Abincin Buɗa Baki

Daga wikishia
(an turo daga Abincin Shan Ruwa)

Abincin buɗa baki, (Larabci: مائدة الإفطار) abinci ne da ake shiryawa wanda ya yi azumi domin buɗa baki, ya zo a cikin hadisin Ahlul-baiti (A.S) cewa ladan ciyar da mai azumi, daidai yake da yin azumi. ciyar da mai azumi wata al'adace ta musulmi wadda suke gudanar ita a ƙasashe daban-daban da kuma, yanayi maban-banta, al'adar ba da abincin buɗa baki ta yaɗu a farko ta hanyar ba da abinci matsakaici ko kaɗan, a wasu lokutan kuma ana raba cikakken abincin buɗa baki a gurare masu tsarki, kamar haramin Imam Ali (A.S) da Imam Rida (A.S).

Falalar Raba Abincin Buɗa Baki

Abincin buɗa baki, shi ne abincin da mai azumi yake shan ruwa da shii, ya zo a hadisi cewa ciyar da mai azumi yana da lada mai yawa.[1] daga jumla akwai hadisan da ya zo daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa, duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da ladan wanda ya yi azumi.[2] kazalaika ya zo a cikin huɗubar Sha'abaniyya cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya ce duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da ladan wanda ya `yanta bawa kuma Allah ya gafarta mishi zunubanshi.[3] ga wani yanki daga huɗubar Sha'abaniyya daga Annabi kan kfalalar ciyar da mai azumi.

Abincin Buɗa Baki

Ciyar da mai azumi al'adace ta musulmi wanda suke aiwatar da ita a ƙasashe da garuruwa daban-daban, su na aiwatar da wannan al'ada a yanayi mabanbanta, Amma a ƙasashan musulmi masu mulki da mutane su na ciyar da mai azumi.[4] a lokacin daular Faɗimiyya daga shekara ta 297 zuwa ta 567 a ƙasar Misira gidan Al'fiɗira ya kasance gurin raba abinci da alewa ga mutane a lokacin shan ruwa.[5]

Wanin yanki daga hudubar sha'abaniyya da Manzon Allah (S.A.W) ya gabatar game da falalar ciyar ba da abincin buda baki ga mai azumi.

يهَا النَّاسُ مَنْ فَطَّرَ مِنْكمْ صَائِماً مُؤْمِناً فِي هَذَا الشَّهْرِ كانَ لَهُ بِذَلِك عِنْدَ اللَّهِ عِتْقُ نَسَمَةٍ ومَغْفِرَةٌ لِمَا مَضَى مِنْ ذُنُوبِهِ. قيل: يا رسول الله، ليس كلنا يقدر على ذلك!! فَقَالَ: اتَّقُوا النَّارَ وَلَوْ بِشِقِّ تَمْرَةٍ اتَّقُوا النَّارَ وَلَوْ بِشَرْبَةٍ مِنْ مَاءٍ.

Tarjama: Ma'ana, ya ku mutane duk wanda ya ciyar da mai azumi muni daga cikinku a wannan watan, to yana da ladan `yanta bawa a gurin Allah, kuma Allah ya yafe mishi zunubanshi da suka gabata, sai akace ya kai Annabin Allah ba kowa bane zai iya hakan a cikinmu, ssi ya ce, ku ji tsoran wuta koda kuwa da gutsiran dabino ne, ku ji tsoran Allah koda da ta hanyar shayar da ruwa ne.[1]

[6]

Amma a lokacin Bawaihiyyin (Mulki: 322-448 hijira) sun kasance su na ba da abincin shan ruwa a dararen watan Ramadan a Bagdaza mutane fiye da dubu suna halarta.[7] Ibn Baɗuɗa ya yi tafiya zuwa Dimashƙ ya ce sarakuna da alƙalai da malamai sun kasance su na kiran mutane da yawa domin shan ruwa da buɗa baki, kai har takai cewa babu wanda yake shan ruwa shi kaɗai adararen watan Ramadana.[8] hakazalika al'adar ba da abincin Buɗa Baki ta yaɗu a Iran a lokacin gwannatin Safawiyya da ƙajariyya.[9] bisa abin da Abdullahi Almustaufi ya ce, a lokacin mulkin ƙajariyya mafi yawancin sanannun mutane su na ba da abincin buɗa baki, wanda ba zai iya ba da abincin buɗa baki ba, to sai ya ba da dabino ga masu azumi a masallaci.[10]

Matsakaicin Abincin buɗa baki

Raba abincin buɗa baki ya yaɗu, inda ake ba da abincin buɗa baki a gurare masu tsarki kamar haramin Imam Ali (A.S)[11] da na Imam Husaini (A.S) a Iraƙ,[12] da kuma haramin Imam Rida (A.S) da na Sayyida Faɗimatul Ma'asuma a Iran,[13] kazalika ana raba abincin shan ruwa a haraim na Makka da masallacin Annabi (S.A.W) a Saudiya.[14] kuma Sayyid Ali Khamna'i shugaban addnini a Jamhuriyyar musulinci ta Iran ya yi umarni da a dawo da yin abincin shan ruwa da kuma raba shi ga masu azumi.[15]

Abincin Da Ya fi Yaɗuwa

Bisa abin da ya zo a hadisi mustahabbi ne mai azumi ya fara buɗa baki da dabino ko kuma ruwa shi ba mai sanyi ba kuma ba mai zafi da yawa ba[16]

Alewowin Zallabiya da Bamiya da ake ci lokacin shan ruwa

Abincin shan ruwa kala-kala ne, misali daga cikin abincin da yafi yaɗuwa akwai, dabino, gishiri, biredi ,nono, tafashashshan ruwa, alawowi masu ɗumi da alawuyin da akayi da gari da sauransu.[17]

Ga wasu alawuyi da suka shahara ana buɗa baki da su a Iran da ƙasashen larabawa, kamar Azilabiyya, Bamiyya, Kinafa, ƙaɗayif da Baƙalawa[18]

Bayanin kula

  1. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 4, shafi na 68-69.
  2. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 4, shafi na 68
  3. Al-Saduq, Uyun Akhbar Al-Rida, juzu'i na 1, shafi na 296.
  4. Al-Yaqubi, Tarikhul Al-Yaqubi, juzu'i na 2, shafi na 291; Ibn al-Tawir, Nuzhat al-Muqaltain fi Akhbar al-Dawlatain, shafi na 211; Al-Qalqashandi, Subh Al-Ashi, juzu'i na 3, shafi na 523.
  5. Al-Qalqashandi, Subh Al-A’shi, juzu’i na 3, shafi na 524-525.
  6. Al-Saduq, Uyun Akhbar Al-Rida, juzu'i na 1, shafi na 296.
  7. Al-Tha'alabi, Yatima Al-Dahr, juzu'i na 3, shafi na 230.
  8. Ibn Battuta,Rehlatu Ibn Battuta, juzu'i na 1, shafi na 120-121.
  9. Afushtay, Naqawat al-Athar, shafi na 565-566.
  10. Al-Mustafi, Sharh Zindgani Min, juzu'i na 1, shafi na 330.
  11. في ضيافة مرقد الامام علي (ع) طيلة شهر رمضان المبارك.. شاهد موائد الافطار في صحن فاطمة (ع)، موقع العتبة الحسينية المقدسة.
  12. مائدة مضيف الامام الحسين (ع) تمتد الى منطقة ما بين الحرمين لإفطار (5000) صائم (يوميا) حتى انتهاء شهر رمضان المبارك، موقع العتبة الحسينية المقدسة.
  13. «افطاری ساده، فرصتی برای همدلی یک شهر»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  14. «پهن کردن سفره‌های افطار در مسجدالحرام و مسجد النبی+ فیلم»، باشگاه خبرنگاران جوان.
  15. «افطاری ساده ۱۳۹۳»، دفتر حفظ و نشر آثار حضرت آیت‌الله العظمی خامنه‌ای.
  16. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 4, shafi na 152-153; Abu Dawud, Sunan Abi Dawud, juzu'i na 2, shafi na 764.
  17. فوائد الافطار على التمر والماء في شهر رمضان، كلية التمريض ـ جامعة المثنى.
  18. . Hadi Al-Touma, Karbala Fiz Zakira, shafi na 255; Abdul Wahab, Ramadan, shafi na 65-73.

Nassoshi