Sayyid Muhammad Bn Ali Alhadi (A.S)

Daga wikishia
Makwancin Sayyid Muhammad bin Ali Alhadi (A.S)

Muhammad Bn Ali Alhadi (A.S) (Larabci: محمد بن علي الهادي (ع)) wanda ya mutu shekara ta 252 hijiri Kamari wanda yafi shahara da Sayyid Muhammad da kuma Sab’u Addujaili (Zakin Dujaili) ya kasance `dane ga Imam Hadi (A.S) wasu sun yi zaton bayan Mahaifinsa shine zai kasance Magajinsa a Imamanci, amma sai dai cewa ya mutu tun kafin rasuwar Mahaifinsa, sannan Imam Hassan Askari (A.S) Imamanci ya dawo gareshi, hakika tsatsonsa ya yadu ta hanyar Jikansa Shamsud-Addini Muhammad wanda yafi shahara da Sultanu Bukhari, sannan zuriyar Alu Ba’aju da suke yankunan Irak da Iran daga tsatsonsa suka fito.

Sayyid Muhammad yana matsayi da kima a wurin Irakawa, ta kai ga suna rantsewa da sunansa, hakika Karamarsa ta shahara, sau da yawa Maziyartan Haramin Askariyaini da Samarra suna zuwa Kabarinsa ziyara, ya rasu a shekara 252 hijiri Kamari a wani gari a Kudancin Samarra kuma a nan ne aka binne shi, farkon ginin Hubbarensa yana komawa ne a karni na hudu hijiri Kamari, bayan a daurori daban-daban Malaman addini Maraji’an Taklidi da Sarakuna sun ta sabunta ginin wurin, a daurori daban-daban Adhadud-Addaula Dailami daya daga cikin Sarakunan Alu Babawaihi, Shah Isma’il Safawi daga Sarakunan Safawiyya, Mirzayi Shirazi Marja’in Taklidi a karni na Goma sha hudu da Mirza Husaini Nuri Malamin Hadisi na Shi’a a karni na goma sha hudu sun sabunta ginin Kabarin Sayyid Muhammad Bn Ali Alhadi (A.S) Anyi rubuce-rubuce daban-daban game da shi yawancinsu an yi su kan abinda ya shafi rayuwarsa da karamarsa da aka nakalto daga gare shi, daga jumlarsu akwai littafin da harshen Larabci mai suna (Hayatu wa Karamat Abu Jafar Muhammad Bn Imam Ali Alhadi {A.S}) wanda Muhammad Ali Ardubadi ya wallafa wanda ya rayu a tsakanin 1312-1380 hijiri kamari sannan an tarjama shi zuwa harshen Farisanci da sunan (Sitare Dujaili)

Tarihin Rayuwarsa

Sayyid Muhammad `dan Imam Hadi (A.S) ne [1] ana kiran Mahaifiyarsa da sunan Hadisu ko Salilu [2] an haife shi cikin shekara 228 a garin Soraya kusada Madina [3] a shekarar 233 hijiri shekarar da Mutawakkil ya bada umarni kirawo Imam Ali Hadi (A.S) zuwa garin Samarra shi Sayyid Muhammad ya zauna a Soraya bai biyo shi Samarra ba [4] sannan dangane da a wacce shekara ce ya dawo Samarra wurin Mahaifinsa babu cikakken rahoto a kai, amma wasu sunce a shekarar 252 hijiri kamari ya bar tashi daga Samarra ya nufi Madina [5] lokacin da ya isa garin Balad sakamakon wani ciwo da yake fama da shi sai Allah ya karbi ransa a nan kuma a wane gari aka binne shi [6] ana yima Sayyid Muhammad Alkunya da Abu Jafar da kuma Abu Ali [7] haka kuma ana masa Lakabi da Sayyid Muhammad Ba’aj [8] Sab’u Dujaili da kuma Sab’u Aljazira [9]

Jikokinsa

Kan asasin abinda Shaik Abbas Qummi Marubucin Tarihi a karni na goma sha hudu hijiri Kamari ya nakalto daga Sayyid Hassan Barraki wanda ya mutu a shekara 1322 hijiri Kamari, zuriyar Sayyid Muhammad ta fadada ta hanyar daya daga Jikokinsa da ake kira Shamsud-Addini Muhammad [10] nasabar Shamsud-Addini Muhammad da wasidar mutum hudu ta tuke ga Sayyid Muhammad, sakamakon haihuwarsa a garin Bukhara kuma acan ya girma sai ya zamana ya shahara a can da Mir Sultan Bukhara sannan zuriyarsa ta shahara da sunan Bukhariyun [11] bayan sai ya tafi garin Rum ya zauna a Garin Barosa kuma a can ne a ka binne shi [12] Shaik Abbas Qummi ya nakalto daga Sayyid Hassan Barraki cewa ya tafi kan cewa Sayyid Muhammad Ba’aj yana cikin Jikokin Sayyid Muhammad [13] ance Sharifai Ba’aj da suke zauna a yankunan Misanu da Zikaru da Wasid, Kadisiya, Bagdad da Najaf [14] Khuzistan Iran duka daga tsatson Ali da Ahmad `ya`yan Sayyid Muhammad ne [15]

Matsayi

A cewar Bakir Sharif Karashi, Ma’abocin zurfafa binciken ilmi a Shi’a wanda ya mutu shekara 1433 hijiri Kamari, hakika Aklak da Ladubban Sayyid Muhammad sun banbanta shi da sauran mutane [16] da wannan dalili ne wasu ba’arin `Yan Shi’a suka yi zaton shine zai ja ragamar Imamanci bayan Imam Hadi (A.S) [17] hakika Sayyid Muhammad a koda yaushe zaka same shi tareda da dan’uwansa Imam Hassan Askari (A.S) [18] a cewa Bakir Sharif Karashi Imam Hassan Askari (A.S) ne ya dauki dawainiyar Tarbiyantar da shi da ilimantar da shi [19] kan asasin abin da Shaik Abbas Qummi ya nakalto, hakika Imam Hassan Askari (A.S) Imam Hasan Askari (A.S) ya yaga wuyan rigarsa a lokacin mutuwar Sayyid Muhammad sannan ya bada amsa kan wadanda suka nuna rashin jin dadinsu kan wannan abu da ya yi ishara da yaga wuyan rigar da Hazrat Musa ya yi a kan mutuwar dan’uwansa Haruna. [20] Kan asasin Rahoton Sa’ad Bn Abdullahi Ash’ari da Hassan Bn Musa Naubekti daga Masanan Firkoki kuma Marubuta a karni da 3-4, wasu gungun Jama’a guda biyu daga Yan Shi’a) sun yi inkari mutuwar Sayyid Muhammad bayan Shahadar Imam Hadi (A.S) sun yi Imani da da imamancinsa da kuma cewa shine Magajin Mahaifinsa kuma Shine dai Mahadi da akayi alkawari da ake jiran Bayyanarsa, kuma shine wanda bababnsa ya ayyana a mastayin Imamanci, to sakamakon haramcin yiwa Imami karya kuma babu wani abu daga Bada’u da ya faru ya canja abubuwa [yadasht1] saboda haka a hakika bai mutu ba yana nan kawai Mahaifinsa ya boye shi daga barin mutane, kamar yanda a baya muka bada labarin wasu wurare an dena jin duriyarsa sai bayan wasu shekaru a lokacin Mahaifinsa yana raye [21] sai dai kuma a ranar da Sayyid Muhammad ya mutu Imam Hadi (A.S) yayi sihara ga mutane da suka yi masa Ta’aziya da Imam Hassan Askari (A.S) a matsayin shine wanda zai gaje ji a bayansa, [22] kan asasin wata riwaya ance a wannan lokaci kusan mutane 150 ne daga Banu Hashim Da Kuraishawa suka hallara a wurin [23] A cewar Mirza Husaini Nuri Malamin hadisi a Shi’a wanda ya mutu shekara 1320 hijiri Kamari riwayoyin Karamomin Sayyid Muhammad mutawatirai ne kuma sannannu hatta a wurin Ahlus-sunna, kan wannan asasi ne mutanen kasar Irak suke jin tsoron rantsewa da sunansa, idan aka zargi wani da satar kudi ya yarda ya dawo da kudin ko da bai dauka ba da ya rantse da sunan Sayyid Muhammad don kare kansa [24] a wasu ba’arin Masadir an nakalto wata Karama ta Sayyid Muhammad daga cikin littafan da suka nakalto akwai littafin Hayatu Wa Karamat Abu Jafar Muhammad Bn Imam Ali Alhadi (A.S), wanda Muhammad Ardibadi ya rubuta hakika ya ambaci Karamomi har guda 60 cikin littafin [25]

Harami

Haramin Sayyid Muhammad bayan harin da `yan ta'adda suka kai kansa

A shekara ta 1395 `Yan Ta’addan Da’ish sun kai hari kan Haramin Sayyid Muhammad da yake Baladi kilomita 85 tsakaninsa da Kazimaini kuma kilomita 50 tsakaninsa da Kudancin Samarra, sakamakon wannan hari na ta’addacin wani sashe daga Haramin ya ruguje, a yawancin lokuta masu zuwa ziyara Haramin Kazimaini sukan karasa Haraminsa don ziyara [26] Babu cikakken tarihi kan wacce shekara aka fara gina Haraminsa amma tare da haka akwai rahoto kan gyara da akayi masa a shekarun 1384 wanda yake nuna a fara gina shi ne a Karni na hudu hijiri Kamari da Umarnin Adhudud Addaula Dailami daya daga cikin sarakun Alu buwaihi [27] gini na biyu kuma yana komawa ga karni na goma hijiri Kamari da Umarnin Shah Isma’il Safawi bayan fatahu Bagdad [28] sannan kuma akwai maganar sabunta ginin a shekara 1118, [29] Haka kuma Zainul-Abidin Bn Muhammad Salmazi wanda ya mutu shekara 1266 hijiri Kamari daya daga cikin Almajiran Sayyid muhammad Mahadi Bahrul Ulum a shekara 1208 hijiri Kamari, karkahsin umarnin Amir Husaini Khan Sardar ya gina Dakunan Saukar Maziyarta a cikin Hubbaren Sayyid Muhammad, sannan a shekara ta 1244 Mulla Salihu Karzwini Ha’iri ya rushe [30] tsohon ginin yayi sabo wannan ginin ya dau dogon lokaci har zuwa shekaru shi aka gama [31] haka Mirzayi Shirazi wanda ya rayu shekara 1230-1312 daya daga cikin Maraji’an Taklidi bayan zamansa a Samarra hakama Mirza Muhammad Tahrani Askari wanda ya rayu 1281-1320 hijiri Kamari shima ya sabunta ginin ya kara gina dakuna [32] a cewar Agha Buzurg Tahrani, Mirza Husaini Nuri wanda ya rayu 1254-1320 hijiri kamari shima yana dga cikin wadanda suka sabunta ginin Hubbaren a shekara ta 1317 hijiri Kamari [33] Sayyid Muhammad Tabataba’i `dan gidan Marja’in Taklidi Agha Husaini Qummi ya gina Hubbaren Sayyid Muhamnmad a shekarun 1379-1384 da kudaden da Mahaifinsa yasa aka tara domin sake gina wurin, sannan an kara gine gine da dakunan Taro wanda ya kai girma 150 square meters kari da Hasumiya kan Hubbare, [34] Setad Bazsaji Atbatu Aliyat a shekarar 1392 ya fara sabunta ginin [35] duk da cewa Kungiyar `Yan Ta’addan Da’ish a watan Tir shekara ta 1395 sun kai hari kan Hubbaren Sayyid Muhammad lamarin ya haifar da tabuwar wani bangare daga Hubbaren [36] sai dai cewa ginin ya cigaba har zuwa lokacin Kaka shekara 1398, [37]

Kallo da Ido Daya

Anyi rubuce daban daban kan Sayyid Muhammad [38] wasunsu sun kasance haka:

  • Hayatu Karamat Abu Jafar Muhammad Bn Imam Ali Alhadi (A.S) talifin Muhammad Ali Ardibadi 1312-1380 hijiri kamari, an tarjama shi zuwa harshen Farsianci da sunan (Sitareh Dujaili) ta hannun Ali Akbar MahadiFur.

Littafin yana bangare biyu bangare na farko yana bayanin waye Sayyid Muhammad da kuma bayanin Hubbarensa [39] bangare na biyu ya kebantu da nakalin Karamomi daga gareshi [40] Malam Ardibadi cikin bangar na farko na littafi tareda ishara zuwa maganar Hassan Bn Musa Naubekti a karshen Bahasin Firkar da aka dangantawa Sayyid Muhammad ya kawo batun mutuwarsa a Samarra [41] da Magana kan Shaharar Hubbaren da yake a garin Baladi wanda ya kamanta shi da hasken Rana [42]

  • Risaleh Dar Karamat Sayyid Muhammad Bn Ali Alhadi, Talifin Abudl Gaffar Kashmiri wanda ya mutu shekara 1320 hijiri Kamari wanda a cewar Agha Buzurg Tahrani Masanin Litattafan SHi'a wanda ya mutu a shekara 1389 ya rubuta wannan littafi bisa rokon Mirza Husaini Nuri [43]
  • Risaleh fi Karamat Assayid Muhammad Bn Ali Alhadi, talifin Hashim Muhammad Ali Baldawi wanda ya mutu shekara 1305 hijiri kamari ya rubuta shi cikin nakali daga littafin Alfada'elul Alfakhira talifin Sayyid Kasim Abldawi [44]

Bayanin kula

  1. Mofid, Al-Arshad, 1413 AH, Juzu'i na 2, shafi na 311-312.
  2. Badawi, Sab'u Al-Jazeera, Saba Al-Dajil Center for Propaganda and Guidance, shafi na 2.
  3. Badawi, Sab'u Al-Jazeera, Saba Al-Dajil Center for Propaganda and Guidance, shafi na 2.
  4. Badawi, Sab'u Al-Jazeera, Saba Al-Dajil Center for Propaganda and Guidance, shafi na 2.
  5. Badawi, Sab'u Al-Jazeera, Saba Al-Dajil Center for Propaganda and Guidance, shafi na 5.
  6. Ibn Sufi, Al-Majdi fi Ansab al-Talbiyin, 1422 AH, shafi na 325.
  7. Harzuddin, Muraqad Al-Maarif, 1371, juzu'i na 2, shafi na 262.
  8. Duba: Harzuddin, Muraqad al-Maarif, 1371, juzu'i na 2, shafi.262.
  9. >Badawi, Sab'u Al-Jazeera, Saba Al-Dajil Center for Propaganda and Guidance, shafi na 2
  10. Qomi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 3, shafi na 1893.
  11. Hosseini Madani, Tohfa Al-Azhar, Al-Trath Al-Maktoob, juzu'i na 3, shafi na 461-462.
  12. Hosseini Madani, Tohfa Al-Azhar, Al-Trath Al-Maktoob, juzu'i na 3, shafi na 461-462.
  13. Qomi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 3, shafi na 1893.
  14. Badawi, Sab'u Al-Jazeera, Saba Al-Dajil cibiyar talla da jagora, shafi na 10.
  15. Harzuddin, Muraqad al-Maarif, 1371, juzu'i na 2, shafi na 262 (labarai na 2).
  16. Qurashi, Mausu'atu Sirati Ahlul-Bait Al-Imam Al-Hasan Al-Askari, 1433 AH, juzu'i na 34, shafi na 26.
  17. Qomi, Mentehi al-Amal, 1379, juzu'i na 3, shafi na 1891; Qurashi, Mausu'atu Sirati Ahlul-Bait Al-Imam Al-Hasan Al-Askari, 1433 AH, juzu'i na 34, shafi na 26.
  18. Urdubadi, Hayatu Wa-Karamat Abu Ja’afar Muhammad bn al-Imam Ali al-Hadi (a.s.), shafi na 21.
  19. Qurashi, Mausu'atu Sairati Ahlul-Bait Al-Imam Al-Hasan Al-Askari, 1433 AH, juzu'i na 34, shafi na 26.
  20. Qomi, Safina Al-Behar, 1414 AH, juzu'i na 2, shafi na 410; Amin, A'ayan al-Shia, 1403 AH, juzu'i na 10, shafi na 5.
  21. Ash’ari, Al-Maqalat wa Al-Feraq, 1360, shafi na 101.
  22. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1363, juzu'i na 50, shafi na 246.
  23. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1363, juzu'i na 50, shafi na 245.
  24. Noori, Najm al-Thaqib, 1384 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 272.
  25. Urdubadi, Hayat wa Karamat Abu Ja'afar Muhammad bn al-Imam Ali al-Hadi (a.s.), 1427 AH, shafi na 50 zuwa gaba.
  26. <a class="external text" href="https://qom.haj.ir/%D8%A7%D9%85%D8%A7%DA%A9%D9%86/%D8%A7%D9%85%D8%A7%DA%A9%D9%86-%DA%A9%D8%A7%D8%B8%D9%85%DB%8C%D9%86-%D9%88-%D8%B3%D8%A7%D9%85%D8%B1%D8%A7/%D8%B3%D9%8A%D8%AF-%D9%85%D8%AD%D9%85%D8%AF-%D8%B9">«سید محمد».</a>
  27. Faqih Bahrul Uloom da Khameyar, Ziyaratgahaye Irak, Mujalladi na 1, shafi na 520.
  28. Faqih Bahrul Uloom da Khameyar, Ziyaratgahaye Irak, Mujalladi na 1, shafi na 520-521
  29. Faqih Bahrul Uloom da Khameyar, Ziyaratgahaye Irak, Mujalladi na 1, shafi na 520-521
  30. Badawi, Saba Al-Jazeera, Saba Al-Dajil Center for Propaganda and Guidance, shafi na 8.
  31. Badawi, Saba Al-Jazeera, Saba Al-Dajil Center for Propaganda and Guidance, shafi na 521
  32. Faqih Bahrul Uloom da Khameyar, Ziyaratgahaye Irak, Mujalladi na 1, shafi na 521.
  33. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, Mujalladi na 17, shafi na 289.
  34. Faqih Bahrul Uloom da Khameyar,Ziyaratgahaye Irak, Mujalladi na 1, shafi na 522.
  35. <a class="external text" href="https://atabat.org/fa/news/50">«چند طرح بازسازی حرم امامزاده سیدمحمد آماده بهره‌برداری»</a>
  36. <a class="external text" href="https://al-aalem.com/news/28088">«الصور: إحباط محاولة تفجير مرقد (سيد محمد) في بلد.. و مقتل ثلاثة انتحاريين أمام بوابة دخول الزائرين»</a>
  37. <a class="external text" href="https://atabat.org/fa/news/50">«چند طرح بازسازی حرم امامزاده سیدمحمد آماده بهره‌برداری»</a>
  38. <a class="external text" href="https://www.imamreza.net/old/arb/imamreza.php?print=1912">«السيّد محمّد بن الإمام الهادي عليه‌السّلام»</a>
  39. Urdubadi, Hayatu wa *Karamat Abu Ja'afar Muhammad bin Al-Imam Ali Al-Hadi (AS), 1427H, shafi na 50.
  40. Urdubadi, Hayat wa Karamat Abu Ja'afar Muhammad bn al-Imam Ali al-Hadi (a.s.), 1427 AH, shafi na 50 zuwa gaba.
  41. Nobakhti, Feraq Al-Shia, 1404H, shafi na 94.
  42. Urdubadi, Hayat wa Karamat Abu Ja'afar Muhammad bn al-Imam Ali al-Hadi (a.s.), 1427 AH, shafi na 35.
  43. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, Mujalladi na 17, shafi na 289.
  44. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, Mujalladi na 17, shafi na 289.

Nassoshi

  • Ibn Sufi al-Nasabah, Al-Majdi fi ansab al-Talibeyin, Qom, mazhabar Ayatullah al-Marashi al-Najafi, 1422H.
  • Urdubadi, Muhammad Ali, Hayatu wa Karamat Abu Ja'afar Muhammad bn al-Imam Ali al-Hadi (a.s.), Darul Mahja al-Bayda, 1427H/2006 Miladiyya.
  • Ash'ari Qomi, Saad bin Abdullah, Al-Maqalaat wa al-Farq, Mohammad Javad Mashkoor, Tehran, Cibiyar Nazarin Kimiyya da wallafe-wallafen al'adu, 1360.
  • Imam Hadi (A.S)”, a Mujallar Farhang Ziarat, No. 25-24, Disamba 2013.
  • Amin, Seyyed Mohsen, A'ayan al-Shia, binciken Hossein Amin, Beirut, Dar al-Taraif don bugawa, 1403 AH/1983 AD.
  • Aghabuzur Tehrani, Mohammad Mohsen, Al-Dhari'a zuwa Saneef al-Shi'a, Qum and Tehran, Ismailians and Islamic Library, 1408 AH.
  • Abdulahi Bn Hassan Badawi سبع الجزیره، عراق، مرکز سبع الدجیل للتبلیغ و الارشاد، بی‌تا.
  • Harz al-Din, Muhammad, Muraqad Al-Ma'arif, Marginia Muhammad Hossein Harz al-Din, Saeed bin Jubeir's pamphlets, 1371/1992 AD.
  • Husseini Madani, Zaman bin Shudaqm, Tohfa al-Azhar da Zalal al-Anhar fi Nasab al-Imaam al-Athar, al-Tratah al-Maktob, Bita.
  • «السيّد محمّد بن الإمام الهادي عليه‌السّلام»، شبکه امام رضا، مشاهده: ۸ فروردین ۱۳۹۹ش.
  • «سید محمد»، حج و زیارت قم، مشاهده: ۱۲ تیر ۱۳۹۹ش.
  • «الصور: إحباط محاولة تفجير مرقد (سيد محمد) في بلد.. و مقتل ثلاثة انتحاريين أمام بوابة دخول الزائرين»، العالم الجدید، انتشار ۱۸ تیر ۱۳۹۵ش، مشاهده ۱۷ اسفند ۱۳۹۸ش.
  • *Qureshi, Baqer Sharif, Encyclopaedia of Ahl al-Bayt al-Imam al-Hassan al-Askari, bincike na Mahdi Baqer al-Qarshi, Najaf, Imam al-Hassan Foundation, 1433 AH/2012 AD.
  • *Qami, Abbas, Safina al-Bihar da Madinah al-Hakm da al-Atar tare da harhada nassin al-Wardah Ali Bihar al-Anwar, Qom, Darul-Sawah, 1414H.
  • Qummi, Abbas, Mantehi Amal fi Tawarikh Al-Nabi wa al-Al, Qom, Dilil Ma, 1379.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bincike na Ali Akbar Ghafari, Tehran, Dar al-Kanb al-Islamiya, 1388.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar al-Jamaa Lederer Akhbar al-Imam al-Athar, Tehran, Islamia, 1363.
  • Mofid, Al-Irshad fi Marafah Hajjullah Ali Al-Abad, Qum, Congress of Sheikh Mofid, 1413 AH.
  • Nobakhti, Hassan bin Musa, FerAq Al-Shia, Beirut, Darul-Azwa, 1404H.
  • Nuri, Mirzahosein, Najm al-Thaqib Fi Akhwal Al-Imam al-Ghaib, Qom, Jamkaran Mosque, 1384 AH.