Muƙamin Sayyida Ruƙayya
Haramin Sayyaهa Rukayya | |
| Kafawa | Ƙarni na 9 bayan hijira |
|---|---|
| Mai amfani | Wurin ziyara |
| Wuri | Dimashƙi -Siriya |
| Faɗi | 4500 nurabba'in mita |
| Salon | irin salon ginin gargajiya na Iran |
Haramin Sayyida Ruƙayya (Larabci:حرم السيدة رقية) Wuri da yake a birnin Damashƙi na ƙasar Siriya, ana danganta shi ga Ruƙayya ɗiyar Imam Husaini (A.S) wannan haramin shi ne hubbare na biyu a wurn ƴanShi'a a birnin Damashƙi bayan haramin Sayyida Zainab (A.S) ɗiyar Imam Ali (A.S). An fara danganta wannan wuri ga Sayyida Ruƙayya a ƙarni na goma sha huɗu bayan hijira; Kafin haka dai wasu madogarai da majiyoyi na ƙarni na goma sun danganta wannan wuri a matsayin maƙabartar ɗiyar Imam Husaini (AS) amma ba tare da ambaton sunan Ruƙayya ba.
Wasu sun yi shakku kan yadda aka jingina wannan hubbaren ga Sayyida Ruƙayya, wasu daga cikinsu suna ganin cewa ita ce maƙabartar Ruƙayya ƴar Imam Ali (A.S) wasu kuma suka ce ita ce makabartar Ruƙayya ɗiyar Imam Ali (A.S), Wasu daga cikinsu sun ce a nan ne wurin Muƙam Ra'asil Husaini. Akwai wani shahararren labari da ya faru a lokacin da ake sabunta ginin wurin, yarinya ce ƙarama ma'abociyar wannan kabari. A yau, Haramin Sayyida Ruƙayya ya ƙunshi wani fili mai faɗin gini kuma ya kasance cakude da fasahar gine-ginen muslunci da na gargajiya na Iran.
Matsayi
Hubbaren Sayyida Ruƙayya a birnin Damashƙi da ake dangantawa da Ruƙayya ƴar Imam Husaini (A.S), a matsayinsa na hubbare na biyu a cikin haramin, bayan haramin Sayyida Zainab (S) ga Shi'a a birnin Damashƙi.[1] Wannan wurin ibada yana ɗaya daga cikin tsoffin kasuwannin Damashƙi mai suna "Kasuwar Al-Amara", kusa da Bab Al-Faradis (Ɗaya daga cikin kofofin tsohuwar Damashƙi), kuma kusa da masallacin Umayyawa. Masallaci da Kasuwar Sham.[2][3]
Danganta Wannan Wuri Zuwa Gare ta
Akwai sabani game da jingina haramin Uwargida Ruƙayya ga Ruƙayya ƴar Imam Husaini (A.S), ko kuma Ruƙayya ƴar Imam Ali (A.S).[4][5]Bisa ra'ayin wani malamin tarihi mai suna Ahmad Kamehyar, asalin ƙabarin sayyida Ruƙayya ya kasance gurin da aka binne kan Imam Husain (A.S) a Damashƙi, wannan shi ne abin da wasu suka tafi akai. ya zo a cikin litatafan da suke da alaƙa da gwamnatin Usmaniyawa cewa, shi wannan guri an san shi a matsayin Muƙam na Sayyida Ruƙayya, kuma ya zo a cikin wasu litatafai da yawa, ƙari akan cewa kabarin sayyida Ruƙayya ne, an anbaci cewa akwai kan Imamu Husaini a gurin, da bambancin cewa an san Ruƙayya a cikin daɗaɗun latattafai waɗanda suka gabata a matsayin ƴar Imam Ali (A.S), kuma a litattafai na baya-bayan nan ana kiranta ƴar Imam Husaini (A.S).
Ance dalilin da yake nuna cewa, wannan ƙabarin na sayyida Ruƙayya ne, an same shi a ƙarni na goma ne, a littafin Muhammad ɗan Abi Ɗalib Al-ha'iri Alkaraki wanda ya rasu a shekara ta 955 a cikin wani littafin shi mai suna Tasliyatul Majalis.[6] Inda ya ce ya ga wani rushasshen gini a gabashin masallacin Umayyawa da ke birnin Damashƙi, wanda a baya masallaci ne, mai ɗauke da sunayen Manzon Allah (S.A.W) da Imamai goma sha biyu (A.S), a rubuce a kan wani dutse a ƙofarsa. Haka nan kuma a kansa an rubuta wannan kabarin Sayyida sarauniya ƴar Husaini ɗan Amirul Muminin (A.S).[7]
Sayyid Muhsin Amin ya yi rubutu game da wannan wurin ziyara a cikin littafinshi mai suna A'ayunush Shi'a, ƙabarin da aka danganta ga Ruƙayya ƴar Imam Husaini, wani wurin ziyara ne a unguwar Al-Amara a birnin Damashƙi, wanda Mirza Ali Asgar Khan ya sabunta gininshi. Babban waziri na Iran a shekara ta 1323 hijira, ya sake sabunta ginin wannan guri tare da rubuta wannan da kwanan wata a saman ƙofa.[8]
Ya zo a cikin kundin Daneshnameh Imam Husaini (A.S), bayan da ya nazarci abin da aka jingina shi ga Ruƙayya (A.S) cewa bisa la'akari da madogaran ruwayoyi da na tarihi, ba zai yi wu a ba da tabbatacciyar magana a kan wannan gurin ba. Amma mu'ujizar da aka gani da kuma ake gani daga wannan wuri suna ƙarfafar matsayinsa, don haka ya kamata a girmama wannan wuri.[9]
Ƙissar Ambaliyar Ruwa Kan Wannan Ƙabari Da Tone shi
Wasu majiyoyin ƙarni na biyu da suka gabata sun yi nuni da cewa labarin tone ƙabari da gano gawar Ruƙayya (A.S), na nuni da cewa ƙabari ne na wata ƙaramar yarinya .[10] An ce aƙalla mutane uku ne suka rawaito wannan labari, na farkonsu shi ne Mumin Shablangi malamin Ahlus-Sunna a ƙarni na sha uku a cikin littafin Nurul Al-Absar,[11] wanda shi kuma ya bayyana ma'abocin ƙabari da Ruƙayya ƴar Imam Ali (A.S). yana mai cewa gawar da aka gani a lokacin da suka fitar da ita daga cikin ƙabarin don gyara shi, gawa ce ta budurwa wadda ba tabalaga ba.[12]
Shaik Muhammad Hashim Khurasani (Rasuwa: 1352 bayan hijira) ya yi la'akari a cikin littafinsa Muntakabul Tawarik, cewa wannan hubbaren hubbare na Ruƙayya ƴar Hussaini Bin Ali, kuma ya kawo labarin ɓarnar da aka yi wa kabarin dalla-dalla. Ya kuma ƙara da anbaton karamominta. Shaik Muhammad Hashim Al-kurasani ya ce: Sayyd Ibrahim Al-Dimashƙi yana da ƴaƴa mata guda uku, a shekara ta 1280 bayan hijira, tsawon dare uku a jere ko wace daga cikinsu daga babba zuwa ƙaramarsu, sai ta ga Ruƙayya a mafarki tana cewa mata: "Ki gaya wa babanki cewa ƙabarina ya cika da ruwa, ya zo ya gyara shi." Malam Ibrahim bai damuwa ba da mafarkin ƴaƴansa mata har dare na huɗu, sai da ta ka ga shi da kanshi ya yi mafarki ya ga Ruƙayya. Bayan haka, a gaban malaman Shi'a da Ahlus-Sunna suka tono ƙabarin. sannan Malam Ibrahim ya yi ta ƙoƙari da kaikawo har sai da aka gyara shi.[13] A cewar mawallafin littafin Mausu'atul Imam Husaini(A.S) duk da ɗimbin dalilan naƙalto waɗannan abubuwa; Amma babu wanda ya rawaito wannan labari sai waɗanda suka dau alhakin kula da wannan haramin, kuma Malam Muhsin Al-Amin bai yi nuni da hakan ba, duk da kasancewarsa a yankin.[14]
a cewar marubutan kundin littafin Daneshname Imam Husaini (A.S) duk da cewa akwai samuwar kwaɗayi cikin rubuta rahotannin wannan labari, amma tare da haka babu waɗanda suka naƙalto wannan labari in banda hadiman wannan harami, Sayyid Muhsin Amin shi ma tare da kasancewar ya zauna wannan unguwa amma kuma bai yi ko da ishara ba kan wannan labari.[15]

Tarihin Sabunta Gini Wannan Ƙabari
Babu wani bayani game da gina haramin farko da tsarin sabunta gina shi har zuwa ƙarni na tara bayan hijira.[16] kamar yadda ɗan Tulun al-Dimashƙi, marubucin littafin Ashshazarat Azzahabiya cikin rabi na biyun ƙarni na tara. Sarki Azzahiri Bardabak, wanda ya zama gwamnan Damashƙi a shekara ta 871. ta hanyar sake gina wannan haramin. ɗaya daga cikin allunan da ke cikin haramin na nuni da cewa Mirza Baba Mustafi al-Khilani ya sake gina haramin a shekara ta 1125 bayan hijira.[17] Sannan kuma a ƙarshen zamanin daular Usmaniyya, Mirza Ali Asgar Khan Atabak babban mai ba da shawara na daular ƙajar ya sake gina wannan wurina shekara ta 1323 bayan hijira.[18]
Kamar yadda wasu malaman tarihi suka ruwaito, sarakunan daular Ayyubiyya a farkon mulkinsu a shekara ta 567 bayan hijira, sun gina wani ɗan ƙaramin ƙabari mai ɗauke da hubbare da ƙubba a cikin haramin Ruƙayya (A.S), wanda yake cikin masallacin Ra'asul Husaini. sannan aka gyara shi kuma aka gina shi a shekara ta 1125 hijira da 1323.[19]
A shekara ta 1343 bayan hijira, Kamal da Muhammad Ali Al Nizam, ƴanShi'a na Damashƙi, sun sake gina ginin da kuɗinsu. Kafin nan ginin hubbaren Sayyida Ruƙayya wani ɗaki ne kuma ƙabarin yana a tsakiyar shi, akwai wani ƙaramin masallaci a gefenshi, kuma faɗin ginin bai wuce murabba'in mita 60 ba a lokacin.[20]
Faɗaɗa Kabarin
A farkon shekarun 1970 miladiyya, wasu ƴan Shi'a da suka haɗa da Nasarullah Khalkali da Imam Musa Sadar suka kafa wani kwamiti da nufin faɗaɗa haramin Sayyida Ruƙayya, inda suka sayi gidaje da shaguna da dama da ke kusa da shi. Aikin sake sabunta ginin ya fara ne a shekara ta 1404 bayan hijira, dai-dai da 1984 miladiyya, kuma mafi yawanshi ya kammala ne a shekara ta 1410 bayan hijira.[21]
A wani sabon ci gaba da aka samu, jimlar girman zarihu ya kai murabba'in mita 4,500, wanda murabba'in mita 600 ya haɗa da farfajiyarsa da wani babban fili, sauran gine-gine ne na ƙasa, sannan an gina wani masallaci mai faɗin murabba'in mita 800. an kuma gina shi a kudancin ginin wurin zairihu da hanyoyinshi a cikin sabon ginin ya kai murabba'in mita 2600.[22]
Fannin Fasahar Gini
Nau'in gine-ginen da aka yi amfani da shi wajen faɗaɗa hubbaren Sayyida Ruƙayya a baya-bayan nan, shi ne tsarin gine-ginen Musulunci na gargajiya na Iran,[23]An ce kayan gini da kayan ado sun sha bamban da sauran kayayyakin gine-gien tarihi na a Damashƙi.[24] Ginin ɗakin zairihu yana da ƙofofin shiga da dama, mafi muhimmanci daga cikinsu ita ce ƙofar kudu maso yamma, a saman wannan kofar akwai wani baka da aka lullube da kayan ado, a samansa an rubuta "Wannan shi ne hubbaren Sayyida Ruƙayya ƴar gidan Husaini shahidin Karbala"[25] A saman kan kofar akwai wata hasumiyar kiran sallah mai tsayin mita 34 daga ƙasa. sannan ƙofar da take jikin babbar farfajiyar haramin tana da siffar kusurwa huɗu kuma tana kewaye da hanyoyi.[26]
Babban bangaren ginin dai ya haɗa da babban ginin zarihu daga yamma, da kuma manya-manyan masallatai guda biyu a tsakiya daga gabas, ta yadda ko wane ɓangare yana da ƙofar shiga harabar farfajiyar da ke arewa, kuma a kusa da wurin ginin zarihu akwai guraren dake da rufi da madubai. An lullube rufin ginin ɗakin zarihu da kayan ado, tsakanin duwatsun ana iya ganin rubutun ayoyin kur'ani da hadisai na falalar Ahlul-Bait(A.S).[27]
Haramin Sayyida Ruƙayya yana tsakiyar garin Damashƙi, kuma a kan shi akwai wani akwati na katako wanda aka lulluɓe da koren kyale mai ɗauke da ayoyin Alƙur'ani, a sama da ƙabarin akwai wani hubbare na azurfa da aka gina a shekara ta 1376 bayan hijira/1956 miladiyya, wanda cibiyar Banu Zahra da ke birnin Tehran ta bayar da ita ga hubbaren Sayyida Ruƙayya, wannan ginin yana tsakanin sabon ginin mai fentin azurfa kuma mafi girma. wanda sassaƙa shi a garin Isfahan aka sanya shi a shekara ta 1414H/1994 miladiyya, saman babban gini yana da tsayin mita 14 daga ƙasa, sannan an lullube samanshi da kayan ado na geometric, kuma saman cikinsa an yi shi da fasalin gini na gargajiya masu kyawun gaske da madubai.[28]
Wanda YakeJagorancin Kula Da Wurin
Bayan labarin mafarkin ƴaƴan Sayyid Ibrahim Dimashƙi, Sulɗan Abdul-Majeed (Daga cikin sarakunan Daular Usmaniyya) ya mika wa Sayyid Ibrahim kula dukkan hubbaren Zainabiyya, da hubbaren Ruƙayya, Sakina, da Ummu Kulsum. Bayan Sayyid Ibrahim Dimashƙi dansa da jikansa suka sune suka zama masu kula da wadannan wurare,[29] kuma a yanzu Ahmed al-Ashƙar shi ne Mai kula da haramin Sayyida Ruƙayya.[30]
Harin Ta'addanci Kan Muƙamin Sayyida Ruƙayya
A shekarar farko ta yunƙurin ƴan ta'addancin takfiriyya a ƙasar Siriya, limamin haramin Sayyida Ruƙayya Shaik Abbas al-Laham ya fuskanci hari daga ƴan ta'adda Takfiriyya a gaban ƙofar shiga haramin, sakamakon wannan harin ta'addanci ne ya yi shahada.[31] ƴan ta'addan da ke a yankin Jobar da ke gabashin Dimashƙi sun yi ta harba harsashi, inda suka yi ta kai farmaki kan hubbaren Sayyida Ruƙayya, sia dai kuma cikin luɗufin ubangiji harsashen da suke harbowa ba su kai ga cima hadafin da aka harba su domin shi ba.[32]
Bayanin kula
- ↑ Qaidan, Amakin Ziyarti Siyahati Suriya, 2007, shafi na 57.
- ↑ Al-Karbasi, Muhammad Sadiq, Da'irat al-Ma'arif al-Husayniyya, Tariikh al-Maradi (Husayni da Ahlinsa da Ansaransa), London, 1998.
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa Ziyaratgahaye Ahlul Baiti (A.S) dar Suriye, 1393, shafi na 237.
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa Ziyaratgahaye Ahlul Baiti (A.S) dar Suriye, 1393, shafi na 237.
- ↑ Al-Tabasi, Shafi na 25.
- ↑ Mohammadi Raishahri, Daneshnameh Imam Husaini (AS), 1388, juzu'i na 1, shafi na 389.
- ↑ Haeri, Teslia Majlis, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi na 93.
- ↑ Amin, Aayan al-Shia, 1421 AH, juzu'i na 7, shafi na 34. ↑
- ↑ Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Husaini (AS), 1388, juzu'i na 1, shafi na 393.
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa ziyaratgahaye Ahlul Baiti (A.S) dar Suriye shafi na 241
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa ziyaratgahaye Ahlul Baiti (A.S) dar Suriye shafi 241
- ↑ Shablanji, Noor al-Absar, Razi Publishing House, shafi na 195.
- ↑ Khameyar, Ayyukan Manzon Allah (SAW) da wuraren ibadar Ahlul Baiti (a.s) a Sham, 1393, shafi na 250
- ↑ Khorasani, Muntakabul Al-Tawarikh, 2008, shafi na 388.
- ↑ Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Husaini (AS), 1388, juzu'i na 1, shafi na 392.
- ↑ Khameyar, Ayyukan Manzon Allah (SAW) da wuraren ibadar Ahlul Baiti (a.s) dar Suriye, 1393, shafi na 246.
- ↑ Khameyar, Ayyukan Manzon Allah (SAW) da wuraren ibadar Ahlul Baiti (a.s) a Sham, 1393, shafi na 246.
- ↑ Qaidan, Amakin Ziyarati wa Siyahati Siriya, 2007, shafi na 57 da 58; Moghadis, Jagoran Wuraren Hajji a Suriye, 2009, shafi na 119 da 120.
- ↑ Khameyar, Ayyukan Manzon Allah (SAW) da wuraren ibadar Ahlul Baiti (a.s) a Sham, 1393, shafi na 247.
- ↑ Khameyar, Ayyukan Manzon Allah (SAW) da wuraren ibadar Ahlul Baiti (a.s) a Sham, 1393, shafi na 250.
- ↑ Qaidan, Amakin Ziyarati Siyahati Suriye, 2007, shafi na 58; Makdisi, Rahnamaye Amakin Ziyarati dar Kishware Suriye, 2009, shafi na 120.
- ↑ Makdisi, Rahnamaye Amakin Ziyarati dar Kishware Suriye, 2009, shafi na 121
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) da wuraren ibadar Ahlul Baiti (a.s) a Sham, 1393, shafi na 250.
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa amakain ziyaratri Ahlul-baiti (a.s) dare Suriye, 1393, shafi na 251
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa Amakin Ziyarati Ahlul Baiti (a.s) dar suriye, 1393, shafi na 251
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa amakain ziyaratri Ahlul-baiti (a.s) dare Suriye, 1393, shafi na 251-252
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa amakain ziyaratri Ahlul-baiti (a.s) dare Suriye, 1393, shafi na 251
- ↑ Khameyar, Asare Payambar (S.A.W) wa amakain ziyaratri Ahlul-baiti (a.s) dare Suriye, 1393, shafi na 251-252
- ↑ Khorasani, Muntakhabul Tarikh, 2009, shafi. 388;«آیا تروریستها به حرم حضرت رقیه حمله کردهاند»، Shafin Mashriq News
- ↑ دیدار تولیت حرم حضرت رقیه با تولیت آستان قدس رضوی
- ↑ «آیا تروریستها به حرم حضرت رقیه حمله کردهاند»، Shafin Mashriq News
- ↑ «آیا تروریستها به حرم حضرت رقیه حمله کردهاند»Shafin Mashriq News
Nassoshi
- «آیا تروریستها به حرم حضرت رقیه حمله کردهاند»، Gidan yanar gizon Masreq News, kwanan watan aikawa: Disamba 28, 2014, kwanan wata ziyara: Agusta 10, 2022.
- Amin, Seyyed Mohsen, Ayan al-Shi'a, Beirut, Dar al-Taqran, 1421H.
- Haeri, Muhammad bin Abi Talib, Tasliya Majlis da Zaina Majlis, Qum, Al-Maarif Islamic Foundation, 1418H.
- Khameyar, Ahmed, Asare Payambar (S.A.W) wa amakin ziyarati Ahlul-baiti (A.S) dar Suriye, Cibiyar Nazarin Hajji da Ziarat, Tehran, Mash'ar, 2013.
- Khorasani, Mohammad Hashem, Muntakab Tawarikh, Tehran, kantin sayar da littattafai na Islama, bugu na 7, 2008.
- «زندگی نامه شیخ نبیل الحلباوی»، Yanar Gizo na Majalisar Ahlul Baiti (AS), ranar ziyarar: 10 ga Agusta, 1401 Hijira.
- Shablanji, Momin bin Hasan, Noor al-Absaar fi Manaqib al-Bayt al-Nabi al-Mukhtar (a.s), Qom, Razi, Bita.
- Qaidan, Asghar, Amakain ziyarati siyahati Suriye, Tehran, Mash'ar, 2007.
- Mohammadi Rishahri, Mohammad et al., Daneshanameh Imam Hossein bar Paye Alqur'ani, Hadisi wa Tarikh, Qum, Darul Hadith, bugu na biyu, 2018.
- Moghadis, Ehsan, Rahnamaye ziyarati dar Kishaware Suriye), Tehran, Mash'ar, 2009
- نماز جمعه حتی یکبار تعطیل نشد, Kamfanin Dillancin Labarai na Hawza, Ranar bugawa: Disamba 8, 2014, Ranar ziyarta: Agusta 10, 2022.