shubairi wanda aka Haifa a shekara 1354 hijirar tafiyar rana, ya daga marubutan Tarihin [4] Fatima (A.S) yace tayi shahada a 3 ga watan Jimada Sani wannan itace maganar da tafi shahara a wurin `yan Shi’a, [5] ya kawo wannan Magana ne bisa jingina da wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) [6] wanda aka cirota daga littafin Dala’ilul Imama.[7]

Shirya zaman makoki

Shirya dan karamin shirin Tamsiliya na Banu Hashim a kwanakin Fatimiyya Jamhuriyar muslunci ta Iran a garuruwa daban daban, wannan bukukuwan zaman makoki suna faraway daga ranar hutun uku ga watan Jimada Sani ranar Shahadar hazrat Fatima (A.S) sun samu matukar bunkasa a shekara 1379 hijirar tafiyar rana karkashin shawarar Ayatullahi Wahidul Kurasani da sanya hannun majalisar [8] dokokin kasar Iran an ayyana ranar 3 ga watan Jimada Sani ranar hutu a hukumance don girmama shahadar Fatima (A.S) da samun damar yin zaman makoki, daga 3 ga watan Jimada Sani da munasabar shahadar Hazrat Fatima ta zama ranar zaman makoki a hukumance, [9] an haifi Aayatullahi Shaik Wahidul Kurasani 1300 hijirar tafiyar rana da kuma Ayatullahi Ludfullahi Safi Gulfaigani wanda ya mutu 1400 hijirar tafiyar dukkaninsu daga Maraji’an Taklidi suna shiga cikin ayarin masu ta’aziyya da tattakin har zuwa Hubbaren Sayyada Fatima Ma’asuma kanwar Imam Rida (A.S) domin zuwa yi mata ta’aziya.[10]

Ana shirya zaman ta’aziya da makoki a kasar Pakistan daidai lokacin da yake gudana a wasu ba’arin jahohi da garuruwa a Iran musammam birnin Qom mai tsarkiana shirya wata Tamsiliya da sunan lungunan Banu Hashim domin ganin masu ta’aziya za a nuna wata Makabarta me kama da Baki’a Farkad don nunawamutane da tunatar da su abinda ya faru, haka Gadir Kum da Fadak.[11] Yan shi’ar Iraki kari kan Fatimiyya ta farko da ta biyu suna yin zaman makoki a ranar 8 ga watan Rabi’us Sani, wannan zaman makoki da suke ya dogara da wata riwaya ce da kawo cfwa Fatima ta yi Shahada ne bayan kwanaki 40 da wafatin mahaifinta (S.A.W), [12] «ایام شهادت حضرت فاطمه الزهرا سلام الله علیها در پاکستان‎»،</ref> da Azerbaijan da Tajikistan [13] da kuma Kasar Astiraliya [14] da cibiyar Hambag [15] da ta Astalkam duka suna raya bikin zaman Makokin shahadar Sayyada Fatima (S)[16]

Tarihin zaman makokin Hazrat Fatima (A.S)

Akwai bayanai da suka zo kan zaman makoki da ta’aziyyar Ahlul Baiti (A.S) game da shahadar Hazrat Fatima (S) [17] an nakalto daga Imam Sadiƙ (A.S) yana shirya zaman makokin shahadarta sannan cikin zaman ta’aziyya yana bayanin yanda tayi barin danta Muhsin (A.S) sakamakon dukan ta da wani ya yi,[18] haka zalika Kadi Abdul Jabbar Mu’utazili wanda ya mutu a shekara 415 hijiri kamari ya yi bayani cewa wasu adadi daga `yan Shi’a a yankunan Misra, Damashk, Bagdad Ramla, Akka, Suri, Askalan, Jabalu Basmak suna zaman makokin shahadar Sayyada Fatima (A.S) da danta Muhassin (A.S).[19]

Bayanin kula

  1. Mazaheri, Farhang Saugi Shi'eh, bugu na farko, shafi na 365.
  2. Mazaheri, Farhang Saugi Shi'eh, bugu na farko, shafi na 366
  3. Duba Lotfi, “Ayyamu Fatimiyyeh wa-Manasiku Shakle Yafte An” shafi na 25.
  4. Ansari Zanjani, Al-Mausu'a al-Kubra An Fatima al-Zahra (a.s), Dilil Ma, juzu'i na 15, shafi na 23.
  5. Shabiri, “Shahadat Fatima (AS)”, shafi na 347.
  6. Tabari Imami, Dala'il al-Imamah, 1413H, shafi na 134.
  7. Shabiri, “Shahadat Fatima (AS)”, shafi na 347.
  8. Duba Lotfi, “Ayyamu Fatimiyyah wa-Mansiku Shakle Yafte An” shafi na 25.
  9. >«ماجرای تعطیل‌شدن روز شهادت حضرت زهرا(س)»
  10. «پیاده‌روی و عزاداری دو تن از مراجع تقلید در قم»
  11. «سومین نمایشگاه کوچه‌های بنی‌هاشم در قم برپا شد/ ساخت ماکت بقیع قبل از تخریب»
  12. «الأيّام الفاطمية أو موسم الأحزان الفاطمية: المعنى والدلالة...»،
  13. «مراسم سوگواری شهادت حضرت فاطمه(س) در جمهوری آذربایجان و تاجیکستان»،
  14. «مراسم فاطمیه دوم در استرالیا»،
  15. سوگواری ایام فاطمیه در مرکز اسلامی مرکز اسلامی هامبوگ»،
  16. «برنامه مراسم عزاداری فاطمیه دوم (۲۰۱۸) در شهرهای مهم اروپادر این ایام، مراسم سوگواری برگزار می‌کنند»
  17. Duba Khasibi, al-Hedayah al-Kubra, 1419 AH, shafi na 408.
  18. Khasibi, Al-Hedayah Al-Kubra, 1419 Hijira, shafi na 408.
  19. Qazi Abd al-Jabbar, Tasbiti al-Dala'ily al-Nubuwa, 1427 AH, Mujalladi na 2, shafi na 595.

Nassoshi