Mu'ujizar Kur'ani Cikin Ƙididdigar Adadi

Daga wikishia

Mu’ujizar Alkur’ani cikin ƙididdigar adadi, (Larabciالإعجاز العددي للقرآن) wata nazariyya ce da take bayanin irin yanda Alkur’ani yake da mu’ujiza a cikin adadi, bisa wannan nazariyya, adadin haruffa da kalmomin Alkur’ani sun yi matuƙar dandaƙewa cikin zirin tsari, kasancewa babu babu wani marubuci da zai iya samar da dandaƙaƙƙen zirin tsari misalin adadin Alkur’ani, sai ake ƙidaya wannan tsari wata alama ta mu’ujizar Alkur’ani, Rashad Khalifa, mai bincike kan Alkur’ani mutumin Misra shi ne farkon wanda ya fara bijiro da wannan nazariyya, akwai Malamai masu tarin yawa da suke da saɓani da wannan nazariyya, masu suka kan wannan nazariyya sun fitar da tarin adadin lissafi da ƙididdiga da suka kasance ba daidai ba, wanda hakan ya haifare da suka mai yawa a kansu.

Gabatar da Nazariyya

Kan asasin nazariyyar Mu’ujizar Alkur’ani ta ƙididdigar adadi, adadin haruffa da kalmomin Alkur’ani sun kasance cikin dandaƙaƙƙen zubin tsari, kasancewa babu wani marubuci da zai iya samar da misalin wannan dandaƙaƙƙen tsari, sai wannan tsari ya zama wata alama ta mu’ujizar Alkur’ani, [1] wannan nazariyyar tana ɗaukar adadin 19 matsayin mabuɗin ramzin mu’ujizar Alkur’ani. [2] Kan asasin wannan nazariyya, ayar bismillahi Ar-rahamanir Ar-rahimi tana da haruffa 19, Kuma jimillar yawan maimaita kalmomin Bismilla a cikin Alƙur'ani, adadi ne na lamba goma sha tara, bismillahi 19, Allahu 2698, Rahamanu 57 da Rahimu, an yi amfani sau 114 a cikin Alkur’ani, dukkaninsu ninki ne na lamba 19, haka kanar yanda adadin bakiɗayan haruffan surorin Alkur’ani ninki daga adadi 19. [3]

Taƙaitaccen Tarihin Wannan Nazariyya Da Ma’abotanta

A ra’ayin ba’arin masu bincike, karon farko a cikin littafin Al-Itƙanu, wanda Jalalud-dini Suyuɗi ya rubuta wanda ya rayu tsakanin shekaru 849-911 h ƙamari, daga Malaman Ahlus-sunna, ya yi ishara zuwa ga mu’ujizar Alkur’ani cikin adadi, [4] sai dai cewa wannan nazariyya ta fito fili ta hannun Rashad Khalifa mai bincike kan Alkur’ani mutumin ƙasar Misra, cikin tsawon shekaru uku ta hanyar amfani da na’ura mai ƙwawaƙwalwa (Computer) ya yi bincike mai zurfi kan Alkur’ani a shekara ta 1351 h shamsi, (1972m) ya bijirar da natijar bincikensa ga kafafen yaɗa labarai, a shekarar 1983 m, nan ma ya fitar da littafinsa mai suna Mu’ujizatul Alkur’anil Alkarim, an buga wannan littafin a Bairut ƙasar Lubnan da kuma Amerika, [5] “Rashad Khalifa” ya yi da’awar cewa ya gano ranar tashin Alƙiyama ta hanyar ƙididdigar adadi ta Alkur’ani. [6] Bayan Rashad Khalifa, an samu Abdur-Razaƙ Naufal, mai bincike kan Alkur’ani shima kuma mutumin Misra, ya ɗora kan abin da Rashad Khalifa ya fara, ya bijiro da sabbin wurare daga Mu’ujizar Alkur’ani cikin adadi; daga jumlarsu, shi ne kasancewar kalmomi masu kishiyantar juna, sune dai rayuwa da mutuwa, sun zo da adadin ninki a cikin Alkur’ani, bayan Abdur-Razaƙ an samu “Abu Alzahra An-Najadi” mai bincike Alkur’ani ɗan Shi’a ya kai ga gano cewa kalmar “Sa’atu”cikin awanni yini da dare awa 24 aka yi amfani da ita, ya kuma gano kalmar Shi’a an yi amfani da ita sau sha biyu (adadin Imam Shi’a). [7] ana cewa a wannan zamani nazariyyar mu’ujizar Alkur’ani cikin adadi ta samu karɓuwa matuƙar gaske daga masu bincike kan Alkur’ani. [8]

Sunayen Mu’ujizar Alkur’ani Cikin Adadi

Wasu daga cikin kididdigar da masu goyon bayan wannan ka'idar suka bayar sun kasance cikin abin da zai zo a ƙasa: A cikin Alkur’ani an fi maimaita Huruful Muƙaɗɗa’atu na kowacce sura dangane sauran haruffan surar. Adadin huruful muƙaɗɗa’atu na dukkanin surori da suke da huruful muƙaɗɗa’atu, ninki ne daga adadin 19. Kalmar “Hayat” wacce take nufin rayuwa tare da kalmomin da aka ciro daga cikinta an yi amfani da su gwargwadon kalmar mutuwa “Mautu” Cikin kalmar “Dunya” da “Akhirat” gwargwadon rayuwa da mutu aka yi amfani da su. Kalmar “Sa’atu” an yi amfani da gwargwadon awanni cikin yini da dare awa 24. Kalmar “Shahar” wata gwargwadon adadin watanni a shekara aka yi amfani da ita. Kalmar “As-samawatul As-saba” sammai bakwai karo bakwai aka yi amfani da ita Kalmar “Sajda” karo 34 aka yi amfani da ita wandai daidai yake da adadin Sujjadar cikin Sallolin farilla. [9]

Suka

Nazariyyar mu’ujizar Alkur’ani cikin adadi ta fuskanci suka da ƙalubale mai yawan gaske, [10] masu suka kan wannan nazariyya sun tafin kan cewa Allah bai saukar da Alkur’ani rufaffe ba ko wani sirri da yake wuce ƙarfin fahimtar mutane ba, wannan littafi an saukar da shi domin shiryar da mutane, wannan nazariyya da kuka kawo bata da alaƙa da shiriya, haka kuma sassaɓawar ƙira’o’i da rashin nassi kan jerantuwar surori suna daga matsaloli da suka hana fitar ingantacciyar ƙididdiga daga adadin haruffan Alkur’ani da kalmominsa. [11] ƙari kan wannan masu suka, sun bayyana cewa aksarin ƙididdigar da masu goyan bayan wannan nazariyyar suka fitar duk ba daidai bace akwai kuskure a ciki, [12] kuma sun ciro wurare masu yawan gaske da suka yi musu suka a kansu, sun kasance kamar haka:

  • ƙididddiga kan yawan maimamita huruful muƙaɗɗa’atu cikin suratul Yasin, ma’ana haruffa guda biyu “Ya’un” da “Sinun” adadin maimaicinsu bai da yawa a cikin wannan sura, a daidai lokacin kan asasin wannan nazariyya ƙididdigar adadin haruffansu sun fi ƙididdigar sauran haruffan surar.
  • ƙididdiga kan yawan maimamaita harafin ƙafun (karyayyen harafi a cikin suratul ƙaf) cikin suratul Shamsi da ƙiyamat da Falaƙi ya haura adadinsa a suratul ƙafu.
  • Wannan ikirari da cewa adadin yawan amfani da dukkan kalmomin Bismillah, Rahman, Raheem, ninki ne na lamba goma sha tara, kaɗai cikini kalmar “Al-Rahman” ne ya kasance daidai kuma yake ɗabbaƙuwa
  • ƙididdigar haruffan Suratul Nasi bai yi daidai da ninki adadin lamba 19 ba.
  • Lambobin huruful muƙaɗɗa’atu (Karyayyun haruffa) na surorin ƙalam da ɗaha bai kasance ninki ƙididdigar lamba 19 ba. [13]

Sanin Littafi

Maƙalar “ Kibatshinasi Adadi wa Riyazat ƙur’an” maƙala ce da cikinta aka faifaice bayani game da mujizar Alkur’ani cikin adadi, wannan maƙala cikinta an gabatar da littafi 118 da Sayit ɗin yanar gizo guda 6 ba’arin litattafai da aka gabatar cikin wannan maƙala sun kasance kamar haka:

  • Mu’ujizatul Alkur’anil Al-Karim, Rashad Khalifa.
  • Mu’jizatul Al-Arƙam Wal-Tarƙim fi ALkur’anil Al-Karim, Abdur-Razaƙ Naufal.
  • Min I’ijazil Al-Balagi wal- Adadi lil Kur’anil Alkarim, Dakta Abu Zahra An-Najadi.
  • Al-Mu’ujizatu: Nazariyya Kur’aniyya fil Al-I’ijazil Alkur’ani, Adnan Gazi Al-Rifa’i.
  • I’ijaz Kur’an, Tahlil Amari Huruf Muƙaɗɗa’ti, Rashad Khalifa, tarjamar Sayyid Musɗafa Taƙiyyu Ayatullahi.
  • Ayat Kubr, Mu’ujizeh Jawid Kur’an Kareem, Sayyid Muhammad Fatimi.
  • I’ijazat Hadisati, Ilmiyya wa raƙmiyya fil Alkur’an, Rafiƙ Abu Al-Sa’ud.
  • I’ijazha wa Shegeftihaye Kur’an, Muhammad Ali Rizayi Isfahani wa Muhsin Mullah Kazimi.
  • I’ijaz Kur’an, Sayyid Rida Mu’addab.
  • Partuye az Shegeftiha wa I’ijazi Kur’an az nazare Ilmi Pishguyi wa Adadi, Muhammad Ali Parhiz.
  • Shegeftihaye Adadi Kur’an, Jafar Shaharudi. [14]

Bayanin kula

  1. Yazdani, "Ijazil Adadi wa nazam riyazi Kur'an", shafi na 62; Alvi Moghadam, “Ijazul Kur’an (2)”, shafi na 26.
  2. Norouzi, "Kitabeshinasi Ijazul Adadi wa Riyazi Kur'an", shafi na 84.
  3. Yazdani, “Ijazul Adadi wa Nazam Riyazi Mu’ujizozi Kur’ani”, shafi na 65.
  4. Alvi Moghadam, "Ijazul Kur'an (2)", shafi na 26; Rezaei Esfahani, Fajuheshi dar Ijazil Ilmi Kur'an, 2008, shafi na 219
  5. Rezaei Esfahani, Fajuheshi dar Ilmi ƙur'an, 2008, shafi na 220.
  6. Pahlavan da Shafaƙi, "Arziyabi wa Nakhade nazriyeh Ijazi Adadi ƙur'an Kareem", shafi na 57.
  7. Norouzi, "Kitabeshinasi Ijazi Adadi Kur'an", shafi na 84.
  8. Norouzi, "Kitabeshinasi Ijazi Adadi Kur'an", shafi na 83.
  9. Yazdani, " Ijazi Adadi wa Nazam Riyazi Kur'an", shafi na 65; Norouzi, "Kitabeshinasi Ijazi Adadi wa Riyazi ƙur'an", shafi na 84; Alvi Moghadam, “Ijazi Al-ƙur’an (2)”, shafi na 27.
  10. Nowrozi, "Kiatbeshinasi Ijaz Adadi wa Riyazi Kur'an", shafi na 83.
  11. Pahlavan da Shafaƙi, "Arziyabi wa Nakhade Nazariye Ijaz Adadi Alkur'nil Alkareem", shafi na 57.
  12. Yazdani, "Ijaz Adadi wa Nzam Riyazi ƙur'an", shafi na 83.
  13. Yazdani, "Ijaz Adadi wa Nzam Riyazi ƙur'an", shafi na 65-66
  14. Nowrozi, "Kiatbeshinasi Ijaz Adadi wa Riyazi Kur'an", shafi na 85, 86, 88, 90, 91, 94.

Nassoshi

  • Pahlavan, Mansour da Shafaƙi, Saeed, " Arziyabi wa Nakhade Nazariyeh Ijazi Adadi Kur'an Kareem", a cikin mujalla na binciken Al-ƙur'ani da Hadith bi-ƙuarterly, Autumn and Winter, 2018.
  • Rezaei Esfahani, Mohammad Ali, Fajuheshi dar Ijaz Ilmi ƙur'an, Rasht, Kitab Mobin, bugu na biyar, 2008.
  • Alvi Moghadam, Seyyed Mohammad, "Ijaz ƙur'an (2)", Payam ƙur'an, No. 4, 1373.
  • Nowrozi, Mojtabi, "KItabeshinasi Ijaz ƙur'an Adadi wa Riyazi ƙur'an", Ayane Fajuhesh, Vol. 27, 2013.
  • Yazdani, Abbas, “ Ijaz Adadi wa Nazam Riyazi Kur’an”, Kihan Andisheh, Mujalladi na 67, 1375.