Jump to content

Addu'a ta Bakwai cikin Assahifatu Assajadiya

Daga wikishia
Addu'a Ta Bakwai Cikin Sahifa Sajjadiyya
Rubutun Sahifah Sajjadiyeh, wanda aka rubuta a cikin rubutun Ahmad Nirizi, wanda aka rubuta a shekara ta 1145 bayan hijira
Rubutun Sahifah Sajjadiyeh, wanda aka rubuta a cikin rubutun Ahmad Nirizi, wanda aka rubuta a shekara ta 1145 bayan hijira
Maudu'iAddu'ar domin neman kawar da matsaloli da damuwa
Ya fito dagaImam Sajjad (A.S)
MarawaiciMutawakkil Bin Haruna
Madogaran Shi'aSahifa Sajjadiyya


Addu'a ta Bakwai, (larabci: الدعاء السابع من الصحيفة السجادية) tana daga addu'ao'in cikin sahifa sajjadiya da aka yi nakalinta daga Imam Sajjad (A.S) addu'a ce da ake yinta lokacin wahala da saukar bala''i da kuma lokacin bakin ciki, domin samun saukakawar tsanani daga hannun Allah da kuma samun sabubban rayuwa ta hanyar rahamar Allah, a cikin wannan addu'ar Imam Sajjad (A.S) ya kasance yana rokon Allah ya warware masa duk wani dabaibayin Rayuwa, haka Imami na hudu cikin wannan addu'a ta bakwai da take littafin Sahifa Sajjadiya ya bayyana cewa dukkanin halittu suna karkashin Iradar Allah, kumma dukkaninsu raunana a gaban Iradar Allah basu da Mataimaki da mai kawo musu dauki, dukkaninsu kaskantattu ne gaban Allah.

Anyi wasiyya da karanta wannan addu'a don kawar da damuwa cikin kebantattun ladubba a cikin karantata bayan sallar Asubahi da kuma tsakanin hudowar rana da faduwarta. Addu'a ta bakwai cikin sharhin Sahifa Sajjadiya misalin littafin Diyar Ashikin, talifin Husaini Ansariyan cikin Harshen Farisanci da kuma Riyadul As-salikin, talifin Sayyid Ali Khan Madani cikin harshen Larabci.

Masallacin Jami'i Korramshahri

Matsayi da Kimarta

Addu'a ta bakwai ta Sahifa Sajjadiya wata addu'a ce da Hazrat Imam Sajjad (A.S) yake karanta ta a lokacin wahala da mutum bai iya jure mata ko kuma lokacin saukar wani bala'i mai tsanani da lokacin bakin ciki da damuwa yana karanta ta ne domin kawar da wadannan abubuwa, cikin wannan addu'a Imami na hudu ya yi bayanin wazifar da take kan mutu a dunkule a lokacin afkowar bala'i,[1] Ayatullahi Ali Khamna'i Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran shima a watan Isfand shekara 1398 wacce tayi daidai da 2019 lokacin yaduwar Annobar cutar korona a Iran da sauran kasashen duniya ya karanta wannan addu'a domin kawar da wannan Annoba[2]

Darasussukan Da Take Koyarwa

Abubuwan da Addu'a ta Bakwai take koyarwa sun kasance kamar haka:

  • Allah shine mai warware duk wani Dabaibayi da duk wani tsanani da wahala
  • Baki dayan Halittu suna da'a ga Iradar Allah.
  • wannan Addu'a tana samar da sabubban rayuwa da tasiri cikin sababin rayuwa ta hanyar Ludufin da Rahamar Allah.
  • gudanar Khada'u da Kadar da kudurar Allah[3]
  • Tabbatuwar Iradar Allah.
  • Allah shina Mafakar baki dayan mutane a lokacin bala'i da tsanani da wahala.
  • Raunin dukkanin halittu a gaban Allah.
  • neman Bude kofofi yayewar musibu daga Ubangiji.
  • neman dandanar dadin Amsa addu'a[4]
  • Addu'a don sauke Wajibai da himmatuwa cikin Mustahabbai
  • gudanar Baki dayan al'amura yana kasancewa kadai da Iradar Allah
  • duk wanda Allah ya kaskantar hakika bashi da mai daukaka shi.[5]

Yanda Ake Karanta Addu'ar

Ya zo a bara'arin wasu rubuce-rubuce cewa akwai wata hanya da ake bi domin Khatamar Addu'a ta Bakwai ta Assahifa Assajjadiya a Ranar Lahadi zuwa kwanaki Talatin, ko wace rana za a karanta ta kafa goma bayan kammala addu'a sai a karanta zikirin Ya Rabbu ya Rabbu Ya Rabbu da numfashi daya har zuwa yankewarsa, sannan ayi Sujjada a gayawa Allah bukata, wasu sunce kafin fara wannan Addu'a ya kamata a yi salati kafa goma haka kuma kafin farawa da bayan gamawa a yi zikrin ya Allahu kafa Arba'in Sannan karanta wannan addu'a tsakanin hudowar rana da faduwarta da kuma bayan sallar Asubahi tareda nesanta Haramun da cika ciki har tsawon kwanaki talatin, haka kuma zama cikin Dahara (Alwala) da zama ana Fuskantar Alkibla da hallaro da zuciya suna daga cikin sharadinta[6]

Sharhi

Cikin sharhin da aka yi kan Sahifa Sajjadiya anyi Sharhin Addu'a ta Bakwai hakika an shrahin Luggarta da take da wahala, Diyar Ashikin[7] Shuhud Shenakt[8] Riyadul As-Salikin[9] da kuma Fi Zilalu Assahifatu Assajadiyatu[10] an yi sharhinta a littafin ta'alikat Ala Sahifa Sajjadiya talifin Faizul Kashani[11] ya yi Karin bayani cikin.

Bayanin kula

  1. Mamdohi, Shuhud Wa Shenakti, 2005, juzu'i na 1, shafi 425.
  2. «دعایی که رهبر انقلاب خواندن آن را در دوران شیوع بیماری توصیه کردند.»
  3. Matani Du'a
  4. Matani Du'a
  5. Ansari, Diyar Asheghen, 1371, juzu'i na 4, shafi 103-224
  6. Akbari Savji, Ab Hayat, 1392, oda 186.
  7. Ansari, Diyar Asheghen, 1371, juzu'i na 4, shafi na 103-224.
  8. Mamdouhi Kermanshahi, Shuhud wa Shenakti , 1385, juzu'i na 1, shafi na 425-435.
  9. Hosseini Madani, Riaz Al-Salkin, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 325-301.
  10. Mughniyeh, Fi Zilali Al-Sahifa al-Sajadiyeh, 1428 AH, shafi na 141-135.
  11. Faiz Kashani, Ta'alikat Ala Al-Sahifa Al-Sajadiyeh, 1407 AH, shafi na 32-33.

Nassoshi

Ayatullahi Al-uzma Khamenei, wanda aka saka a ranar 13 ga Maris, 2018, an duba shi a ranar 12 ga Disamba, 2019.

  • Faiz Kashani, Mohammad Bin Mortaza, Sharhin Ali Sahifa Al-Sajadiyyah, Tehran, Al-Paqeeh da Cibiyar Bincike ta Al-Thaqafiyah, 1407H.
  • Mughniyeh, Mohammad Javad, fi zilali Al-Sahifa al-Sajadiyya, Qum, Dar al-Kitab al-Islami, 1428H.
  • Mamdouhi Kermanshahi, Hasan, Hankali da Ilimi: Fassara da Sharhin Sahifa Sajjadiyeh, tare da gabatarwar Ayatullah Javadi Amoli, Qom, Bostan Kitab, 2005.