Mukamul Mahmud

Daga wikishia
Gutsiren zanen rubutun aya ta 79 suratul Isra'i

Mukamul Mahmud (Larabci: مقام محمود) yana daukar ma’anar wani matsayi da Madaukakin Mukami, yana daga cikin lakubban Annabi (S.A.W) wanda Allah ya ba shi sakamakon zage dantsensa da raya darare da ibada, Malaman Tafsiri a karshen aya ta 79Suratul Isra’i sun bayyana wannan matsayi da shine dai Mukamin ceto da zai yi ranar lahira. Wasu ba’arin Malaman Tafsiri sun fassara Mukamul Mahmud da fifitar Annabin Muslunci (S.A.W) kan dukkanin halittu da kumar kurewar kusancinsa ga Allah, na’am wadannan ma’anoni guda biyu suna tattaro mukamin ceto, sannan kan asasin wata gaba cikin Ziyaratu Ashura, Imam Husaini (A.S) shima yanada mukamin ceto.

Matani da kuma Tarjama

وَ مِنَ اللَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِ نَافِلَةً لَّكَ عَسىَ أَن يَبْعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامًا مَّحمُوداً


Daga dare ka tashi ka raya shi ka yi sallah farilla ce kari gareka kai kadai sarai Allah ya baka wani matsayi abin yabawa.



(Suratul Isra'i: 79)


Matsayi abin yabawa ga Manzon Allah (S.A.W)

Malamai da masu Tafsiri sun fassara Mukamul Mahmud da cewa wani Madaukakin Mukami ne abin yabawa wanda Allah ya baiwa Annabi (S.A.W) [1] sakamakon salolin dare da yake yi.

Tusi, Al-Tebyan, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, juzu'i na 6, shafi na 510-511; Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 6, shafi 671; Faiz Kashani, Tafsir al-Safi, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi.210; Bahrani, Al-Burhan, 1416 AH, juzu'i na 3, shafi na 569; Ayashi, Kitab al-Tafseer, 1380, juzu'i na 2, shafi na 314; Tabatabaei, Tafsir al-Mizan, 1377, juzu'i na 1, shafi na 178; Makarem Shirazi, Tafsir al-Nashon, 1370, juzu'i na 12, shafi na 232; Javadi Ameli, Tafsir Tasnim, 1378, juzu'i.4, shafi.285; Shabar, Tafsirin Al-Kur’an al-Karim, 1412 AH, shafi na 286; Fakhr Razi, Mufatih al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 21, shafi na 386-387; Qurtubi, Yom al-Faz al-Akbar, Maktaba al-Qur'an, shafi na 155.

Dangane da ma’anar Mukamul Mahmud akwai sabanin ra’ayoyin Malamai sai dai cewa matsayin ceto ya tattaro baki dayan ma’anonin:

  • Mukamin ceto: da yawa daga Malaman Tafsiri na Shi’a [2] da Ahlus-sunna [3] bisa jingina da riwayoyi sun bayyana Mukamin ceto matsayin shi ne Mukamul Mahmud, da wannan ne zai samu damar ceton al’ummarsa ranar lahira [4] ko kuma dai duba da riwayar da aka rawaito daga Imam Bakir (A.S) ko Imam Sadik (A.S) cikin Tafsirin ayar da muka ambata a sama cikin suratul Isra’i, an fassara Mukamul Mahmud da ceto [5] wasu adadi daga malaman Tafsiri sun bayyana wannan mukami da Shafa’atul Kubra (ceto mafi girma), [6] kamar yanda Assayid Mahmud Husaini Tahrani wanda ya rayu tsakanin shekara 1344-1416 hijirar tafiyar rana [7] a mahangarsa akwai cikakkiyar kyawunta da kamala cikin Mukamul Mahmud, kuma wannan mukami da matsayi saki babu kaidi ba tareda wani dabaibayi ko sharadi Allah ya mika shi ga Annabi (S.A.W) da ma’anar cewa duk wani yabo da yabawa daga dukkanin mai yabawa da dukkanin abin yabawa ya ta’allaka da Annabi (S.A.W). [8]

fifita kan halittu: wasu jumla daga Malaman Tafsiri, sun tafi kan cewa ba wani abu ne Mukamul Mahmud illa fifita kan dukkanin halittu, daga ciki akwai ceto da Allah ya bashi. [9] Kurewar kusanci ga Allah: cikin Tafsir Namuneh: an kawo wannan fuskar a matsayin shine ma’anar Mukamul Mahmud kure kusanci da Allah na daga kufaifayin Shafa’atul Kubra. [10]

Mukamul Mahmud a wurin Imamai (A.S)

A fadin Ayatullahi Nasir Mukarim Shirazi babban Malamin Tafsiri na Shi’a, duk da cewa aya ta 79 cikin Suratu Isra’I kai tsaye tana Magana kan Annabi (S.A.W) ne amma bama kore cewa ta tattaro da wasu, da ma’anar cewa Mumini Ma’abocin sallar dare gwargwadon kusancinsa da Allah, zai amfani da wani bangare daga ceton sauran mutane. [15]

Bayanin kula

  1. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 6, shafi 670; Tabarsi, Tafsir Jawame'ul Al-Jame, Tehran, 1377, juzu'i na 2, shafi na 341.
  2. Tusi, Al-Tabayan, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, juzu'i na 6, shafi.512; Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 6, shafi 671; Faiz Kashani, Tafsir al-Safi, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 211-212; Bahrani, Al Burhan, 1416 AH, juzu'i na 3, shafi 570-574; Ayashi, Kitab al-Tafseer, 1380, juzu'i na 2, shafi na 314; Tabatabaei, Tafsir al-Mizan, 1377, juzu'i na 1, shafi na 178; Makarem Shirazi, Tafsir al-Nashon, 1370, juzu'i na 12, shafi na 232; Javadi Ameli, Tafsir Tasnim, 1378, juzu'i.4, shafi.285; Shabar, Tafsirin Kur’ani Karim, 1412 Hijira, shafi na 286.
  3. Fakhr Razi, Mufatih al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 21, shafi na 387; Qurtubi, Yom al-Faz al-Akbar, Maktaba al-Qur'an, shafi na 155.
  4. Ibn Hanbal, Musnad, Dar Sadhir, Mujalladi na 2, shafi na 441.
  5. Ayashi, Kitab al-Tafseer, 1380, juzu'i na 2, shafi na 314.
  6. Tabatabaei, Tafsir al-Mizan, 1377, juzu'i na 1, shafi na 178; Makarem Shirazi, Tafsir al-Namuneh, 1370, juzu'i na 12, shafi na 232; Javadi Ameli, Tafsir Tasnim, 1378, juzu'i na 4, shafi na 285.
  7. Hosseini Tehrani, Imam Shinasi, juzu'i na 9, shafi na 164.
  8. Hosseini Tehrani, Imam Shinasi, Mujalladi na 9, shafi na 162.
  9. Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 6, shafi 671; Ibn Arabi, Fatuhat Makiya, Mu’assasa ta Al-Baiti ta Farfado da Al’ada, Mujalladi na 4, shafi na 57; Auren Hawizi, Tafsirin Nur al-Saqlain, 1415 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 206.
  10. Makarem Shirazi, Tafsir al-Namuneh, 1370, juzu'i na 12, shafi na 231-232.
  11. , Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 30
  12. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 101, shafi na 292.
  13. Sadouq, Man Laihdrah al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi: 605; Tusi, Tahzeeb Al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 88.
  14. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 101, shafi na 292.
  15. Makarem Shirazi, Tafsir al-Namuneh, 1370, juzu'i na 12, shafi na 231-232.

Nassoshi

  • Ibn Hanbal, Ahmad, Musnad, Beirut, Dar Sadir, [Bita].
  • Ibn Arabi, Mohi Al-Din, Fatuhat Makiyah, Kum, Al-Bait (A.S.) Foundation for Revival of Tradition, [Bita].
  • Bahrani, Sayyid Hashim, Al-Burhan fi Tafsirin Qur'an, Tehran, Ba'ath Foundation, 1416H.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tafsir Tasnim, Qum, Esra Publishing Center, 1378.
  • Shabar, Sayyid Abdullah, Tafsirin Kur'an al-Karim, Beirut, Dar al-Balaghah na bugu da bugawa, 1412 AH.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali bin Baboyeh, Man Lai Ya-Hazara Al-Faqih, bincike na Ali Akbar Ghafari, Qum, Islamic Publications Office, bugu na biyu, 1413 AH.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Tafsir al-Mizan, Qom, Islamic Publications Office, 1377.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Tafsir al-Jamae Jameed, Tehran, Jami'ar Tehran Publications and Administration of Qom Academic Faculty, 1377.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow Publications, 1372.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tebyan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Dar Ihya al-Tarath al-Arabi, [Bita].
  • Tousi, Muhammad bin Hassan, Tahzeeb al-Ahkam, Hasan Mousavi Khorsan, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya ya yi bincike, bugu na 4, 1407H.
  • Daurin Auren Hawizi, Abd Ali Bin Juma, Tafsir Noor al-Saqlain, Qum, Isma'il Publications, 1415H.
  • Ayashi, Mohammad Bin Masud, Kitab al-Tafsir, Tehran, Ilmia Printing House, 1380H.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatih al-Ghaib, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H.
  • Faiz Kashani, Hilmasan, Tafsir Al-Safi, Tehran, Sadr Publications, 1415 AH.