Riyada

Daga wikishia

Riyada (Larabci: رياضة النفس) ko Horar da Nafsu yana nufin jurewa wahala ta hanyar kin biyewa abinda rai yake so da watsi da Sha’awe sha’awe, da kuma zage dantse da yin Ibada domin samun damar tsarkake Ruhi wanda cikin ba’arin litattafan Irfani aka kiraye shi da Jihadul Akbar, hakika Muslunci ya yi wasicci da yin haka, Raye Dare da Ibada, `karantar Magana, `Karanta cin abinci da kuma kebance kai da Halwa duka suna daga rukunan horar da Nafsu. Yafiya,Jarumta, Kishi, Kankan da kai a gaban gaskiya, ana kidaya su daga Natijojin Horar da Nafsu, Muslunci ya hana amfani da wasu hanyoyi cikin Horar da Nafsu, misalin Rahbaniyanci. Mulla Sadra yana ganin Farawa da Riyada kafin samun Ma’arifa da kammalallen aiki zuwa ga Ibada ta shari’a ba komai bane bace face bata.

Sanin Mafhumi

Riyada ko Horar da Nafsu ma’anarsa shi ne jurewa wahala cikin barin Sha’awa da kuma zage dantse da yin Ibada domin tsarkakar Ruhi [1] cikin ayoyin Alkur’ani Mai girma da riwayoyin Ma’asumai anyi Wasicci da riko da shi [2] Magana kan Riyada ta zo cikin Litattafan Irfani tare da Mabanbantan Ma’anoni [3] daga cikinsu akwai Horar da Nafsu domin tsarkake Magana da aiki da niyya domin Allah [4] haka kuma ana kiran Riyada da Jihadul Akbar, sannan Raya dare da ibada, rage yawan Magana da kebance kai da Halwa suna daga cikin Rukunan Riyada [5]

Kufaifayi da Natijoji

Kawar da Rowa,Hassada, Girman kai, da kwadayin duniya suna daga Natijojin Riyada [6] haka kuma samun kaiwa ga kyawawan Siffofi misalin Kyauta, Jarumta, Kishi, Kaskantar da kai a gaban gaskiya da kuma Tawali’u suma suna cikin Kufaifayin da Natijojin Riyada [7] Wasu ba’arin ayoyin Alkur’ani Mai girma ana ganin suna ishara ne zuwa ga Riyada [8] daga cikinsu akwai aya ta 40-41 suratul Annazi’at kan asasin wadannan ayoyi duk wanda ya ji tsoran Mukamin Ubangiji ya kuma kwabi Nafsu daga barin soye-soyen rai lallai Aljanna ce Masukinsa [9] an nakalto daga Imam Ali (A.S) cewa duk wanda ya lazimci horar da Nafsu zai samu Riba [10] Wurare da aka yin Riyada Shari’a ta hana Yin Riyada ta hanyar amfani da tsari da uslubin da ya sabawa shari’a [11] daga cikinsu akwai Rahbaniyyanci da ma’anar watsi da Duniya baki dayanta [12] an hana yin hakan [13] Mulla Sadra yace: Farawa da Riyada Gabanin Sanin Shari’a da Ma’arifa da kamallallen aiki na Ibada ta shari’a baya bakin komai sai batar da mutum [14] kuma kan wannan asasi ne ya yi Imani da cewa zuwa lokacin da ibadar shari’a ta karanta to babu maganar yin Riyada, hada Ibada ta hikima da Riyada ta suluki [15]

Bayanin kula

  1. Farhang Bozor Sokhon, 1390, juzu'i na 4, shafi 3767.
  2. Majmu'eh Nawisadigani, Farhang Fiqh, 2009, juzu'i na 4, shafi na 213.
  3. Misali, duba: Khatami, Aine Makarem, 1368, juzu’i na 1, shafi na 140; Goharin, Sharh Isdlahat Tasawwuf, 1380, juzu'i na 6, shafi 142-143.
  4. Al-Qasani, Sharh Manazel al-Saerin, 2005, shafi na 218.
  5. Mousavi Tabrizi, Mukaddime bar Irfani Amali, 2007, shafi na 247.
  6. Majmu'eh Nawisadigani, Farhang Fiqh, 2009, juzu'i na 4, shafi na 213.
  7. Majmu'eh Nawisadigani, Farhang Fiqh, 2009, juzu'i na 4, shafi na 213.
  8. NasirulDin Tusi, Ausaful Al-Ashraf, 1369, shafi na 35.
  9. Suratul Nazaat, aya ta 40 da ta 41; A bisa fassarar Makarem Shirazi.
  10. Man estadama riyaizatah nafse intfea (Amadi, Gharar al-Hakm, 1410 AH, shafi na 608, H. 660).
  11. Golpayegani, Ershad Al-Sa'il, 1413 AH, shafi na 197.
  12. Anuri, Farhang Bozor Sokhon, 1390, juzu'i na 4, shafi 3760.
  13. Majmu'eh Nawisadigani, Farhang Fiqh, 2009, juzu'i na 4, shafi na 213.
  14. Sadr al-Din Shirazi, Kasr Asnam al-Jahiliyyah, 2001, shafi na 35.
  15. Sadr al-Din Shirazi, Kasr Asnam al-Jahiliyyah, 2001, shafi na 38.

Nassoshi

  • Amadi, Abdul Wahid bin Muhammad, Gharar Al-Ahkam da al-Kalam, editan Mahdi Rajaee, Kum, Dar al-Kitab al-Islami, 1410 AH/1990 miladiyya.
  • Anuri, Hassan, Farhang Bozor Sokhon, Tehran, Sokhon, 2013.
  • Khatami, Ruhollah, Aineh Makarem: Bayanin Sallar Makarem al-Akhlaq na Imam Sajjad (a.s.), Tehran, Zalal, 1368.
  • Sadr al-Din Shirazi, Muhammad bin Ibrahim, Kasr Asnam al-Jahiliyyah, gyare-gyare da bincike da gabatarwa na Mohsen Jahangiri, tare da amincewar Sayyid Mohammad Khamenei, Tehran, Sadra Islamic Wisdom Foundation, 2013.
  • Al-Qasani, Abd al-Razzaq, Sharh Manazel As-Saerin Khwaja Abdullah Ansari, bincike na Mohsen Bidarfar, Kum, Bidar, 1385/1427 AH.
  • Golpaygani, Mohammad Reza, Irshad al-Sa'il, Beirut, Dar al-Safwa, 1413 AH/1993 AD.
  • Goharin, Sadegh, Sharh Istilhat Tasawwuf, Tehran, Zovar, 1380.
  • Majmu'eh Nawisandigan, Farhang Fiqhu: Mutabik Mazhab Ahlul-Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, karkashin kulawar Mahmoud Hashemi Shahroudi, juzu'i na 4.مؤسسه دائرة المعارف فقه اسلامی بر مذهب اهل بیت(ع)، shekara ta 1389 h shamsi.
  • Mousavi Tabrizi, Mohsen,Mukaddime bar Irfani Amali wa Shenakt daharat Nafsu insan, Tehran, Cibiyar Al'adu Noor Ali Noor, 1387.
  • Nasir al-Din Tousi, Muhammad bin Muhammad, Ausaful al-Ashraf, gyara da tsarawa da bincike daga Mehdi Shams al-Din, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, 1369.