Mu'alla Ɗan Khunais
Mu'alla ɗan Khunais (Larabci: معلى بن خنيس) ya rasu a shekara ta 131 hijira, yana daga cikin Sahabban Imam Sadiƙ (A.S) da kuma ciikin walkilanshi, kuma malamai da yawa sun ce shi Siƙa ne, daga cikinsu akwai Shaik Tusi da Ahmad ɗan Abdullahi Albarƙi kuma yana daga cikin malaman Aƙida da masu rawaito hadisi, kuma da Allama Hilli, kazalika mafi yawancin malaman baya bayannan ma sun ce shi Siƙa ne(Amintacce). Amma wasu malamai kuma sun tafi kan cewa shi rarrauna ne, daga cikinsu akwai Annajashi da Ibn Gada'iri.
Sayyid Khuyi ya ce yana da ruwaya tamanin kuma ya naƙalto mafi yawansu daga Imam Sadiƙ (A.S) ba tare da wani a tsakiyarsu ba, kuma Ibn Muskan wanda ake ganin yana cikin As'habul Ijma ya rawaito ruwaya daga gare shi da Huraiz ɗan Abdulah Assajastani da wasunsu sun rawaito daga gare shi, kuma hadisan daga aka rawaito daga gare shi sun shafi abubuwa daban-dabana, daga cikinsu akwai abin da ya shafi Fiƙihu da Tafsirin Kur'ani kuma yana da ruwayoyi kan Idin Noruz. An kashe shi a shekara ta 131 hijira da umarni Dawud ɗan Ali gwamnan Madina a lokacin Abbasiyawa.
Rayuwarshi
Mu'alla ɗan Kunais Abu Abdullah Kufi Biziz, bawan Imam Sadiƙ (A.S) kuma wakilinshi ne kafin nan ya kasance bawa ne ga Bani Asad,[1] amma litattafan masu rawaito hadisi ba su faɗi tarihin haihuwarshi ba,[2] ya kasance yana sayar da kyalle da yadudduka.[3]
An kasheshi a shekara ta 131 hijira da umarni Dawud ɗan Ali gwamnan Madina a lokacin Abbasiyawa, kuma Imam Sadiƙ (A.S) ya nuna rashin amincewarsa kan kashe shi da aka yi, sai ya ce wa Dawud ka kashe bawana kuma ka ɗauke kuɗi na? Sai Dawud ya ce ba ni ba ne na kashe shi kuma ban ɗauki kuɗinka ba, amma wanda ya kashe shi, shi ne ɗan Sandana, sai Imam ya ce mishi da izininka ya kashe shi kuma ba da izininka ba? Sai Dawud ya ce ba da izinina ba ya kashe shi, sai Imam (A.S) ya ba da umarni da akashe wanda ya kashe Mu'alla.[4]
Amanarshi Kan Rawaito Hadisi
- Maganar malamai ta banbanta kan amincinshi ko rashin aminci kan rawaito hadisi;
Wasu gungun malamai sun yi imanin cewa abin dogaro ne, daga cikinsu akwai: Sheik Ɗusi.[5] Ahmad ɗan Abdullah Albarƙi malamin hadisi ne kuma malamin Shi'a, ɗaya daga cikin fitattun mutane a karni na uku,[6] da Allama Hilli a cikin littafinsa Khulasatul Ak'wal, ya yi gini bisa ra'ayin Sheikh Ɗusi:[7] kuma mafi yawan malamai daga baya su ma sun yabe shi kan rawaito hadisai.[8]
- Wasu gungun malamai su na ganin shi mai rauni wajan naƙalto hadisi, daga cikinsu akwai: Annajashi.[9] Da Ibn Gada'ir, inda yake cewa: “Farkon al'amarinshi ba tsayayye ba ne, sannan ya kira zuwa Muhammad ɗan Abdullah ɗan Hasan (wanda aka fi sani da Nafsuz Zakiyya) don haka ne Dawud ɗan Ali ya kama shi ya kashe shi. kuma ruwayoyinshi madogara ce ga masu wuce iyaka, kuma ni ban ga abin dogara ba kan wani hadisi nashi.[10]
- Sayyid Khuyi cikin littafinsa Mujamul Rijal Hadis, bayan ya nazarci ruwayoyin yabonsa da suka: “...kuma wannan yana nuna cewa shi mutum ne mai gaskiya, don ta yaya maƙaryaci zai cancanci Al-jannah, kuma ya zama wanda Imam Sadik (A.S) ake yabonsa...sai ya ce: Watakila mabubbugar rauninsa shi ne shahararriyar sifarsa ta tsattsauran ra'ayi da guluwi, kuma malaman ahlus-sunna suna jingina da shi don raunana ruwayoyin da aka karbo daga maruwaitan Shi'a.[11] Haka nan Husaini Al-Sa'adi ya yi imani da gaskiyarsa da aminci cikin nakalto hadisi,a inda ya rubuta hakan a cikin littafinsa mai suna (Al-Mu'alla Bin Khunais).
Ruwayoyinshi
Madogaran ruwaya sun ambaci hadisai da dama na Mu'alla ɗan Khunais, musamman a cikin sanannun littafai guda hudu a wurin `yan shi'a.[12] Sayyid Khuyi ya ce yana da ruwayoyi 80.[13] Mafi yawan ruwayoyinshi sun zo ne daga Imam Sadik (A.S) ba tare da wani a tsakaninsu ba.[14]
Ibni Muskan wanda ake gani ɗaya daga cikin As'habul ijma ya ruwaito hadisi daga gare shi.[15] da Huraiz bin Abdullah Assajastani.[16] da Mu'alla bin Usman.[17] Hadisan da aka ruwaito daga gare shi sun zo a fagage daban-daban, daga cikinsu akwai: a fagen fiƙihu.[18] aƙida,[19] ladubban Musulunci,[20] da tafsirin Alkur'ani,[21] kuma yana da ruwayoyi game da Idin Noruz.[22]
Bayanin kula
- ↑ Al-Tusi, Al-Ghaybah, shafi na 347; Al-Tusi, Rijal Al-Tusi, shafi na 304; Al-Saadi, Al-Mu'alla bin Khanis, shafi na 17.
- ↑ Al-Khoei, Mujam Rijal al-Hadith, juzu'i na 19, shafi na 258; Al-Tafrashi, Nakhdul Rijal, juzu'i na 4, shafi na 395.
- ↑ Al-Najashi, Rizal Al-Najashi, shafi na 417.
- ↑ Al-Tosi, Rizal Al-Kashi, shafi na 377.
- ↑ Al-Tosi, Rizal Al-Tosi, shafi na 304; Al-Tusi, Al-Ghaiba, shafi na 347.
- ↑ Al-Barqi, Rijal Al-Barqi, shafi na 25-26.
- ↑ Allamah Al-Hilli, Khulastuyl Ak'wali, shafi na 409.
- ↑ Al-Saadi, Al-Mu'alla bin Khunaisi, shafi na 51.
- ↑ Al-Najashi, Rijal Al-Najashi, shafi na 417.
- ↑ Ibn al-Ghazairi, al-Rijal Li Ibn al-Ghazairi, shafi na 87.
- ↑ Al-Khoei, Majam Rijal al-Hadith, juzu'i na 19, shafi na 269.
- ↑ Duba, misali: Al-Saduq, Min La Yahdurah Al-Faqih, juzu'i na 1, shafi na 410; Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 13, shafi na 126; Al-Tusi, Tahdheeb Al-Ahkam, juzu'i na 6, shafi na 388.
- ↑ Al-Khoei, Mujam Rijal al-Hadith, juzu'i na 19, shafi na 257.
- ↑ Duba, misali: Al-Saduq, Min La Yahdurah Al-Faqih, juzu'i na 1, shafi na 410; Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 13, shafi na 126; Al-Tusi, Tahdheeb Al-Ahkam, juzu'i na 6, shafi na 388.
- ↑ Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 354.
- ↑ Al-Barqi, Al-Mahasin, juzu'i na 1, shafi na 255.
- ↑ Al-Barqi, Al-Mahasin, juzu'i na 1, shafi na 235.
- ↑ Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 3, shafi na 336.
- ↑ Al-Barqi, Al-Mahasin, juzu'i na 1, shafi na 255.
- ↑ Al-Barqi, Al-Mahasin, juzu'i na 2, shafi na 561.
- ↑ Al-Qummi, Tafsirul Qummi, juzu'i na 1, shafi na 222; Al-Ayyashi, Tafsirul Al-Ayyashi, juzu'i na 2, shafi na 255.
- ↑ Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 56, shafi na 93.
Nassoshi
- Ibn al-Ghadhairi, Ahmad bin Hussein, Al-Rijal li Ibn al-Ghadha'iri, bugun: Muhammad Reda al-Jalali, Qum, Darul-Hadith, 1422 AH/1380H.
- Al-Barqi, Ahmed bin Abdullah, Rijal Al-Barqi, Tehran, Tehran University Press, D.T.
- Al-Barqi, Ahmad bin Muhammad, Al-Mahasin, bugun: Jalaluddin Muhaddith, Kum, Darul Kutub al-Islamiyyah, 1371H.
- Al-Tavarshi, Mustafa, Nakhzul Rijal, Qum, Mu'assasar Al-Baiti, Amincin Allah ya tabbata a gare su, don Rayar da Al'adunmu, d.
- Al-Khoei, Abu Al-Qasim, 'Mujam Rijal Hadith, Al-Najaf Al-Ashraf, Al-Khoei Islamic Foundation, D.T.
- Al-Saadi, Hussein, Al-Mu'alla ibn Khunais, Qom, Darul-Hadith, 1383H.
- Al-Saduq, Muhammad bin Ali, Man Lah yahaduruhul fakihu, Tehran, Saduq, 1367H.
- Al-Tusi, Muhammad bn Al-Hasan, Ghaiba, editan: Ebad Allah Al-Tahrani da Ali Ahmad, Qum, Mu'assasar Ilimin Musulunci, 1411H.
- Al-Tusi, Muhammad bin Al-Hasan, 'Tahdheeb Al-Ahkam, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1407H.
- Al-Tusi, Muhammad bin Al-Hasan, Rijalul Tusi, Qum, Mu'assasa Mawallafin Musulunci, 1415H.
- Allamah Al-Hilli, Al-Hassan bin Yusuf bin Mutahhar, 'Khulasatul Ak'wal an marifatil Rijal, editan: Jawad Al-Qayumi, D.M., Mu'assasar Daba'ar Musulunci, bugu na daya, 1417H.
- Al-Ayyashi, Muhammad bin Mas'ud, 'Tafsir Al-Ayyashi, Tehran, Bugun Kimiyya, 1380H.
- Al-Qummi, Ali bin Ibrahim, 'Tafsir Al-Qummi, edited by: Tayyab Musawi Jazairi, Qum, Darul Kitab, 1404H.
- Al-Kulayni, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, bugun: Ali Akbar Al-Ghafari da Muhammad Al-Akhundi, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1407H.
- Al-Kulayni, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, Qom, Darul Hadith, bugun farko, 1387H.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Gidan Revival Heritage Arab, 1404H.
- Al-Najashi, Ahmed bin Ali, 'Nakzul Rijal, Qum, Mu'assasa Mawallafin Musulunci, bugu na 6, 1418H.