Mafarkin gaskiya (Larabci: الرؤيا الصادقة) ko kuma ace mafarki da ya dace da abin da yake a waje shi ne abin da ake kira da suna kashafi da shuhudi wanda yake bada mafarki a lokacin bacci, ana kiransa da sunaye misalin (Ru’uya Hasana) da (Ru’uya Saliha), kan asasin hadisi ƙari kan Annabawa da Imamai, Muminai ma za su iya ganin Ru’uya Sadiƙa, mafarkin gaskiya ɗaya daga cikin busharorin Allah ne ga Muminai a duniya.
Mafarkin gaskiya ya rarrabu zuwa gida uku; 1 mafarki wanda baya buƙatar fassara da tawili, misalin mafarkin Hazrat Ibrahim (A.S) game da yanka ɗansa Isma’il, 2 mafarki wanda wani ɓangare daga cikinsa yake buƙatar fassara wani ɓangarensa kuma baya buƙatar fassara, misalin mafarkin Hazrat Yusuf (A.S) wanda cikinsa ya ga rana da wata, mafarki ne d ayake buƙatar fassara, amma sujjadar da yaga suna masa wannan baya buƙatar fassara fiye da ita kanta sujjadar, 3 mafarkin da yake buƙatuwar da kammalalliyar fassara, misalin mafarkin da Sarkin Misra ya yi a zamanin Hazrat Yusuf (A.S) Cikin Alkur’ani an kawo wasu samfura da misalai game da mafarkin gaskiya daga jumlarsu mafarkin da Annabin Muslunci (S.A.W) ya yi kafin fatahu Makka, wanda ya ƙunshi bayanin cewa Sahabbansa za su shiga garin Makka su yi aikin Hajji, cikin aya ta 27 Suratul Fatahu an yi masa alƙawarin tabbatuwar wannan mafarki nasa, da kuma mafarkin Annabin Muslunci (S.A.W) dangane da tsinanniyar Bishiya da maganarta ta zo a aya ta 60 Suratul Isra’i, wannan mafarki yana daga cikin daga sauran misdaƙan mafarkin gaskiya mafarkin da Annabi (S.A.W) cikinsa ya ga wasu adadin Birrai suna hawa da sauka kan mimbarinsa, an ce fassarar wannan mafarki ya kasance halifancin Banu Umayya bayan Annabi (S.A.W) Tsarkakuwar zuciya da horar da ita suna daga cikin dalilai da sabubba na samun ganin mafarkin gaskiya, sannan kuma cika ciki da aikata zunubi da rashin lafiyar zauƙi suna daga katangu da shinge daga ganin mafarkin gaskiya
Sanin Mafhumi Da Muhimmanci
Ru’uya Sadiƙa (mafarkin gaskiya), suna ne na mafarkin da ya dace da abin da yake a waje. [1] cikin riwaya an kirayi shi Ru’uya Sadiƙa da sunan (Ru’uya Hasana) [2] da (Ru’uya Saliha) [3] Malaman falsafa da Arifai na Musulmai suna ganin Ru’uya Sadiƙa wani nau’i ne na kashafi da shuhudi da yake bayyana da surar mafarki a cikin bacci. [4] Cikin litattafan riwaya na Shi’a [5] da Ahlus-sunna [6] Magana dangane da Ru’uya Sadiƙa ta zo an bayyana shi matsayin busharar Allah ga Muminai, [7] kuma ana ƙidaya shi ɗaya daga sassan Annabta. [8] Haka kuma cikin rubuce-rubucen falsafa da irfani na Musulmai, an yi bahasi kan mafarkin gaskiya kusa da bahasin mukashafa da wahayi an yi munaƙasha kan menene haƙiƙaninsa da illolinsa, [9] Allama Majlisi shima cikin Biharul Al-Anwar ya yi Magana filla-filla kan wannan mas’ala, sannan ya yi suka kan ra’ayin Falasifa dangane da Ru’uya Sadiƙa. [10] Mafarkin gaskiya yana daga ɓoyayyu abubuwa, ko kuma bada labarin abubuwan da za su faru a gaba, Malamai suna ganinsa matsayin dalili kan samuwar ruhu. [11]
Adgasu Ahlam (Yaye-yayen Mafarki)
Digsu a harshen Larabci yana nufin ƙulla daga tarin ƙaya da sarƙaƙiya, 12 idan cikin Alkur’ani cikin surori biyu suratul Yusuf aya ta 44 da suratul Anbiya aya ta 5 an kamanta mafarki mai ban tsoro da yaye-yayen ƙaya da sarƙaƙiya, [12] idan ya zamana cikin ayoyi biyu daga Alkur’ani suratul Yusuf aya ta 44 da suratul Anbiya aya ta biyar an kwatanta mafarki mai ban tsoro da yaye-yayen ƙaya da sarƙaƙiya a cewar Sayyid Muhammad Husaini ɗabaɗaba’i Malamin tafsiri da falsafa, haka ta faru duba da cewa wasu ba’arin Mafarkai suna zuwa da sura daban-daban masu tsoratarwa, kowanne ɗaya daga cikinsu yana da tasa fassara da tawaili mai cin gashin kansa, saboda ɗaiɗaikun ba a bayyane suke ba sun cuɗaya da juna saboda gano fassararsu abu ne mai matuƙar wahala. [13]
Su Wanene Suke Ganin Mafarki Na Gaskiya?
A cewar Muhammad Baƙir Majlisi a cikin Biharul Al-Anwar, sune Annabawa, Imamai da Muminai, a imaninsa bakiɗayan Mafarki Annabawa mafarki ne na gaskiya, wannan mafarki na su a haƙiƙa wani nau’i ne daga wahayi, Majlisi ya tafi kan cewa Imamai suma suna ganin ru’uya sadiƙa duk ba a iya kiran mafarkinsu da wahayi, amma yana cikin hukuncin wahayi, [14] haka kuma cikin naƙalin wasu hadisai daga Annabi (S.A.W) ya zo cewa bayan Annabi bakiɗayan juz’an Annabta sun tafi in banda ru’uya sadiƙa. [15] Majlisi tare da jingina da wasu riwayoyi ya yi imani kan Muminai ma suna ganin mafarkin gaskiya, [16] cikin ba’arin tafsirai na riwaya na Shi’a da Ahlus-sunna ƙarshen ayar
Suna da bushara cikin rayuwar duniya da rayuwar lahira, [17] ya zo cewa abin da ake nufi daga busharar Muminai shi ne dai ru’uya saliha da suke gani a bacci. [18]
Bambancinta Da Wahayi
A imanin Muhiyid-dini Arabi ru’uya sadiƙa ba ta da wani bambanci da wahayi, dukkaninsu suna fitowa ne daga tushe ɗaya kaɗai suna da ɗan bambanci cikin kasancewar wahayi ido buɗe amma shi kuma ru’uya sadiƙa cikin duniyar mafarki a cikin bacci
Lallai ru’uya sadiƙa da wahayi dukkaninsu daga tushe ɗaya suka fito babu bambanci tsakaninsu face ɗaya ido buɗe ɗaya kuma cikin bacci. [19] misalin mafarkin Annabi (S.A.W) game da Hudaibiyya wanda ya ginu kan nuna cewa za su shiga Masallacin Harami tun kafin fatahu Makka, da wannan ru’uya sadiƙa ta kasance yanki daga juz’an Annabta guda 46, kaɗai wanda zai iya karɓar wahayi shi ne wanda yake da ƙarfaffar nafsu da zai samu sadarwa da Alamul Mujarradat, wannan ƙarfin nafsu shi ne ya zama sababin Karamomi da mujizozi da abubuwa da suka shallake tunani. [20]
Ru’uya Sadiƙa A Cikin Alkur’ani
Ance cikin Alkur’ani akwai aƙalla Samfura bakwai daga suke bayani game da ru’uya sadiƙa:
- mafarkin Annabin Muslunci (S.A.W) kafin fatahu Makka, wanda ya ginu kan nuna cewa shi da Sahabbansa za su shiga garin Makka su yi aiki Hajji, a cikin aya ta 27 suratul Fatahu an bada alƙawarin tabbatar wannan mafarki.
- mafarkin Annabin Muslunci (S.A.W) dangane da tsinanniyar bishiya da bayaninta ya zo a aya ta 60 suratul Isra’i, cikin wannan mafarki Annabi (S.A.W) ya ga wasu adadin Birrai suna hawa mimbrinsa suna sauka, an ce fassarar wannan mafarki shi ne mulkin da Banu Umayya suka yi a bayansa.
- mafarkin Hazrat Ibrahim dangane yanka ɗansa Isma’il da aka yi bayaninsa cikin aya ta 102 suratul Sa’fat da kuma ya ta 104-15 cikin wannan sura an tabbatar da gaskiyar wannan mafarki.
- mafarkin Annabi Yusuf (A.S) lokacin da yake yaro ya yi mafarkin Taurari goma sha ɗaya tare da Rana da Wata suna yi masa sujjada, suratul Yusuf aya ta 4, bisa ayoyin Alkur’ani, bayan shuɗewar shekaru lokacin da Yusuf ya zama Azizu Misra sannan ƴan’uwansa goma sha ɗaya tare da mahaifinsa da matarsa suka girmama shi sai wannan mafarki ya tabbata, suratul Yusuf aya ta 100.
- mafarkai guda biyu da abokan zaman Kurkuku tare da shi suka gani, ɗayansu ya yi mafarki yana shirya giyar Inibi, ɗayan kuma ya yi mafarki yana ɗauke da gurasa a kansa tsuntsaye suna cin wannan gurasa, suratul Yusuf aya ta 41. Kan asasin aya ta 41 daga wannan sura an fassara waɗannan mafarkai biyu kamar haka: na farkonsu za sake shi daga Kurkuku kuma zai zama mai shayar da Sarki giya, na biyunsu kuma za a soke shi a saman saƙandami, tsuntsaye za sauka kansa su dinga cin ƙwaƙwalwarsa.
- mafarkin Sarkin Misra wanda cikinsa ya ga ramammun Shanu guda bakwai suna cinye ƙosassun Shanu guda bakwai, da korayen zangarniya guda bakwai, da kuma wasu busassu guda bakwai, suratul Yusuf aya ta 43, kan asasin aya ta 46 da 47 daga wannan sura, Yusuf ya fassara wannan mafarki da cewa za a fuskanci shekaru bakwai masu albarka mamakon ruwan sama akai akai, bayansu kuma wasu shekaru bakwai za su zo cikin fari da rashin ruwan sama. [21]
Rabe-rabe
Tahanawi masanin Isɗilahi a ƙarni na goma sha ɗaya da goma sha biyu h ƙamari, ya rarraba ru’uya sadiƙa (Mafarkin gaskiya) zuwa gida uku:
- mafarki wanda yake ba ya buƙatar fassara da tawili, misalin mafarkin Hazrat Ibrahim (A.S) yana yanka ɗansa Isma’il (A.S).
- mafarki wanda wani ɓangarensa yake buƙatar fassara ɗayan ɓangaren kuma baya buƙata, misalin mafarkin Hazrat Yusuf (A.S) wanda ya ga Rana da Wata da Taurari, wannan ɓanbaren yana buƙatar fassara, amma sujjada da take cikin mafarkin bata da wata fassara da ta wuce sujjada.
- mafarki da yake buƙatar kammlalliyar fassara; misalin mafarkin Sarkin Misra a zamanin Annabi Yusuf (A.S) [22]
Sabbuba da Shingayen Ru’uya Sadiƙa
Cikin litattafan Muslunci an yi Magana dangane da sabubba da shingayen ru’uya sadiƙa, Mulla Sadra, ya bayyana cewa tsaftatar zuciya, barranta daga duniya da horar da nafsu suna daga sabubban ganin ru’uya sadiƙa, [23] Allama ɗabaɗaba’i, Yana ganin kulawar yau da kullum a matsayin dalilin karbar mafarki na gaskiya da tamassuli tare da luɗufi. Sannan aikata zunubi da rashin lafiyar zauƙi da shaye-shaye suna daga shinge da katangu daga samun ru’uya sadiƙa. [24]
Bayanin kula
- ↑ Jam'i az Muhaƙƙiƙani Farhang Ulumi, 1394, shafi na 573; Makarem Shirazi wa digaran, Payam ƙur'an, 1368, juzu'i na 1, shafi na 278.
- ↑ Misali, duba Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu’i na 8, shafi.90-91; Sheikh Sadouƙ, Man La Yahzara Al-Faƙih, 1413 AH, Mujalladi na 1, shafi na 134-133; Ibn Fahad Hilli, Uddatul Al-Da’i, 1407H, shafi na 278.
- ↑ Misali, duba Ibn Abi Jumhur, Awali al-Le'ali, 1405 AH, Mujalladi na 1, shafi na 162; Ibn Fahd Hilli, Uddatul Al-Da’i, 1407H, shafi na 278; Bahrani, Al-Burhan, 1374, shafi na 41.
- ↑ Sajjadi, Farhang Ulum Islami, 1373, juzu'i na 2, shafi na 928.
- ↑ Misali, duba Ibn Shahr Ashub, Manaƙib, 1379, juzu’i na 2, shafi:356; Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Mujalladi na 8, shafi na 90-91; Sheikh Sadouƙ, Man La Yahzara Al-Faƙih, 1413 AH, Mujalladi na 1, shafi na 134-133; Sheikh Sadouƙ, Man La Yahzara al-Faƙih, 1413 AH, Mujalladi na 2, shafi na 584; Ibn Fahd Hali, Kit al-Da'i, 1407H, shafi na 278; Ibn Abi Jumhur, Awali al-Le'ali, 1405 AH, juzu'i na 1, shafi na 162; Ibn Fahd Hali, Kit al-Da’i, 1407H, shafi na 278; Bahrani, Al-Burhan, 1374, juzu'i na 3, shafi na 41.
- ↑ Misali, duba Motaghi Hindi, Kanzal-Amal, 1409 AH, shafi na 362-372.
- ↑ Majlesi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 48, shafi na 192.
- ↑ Duba Ibn Fahad Hilli, Uddatul Al-Da’i, 1407H, shafi na 277; Sheikh Sadouƙ, Man La Yahzara al-Faƙih, 1413 AH, Mujalladi na 2, shafi na 584.
- ↑ Misali, duba Ibn Sina, Al-Mabda wa Al-Ma’ad, 1363, shafi na 117-119; Mulla Sadra, Al-Mabda wa Al-Ma'ad, 1354, shafi na 467-469.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 58, shafi na 195-219.
- ↑ Mohseni, Ruhu Az nazare Akle wa ilmi Ruhi jadid, 1376, shafi na 10.
- ↑ Rajeb Esfahani, Al-Mufardat fi Gharib al-ƙur'an, 2003, juzu'i na 2, shafi na 459
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1374, juzu'i na 11, shafi na 255
- ↑ Duba Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 58, shafi na 210.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 58, shafi na 192.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403H, juzu'i na 58, shafi na 190-192.
- ↑ Suratul Yunus, aya ta 64.
- ↑ Bahrani, Al-Burhan, 1374, juzu'i na 3, shafi.41; Siyuti, Al-Durrul al-Manthor, 1404 AH, juzu'i na 3, shafi na 311.
- ↑ Ibn al-Arabi, Tafsir Ibn Al-Arabi, 1422H, juzu'i na 1, shafi na 229.
- ↑ Ibn al-Arabi, Tafsir Ibn Al-Arabi, 1422H, juzu'i na 1, shafi na 229.
- ↑ Makarem Shirazi wa Digaran, Payam ƙur'an, 1368, juzu'i na 1, shafi na 278-287.
- ↑ Al-Thanavi, Kashaf Isɗilahat Al-Funun wa Ulum, 1996, juzu'i na 1, shafi na 886.
- ↑ Mulla Sadra, Al-Mabda wa Al-Ma'ad, 1354, shafi na 467.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 58, shafi na 209-210.
Nassoshi
- Alƙur'an Kareem
- Ibn Abi Jumhur, Muhammad Bin Zain al-Din, Awali Al-La'ali al-Aziziya fi al-Ahadith al-Diniya, bincike da gyarawa na Mojtaba al-Iraƙi, bugun Dar Seyyed al-Shahada, bugu na farko, 1405H.
- Ibn Sina, Hossein bin Abdullah, Al-Mobda wa Al-Maad, Tehran, Cibiyar Nazarin Musulunci, bugun farko, 1363.
- Ibn Shahr Ashub Mazandarani, Muhammad Bin Ali, Manaƙib Al Abi Talib, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Kum, Allameh, bugu na farko, 1379H.
- Ibn al-Arabi, Muhi al-Din, Tafsir Ibn al-Arabi, bincike da gyara: Sheikh Abd al-Warith Muhammad Ali, Beirut - Darul Kutub Al-Elamiya, 1422H.
- Ibn Fahd Hilli, Ahmad bin Muhammad, Uddatul Al-Da'i wa Najah Al-Sa'i, Ahmad, Mohadi ƙomi, Dar al-Kutub al-Islami, bugun farko, 1407H.
- Bahrani, Sayyedhashim bin Suleiman, Al-Burhan fi Tafsir al-ƙur'an, ƙom, Ba'ath Institute, bugun farko, 1374.
- Tahanwi, Mohammad Ali bin Mohammad, Keshaf isɗilahat Al-Funun wa Uloom, Beirut, Publishers, bugun farko, 1996.
- jam'i az Muhaƙƙiƙan, Farhang Nameh ƙur'an, ƙum, ofishin yada farfagandar Musulunci, Cibiyar Bincike na Kimiyya da Al'adun Musulunci, bugu na farko, 1394.
- Ragheb Esfahani, Al-Mufardat fi Gharib al-ƙur'an, wanda Gholamreza Khosravi Hosseini ya fassara, Tehran, Mortazavi Publishing House, Ch3, 1383.
- Sajjadi, Jafar, Farhang Maarif Islami, Tehran, Komesh, 1373.
- Siyuti, Jalal al-Din, Al-Durrul Al-Manthur a cikin Tafsir al-Mathur, ƙum, Laburare Ayatullah Murashi Najafi, 1404H.
- Sheikh Sadouƙ, Muhammad Bin Ali, Man Laihdara al-Faƙih, bincike da gyarawa daga Ali Akbar Ghafari, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci mai alaka da al'ummar makarantar hauza ta Kum, bugu na biyu, 1413 AH.
- Tabatabaei Mohammad Hossein, Tafsir al-Mizan, Mohammad Bagher Mousavi Hamdani ya fassara, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na kungiyar malamai ta ƙum Seminary Society, Ch5, 1374.
- Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, Al-Kafi, Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, suka yi bita, 1407H.