Naufu Ɗan Fudala Al-bikali

Daga wikishia

Naufa ɗan Fudala Al-bikali, (Larabci: نَوف بن فُضالَة البِكالي أو البَكالي) wanda aka fi sani da Naufu Al-bakali, ya kasance dogari na Amirul Muminin (A.S) a zamanin gwamnatinshi, wasu masu wa'azi sun kawo a cikin huɗubobinsu da cikin wasu hikimomi na Imam Ali (A.S) a ciki Nahjul Balaga cewa ba a kawo sunanshi ba a cikin litattafai na Ilmul Rijal, sai dai cewa wasu ruwayoyinshi sun zo a cikin litatafan hadisi.

Rayuwarshi

Naufu ɗan Fudal ɗan ƙabilar Bakal ne,[1] amma wasu suna ganinshi a matsayin ɗan ƙabilar Hamadan, sai dai kuma Shaik Mamaƙani a cikin littafinshi Tanƙihil Maƙal ya ce wannan maganar ba ta inganta ba,[2] amma wasu littafai sun ambaci cewa Abdullahi ne babanshi,[3] kazalika sun kawo cewa, Amma Abakali wanda aka yanke ɗan yatsarshi a yaƙin Yarmuk ɗan uwanshi ne.[4]

Naufu ya kasance daga yankin Shama,[5] don haka ne ma ake masa laƙabi da Shami, amma Ibn Asakir ya dauke shi a matsayin dan yankin Dimashƙi ya kawo tarihinshi a cikin littafinsa na tarihin garin Dimashƙ,[6] amma an ruwaito daga wasu cewa Naufu ɗan yankin Falasɗin ne.[7] alkunyarshi ita Abu zaid,[8] Ko Abu Amru ko Abu Rashid,[9] Aɗɗaabari ya ambaci sunansa a cikin Tabi'ai.[10]

Suka ce mahaifiyar Naufu ta auri Ka'abul Ahbar bayan mutuwar mijinta,[11] Ibini Asakir ya ce an kashe Naufu a ɗan Fadil ne a yaƙin da ya gudana tsakanin Muhammad ɗan Marwan da Rumawa.[12]

Alakarsa Da Imam Ali (A.S)

Imam Ali (A.S) Ya cewa Naufu Al-bakali

يَا نَوْفُ! طُوبَى لِلزَّاهِدِينَ فِي الدُّنْيَا، الرَّاغِبِينَ فِي الْآخِرَةِ، أُولَئِكَ قَوْمٌ اتَّخَذُوا الْأَرْضَ بِسَاطاً، وَتُرَابَهَا فِرَاشاً، وَمَاءَهَا طِيباً، وَالْقُرْآنَ شِعَاراً، وَالدُّعَاءَ دِثَاراً، ثُمَّ قَرَضُوا الدُّنْيَا قَرْضاً عَلَى مِنْهَاجِ الْمَسِيح‏.

Ya Naufu Farin ciki ya tabbata ga masu gudun duniya, masu kwadayi cikin lahira, su ne mutanen da suka riki kasa shimfida, suka dauki kasa matsayin gadon kwanciya, ruwanta suka rike shi matsayin ruwa mai kamshi, suka riki kur'ani matsayin wuridi da yake kan harshensu kullum, suka dauki addu'a matsayin takensu, suka yanke duniya daga jikinsu kamar dai yadda Almasihu Isa dan Maryam ya yi.

Shaik Saduk, Al-Khisal, bugun shekara ta 1362 shamsi, juzu'i 6 shafi na 39,

An yi la'akari da Naufu Albakali ɗaya daga cikin sahabban Imam Ali (A.S)[13] kuma ya kasance dogari na imam Ali (A.S).[13] Sai ya nemi Imam Ali (A.S) ya yi masa nasiha, don haka ya yi masa nasiha da sada zuminci da son iyali gidan manzo (S.A.W), da nisantar giba,da nisantar taimakawa azzalimi, ya kuma yi masa nasiha da kyawawan dabi'u da dama.[14] Shaik Mamaƙani yana ganin nasihar da Imam Ali ya yiwa Naufu dalili ne kan cewa shi Naufu yana da karfin imani.[15]

Ruwayoyi

A cikin littafai na hadisan Shi'a, akwai ruwayoyi da Naufu ya ruwaito daga Imam Ali (A.S) a cikin Nahjul Balagha, akwai hikimumi da huɗubobi da Naufu Albakali ya rawaito daga imam Ali (A.S).[16]

Haka nan kuma yana da ruwaya ta Kuɗubar Himama amam da banbanci kaɗan da wadda tazo a Nahjul Balagha,[17] haka nan kuma ya kawo munajatin Imam Ali (A.S),[18] kuma Shaik Ɗusi ambaci wani hadisi a cikin littafinshi mai suna Amali da ya ruwaito daga Ali (A.S) kan bayanin sifofin Shi'arsa.[19]

Naufu ya ruwaito daga Abdullahi Ɗan Amru ɗan Asi da Abi Ayyub Al-ansari,[20] kuma Abu Ishaƙ Alhamdani da Nusairu Ɗan Zu'uluƙ da Khalid Ɗan Subaih da Abdulmali Ɗan Habib Aljuni Ɗan Juwaini da ammara Ɗan Juwain Al'abdi da Shahar Ɗan Hushab Al'ashi'ari,[21] da Abu Abdul-shami da Abdul A'ala,[22] da Alƙama Ɗan ƙais sun ruwaito daga gare shi.[23]

Kuma ba a ambaci sunansa ba a littafan Shi'a da suka gabata, kuma kamar yadda Sayyid Khuyi ya taƙaita da rawaito ruwaya daga gareshi batare da ya bayyana ra'ayinsa game da shi ba,[24] An ruwaito daga wasu litattafai na Ahlus-Sunna cewa,shi Naufu ya yi imani da cewa Musa a cikin ƙissar Musa da Khidr ba Annabi Musa (A.S) bane wani Musan ne daban, don haka ne Ibn Abbas ya ƙaryatashi, kuma ya daukeshi matsayin maƙiyin Allah.[25]

Bayanin kula

  1. Al-Mamaqani, Tankihul Makal, juzu'i na 3, shafi na 277.
  2. Al-Mamaqani, Tankihul Makal, juzu'i na 3, shafi na 277.
  3. Sheikh Tusi, Al-Amali, 1414 BC, shafi na 576.
  4. Ibn Hajar, Al-Isaba, 1995 BC-1415 BC, juzu'i na 4, shafi na 580.
  5. Ibn Asaker, Tarikhu Madinati Damashki, juzu'i na 62, shafi na 303.
  6. Ibn Asaker, Tarikhu Madinati Damashki, juzu'i na 62, shafi na 303-313
  7. Ibn Asaker, Tarikhu Madinati Damashki, juzu'i na 62, shafi na 303.
  8. Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, 1967 AD-1387 AH, juzu'i na 11, shafi na 383.
  9. Al-Mamaqani, Taniqhul al-Maqal, juzu'i na 3, shafi na 276; Ibn Asakir, Tarikhu Madinati Damashki, juzu'i na 62, shafi na 303.
  10. Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, 1967 AD-1387 AH, juzu'i na 11, shafi na 683.
  11. Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, 1387H, juzu'i na 11, shafi na 164, 664.
  12. Ibn Asaker, Tarikhu Madinati Damashki, juzu'i na 62, shafi na 313.
  13. Ibn Abi al-Hadid, Sharhu Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 10, shafi na 77.
  14. Sheikh Al-Saduq, Al-Amali, shafi na 209-210.
  15. Al-Mamaqani, Tankihul Makal, juzu'i na 3, shafi na 276.
  16. Nahj al-Balagha, Subhi Saleh, Huduba ta 182.
  17. Allama Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 65, shafi na 192-193.
  18. Allama Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 73, shafi na 359.
  19. Al-Tusi, Al-Amali, shafi na 576.
  20. Ibn Asakir, Tarikhu Madinati Damashki, juzu'i na 62, shafi na 303.
  21. Ibn Asakir, Tarikhu Madinati Damashki, juzu'i na 62, shafi na 303.
  22. Sheikh Al-Saduq, Al-Khisal, juzu'i na 1, shafi na 337.
  23. Sheikh Mufid, Al-Amali, 1413 BC, shafi na 132-133.
  24. الخوئي، معجم رجال الحديث، ج 19، ص 185-186.
  25. Kermani, Al-Kawakib Al-Durari, juzu'i na 14, shafi na 50.

Nassoshi

  • Ibn Abi Al-Hadid, Abdul Hamid bin Hibatullah, Sharhu Nahj Al-Balagha, Gyara: Muhammad Abu Al-Fadl Ibrahim, Ayatullah Al-Marashi Al-Najafi Library, Qum, 1404H.
  • Ibn Hajar Al-Asqalani, Ahmed bin Ali, Al-Isaba fi Tamyiz Al-Sahaba, bincike: Adel Ahmed Abdel Mawjoud da Ali Muhammad Moawad, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, 1415H.
  • Ibn Asakir, Ali bin Al-Hassan, Tarikhu Madinati Damashki, wanda: Ali Shiri, Darul Fikr, Beirut, 1418 H.
  • Amin, Mr. Mohsen, fitattun 'yan Shi'a, Hassan Amin, Dr. T.
  • Al-Khoei, Al-Sayyid Abu Al-Qasim, Mujam Rijal Al-Hadith, Cibiyar Buga Tarihin Shi'a, Qum, 1410H.
  • Sheikh Al-Saduq, Muhammad bin Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, 1376 Hijira.
  • Sheikh Al-Saduq, Muhammad bin Ali, Al-Khisal, wanda: Ali Akbar Ghafari, Qom, Jami'ar Malamai, 1362 H.
  • Sheikh Al-Tusi, Muhammad bin Al-Hasan, Al-Amali, Gyara: Wanda ya assasa Manzo, Qum, Gidan Al'adu, 1414H.
  • Sheikh Al-Mufid, Muhammad bin Numan, Al-Amali, Gyara: Ali Akbar Ghafari, Kum, Kangarh Sheikh Mufid, 1413H.
  • Al-Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikhu Al-umam wa Al-muluk, wanda: Muhammad Abu Al-Fadl Ibrahim, ya buga a Beirut, Dar Al-Turath, 1387H.
  • Allamah Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Darahya Al-Tarat Al-Arabi, 1403H.
  • Al-Kermani, Muhammad bin Yusuf, Al-Kawakib Al-Darari fi Sharh Sahih Al-Bukhari, Beirut, Dar Al-Haya’ Al-Turath Al-Arabi, 1401H.
  • Al-Mamaqani, Abdullah, Tankihul Al-makal Fi Ilmi Rijal, Najaf, Al-Murtazawiya Press, 1352H.
  • Nahj al-Balagha, Tas'hihu: Subhi Saleh, Kum, Hijira, 1414H.