Misalan Da Aka Kawo Cikin Kur'ani

Daga wikishia

Misalsalan Kur'ani, (Larabci: الأمثال القرآنية) suna daga wallafe-wallafe na tushe da aka yi cikin bayanin ilimin kur'ani da ma'anoninsa, haka nan ana kiransu da sunan misalsalan kur'ani cikin mu'ujizar bayani, a cikin riwayoyin shi'a an bada kulawa ta musamman kan waɗannnan wallafe-wallafe tare da umarni kan zurfafa tunani cikin tabbatattun abubuwa da suka zo cikin kur'ani. A ra'ayin malaman tafsiri, babban hadafi da manufa daga bayanin misalsalai a cikin kur'ani shi ne sauƙaƙa bayanan kur'ani da hankali ke riskarsu tare da rina su da rinin abubuwa da ake iya riskarsu da mariskai domin gama garin mutane su iya fahimtar kur'ani cikin sauƙi. Malaman tafsiri sun yi magana kamar da larurar samuwar misalsalan kur'ani ƙari kan dalilai da jidali mafi kyawu da kuma wa'azi domin fahimtar da gama garin mutane, an ce misalan kur'ani sun ɗauke da haduffa na tarbiyya kuma an yi ishara zuwa ga dokoki da kyawawan halaye da kuma samfura da misalsalai da ake iya gani da idanu.

Game da misalsalan cikin kur'ani akwai minhaji guda biyu, wasu ba'arin malamai suna ganinsu matsayin kamantawa ce kaɗai domin kusanto bayanai na hankali zuwa ga kwakwale. Kishiyar wannan magana wasu sun yi amanna kan cewa babu wata maganar kamantawa ko kuma amfani da ma'ana ta aro a cikin misalsalan kur'ani, lallai su misalsalai suna bayani kan samuwar misali na haƙiƙa kuma tabbatacce. a ra'ayin malaman tafsiri, misalan cikin kur'ani ta fuskacin "fayyace bayanin sinadaran kamanceceniya" da ta fuskacin "Adadin ɗaiɗaiku da aka kamanta su" da kuma fuskacin "Fuskar kamanceceniya" suna da mabambantan rabe-rabe, akwai siffofi da aka yi bayani kan misalan kur'ani wurare misalin "Tattaro komai da kuma faɗaɗuwa", "Sauƙaƙawa da kuma sauƙin fahima" wani ɓangare ne na su.

Cikin fagen misalsalan kur'ani an yi rubuce-rubuce masu tarin yawa , daga jumlarsu za a iya ishara da littafin Raudatul Al-amsal (Fi Al-amsal Al-kur'an Al-karim) talifin Ahmad ɗan Abdullahi Al-kuzkanani Al-najafi.

Misalsalai Ta Fuska Biyar Na Bayanin Kur'ani

Kan asasin wata ruwata daga Annabi (S.A.W), buga misali cikin ɗaya ne daga cikin fuskoki gua biyar.[1] a mahangar masu dandaƙe bincike, buga misalsalai cikin kur'ani, a kankin kansu za su iya taka rawa mai yawan gaske daga ɓangaren ilimi, kyawawan halaye, tarbiya da zaman takewa.[2] ba'ari daga masu nazarin kur'ani suna lissafa misalsalan kur'ani ɗaya ne daga cikin misdaƙan mu'ujiza ta bayani.[3]

Imam Sajjad (A.S):
Ya Allah! ka yi salati ga Muhammad da iyalansa, ka sanya kur'ani ya kasance mai ɗebe mana haso da firgici cikin duhun dare… domin zukatanmu suka gane abubuwan al'ajabinsa, da kuma misalsalansa masu ban mamaki da ban al'ajabi waɗanda tsaunuka masu tsauri basu iya ɗaukar su ba, ka tsugunar da su cikin zukatanmu.[4]

Cikin riwayoyin shi'a an himmatu da batun misalan cikin kur'ani; alal misali a cikin wata riwayada aka naƙalto daga Imam Ali (A.S) ɗaya daga cikin fa'idojin buga misalsalai a cikin kur'ani, wa'aztuwa daga misalan da aka ambata.[5] a wasu wuraren daban an ajiye misalsalan kur'ani kusa da wasu hususiyoyi misalin shiryarwar kur'ani, da isar da saƙo a bayyane.[6] bisa wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Baƙir (A.S), an saukar da kur'ani kan mihiwari guda huɗu ɗaya daga cikinsu ya kasance sunnoni da misalsalai da a aka ambata cikin kur'ani.[7] cikin wani hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S) an rawaito cewa misalan da aka buga cikin kur'ani suna ɗauke da fa'idoji; bayan kun yi dandaƙe tunani cikinsu ku sanya lura cikin ma'anoninsu kada ku yi sakaci cikinsu.[8]

Rawar Da Misalsalai Suke Takawa Cikin Fahimtar Kur'ani

Jawadi Amoli, malamin tafsiri ya rubuta saƙon kur'ani da manufarsa ta duk duniya kuma isar da saƙonsa zuwa ga bakiɗayan mutane har zuwa ranar sakamako. Da wannan ne ƙari kan dalili , jidali mai kyau da kuma wa'azi an buga misalsalai domin sauƙaƙawa mutane fahimtar kur'ani.[9] a bayanin Allama Ɗabaɗaba'i, domin bayanin maɗaukakan bayanan kur'ani babu abin da ya rage sai amfani da buga misali domin gama garin mutane sun fi fahimtar abubuwa ta wannan hanya.[10] Jawadi Amoli tare da jingina da ayar:

«وَ تِلْکَ الْأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ ۖ وَمَا یَعْقِلُهَا إِلَّا الْعَالِمُونَ؛

Waɗancan misalai ne da muke bugawa domin mutane babu masu hankalta da su sai masu ilimi,[11] malamin yana cewa misalai kamar gada je da mutane zai bi ta kanta ya cirata da ilimi hissi (ilimin na mariskai) zuwa ga ilimi na hankali, daga nan kuma su cirata su shiriya zuwa ilimi na shuhud na zuciya.[12] Sanin Ma'anar Misalsalai Allama Ɗabaɗaba'i yana ganin misalsalai matsayin wasu tabbatattun ƙissoshi ko kuma na jeka nayika , waɗanda mai faɗarsu yake amfani da su sakamakon kamanceceniyarsu da maganarsa domin samar da kammalalliyar fahimta sauƙaƙaƙƙa a kwakwalen masu saurarensa.[13] Jawadi Amoli yana ganin hususiyar misalsalai cikin taƙa muhimmiyar rawa wajen sauƙaƙa nauyayan bayanai da rina su da rinin abubuwa da ake iya gani domin sauƙaƙawa masu saurare fahimtarsu.[14] a imanin malamin buga misalsalai bai kasance daga minhaji da hanya irin ta manɗiƙi ba, buga misalsalai ana yinsu kaɗai domin sauƙaƙa fahimtar bayanai.[15]

Mahanga Guda Biyu Game da Misalan Cikin Kur'ani

Akwai mahanga guda biyu game da bayani kan misdaƙan misalan kur'ani:[16] 1. Misalai da suka zo cikin kur'ani sun kasance zallan kamantawa, kuma an yi amfani da su ne domin kusanto da kwakwalen zuwa ga bayanan kur'ani. 2. Kwata-kwata babu kamantawa ko ma'anar ta aro cikin misalan kur'ani , misalsalan kur'ani bayani ne kan tabbatuwar waɗannan abubuwa da aka buga misalinsu.[Tsokaci 1]

Ba'arin malaman tafsiri na shi'a misalin Allama Ɗabaɗaba'i[17] da Abdullahi Jawadi Amoli[18] da kuma wasu ba'ari daga malaman tafsiri na ahlus-sunna misalin Muhammad Abduhu[19] sun tafi kan cewa ayoyi da suke da alaƙa da ma'ad da farkon halitta misalin ayar halittar mutum, sujjadar mala'iku, saɓawa umarni da Iblis ya yi da .... duk da cewa suna da asalai da tushe daga al'amari ne na halitta da haƙiƙa ta gaibu amma tare da hakan a zahiri suna ɗauke da bayani na haƙiƙa ba na jeka nayika ba, amma bakiɗayansu wani misali ne rufaffe na halitta, za a iya kiran wannan nazariyya da sunan "Misali na halitta".[20]

Hususiyoyin Misalsalan Kur'ani

Game da siffofi da hususiyoyin misalan kur'ani an yi ishara zuwa ga abubuwa misalin "Tattarowa da faɗaɗuwa", "Sauƙaƙa da sauƙin fahimta", "Suranta ra'ayoyi da raya lafuzza" da kuma "Amfani mabayyanai da halittu na ɗabi'a".[21] Alal misali an yi ishara da hususiyyar "Sauƙaƙa da sauƙin fahimta" da kuma wurare kamar misalin misalta kore yiwuwar shigar kafirai aljanna da misalin rashin yiwuwar ƙetarawar raƙumi ko kakkaurar igiya ta cikin ramin ƙofar allura"[22] da kamanta gulma da misalin "Cin naman Ɗan uwa da ya mutu"[23] da kamanta "Mutumin da baya amfani da iliminsa da misalin Jaki[24] da yake dakon litattafai da bai san abin da yake ɗauke da shi ba"[25]

Haduffa Da Kufaifayin Tarbiyya Daga Misalan Kur'ani

Misalan kur'ani suna ɗauke da hadufffa da kufaifayin tarbiyya; daga jumlar tarbiyya ta hanyar "Mayar da hankali zuwa ga kyawawan ɗabi'u da halaye masu inganci", "Suranta tabbatattun abubuwa na gaibu cikin zirin al'amura da ake iya gani da taɓawa", "Gabatar da samfura da misalsalai da idanu ke iya gani" da kuma "Motsa ƙarfin tunani da basirar mutane".[26] alal misali, game da hadafin tarbiyya kan asasin mayar da hankali zuwa ga kyawawan ɗabi'u, Allah a cikin aya ta 261 suratul baƙara ya kamanta masu ciyarwa da misalin kwayar shuka, amma kishiyarsa a cikin aya ta 264 suratul baƙara sai ya kamanta ciyarwa da ake yinta haɗe da gori da cutarwa da misalin falalen dutse da yake ɗauke da turɓaya a samansa wanda da farawar saukar yayyafin ruwan sama sai ya wanke wannan ƙasa ta ɓace ɓat.[27] Allama Ɗabaɗaba'i marubucin tafsirin Al-mizan cikin bayanin haduffa misalsalai na kur'ani a cikin tafsirin aya 39 suratul furƙan «وَكُلًّا ضَرَبْنا لَهُ الْأَمْثالَ؛ (Kuma ko wane guda daga gare su mun buga masa misalai) da ma'anar tunatarwa, wa'azi da gargaɗi.[28]

Sanin Littafi

A fagen misalai na kur'ani an yi rubuce-rubuce masu yawa, ba'arinsu su ne kamar haka:

  • Raudatul Al-amsal (Fil Aal-amsal Al-kur'anil Al-karim), talifin Ahmad Ɗan Abdullahi Al-kuzkanani Al-najafi, an buga shi shekarar 1325 hijira ƙamari..[29]

Wannan littafi an yi bahasi da bincike kansa cikin maƙalar «روضه الامثال»،.[30]z

  • [[30]://www.gisoom.com/book/1269616/کتاب-امثال-قرآن/ امثال قرآن]،, talifin Ali Asgar Hikmat (cibiyar Bunyad kur'an tehran ta buga wannan littafi)
  • Amsalul Al-kur'an, talifin Isma'il Isma'ili (bugun farko ya kasance a shekarar 1369 ta hannun kamfanin Usweh, an tsara shi kan asasi da tushen littafin Amsal kur'an da tauzihatul Suyuɗi cikin littafin Al-itƙan.)
  • تمثیلات قرآن، ویژگیها، اهداف و آثار تربیتی آن،, talifin Hamid Muhammad Ƙasimi (Hususiyoyin wannan littafi da aka buga a shekarar 1382 hijira shamsi sun kasance daga kallon misalai na kur'ani daga zawiyyar mas'aloli na tarbiya).

Bayanin Kula

  1. Tusi, Al-Amali, 1414H, shafi na 357.
  2. Muhammad Qasimi,Tamsilat Alqur’an, 1382H, shafi na 50.
  3. Al-Bayanou,Darbul Al-Amsal fi Alkur’an, aya, shafi na 39; Suyuti, Mu’tarak al-Azār fī I’jizil Al-Kur’ani, Beta, juzu’i na 1, shafi na 464.
  4. Al-Sahifa Al-Sajjadiyyah, 1376H, shafi na 178.
  5. Tamimi Amidi, Gharar al-Hikam wa Durar al-Kalam, 1410 AH, shafi 572.
  6. Ayyashi, Tafsirul Ayyashi, 1380 AH, shafi na 7.
  7. Ayyashi, Tafsir al-Ayyashi, 1380 AH, juzu'i na 1, shafi na 9.
  8. Muhammad Ray Shahri, Shanakht Nameh Qur’an, 1391 AH, juzu’i na 4, shafi na 397.
  9. Javadi Amoli, Tasnim, 1387 AH, juzu'i na 2, shafi na 510.
  10. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 3, shafi na 62.
  11. Suratul Ankabut, aya ta 43.
  12. Javadi Amoli, Tafsir Tasnim, 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 329.
  13. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 386.
  14. Javadi Amoli, Tafsir Tasnim, 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 327.
  15. Javadi Amoli, Tafsir Tasnim, 1378 AH, juzu'i na 8, shafi na 582.
  16. Javadi Amoli, Tafsir Tasnim, 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 332.
  17. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 132-133.
  18. Javadi-Amoli, Kur’ani Hakim az manzare Imam Reza, 1382, juzu’i na 5, shafi na 397.
  19. Rashidreza, Tafsirin Kur'an al-Hakim, 1366H, juzu'i na 2, shafi na 190.
  20. نگاه کنید به: محمدی پارسا، «تأمّلی بر رویکرد تمثیلِ تکوینی در تبیین آیات خلقت انسان».
  21. Duba: Mohammad Qasmi, Tamthilat Qur'an, 1382, shafi na 97-57.
  22. Duba: Suratul A'araf, aya ta 40.
  23. Suratul Hajrat, aya ta 12.
  24. Suratul Juma, aya ta 5.
  25. Muhammad Qasimi, Tamsilat Alqur’ani, 1382H, shafi na 62.
  26. Mohammad Qasmi, Tamsilat Kur’ani, 1382, shafi na 104-244. ↑
  27. Duba: Mohammad Qasmi, Tamthilat Qur'an, 1382, shafi na 127-128.
  28. Tabatabaei, Al-Mizan, Ismailian Charters, juzu'i na 15, shafi na 218.
  29. طهرانی، الذریعة الی تصانیف الشیعه، ۱۴۰۸ق، ج۱۱، ص۲۸۸؛ «روضه الامثال»، سایت کتاب بدیا.
  30. نگاه کنید به: رضایی کرمانی، نقد و بررسی کتاب تفسیری «روضة الأمثال».

Tsokaci

  1. Bambance-bambancen da ke tsakanin wadannan ra’ayoyi guda biyu an san shi a can, misali a cikin Alkur’an, An kwatanta fuskokin mutane da "jakuna" ko "karnuka"; Yanzu, bisa ga fahimtar farko, suna da hali kama da halayen waɗannan dabbobi. Amma bisa ra'ayi na biyu, wannan kamanatawa yana bayyana gaskiyar hakikaninsu da za ta bayyana a tashin kiyama, (Javadi Amoli, Tafsir Tasnim, 1378, juzu'i na 2, shafi na 332.)

Nassoshi

رضایی کرمانی، محمدعلی، نقد و بررسی کتاب تفسیری «روضة الأمثال»، نشریه مطالعات تفسیری، دوره۹، ش۳۴، ۱۳۹۷ش.

  • Al-Bayanuni, Abd al-Majid, Zarb al-Amsal fi Qur'an, Damascus da Beirut, Darul Qalam da Darul Shamiya, 1411H.
  • Al-Meidani, Abd al-Rahman Hasan Hanbakah, "Amsal al-Qur'an wa Sur Man Adba Al-Rafi'i", Damascus, Dar al-Qalam, 1412H.
  • Ayashi, Muhammad bin Mas'ud, Tafsir Al-Ayyashi, Sayyid Hashem Rasouli Mahallati, Tehran, Mawallafin Kimiyya, 1380 A.D.
  • Jahanbakhsh, Sawaqib,Tashbihat wa tamsilat qur'an, Tehran, Nash Qu, 1376.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Hedayat dar Kur'ani, Kum, Gidan Bugawa na Esra, 2008.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Kur'ani az manzare Imam Riza (a.s.), Qum, Esra Publishing House, 1382.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tafsir Tasnim, Qum, Esra Publishing House, 1378.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tauhidi, Kum, Gidan Bugawa na Esra, 1390.
  • Marifat, Muhammad Hadi, Amozesh Ulum Qur'an, Qom, Farhangi Publications Foundation, Al-Tamheed, 1387 AH.
  • Muhammad Qasimi, Hamid, Tamsilat qur’ani, Qum, Wallafa Aswa, 1382H.
  • Muhammad Ray Shehri, Muhammad, Shanakhtnameh Qur'an Bar Payeh Qur'an wa Hadith, Qom, Dar Al-Hadith, 1391 AH.
  • Rashidreza, Muhammad, Tafsir Kur'an al-Hakim (wanda aka fi sani da Tafsirin Al-Manar), Bija, Bina, 1366H.
  • Suyuti, Abd al-Rahman bin Abi Bakr, Mu’trak al-Iqraan fi Mu’ujizar Kur’ani, Beirut, Darul Fikr al-Arabi, Beta.
  • Suyuti, Abd al-Rahman bin Abi Bakr, al-Itqan fi Ulum al-Qur’an, wanda Sayyid Mahdi Haeri Qazvini ya fassara, Tehran, Amirkabir Publications Foundation, 1363H.
  • Tabatabai, Seyyed Muhammad Hossein, Al-Mizan, Publisher of Ismailian Publications, Beta, Beja.
  • Tabatabai, Seyyed Muhammad Hussein, Al-Mizan, Chap Najm, Qom, Islamic Publishing Library, 1417 BC.
  • Tamimi Amadi, Abdul Wahid bin Muhammad, Ghurar al-Hikam wa Darr al-Kalam, Mahdi Rajai, Kum, Dar al-Kitab al-Islami, ya gyara, Ch2, 1410 AH.
  • Tehrani, Aqa Bozorg, Al-Dhari’a, Qum and Tehran, Book of Faroushi Islamiyya and Ismailian, 1408 A.H.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Amali, Qum, House of Culture, 1414 BC.
  • محمدی پارسا، عبدالله، «تأمّلی بر رویکرد تمثیلِ تکوینی در تبیین آیات خلقت انسان»، دوره ۱۵، ش۳، مهر ۱۳۹۴ش.

{[end}}