Jump to content

Sayyid Muhammad Ali Ale Hashim

Daga wikishia
Sayyid Muhammad Ali Ale Hashim
Tarihin HaihuwaShekarar1962 kalandar Miladiyya
Wurin HaihuwaTabriz Iran
Tarihin Shahada20 Mayu, 2024 kalandar Miladiyya
AikiLimamin Juma'a a garin Tabriz Iran
Adireshin Mai Lasisihttps://www.ale-hashem.ir


Sayyid Muhammad Ali Ale Hashim (Larabci:السيد محمد علي آل هاشم ) (1341-1403. h. shamsi) ya kasance limamin masallacin juma'a na garin Tabriz kuma wakilin waliyul faƙihi a lardin Azerbaijan ta gabas. Hakan nan ya kasance wakilin al'ummar Azerbaijan ta gabas a daura ta shida a majalisar kwararrun jagoranci, haka nan yana da muƙami a rundunar sojojin jamhuriyar muslunci ta Iran a ɓangaren aƙidu.

A ranar lahadi 30 ga watan Urdibesheshti shekara ta 1403 h. shamsi, wanda ya zo dai-dai da 19 ga watan Mayu 20244 miladiyya tare da shugaban ƙasar Iran Sayyid Ibrahim Ra'isi, da kuma Husaini Amir Abdullahiyan ministan harkokin waje na jamhuriyar muslunci ta Iran sun yi bankwana da wannan duniya sakamakon hatsarin jirgi mai saukar ungulu da suka kasance cikinsa.

Rayuwa

Sayyid Muhammad Ali ale hashim ɗan Sayyid MuhammadTaƙiyyu Ale Hashim yana daga cikin malaman addini a garin banam Tabriz, ya kammala karatun sakandire a Tabriz, ya fara karatun addini a hauzar ilimi ta Tabriz, bayan nan sai ya tafi birnin ƙum domin ci-gaba da karatun addini, ya halarci darasin karijul fiƙihu da Sayyid Ali Khamna'i ke yi har tsawon shekaru 14.[1]

Mukamai na Hukuma da na Siyasa

A ranar goma ga watan Khordar shekara ta 1396 kalandar Farsi, wanda ya zo dai-dai da 31 ga watan Mayu 2017 miladiyya, Ayatullahi Khamna'i ya naɗa Sayyid Muhammad Ale Hashim limanci sallar juma'a a garin Tabriz.[2] Bayan fara wannan aiki sai ya bada umarni cire benaye da masu manyan muƙami suke zama domin bambanta kansu da sauran masallata.[3]

Ale Hashim daga 28 ga watan Tir shekara 1388 h, kalandar Farsi, dai-dai da 19 ga watan Yuli 2009 miladiyya,[4] har zuwa 11 Tir 1396, dai-dai da 2 ga watan Yuli 2017 miladiyya, ya ci-gaba da kasancewa wakilin Waliyul faƙihi a Azerbaijan sharƙi, tare da shugabanci ɓangare na aƙida da siyasa cikin rundunar sojojin jamhuriyar muslunci ta Iran,[5] a wannan daura karo uku yana samun nasarar samun daraja ta ɗaya tsakanin sauran ma'aikatun kula da aƙidu da siyasa a rundunar sojoji.[6]

A wajen bude zaman majalisar kwararrun ta shugabanci karo na shida, an lura da kujera babu kowa akai da aka tanada ga Sayyid Muhammad Ale Al-Hashem.[7]

Ale Hashim a daura ta shida a majalisar kwararrun jagoranci, ya shiga wannan majalisa a matsayin wakilin azerbaijan sharƙi, bayan samu ƙuri'u 843108 an bayyana shi matsayin wanda ya samu mafi yawan ƙuri'a cikin wannan zaɓe da ya gudana a azerbaijan sharƙi.[8] Sauran muƙamai da ya riƙe za su iya kasancewa kamar haka:[9]

  • Shugabancin hukuma kula da sallar juma'a a tabrzi
  • Jami'in akidar Siyasa na Cibiyar Tallafawa Rundunar Sojojin Kasa
  • Shugaban akida da siyasa na sashi na 21 na Rundunar Hamza Azarbaijan
  • Shugaban Sashen Akidun Siyasa na Yanki na Azerbaijan
  • Mataimakin Shugaban tabligi da Hulɗa da Jama'a na Kungiyar akidar Siyasa ta Yanki ta Azerbaijan
  • Magajin Sashen Akidun Siyasa na Rundunar Sojan Ruwa
  • Magajin Sashen Akidun Siyasa na Rundunar Sojojin ƙasa
  • Mataimakin kodinetan kungiyar akidar siyasa ta Sojoji
  • Magajin kungiyar akidar siyasa ta sojoji tare da amincewar babban kwamanda
  • Memba na Azerbaijan a majalisar fayyace maslahar hukuma
  • Shugaban Sashen Akidun Siyasa na Rundunar Sojojin ƙasa.

Rubuce-rubucensa

Ale hashim ya yi wallafe-wallafe na musammam domin sojojin ƙasa, ɗalibai da kuma sauran jama'a[10] daga jumlar ayyukansa za a iya ishara da abin da zai zo a ƙasa kamar haka:

  • Shamimu Akhlaƙ wa tarbiyati islami.[11]
  • Sireh Akhlaƙi wa tarbiyati.[12]
  • Barasi fiƙihi jange rawani.[13]
  • Payame Jume'eh-mujalladi shida da ya ƙunshi huɗubobi da ya yi a sallolin juma'a.[14]
Jana'izar Sayyid Muhammad Ale Hashim a garin Tabriz.[15]

Rasuwa

A ranar lahadi 30 ga watan Urdibeheshti shekara ta 1403 h, shamsi, Jirgin mai saukar ungulu dauke da Sayyid Ibrahim Rai'si da Sayyid Mohammad Ali Al-Hashem, wanda ya je Gabashin Azarbaijan domin kaddamar da wani aikin gini, ya yi hatsari a hanyar dawowa tsakanin Warzaghan da Julfa..[16] kuma ya rasa ransa.[17]

Bayanin kula

  1. «امام جمعه تبریز همچنان ‌آذربایجانی‌ها را غافلگیر می‌کند»، Mashriq News.
  2. "Nadin wakilin mai kula da shari'a a lardin Azarbaijan ta Gabas da Imam Juma na Tabriz", Khamenei dot IR.
  3. «امام جمعه تبریز همچنان ‌آذربایجانی‌ها را غافلگیر می‌کند»،Mashariq News.
  4. "Nadin Hojjat-ul-Islam Seyyed Mohammad Ali Al-Hashem a matsayin shugaban kungiyar akidar siyasa ta sojojin", Khamenei dot IR.
  5. "Nadin Hojjat-ul-Islam Seyyed Mohammad Ali Al-Hashem a matsayin shugaban kungiyar akidar siyasa ta sojojin", Khamenei dot IR.
  6. Biography", shafin yanar gizon Hazrat Ayatullah Sayyid Muhammad Ali Al-Hashem
  7. «صندلی خالی شهیدان رئیسی و آل هاشم در مراسم امروز مجلس خبرگان+ عکس»، Kamfanin labarai na Hauza.
  8. "Ale Hashem" ya karya tarihin masana", Khabaronline.
  9. "Tarihin Rayuwa", gidan yanar gizon Hazrat Ayatullah Sayyid Muhammad Ali Al-Hashem.
  10. "Tarihin Rayuwa", gidan yanar gizon Hazrat Ayatullah Sayyid Muhammad Ali Al-Hashem.
  11. "Tarihin Rayuwa", gidan yanar gizon Hazrat Ayatullah Sayyid Muhammad Ali Al-Hashem.
  12. "Tarihin Rayuwa", gidan yanar gizon Hazrat Ayatullah Sayyid Muhammad Ali Al-Hashem.
  13. "Tarihin Rayuwa", gidan yanar gizon Hazrat Ayatullah Sayyid Muhammad Ali Al-Hashem.
  14. "Kallon rayuwa da aikin ƴan takarar ƙwararrun jagoranci a Gabashin Azerbaijan", gidan yanar gizon IRNA.
  15. «تشییع پیکر مطهر شهید آیت‌الله آل هاشم در تبریز»،Barna News.
  16. «بالگرد حامل رئیس جمهور دچار سانحه شد/با ۲ نفر از سرنشینان بالگرد رئیس‌جمهور ارتباط برقرار شد»، ISNA.
  17. "Tabbatar da Shahadar Hojjat-ul-Islam Al-Hashem", Kamfanin Dillancin Labarai na Ilna.

Nassoshi