Suwaid ɗan Amru
| Shahidin Karbala | |
|---|---|
Makwancin shahidan karbala a cikin Haramin Imam Husaini (A.S) | |
| Cikakken Suna | Suwaid ɗan Amru |
| Ƙabari | Haramin Imam Husaini (A.S) |
Suwaid ɗan Amru ɗan Abi Muɗa'a Khas'ami (Larabci:سويد بن عمرو بن أبي مطاع الخثعمي) Shi ne shahidi na ƙarshe a waƙi'ar Karbala, wanda ya yi shahada jim kaɗan bayan Imam Hussain (AS).
Suwaid ɗan Amru ɗan Abi Muɗa'a Khas'ami ya fito daga ƙabilar Khas'am, a cewa Samawi (Rasuwa: 1370 h) cikin littafin Ibsarul Aini haƙika ya kasance mutum mai mutunci da daraja, Mai yawan ibada, jarumi mai ƙwarewa a fagen yaƙi.[1]
Kamar yadda ya zo a cikin ruwayar Muhammad ɗan Jarir Ɗabari (ya rasu a shekara ta 310 bayan hijira) a cikin littafin Tarikh Ɗabari, Suwaid shi ne shahidin Karbala na ƙarshe wanda ya tafi filin,[2] ya yi yaƙi har sai da ya samu rauni, ya faɗi sumamme cikin sauran gawawwakin shahidai. Kowa ya ɗauka an kashe shi, bayan wani lokaci, Suwaid ya ji suna cewa: An kashe Husaini. Sai ya farka ya tashi, ya ɗauki takobinsa, ya yi yaƙi da wannan takobin da yake ɗauke da ita har ya yi shahada, kamar yadda Ɗabari,[3] da Balazri.[4] suka ce Urwa ɗan Baɗɗan Sa'albi da Zaid bin Ruƙad Junabi suka kashe shi. Amma a cikin littafin Tasmiyya Man ƙutila Ma'al Husaini (Wanda aka rubuta a ƙarni na 2), an rubuta cewa Hani ɗan Sabit Hazrami ya Kashe shi.[5] Wakar Fagen yaki da aka danganta ta ga Suwaidu Bin Amru a wace ya rera ta a ranar Ashura:
Tarjama: Ka matsa gaba, Ya Husaini! Domin a yau, za ka hadu da Annabi (S.A.W), da mahaifinka mai alheri da tausayi, Kuma Hassan, mai fuskar kamar wata, wanda ya hadu da masu albarka. Kuma za ka hadu da kawunka gwarzo mai kyawawan halaye, Hamza, Wanda aka sani da sunan "Zakin Allah". Kuma Jafar al-Tayyar, wanda matsayinsa ke kara daraja a Aljanna.[6]
Bayanin kula
- ↑ Samawi, Absar al-Ain, 1384, shafi. 169.
- ↑ Ɗabari,Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1403H, juzu'i na 5, shafi na 446.
- ↑ Ɗabari,Tarikh Al-Umam wa Al-Muluk, 1403H, juzu'i na 5, shafi na 453.
- ↑ Balazri, Ansab al-Ashraf, 1397 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 204.
- ↑ Fazil bin Zubair,Tasmiyya Man Qutila ma'al al-Hussein, 1405H, shafi na 28.
- ↑ Amin, Ayan al-Shi'a, Beta, vol. 7, ku. 325.
Nassoshi
- Amin, Seyyed Mohsen, Ayan-al-Shia, bincike na Hasan Amin, B.T. Belazari, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf (Juzu'i na 3), Bincike: Mohammad Baqer Mahmoudi, Beirut, Dar al-Taraif na jarida, 1977 AD/1397 AH. Samavi, Mohammad, Ibsar al-Ain fi Ansar al-Hussein, Qom, Zamzam Hedayat, 2004. Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarihin Al'ummai da Al-Muluk, Beirut, Cibiyar Al-alami, 1403H. Fazil bin Zubair, sunan wanda ya kashe Hussaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da dana, da dan'uwansa, da iyalansa, da mabiyansa, wanda Sayyid Muhammad Reza Hosseini Jalali ya yi bincike a kansa, a Qom, shekara ta 1405 bayan hijira.