Mikewar Imam Mahadi (A.F) (Larabci: قيام الإمام المهدي (ع)) wani motsi ne daga Imami na Sha biyu bayan bayyanar sa domin kafa Adalci a duniya baki daya, babu wanda ya san hakikanin lokacin da wannan motsi da yunkuri zai kasance, a modagarar riwayoyi, mikewar sa za ta kasance ta fara bulla ne a masallacin Harami a garin Makka Mukarrama zai dauki tsawon watanni takwas Mahallin Asali zai kasance kasar Iraki, Imam Hujja (A.S) a wannan yanki zai tarwatsa rundunar Sufyani ya yi nasara a kansu.

Ya zo a riwaya ce akwai mutane 313 da za su kasance kebantattun Sahabban Imam Zaman (A.F) kuma Mataimaka sojoji da zai yaki tare da su, amma adadin wanda zasu yi tarayya cikin wannan yunkuri ya ninninka adadin kebantattun Sahabbansa, yawancin su Samari ne, sannan hatta Hazrat Isa (A.S) shima zai shiga wannan yunkuri zai taimakawa Imam Mahadi, a wata riwayar ma ya zo cewa wasu ba'arin Annabawa da Waliyyan Allah misalin Mutanen Kogo (Ashabul Kahfi) da Yusha'u Ibn Nun (A.S) da Muminu Alu Fir'auna, Salmanul Farisi da Abu Dujanatu Ansari da Malikul Ashtar Annaka'i duk za su yi Raja'a su dawo duniya su taimaka masa cikin wannan yunkuri. Wasu ba'arin Malamai bisa dogara da wasu riwayoyi sun imani cewa Makamin Imamul Mahadi a wannan yunkuri wata Takobi ce tare da mu'ujizar da Allah ya sanya cikin wannan Takobi zai karya Makiyansa da ita, wasu kuma sun tafi kan cewa Makaman zamani na kimiyya za su tsaya su dena aiki a lokacin yunkurin sa ta hakan zai samu nasara da Takobinsa, amma wasu kuma sun tafi kan cewa ita wannan Takobi da ta zo a a riwaya ba komai bace face nuni da ishara yunkuri na Soja.

Matsayi da muhimmanci

Mikewar Imamul Zaman (A.S) wata ishara ce kan wani motsi da Imami Ma'asumi na goma sha biyu bisa imanin `yan shi'a wanda zai kasance bayan bayyanarsa domin tabbatar da adalci a fadin duniya,[1] duk da cewa mikewar da yunkurinsa yana zuwa da ma'ana guda daya,[2] sai dai cewa fitaccen Masanin shi'anci Malam Murad Sulaimiyan yana cewa: wadannan batutuwa ne guda biyu da suke da banbanci da juna shi Yunkuri yana zuwa ne bayan bayyanar sa.[3] Ya zo a riwaya kan ishara kan yunkurinsa (A.S) a ciki sai aka yi amfani da Kalmar fitowa da,[4] sannan a wata riwayar daga littafin Alkhisal na Shaik Saduk cewa yunkurin Imamul Zaman da Raja'a da ranar Alkiyama ana kirga su daga ranakun Allah,[5] saboda a wasu riwayoyi ya zo cewa yunkurin Imamul Zaman (A.S) zai dau lokaci har zuwa wata takwas,[6] Imam zai tabbatar hukumar adalci a fadin duk duniya.[7]

Zamani da tsawon lokacin da zai yi

Sani da tantacce hakikanin lokacin da Imamul Mahadi (A.S) zai yunkura yana da wahalar gaske,[8] bai zama bayyane ba, amma sai dai cewa wasu ba'ari daga kususiyya zamanin yunkuri da suka zo a riwayoyi anyi bayanin su; daga cikinsu ya zo cewa wannan yunkuri zai kasance a Shekaru da suke tanka ba tagwai kuma zai kasance a ranar Ashura Ranar Asabar,[9] Sayyid Muhammad Sadar Mawallafin littafin Tariku Ma Ba'ada Zuhur, ya tafi kan cewa idan aka cire riwayar ranar Ashura sauran riwayoyin Isnadinsu yana da rauni.[10] Dangane da tsawon lokacin da yunkurin zai dauka ya zo a riwaya cewa zai kai har tsawon wata takwas[11] yana gwabzawa da Makiya.

Wuri

Kan asasin galibin riwayoyi wannan yunkuri zai fara daga garin Makka,[12] daga cikin riwayoyin akwai riwayar da Shaik Muhammad Ibn Yakubu Kulaini ya kawo cikin littafin Alkafi da Kuma Shaik Nu'umani cikin littafin Algaiba,[13] a cikin riwayar da ta zo cikin littafin Uyunul Akbar Rida, na Shaik Saduk ya zo cewa garin Tahama[14] shi ne Mahallin yunkurin nasa sannan shi Tahama daya da cikin sunayen garin Makka ne.[15] A cikin wata riwayar yunkurin zai fara ne da wani kauye da ake Kur'atu da Kur'atu,[16] sai dai cewa Masana Tarihin Imam Mahadi (A.S) sun yi watsi da wannan magana, sun ce akwai yiwuwa an samu kuskure cikin riwayar da ta cakuda yunkurin Imamul Zamani da fitowar Yamani,[17] an kirkiri wannan riwaya ne domin karfafa Jabun Mahadi na Daular Fatimiya da ta kasance a Arewacin Afrika.[18] Kamar yanda ya zo cikin littafin Daneshnameh Imam Mahadi (A.S) kan asasin wata riwaya, mutum dubu goma za su yi masa Mubaya'a a garain Makka kuma zai aika da Sojoji zuwa garin Madina, a wata riwayar kuma shi da kansa ne zai tafi Madina, bayan nan sai ya tafi kasar Iraki domin fara gwabzawa da Sufyani.[19] Haka ya zo a riwaya dangane da Fatahu[20] Rum da Dailama da Indiya da garin Kabul da Kazar cewa Hazrat Isa (A.S) zai shiga cikin rundunar sa a Baitul Mukaddas,[21] karshen gwabzawa zai kasance garin Kufa domin nan ne cibiyar Daular Imam Zaman (A.F)[22]

Ta yaya farawar zata kasance

Kan asasin riwayoyi da suka zo, hakika Imam Mahadi (A.F) zai yi sallar Isha a Masallacin Harami,[23] bayan idar da sallar ne yunkurin zai fara daga Kusa da Ka'aba, hakika zai kasance tare da kayayyakin da ya gada daga Annabi (S.A.W) daga Takobi Rawani da Sanda da Tuta,[24] a Rukunu da Makam Ibrahim ne zai fara karbar mubaya'a daga mataimakansa.[25] Shaik Saduk ya nakalto cewa; Imamul Zaman tareda Rakiyar Sahabban sa mutum 313 za su bayyana a Masallacin Harami zai bude hudubarsa da wannan ayar ta 86 Suratul Hudu daga Kur'ani Mai girma:

بَقِيَّتُ اللَّهِ خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ

Ragowar Allah shi ne Mafi alheri gare ku idan kun kasance Masu Imani. Bayan nan tare da bayanin wannan jumla:

«أَنَا بَقِيَّةُ اللَّهِ فِي أَرْضِهِ وَ خَلِيفَتُهُ وَحُجَّتُهُ عَلَيْكُمْ»

Ni ne Bakiyatullahi a cikin kasar sa ni ne Halifan sa ni ne Hujjar sa a kanku.[26] Zai bayyana kan matsayin misdakin wancan ayar a yayin da adadin Mataimakan sa ya kai mutum dubu goma a lokacin zai fara yunkuri.

Makami

Kan asasin dogara da riwaya Makamin Imam (A.S) zai kasance Takobi,[27] kan haka wasu suka tafi kan cewa duk wani Makamin fasaha da kimiyya na zamani zai daina aiki yayin yunkurin sa, wasu kuma sun tafi kan cewa sakamakon yakokin da za su kasance gabanin bayyanar sa ne dukkanin Makaman zamani za su kare, wasu kuma sun yi imani da cewa Sakamon mu'ujizar da Allah ya ajiye cikin Takobin sa ne zai sanya ta fifice dukkanin wani Makamin zamani.[28] An samu wasu da suka sabawa duk ra'ayoyin da aka kawo su sun tafi kan cewa Kalmar Takobi ta zo ne da kinaya da ishara kan karfin Soja[29] da zai gwabza yaki da Makiya, ba wai dole ne ya zama sai ya yi amfani da Takobi da muka sani ba.[30]

Sojojinsa

Daya daga cikin Hususiyar Mayakan sa daga fuskanin adadi, hususiya ta daidaiku da fitattun mutane sanannu da zasu kasance tare da shi an anbace su cikin riwaya.

Adadi

Adadin Mataimakan Imam (A.F) kamar yanda ya zo a galibin riwayoyi adadin ya kai mutum 313 gwargwadon adadin Sahabban Annabi (S.A.W) a Yakin Badar,[31] sai dai cewa a wata riwayar adadin yah aura haka kamar misalin dubu goma,[32] zuwa dubu goma sha biyu har a wata ma ya kai dubu goma sha biyar,[33] kan wannan asasin wasu ke cewa Adadin Sahabbansa mayakansa ya haura 313, kadai mutum 313 za su kasance kebantattun Sahabbansa Mayakansa.[34]

Hususiya ta daidaiku

A cikin littafin Algaiba wallafar Shaik Nu'umani cikin wani hadisi ya zo cewa galibin Mayakansa matasa ne wasu adadi ne kadan daga[35] cikinsu suke Tsofaffi, haka kuma zaka same su Jarumai karfafa, masu raya dare da ibada, masu tsayu kyam kan digadigansu.[36]

Sanannun mutane

Kan asasim dogara da riwaya Hakika Hazrat Isa (A.S) shima zai kasance cikin Mataimakansa,[37] haka kuma wasu jama'a daga Waliyyan Allah da suka mutum a baya za su dawo duniya , daga cikin wasu da sunan su ya zo a riwaya sune: Abu Dujana Ansari, Muminu Alu Fir'auna da Malikul Ashtar da Salmanul Farisi.[38]

Bayanin kula

  1. Salimian,Darasnameh Mahdaviyat, 2009, juzu'i na 3, shafi na 171-170.
  2. Sadr, Mausuatu Mahdawiyya, 1412 BC, Part 3 (Tariku ma baada zuhur), shafi na 195.
  3. Salimian,Darasnameh Mahdaviyat, 2009, juzu'i na 3, shafi na 176
  4. Sheikh Sadouq, Kamal al-Din, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 377 da 378
  5. Sheikh Sadouq, Khasal, 1362, juzu'i na 1, shafi na 108.
  6. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 164, h5.
  7. Sadr, Mausuatu Mahdawiyya, 1412 BC, Part 3 (Tariku ma baada zuhur), shafi na 449
  8. Sadr, Mausuatu Mahdawiyya, 1412 BC, Part 3 (Tariku ma baada zuhur), shafi na 207
  9. Sadr, Mausuatu Mahdawiyya, 1412 BC, Part 3 (Tariku ma baada zuhur), shafi na 212-213
  10. Sadr, Mausuatu Mahdawiyya, 1412 BC, Part 3 (Tariku ma baada zuhur), shafi na 213
  11. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 164, h5.
  12. Mohammadi Rishahri wa Digaran, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 8, shafi na 199.
  13. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 231, h3; Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi 313, 315
  14. Sheikh Saduq, Uyun Akhbar on Al-Ridha, 1378 Q. Part 1, shafi na 62-63.
  15. Mohammadi Rishahri wa Digaran, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 8, shafi na 199
  16. Erbali, Kashf al-Gumma, 1381 AH, juzu'i na 2, shafi na 469; Faiz Kashani, Kitab al-Wafi, 1406 AH, juzu'i na 2, shafi.467.
  17. Mohammadi Rishahri wa Digaran, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 8, shafi na 199
  18. Mohammadi Rishahri wa Digaran, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 8, shafi na 199
  19. Mohammadi Rishahri wa Digaran, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 8, shafi na 201
  20. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 235, h. 22.
  21. Salimian, Darasnameh Mahdaviyat, 2009, juzu'i na 3, shafi 179.
  22. Salimian, Darasnameh Mahdaviyat, 2009, juzu'i na 3, shafi 179
  23. Mohammadi Rishahri wa Digaran, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 8, shafi na 200-201.
  24. Nomani, Al-Ghabiyah, 1397 AH, shafi na 270.
  25. Sheikh Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 454; Mofid, Ershad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi.379.
  26. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1395 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 331
  27. Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 8, shafi na 50, h13; Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 1, shafi na 321-322.
  28. Salimian,Darasnameh Mahdaviyat, 2009, juzu'i na 3, shafi 176.
  29. Makarem Shirazi, hukumat jahani mahdi, 1380, shafi na 251-253.
  30. Makarem Shirazi, hukumat Imam Mahdi Jahani, 1380, shafi na 251.
  31. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 654, h20 da 21; Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 314-315, H7,8,9; Sadouq, Al-Khasal, 1362, juzu'i na 2, shafi.649, h43; Tabari,
  32. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 314, h2; Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi.654, h20.
  33. Syed bin Tawoos, almalahim walfitan, 1398 s, shafi na 64-65.
  34. Zamani, Mahdi: Ayineh Fayambaran, 1396, shafi na 219; Qaraati, sharhu du'u iftitahi sharef, 1392, shafi na 111; Samadi, Tarihin Imam Mahdi, 1393, shafi na 190.
  35. Nomani, Al-Ghabiyah, 1397 AH, shafi na 315-316, H10.
  36. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 52, shafi na 386
  37. Sayyid ibn Tawus, Al-Malahim wa al-Fitn, 2010, shafi.
  38. Hurru Ameli, Isbatu Hudat, 1425Q, juzu'i na 5

Nassoshi

  • Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghamma fi Marafah al-Imam, tare da gabatarwar Jafar Sobhani Tabrizi da gefen Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, Tabriz, Makarantar Bani Hashemi, 1381H.
  • Har Amili, Muhammad Bin Hasan, isbat hudat bin nususi walmujizat , Beirut, A'lami, bugu na farko, 1425H.
  • Zamani, Sayyid Hassan, Hazrat Mahdi Ayineh Fayambaran, Qum, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation, 1396.
  • Salimian, Khodamorad, Darasnameh Mahdaviyat, Qum, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation, bugu na biyu, 2009.
  • Sayyid Ibn Tavus, Al-Malaham wa Al-Fattan fi Zahor al-ghaib al-Mantazhar, Qum, Razi Publications, bugu na 5, 1398 AH/1978 miladiyya.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Al-Khasal, gyara/bincike daga Ali Akbar Ghafari, Qum, Qum seminary community, bugun farko, 1362.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza (AS), Mahdi Lajurdi, Tehran, Nash Jahan, bugun farko, 1378H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tammam al-Naimah, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya ya gyara/bincike, bugu na biyu, 1395H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ghaibah, Ebadullah Tehrani da Ali Ahmad Naseh, Qum, Dar al-Maarif al-Islamiya suka gyara/bincike, bugu na farko, 1411H.
  • Sadr, Seyyed Muhammad, Al-Masu'a al-Mahdawiyyah, juzu'i na 3 (Tarihin Bugawa), Beirut, Dar al-Taarif, 1412 AH/1992 Miladiyya.
  • Samadi, Qanbar Ali, Tarihin Imam Mahdi, Qum, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation, 1393.
  • Tabari Amoli, Muhammad bin Jarir, Dalai al-Imamah, Qum, Ba'ath, bugun farko, 1413H.
  • Faiz Kashani, Molly Mohammad Mohsen, Kitab al-Wafi, wanda Ziauddin Hosseini Isfahani ya yi bincike, Isfahan, Makarantar Imam Amirul Momineen Ali (AS), 1406H/1365H.
  • Qaraati, Mohsen, Sharhu Dua Iftitah Sherif, Qom, Hazrat Mahdi Mououd Cultural Foundation, 1392.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi suka gyara/bincike, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
  • Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jamaeeh Leder Akhbar al-Imaa al-Athar, gyara/bincike daga ƙungiyar masu bincike, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403 AH.
  • Mohammadi Rayshahri, Muhammad wa Digaran,Daneshnameh Imam Mahdi (a.s.) da ya dogara da Alkur’ani, hadisi da tarihi, Qum, Darul Hadith, 2013.
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Arshad fi Mafarah Hajjullah Ali Al-Abad, gyara/bincike daga Cibiyar Al-Baiti, Qum, Sheikh Mofid Congress, bugu na farko, 1413 AH.
  • Makarem Shirazi, Nasser, hukumat Mahdi Jahani, Qom, Zaman Matasa, bugu na 10, 1380.
  • Nomani, Mohammad bin Ibrahim, Al-Ghaibah, edita/bincike ta Ali Akbar Ghafari, Tehran, Publishing Sadouq, 1397 AH.