Yaumul Fasli
Yaumul Fasli (Larabci:يوم الفَصل) Ranar rarrabewa da hukunci, ɗaya ce daga cikin sunayen ranar ƙiyama da aka ambata a cikin kur'ani mai girma. Malaman tafsiri sun ce an ambace ta da wannan sunan ne domin a raba gaskiya da ƙarya a ranar alƙiyama.
Ma'ana
Ya zo a cikin littafin Al-Mufradat fi Ghareeb Al-ƙur'an cewa ranar Fasal na nufin a bambanta wani abu daga wani abu daban, ta yadda za a samu tazara a tsakaninsu. misalin ayar:
Tarjama: Wannan rana ce ta rarrabewa tsakanin ƙarya da gaskiya da kuka kasance kuna ƙaryatawa.[2]
A Cikin Alkur'ani Mai girma
- Isdilahin yaumul fasli dangane da ranar alƙiyama ya zo a wurare masu yawan gaske cikin zargi da barazana ga mushrikai ko kuma masu ƙaryata sako.
Aya ta 21 a cikin suratu As-Safat Wannan ita ce ranar rarrabewa wadda kuka kasance kuna ƙaryatawa.[3] Haka nan cikin aya 40 suratul dukhan ta zo ne dangane da barazana. ayar da ta zo bayanta, ta kawo bayanin bambancewa kamar haka, ranar rarrabewa wata rana ce masoyi ba zai iya taimakawa masoyinsa komai ƙanƙantar taimakon, babu wanda zai samu taimako daga ko wace irin fuska sai wanda rahamar Allah ta same shi lallai shi Allah mabuwayi ne mai jin kai.[4]
- Cikin suratu Mursalat karo uku aka ambaci wannan siffa game da ranar alƙiyama a aya 12-14 cikin bayanin girmamar wannan rana ya zo kamar haka: "Don me aka jinkirtata domin ranar rarrabewa, kuma menene ranar rabbewa?"[5]
Aya ta 38 a cikin suratu Mursalat azaba tabbata ga masu ƙaryata rananan ta alƙiyama.[6] Aya ta 17 a cikin suratul Naba'i, Lallai ranar rarrabewa wani lokaci ne ƙayyadadde".[7]
Tafsiri
Allama Ɗabataba'i yana ganin cewa abin da ake nufi da ranar rarrabewa, ita ce ranar alƙiyama. Domin kuwa kamar yadda aya ta 17 a cikin suratu Hajji Allah ya bayyana a wannan ranar: "Lallai a wannan rana ne Allah zai bambance tsakanin halittu".[8] kuma ana kiran ta da ranar rarrabuwa domin ita ce ranar ta rarrabe tsakanin gaskiya da karya, kamar yadda Allah Ta'ala ya faɗa a cikin aya ta 59 a cikin suratu Yasin:
Kuma ku rarrabe a yau, ya ku masu laifi. wannan ɗaya daga cikin shaida ce kan wannan ma'ana[9] Allama Majlisi cikin Biharul Al-Anwar cikin bayanin yaumul fasli ya tafi kan cewa rana ce Allah zai bambance mutanen kirki daga mutanen banza ya bawa kowa ladan aikinsa.[10]
Mawallafin Tafsirin Al-amsal ya ce ranar rarrabewa ranar yin hukunci ce, domin a wannan ranar ne Allah Masani da adalci yake yin hukunci tsakanin bayinsa. alhali ɗabi'ar tashin kiyama ita ce rabuwar gaskiya da ƙarya. Don haka ɗaya daga cikin sunayen ranar ƙiyama a cikin kur'ani shi ne ranar sakamako.[11]
Bayanin kula
- ↑ Suratul Safat, aya ta 21.
- ↑ Qureshi Bonabi, ƙamus Qur'ani, 1371, juzu'i na 5, shafi na 180.
- ↑ Wannan shi ne ranar rarrabuwa (ko hukunci) da kuke musantawa. Suratul-Saffat (Aya ta 21)
- ↑ Tabatabai, fassarar Tafsirin al-Mizan, juzu'i na 18, shafi na 224;Ranar da wani ba zai iya taimakon wani ba ko kadan, kuma ba za su sami taimako ba. Sai wanda Allah ya yi masa rahama. Lallai Shi ne Mai girma, Mai rahama.
- ↑ Don wane rana aka jinkirta? Don ranar rarrabuwa. Kuma menene ya sanar da kai menene ranar rarrabuwa
- ↑ bone da halaka mai girma ya tabbata a ranar nan, ga masu musantawa! Wannan shi ne ranar rarrabuwa, mun tattara ku tare da na farko
- ↑ Lallai, ranar rarrabuwa ita ce ranar haduwa da alkawari ga kowa.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan tarjama juzu'i na 20, shafi na 237; Suratul-Hajj (Aya ta 17) tana nufin: "Lallai Allah zai rarrabe tsakaninsu a ranar kiyama
- ↑ Tabatabaei, Tafsir al-Mizan, manshurat Ismailiyan, juzu'i na 17, shafi na 130.
- ↑ Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 24, shafi na 205.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh juzu'i na 19, shafi na 32.
Nassoshi
- Qorshi Banabi, Ali Akbar, Kamus Quran, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1371.
- Tarin ayyukan Jagora Shahid Morteza Motahari, Tehran, Gidan Bugawa na Sadra, 2009.
- Tabatabai, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1390 AH.
- Majlisi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, mawallafi: Mu'assasar Al-Wafa, bugu na biyu, 1403 AH, ba a wurinsa ba.
- Makarem Shirazi, Nasser tare da haɗin gwiwar ƙungiyar marubuta, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kutb al-Islamiya, 1387-1354.