Sujjadar Tilawa

Daga wikishia
wannan wani rubutu ne game da bayanin ra'ayin fikihu, ba zai iya zama ma'auni kan ayyukan addini ba, a duba wasu madoran domin ayyukan addini.

Sujjadar Tilawa, (Larabci: سجدة التلاوة) sujjada ce da ake yinta yayin da aka karanta ko a kaji ayoyin Sujjada daga Alkur’ani na wajibi da na Mustahabbi. [1] a ra’ayin Malaman Fiƙihu aya ta 15 daga suratul Sajada, Aya ta 37 daga suratul Fussilat, aya ta 37 daga SUratul Najamu, aya ta 1 daga suartul Alaƙ, sune ayoyin da idan aka karanta su ko aka ji wajibi a yi sujjada. [2] haka kuma acewar Marubucin littafin Jawahir-Al-Kalam ayoyi 11 cikin Alkur’ani Mustahabbi yin Sujjada idan aka karanta su ko a ka ji karatunsu. [3]waɗannan ayoyi sun kasance daga aya ta 206 Suaratul Ra’adu, aya taɓ 49-50 suratul Nahal, aya ta 109 Suratul Isra, aya ta 58 Suratul Maryam aya ta 18 da aya ta 77 suratul hajji, Aya ta 60 Suratul Furƙan, aya ta 26 suaratul Sad, aya ta 21 suratul Inshiƙaƙ. [4] sannan kan asasin abin da aka danganta shi zuwa gay Shaik Saduƙ yace samun Kalmar sujjada cikin aya yana sanya yin sujjada cikin wannan aya ya zama mustahabbi. [5]

Zikirin cikin tilawar Sujjada

لا اِلهَ اِلَّا اللهُ حَقًّا حَقًّا، لا اِلهَ اِلَّا اللهُ ایماناً وَ تَصْدیقاً، لا اِلهَ اِلَّا اللهُ عُبُودِیةً وَرِقّاً، سَجَدْتُ لَک یا رَبِّ تَعَبَّداً وَرِقّاً، لا مُسْتَنْکفاً وَ لا مُسْتَکبِراً، بَلْ اَنَا عَبْدٌ ذَلیلٌ ضَعیفٌ خائفٌ مُسْتَجیرٌ»

[6]

An yi Magana kan hukunce-hukuncen sujjadar tilawaa litattafan a cikin babukan ɗahara [7] da sallah [8] ba’arinsu sun kasance kamar haka: Sujjadar wajibi ta tilawar Alkur’ani wajabci ne na take babu jinkiri, da wannan dalili ne da zarar an karanta ayar Sujjada ko anji karatunta daga surorin Aza’im wajibi kai tsaye a yi sujjada. [9] Cikin sujjadar tilawa yin alwala, fuskantar Alƙibla da kebantaccen zikiri duka ba sharaɗi bane, amma kuma dole a ɗora Goshi kan wani da sujjada ta inganta ayi a kansa. [10] tare da haka an naƙalto keɓantaccen zikiri da ake yi a sujjadar tilawa. [11] Idan Mai janaba ko Mai haila suka ji karatun Ayar tilawar sujjada wajibi ne su yi sujjada. [12] na’am a fatawar Malam fiƙihu haramun ne Mai Janaba [13] ko Mai haila [14] su karanta surorin Aza’im. Idan wani cikin mantuwa da rafkana ya karanta Surorin Aza’im cikin Sallah idan ya tuna ka isa ayoyin sujjadako kuma yana tsakiyar surar wajibi ya dagatar da karatun wannan sura ya canjata da wata surar daban, amma idan ya isa kan ayar sujjada ko kuma ya kai tsakiyar surar, danganae da ƙaƙa zai kawo sujjada alhalin yana cikin sallah lallai Malamai sun samu saɓani cikin wannan mas’ala. [15] bisa fatawar Imam Khomaini a cikin wannan hali wajibi ya yi sujjada ta hanyar ishara ya kuma wadatu da iya karatun Sura mai Sujjada. [16] haka kuma a ra’ayi Ayatullahi Sistani da Sayyid Musa Shubairi Zanjani, idan bai kawo sujjadar wajibi nta tilawar ayar sujjada ba sallarsa ta inganta duk da cewa ya aikata lefi. [17] a fatawar Malaman fiƙihun Shi’a karanta sura wacce cikinta akwai sujjadar tilawar da gangan yana ɓata sallah. [18]

Bayanin kula

  1. Mu'assaseh Dayiratul Almaref Islami Bar Mazhab Ahlul-Baiti (A.S.), Farhnag Fikh Mutabik Mazhab Ahlul Baiti (A.S.) Madhhab, 1392-1395, juzu'i na 4, shafi na 391.
  2. Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 577.
  3. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 10, shafi na 217.
  4. Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419 AH, Juzu'i na 2, shafi na 577-578.
  5. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 10, shafi na 217.
  6. طباطبایی یزدی، العروة الوثقی، ۱۴۱۹ق، ج۲، ص۵۸۴.
  7. Misali duba: Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, Mujalladi na 1, shafi na 510 da shafi na 603.
  8. Misali duba: Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419H, Mujalladi na 2, shafi na 578.
  9. Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa al-Waghti, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 578.
  10. Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419 AH, Juzu'i na 2, shafi na 582-583.
  11. Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419 AH, Juzu'i na 2, shafi na 582-584.
  12. Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419 AH, Juzu'i na 2, shafi na 582-583.
  13. Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419 AH, Juzu'i na 1, shafi na 510.
  14. Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419 AH, Juzu'i na 1, shafi na 603.
  15. Imam Khumaini, Tauzihul Al-Masail (Mohashi), 1424H, Mujalladi na 1, shafi na 546-545, shafi na 984.
  16. Imam Khumaini, Tauzihul Al-Masail (Mohshi), 1424 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 545, 984 Miladiyya.
  17. Imam Khumaini,Tauzihul Al-Masail (Mohashi), 1424 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 546, Maris 984.
  18. Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wughta, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 580; Imam Khumaini, tauzihul Al-Masail (Mohashi), 1424 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 545, 983 Miladiyya.

Nassoshi

  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tauzihul Masa'il (Mohashi), wanda Sayyid Mohammad Hossein Bani Hashemi Khomeini, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci da ke da alaka da kungiyar malamai ta Kum Seminary Society, 1424 H.
  • Bani Hashemi Khomeini, Sayyid Mohammad Hasan, Tauzihul Al-Masal Maraja'ah, ƙum, Islamic Publishing House, 1378.
  • Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Urwa Al-Wugtha, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1419 AH.
  • Tarikh, Fakhreddin, Majmaul-Bahrain, wanda Sayyid Ahmad Hosseini ya yi bincike a Tehran, kantin sayar da littattafai na Mortazaɓi, 1416 Hijira.
  • Tousi, Muhammad bin Hassan, Tahzib al-Ahkam, Hasan Khorsan Mousaɓi, Tehran, Dar al-Kitab al-Alamiya, ya yi bincike, 1407H.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher Al-Kalam fi Sharh Shree'-e-Islam, wanda Abbas ƙochani ya yi bincike, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1362.
  • Muassaseh Dayiratul Almaref Islami bar mazhab Ahlul Baiti (AS), Farhang fikih Mutabik Mazhab Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ƙum, Cibiyar Nazarin Fikihu ta Musulunci ta Addinin Ahlul-Baiti (AS) ta ce. Bayt (AS), 1392-1395.