wikishia:Featured Article
Imaman shia goma shabiyu ne dukkan su daga Ahlubaitin Anabi ,wato dukkan su daga iyalan gidan manzo suke.Bisa wasu ruwayuyi sune Halifofin manzan Allah bayan bashi to sune shiwagabanin al-umar musilmi.Imam Ali shi ne imami na farko,sauran kuma ƴaƴan shi ne da kuma jikokin shi. shi da Faɗima yar manzan Allah(SAW) Bisa Imani a gun ƴan shia imamai Allah ne ya nada su,suna kuma da siffofi na masamman kamar Isma abun nufi basayin saɓo,suna da sifa ta fifiko a kan sauran mutane,suna kuma da ilimin Gaibu dakuma haƙƙin ceto ranar Alƙiyama,Suna da muƙamai irin na manzan Allah ban da saukar wahayi da kawo saban sharia. Ƴan sunna basu yarda da imamancin imaman ƴan shia ba,amma suna nuna musu so kuma sun san su malaman addini ne sun kuma tabbatar da cewa suna da ilimi. A al-ƙurani baa anbaci sunan imaman shia ba,amma sunayan su yazo a hadisin manzan Allah tsira da amunci sutabbata a gare shi da iyalin gidan shi,kamar a hadisin da jabir ya rawaito da hadisin kalifofin manzon Allah goma sha biyu ne da wasu daga cikin hadisai.To bisa wanna hadisan kalifofin manzo Allah su goma sha biyu ne kuma dukan su daga Ƙureshi kuma daga cikin iyalin manzon Allah. Kara karanta...