Yaumul Fasli

Daga wikishia

Yaumul Fasli (Larabci:يوم‌ الفَصل) Ranar yanke hukunci ɗaya ce daga cikin sunayen ranar kiyama da aka ambata a cikin Alkur’ani mai girma. Malaman tafsiri sun ce an ambaci sunansa da wannan sunan ne domin a raba gaskiya da karya a ranar kiyama.

Ma'ana

Ya zo a cikin littafin Al-Mufradat fi Ghareeb Al-ƙur’an cewa ranar Fasal na nufin a bambanta wani abu daga wani abu daban, ta yadda za a samu tazara a tsakaninsu. misalin ayar:

«هذا يَوْمُ الْفَصْلِ الَّذِي كُنْتُمْ بِهِ تُكَذِّبُونَ»

[1]

tarjama: wannan rana ce ta alkiyama ranar bambance karya da gaskiya da kuka kasance kuka karyatawa.[2]

Alkur'ani Mai girma

  • Isdilahin yaumul fasli dangae da ranar alkiyama ya zo a wurare masu yawan gaske cikin zargi da barazana ga mushrikai ko kuma masu karyata sako.

Aya ta 21 a cikin suratu As-Saffat Wannan ita ce ranar sakamako wadda kuka kasance kuna karyatawa.[3] haka nan cikin aya 40 suratul dhukan ta zo ne dangane da barazana. ayar da ta zo bayanta, ta kawo bayanin bambanceewa kamar haka, ranar bambancewa wata rana ce masoyi ba zai iya taimakawa masoyinsa komai kankantar taimakon, babu wanda zai samu taimako daga kowacce irin fuska sai wanda rahamar Allah ta same shi lallai shi Allah mabuwayi ne mai jin kai.[4]

  • Cikin suratu Mursalat karo uku aka ambaci wannan siffa game da ranar alkiyama a aya 12-14 cikin bayanin girmamar wannan rana ya zo kamar haka: “Don me aka jinkirtata domin ranar sakamako, kuma menene ranar sakamako?[5]

Aya ta 38 a cikin suratu Mursalat azaba tabbata ga masu karyata rananan ta alƙiyama.[6] Aya ta 17 a cikin suratun Naba, Lallai ranar sakamako wani lokaci ne”.[7]

Tafsiri

Allama ɗabataba’i yana ganin cewa abin da ake nufi da ranar sakamako, ita ce ranar alƙiyama. Domin kuwa kamar yadda aya ta 17 a cikin suratu Hajji Allah ya bayyana a wannan ranar: " Lallai a wannan rana ne Allah zai bambance tsakanin halittu.[8] kuma ana kiran ta da ranar rarrabuwa domin ita ce ranar ta rarrabe tsakanin gaskiya da karya, kamar yadda Allah Ta’ala ya faɗa a cikin aya ta 59 a cikin suratu Yasin:

وَ امْتازُوا الْيَوْمَ أَيُّهَا الْمُجْرِمُونَ

Kuma ku bambanta a yau, ya ku masu laifi. wannan daya daga cikin shaida ce kan wannan ma'ana[9] Allama Majlisi cikin Biharul-Al-Anwar cikin bayanin yaumul fasli ya tafi kan cewa rana ce Allah zai bambance mutanen kirki daga mutanen banza ya bawa kowa ladna aikinsa.[10]

Mawallafin Tafsirin Alamsal ya ce ranar sakamako ranar yin hukunci ce, domin a wannan ranar ne Allah Masani da adalci yake yin hukunci tsakanin bayinsa. alhali ɗabi'ar tashin kiyama ita ce rabuwar gaskiya da karya. Don haka ɗaya daga cikin sunayen ranar kiyama a cikin Alkur’ani shi ne ranar sakamako.[11]

Bayanin kula

  1. Suratul Safat, aya ta 21.
  2. Qureshi Bonabi, ƙamus Qur'ani, 1371, juzu'i na 5, shafi na 180.
  3. هذا یوْمُ الْفَصْلِ الَّذی کنْتُمْ بِهِ تُکذِّبُونَ؛ سوره صافات، آیه۲۱
  4. Tabatabai, fassarar Tafsirin al-Mizan, juzu'i na 18, shafi na 224;يَوْمَ لا يُغْنِي مَوْلًى عَنْ مَوْلًى شَيْئاً وَ لا هُمْ يُنْصَرُونَ إِلاَّ مَنْ رَحِمَ اللَّهُ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ.
  5. لِأَيِّ يَوْمٍ أُجِّلَت‏ لِيَوْمِ الْفَصْلِ وَ ما أَدْراكَ ما يَوْمُ الْفَصْلِ
  6. وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِلْمُكَذِّبِينَ هذا يَوْمُ الْفَصْلِ جَمَعْناكُمْ وَ الْأَوَّلِين
  7. إِنَّ یوْمَ الْفَصْلِ کانَ میقاتا: ترجمه: همانا روز فصل روز میقات و وعده‌گاه همگان است.
  8. Tabatabai, Al-Mizan tarjama juzu'i na 20, shafi na 237; إِنَّ اللَّهَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيامَةِ. ترجمه: همانا خداوند بین مردم در روز قیامت فاصله می‌اندازد.o.
  9. Tabatabaei, Tafsir al-Mizan, manshurat Ismailiyan, juzu'i na 17, shafi na 130.
  10. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 24, shafi na 205.
  11. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh juzu'i na 19, shafi na 32.

Nassoshi

  • Qorshi Banabi, Ali Akbar, Kamus Quran, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1371.
  • Tarin ayyukan Jagora Shahid Morteza Motahari, Tehran, Gidan Bugawa na Sadra, 2009.
  • Tabatabai, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1390 AH.
  • Majlisi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, mawallafi: Mu'assasar Al-Wafa, bugu na biyu, 1403 AH, ba a wurinsa ba.
  • Makarem Shirazi, Nasser tare da haɗin gwiwar ƙungiyar marubuta, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kutb al-Islamiya, 1387-1354.