Ayar Nafsu Mudma'inna
Kar a yi kuskure da Nafsu Mudma'inna.
Ayar Nafsu Mudma'inna (Larabci: آية النفس المطمئنة) ko kuma ace ayoyin Nafsu Mudma'inna ayoyi ne hudu na karshen Suratul Fajri wanda suke kunshe da siffofin Nafsu Mudma'inna tare da bayanin lada da kuma shiga Aljanna da ka yi tagoma shi da shi ga Ma'abocin wannan Nafsu Malaman Musulmai sun bayyana Nafsu Mudma'inna a matsayin wani Mutum wanda cikin Imani da Allah ya kai ga samun yakini da nutsuwa kuma samsam bai da sha'awar aikata zunubi, daya daga cikin siffofin ta akwai Radiyatun Mardiya, Radiya na nufin yarda da Ladaddakin Allah da ya bata ko kuma yarda da Khada'u da Kadar na Allah (Hukunci da Kaddara) Kan asasin Riwayoyi daban-daban an kirga Imam Ali (A.S) da Imam Husaini (A.S) da `Yan Shi'a matsayin Misdakan Nafsu Mudma'inna
Matani da Tarjama
Aya ta 27-30 daga Suratul Fajari sune Ayoyin Nafsu Mudma’inna
يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ ﴿٢٧﴾ ارْجِعِي إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرْضِيَّةً ﴿٢٨﴾ فَادْخُلِي فِي عِبَادِي ﴿٢٩﴾ وَادْخُلِي جَنَّتِي
Ya ke nafsu Mudma’inna ki koma ya zuwa Ubangijinki kina halin yarda kuma yardadda*sai ki shiga cikin Bayina* kuma ki shiga Aljannata.
(Kur'ani: Fajar: 27-29)
________________________________________
Ta'arifin Nafsu Mudma'inna
Asalin Makala: Nafsu Mudma'inna Nafsu Mudma'inna wani Hali ne da Nafsu take shigarsa wanda cikin wannan hali mutum yake samun nutsuwa kuma baya karkata zuwa ga aikata zunubi[1] Malaman Musulmai sun fitar da wasu Martabobi da Halaye ga Nafsu mafi kaskantarsu shi ne Nafsu Ammara wacce cikin ta mutum yana karkata zuwa ga sha'awar Zunubi, sannan Mafi daukaar Martaba daga Ammara itace Nafsu Lawwama cikinta idan mutum ya aikata wani mummunan aiki sai ya yi nadama ya zargi kansa, sannan mafi daukakar matsayi daga dukkaninsu itace Nafsu Mudma'inna[2]
Tafsiri
Malaman Tafsiri sun bayyana cewa abinda ake nufi da (Nafsu Mudma'inna) da take aya ta 27 a Suratul Fajar shi ne Muminai wanda suka kai ga yakini da nutsuwa kuma babu shakka da kokwanto cikin imaninsu[3]Allama Tabataba'i ya yi Imani da cewa Nafsu Mudma'inna mutum ne wanda ya samu nutsuwa ta hanyar dogara da Allah, ya yarda da dukkanin abinda Allah ya yarda da shi fitintinun rayuwa basa masa tasiri, shi Mutum ne wanda ya samu kamala a cikin ibada kuma baya karkacewa daga barin Madaidaicin tafarki[4] Tafsir Majma'ul Albayan yana ganin Nafsu Mudma'inna nafsu da ta samu nutsuwa daga tarsashin hasken Imani ta kai ga isa ga martabar Imani da yakini tareda gaskata gwaggwaban lada a ranar Lahira kuma,[5] Ɗabarasi cikin Majma'ul Albayan ya bayyana ma'anar Radiya Mardiya cikin wannan jeri: Ma'abocin Nafsu Mudma'inna ya gamsu da ladan da Allah ya bashi kuma ya gamsu da Ayyukansa,[6] Allama Tabataba'I shima ya bayyana cewa ta wannan fuska (Radiya) da (Mardiya) ta siffantu da cewa Nutsuwa da Allah ya samar da yarda Nafsu ga Kada'u da Kadar, saboda haka fitintinnu basa bata amsa rai kuma baya cudanya da aikata zunubai, da wannan dalili ita (Mardiya) Allah yake yarda da ita, saboda mutum yana fusata lokacin da ya fita daga bauta[7] Kan asasin abinda ya zo cikin tafsir Namuneh hakika Kalmar (Radiyatu) tana nuni kan dukkanin alkawurran Allah da suka tabbata ta gamsu da su, hakika wannan mukami (Makamu Rida) da kuma cikakkar sallamawa da mika wuya suna nuni da mukamin da yake cikinta ma'ana hanyar Allah ta fifici komai, (Mardiya) shima yana bada ma'ana da cewa suma Allah ya yarda da su[8] Wasu ba'ari su nce Maganar da aka fuskantar zuwa ga Nafsu Mud'ainna (ki koma zuwa ga Ubangijinki) a Ranar Alkiyama ne, ana son Muminai su shiga Aljanna, daga wadanda suka yi Imani da cewa ana magana ne da ita a lokacin fitar rai[9] akwai Allama Tabataba'i shima ya zabi ra'ayi na biyu 10 haka mahangarsa a kan jumlar[10] (ki shiga cikin Bayina) jumlar tana nuni kan cewa Nafsu Mudma'inna ta kai ga kammalallen Mukamin Bauta , ma'ana wannan mukami mutum zai kasance babu abinda yake so sai abinda Allah yake so[11] a cewar Malamin cikin Kalmar (ki shiga Aljannata) wata girmama ce ta musammam, domin iata kadai ayar Kur'ani da Allah ya danganta Aljanna ga kansa[12]
Tafsirin Riwaya kan Nafsu Mudma'inna
Cikin litattafan tafsiri na riwaya da sauaran Litattafan hadisi anyi bayani misdakan Nafsu Mudma'inna, hakika kan asasin hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S) cikin Tafsir Furat Kufi[13] da Shawaheed At-Tanzil[14] Imam Ali (A.S) shi ne Misdakin ayar, haka ya zo a cikin Biharul_Anwar cewa suratul fajar surar Husaini (A.S)[15] saboda yana da Nafsu Mudma'inna, cikin wannan Hadisi an bayyana Mataimaka matsayin Misdakan Radiyatu[16] Cikin Littafin Alkafi talifin Kulaini an kawo wata riwaya cewa Imam Sadiƙ (A.S) ya fassara ayar Nafsu Mudma'inna kamar haka: (Yake Nafsu wacce da kike da nutsuwa da yakini da Muhammad da Ahlin gidansa (A.S) ki koma zuwa ga Ubangiji alhalin kina Mai yarda da wilayar Ahlil-Baiti zaki yarda da Ladan Allah, saboda haka ki shiga Aljana cikin Zumrar Bayina ma'ana Muhammad da Ahli-baitinsa[17]
Bayanin kula
- ↑ Mesbah Yazdi, Ayineh Farwaz, 2019, shafi na 27.
- ↑ Mesbah Yazdi,Ayineh Farwaz, 2019, shafi 26-27; Motahari, Majmu'eh Asar, 2009, juzu'i na 3, shafi na 595-596.
- ↑ Misali, duba Ɗabarasi, Majmaal Bayan, 1372, juzu’i na 10, shafi na 742; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 26, shafi na 475-477.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 20, shafi na 285.
- ↑ Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 742.
- ↑ Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 742
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 20, shafi na 285.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir al-Nashon, 1374, juzu'i na 26, shafi na 475-477.
- ↑ Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 742.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 20, shafi na 285.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 20, shafi na 285-286.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 20, shafi na 286.
- ↑ Firat Kufi, Tafsir Furat Al-Kufi, 1410H, shafi na 555.
- ↑ Haskani, Shawaheed Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi.429.
- ↑ Qommi, Tafsir Qummi, 1404H, juzu'i na 2, shafi na 422.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 24, shafi na 93.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407H, mujalladi na 3, shafi na 127-128.
Nassoshi
- Haskani, Obaidullah bin Abdullah, Shawaheed Al-Tanzil na Qawam Al-Tafazil, bincike da gyarawa: Mohammad Baqer Mahmoudi, Tehran, Majalisar Rayar da Al'adun Musulunci da ke ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, bugu na farko, 1411H.
- Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qum, Islamic Publications Office, bugu na biyar, 1417H.
- Tabarsi, Tafsir of Majam al-Bayan, Dar al-Marafa [Bio] [Beta]
- Furat Kofi, Forat bin Ibrahim, Tafsir Forat Al-Kofi, bincike da gyara na Mohammad Kazem, Tehran, Cibiyar Buga Ma'aikatar Al'adu da Shiryar Musulunci, bugu na farko, 1410H.
- Qommi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsir Qummi, bincike da gyara Tayyab Musavi Jazayari, Qum, Darul Kitab, bugu na uku, 1404H.
- Kilini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bincike da gyara na Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
- Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jamaeeh shugaban Akhbar Imama al-Athar, Beirut, Darahiya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
- Misbah Yazdi, Mohammad Taqi, Ayineh Farwaz, Javad Mohaddisi ya tattara, Qum, wallafe-wallafen Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini, bugu na 9, 1399.
- Motahari, Morteza, Majmu'eh Asar, Tehran, Sadra Publishing House, 2009.