Matan Imam Hassan (A.S)

Daga wikishia

Matan Imam Hassan (A.S) (Larabci: زوجات الإمام الحسن (ع)) wasu mata ne da litattafan tarihi suka bada rahoto cewa su ne matan Imam Hassan (A.S) Cikin ba’arin wasu masadir na tarihi tare da jingina yawan auri saki ga Imam Hassan (A.S) an kira shi da Miɗlaƙ (Mai yawan saki) kishiyar wannan Magana an ce Abbasiyawa ne sakamakon gaba da ƙiyayyar da suke yiwa Sharifai ƴaƴan Imam Hassan (A.S) sai suka danganta wannan Magana ga Imam Hassan (A.S) tabbas da ace wannan tuhuma tana da ƙamshin gaskiya da Umayyawa ne za su fara jinginawa Imam Hassan (A.S) wannan Magana tun yana raye. Malaman Ilimin Rijal na Shi’a a Ahlus-sunna suna ganin cewa Marawaitan Asalin wannan Magana marawaita ne da ba za a iya dogara da maganarsu ba, kuma hakan yana daga cikin suka da aka yi kan wannan riwaya, haka kuma ba a kawo sunayen matayen da aka ce Imam Hassan (A.S) ya aure su ba, rashin dacewar adadin matan da adadin ƴaƴan da ya haifa, da rashin dacewar ayyukan da ya shagaltu da su na zamantakewa da lamurran addini da yawan aure-aure. Cikin masadir an ambaci Khaulatu Bint Manzur mahaifiyar Hassan Musanna, Ummu Is’haƙ ƴar ɗalhatu Bn Ubaidullahi Taimi, Ummu Bashir ƴar Uƙbatu Bn Amru Mahaifiyar Zaidu, Ja’adatu ƴar Ash’asu da Nufailato ko Ramlatu Mahaifiyar ƙasim, Abdullahi da Umar matsayin Matayen Imam Hassan (A.S)

Sunayen Matayensa

Cikin masadir an kawo mata goma sha bakwai matsayen matayen Imam Hassan (A.S) 1-Khaulatu Bint Manzur Farazi mahaifiyar Hassan Musanna. 2-Ummu Is’haƙ Bint ɗalhatu Bn Ubaidullahi Taimi. 3-Ummu Bashir Bint Uƙbatu Bn Amru Mahaifiyar Zaidu. 4-Hafsatu Bint Abdur-Rahman Bn Abubakar. 5-Hindu Bnit Suhailu Bn Amru 6-Ja’adatu Bint Ash’as. 7-Ummu Kulsum Bint Fadlu Bn Abbas Bn Abdul-Muɗallib. 8-wata mata daga dangin Bani Saƙif. 9-wata mata daga dangin Alƙamatu 10-wata mata daga dangin ƙabilar Kilabu. 11-wata mata daga ƙabilar Amru Bn Ibrahim Munƙiri 12-wata mata daga ƙabilar Bani Shaiban daga dangin Hammam Bn Murra. 13-Asma’u Bint Aɗarid Bn Hajib. 14- ɗiyar Umairu Bn Ma’amun. 15- ɗiayr Shalilu Bn Abdullahi (ƴar ɗan’uwan Jariru Bn Abdullahi Bajali) [1] 16-Nufailatu ko Ramlatu: Mahaifiyar ƙasim da Abdullahi da Umar. [2] 17-A’ishatu Khas’amiyya. [3]

Danganta Miɗlaƙ (Mutum Mai Yawan Saki) Ga Imam Hassan (A.S)

Wasu ba’arin masadir tare da jingina yawan aure ga Imam Hassan (A.S) sun kira shi da Miɗlaƙ (Mutum mai yawan Saki), [4] cikin waɗannan masadir an ambaci cewa ya auri mata saba’in, [5] casa’in [6] ɗari biyu [7] da kuma ɗari biyu da hamsin [8] a cewar Madulangi mutum na farko da ya fara yaɗa jita-jita cewa wai Imam Hassan (A.S) yana da mata guda casa’in, shi ne “Muhammad Bn Kalabi” Mada’ini wanda ya mutu shekarar 225 h ƙamari, shi ne mutumin da ya ƙirƙiri wannan adadin mata kuma tare da haka goma sha ɗaya kaɗai ya iya kawo sunansu sannan guda biyar cikinsu akwai shakku da kokwanto kan ingancin aurensu da Imam Hassan (A.S). [9] Bisa rahotannin masadir da aka ambata, lokuta da dama Imam Ali (A.S) ya nuna damuwarsa kan yawan aurace-auracen Imam Hassan (A.S) [10] da wannan dalili ne ya nemi mutanen garin Kufa sai daina aurawa masa ƴaƴansu, [11] Baƙir Sharif ƙarashi Mai zurfafa bincike kuma ɗan shi’a, ya bayyana cewa waɗannan riwayoyi Abbasiyawa ne suka ƙirƙiresu da niyyan ɓata suna da ƙalubalantar sharifai ƴaƴan Imam Hassan (A.S), [12] a rahotan masadir ɗin tarihi3, Mansur Abbasi lokacin da Abdullahi Mahaz jikan Imam Hassan (A.S) sakamakon ƙin faɗar maɓoyar ɗansa Nafsuz Zakiyya wanda ya yi fito na fito da Mansur, sai ya ɗaure shi a kurkuku, ya kuma bijiro da wannan jita-jita, [13] da wannan dalili ne wasu marubuta suka ce wannan shi ne karo na farko da aka bijiro da wannan tuhuma ta hannun Mansur Dawaniƙi. [14] da ace wannan Magana gaskiya ce da Umayyawa sun ƙalubalanci Imam Hassan (A.S) da ita tun yana raye. [15] Haka kuma a cewar wasu ba’arin marubuta, Asalin waɗanda suka rawaito wannan Magana su ne Abu Hassan Mada’ini, Abu Abdullahi Waƙidi, Abu ɗalib Makki, DSS... daga Malaman Tarihi na Ahlus-sunna a lokacin Abbasiyawa sun naƙalto wannan rahoto ne sakamakon ƙiyayya ko kuma yarda da hakan, kuma daga gare su ne waɗannan riwayoyi suka tsallaka litattafan Shi’a [16]tare da cewa Malaman Ahlus-sunna basa dogara da riwayoyin waɗannan marawaita. [17] Haka kuma ba a ambaci sunayen matayen da aka ce ya aura ba, [18] da kuma rashin dacewar adadin matan da adadin ƴaƴansa, [19] da kuma rashin dacewar shagaltuwa Imam Hassan (A.S) da ayyukan zamantakewa da al’amuran addini da yawan waɗannan mata da aka ce yana da su. [20]

Bayanin kula

  1. Shushtri, Rasala fi Tawarikh Al-Nabi wa Al-Al, 1423 AH, shafi na 71-72.
  2. ƙurashi, Hayat al-Imam al-Hasan bin Ali, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 455-460.
  3. ƙurashi, Hayat al-Imam al-Hasan bin Ali, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 455-460.
  4. Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414 AH, Thabƙa 5 th 1, shafi 290; Balazri, Ansab Al-Ashraf, 1397 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 25.
  5. Ibn Kathir, Al-Bidayah wa Al-Nihayah, 1407H, Mujalladi na 8, shafi na 38.
  6. Balazri, Ansab Al-Ashraf, 1397 AH, juzu'i na 3, shafi na 25; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashƙ, Darul Fikr, juzu'i na 13, shafi na 249.
  7. Moghdisi, Al-Bada'u wa Al-Tarikh, Maktabat Al-Thaƙafah Al-Diniya, juzu'i na 5, shafi na 74.
  8. Ibn Shahrashob, Manaƙib Al Abi Talib, 1379 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 30.
  9. Madelong, Janishini Muhammad, 1377, shafi na 514-515.
  10. Balazri, Ansab Al-Ashraf, 1397 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 25.
  11. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashƙ, Darul Fikr, juzu'i na 13, shafi na 249.
  12. ƙurashi, Hayat al-Imam al-Hasan bin Ali, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 453-454.
  13. Tabari, Tarikh Al-Umam wa al-Muluk, 1387 H., juzu'i na 8, shafi na 93; Masoudi, Moruj Al-Dhahab, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 300.
  14. Taƙizadeh Davari, Taswiri Imaman Shi'eh dar Da'iratul Al-Ma'arif Islam (Tarjumeh wa Nakhade), 2005, shafi na 133.
  15. Vardi, "Fasukh be Shubuhate Miɗlaƙ Budane Imam Hassan (A.S), shafi na 423-424.
  16. Misali, duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu’i na 6, shafi na 56; Ibn Shahrashob, Manaƙib Al Abi Talib, 1379 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 30.
  17. Vardi, "Fasukh be Shubuhate Miɗlaƙ Budane Imam Hassan (A.S), shafi na 424-431
  18. "Fasukh be Shubuhate Miɗlaƙ Budane Imam Hassan (A.S), shafi na 434
  19. Taƙizadeh Davari, Taswir Imaman Shi'eh dar Da'iratul Almarif Islam (Tarjumeh wa Nakade), 1385, shafi na 137.
  20. Fasukh be Shubuhate Miɗlaƙ Budane Imam Hassan (A.S), shafi na 439-440

Nassoshi

  • Ibn Sa’ad, Muhammad bin Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, bincike na Muhammad bin Samil al-Salami, Al-Taif, Makarantar Al-Sadiƙ, 1414 Hijira/1993 Miladiyya.
  • Ibn Shahrashob, Muhammad Bin Ali, Manaƙib Al Abi Talib, ƙum, Allameh, 1379H.
  • Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarikh Madinati Damashƙ, Bincike na Hasan Ibn Ahmad da Hasan Ibn Hilal, Darul Fikr, Beta.
  • Ibn Kathir, Ismail Ibn Umar, Al-Badayah da Al-Nahiyah, Beirut, Darul Fikr, 1407H/1986 Miladiyya.
  • Belazari, Ahmad bin Yahya, Ansab al-Ashraf (Juzu'i na 3), wanda Mohammad Baƙer Mahmoudi ya yi bincike, Beirut, Dar al-Taraif don manema labarai, 1977/1397.
  • Taƙizadeh Davari, Mahmoud, Taswir Imaman Shi'eh dar Da'iratul Almaruf Islam (Tarjumeh wa Nakade), Shi'a Science Publications, 1385.
  • Zamani, Ahmad, Haƙa'iƙ Pinhan, Fajuheshi dar ziundagane siyasi Imam Hassan Mujtaba (A.S), ƙum Cibiyar Buga ofishin yada farfagandar Musulunci, 1380.
  • Shushtri, Mohammad Taƙi, Risala fi Tawarikh Al-Nabi wa Al-Al, ƙom, Modaresin Society, 1423 AH.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarihin al’ummai da Al-Muluk, wanda Muhammad Abulfazl Ibrahim ya yi bincike a Beirut, Darul Trath, 1967 miladiyya/1387H.
  • ƙurashi, Baƙar Sharif, Hayat al-Imam al-Hasan bin Ali, Beirut, Dar al-Balaghah, 1413 AH.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, al-Kafi, Ali Akbar Akhundi da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya suka gyara, 1407H.
  • Madelong, Wilfred, Ahmed Namee waa digaran, Janishini Hazrat Muhammad, Mashhad, Astan ƙuds Razavi: Islamic Research Foundation, 1377.
  • Masoudi, Ali bin Hassan, Moruj Al-Dahab wa ma'adinan Al-Jawhar, bincike na Asad Dagher, ƙum, Dar al-Hijrah, 1409H.
  • Moghadsi, Motaher bin Taher,Albada'u wa Al-Tarikh, Bursa'id, School of Al-Taƙfah al-Diniya, Bita.
  • Wardi, Sayyid Taƙi, "Fasukhe Shubuhate Miɗlaƙ Budane Imam Hasan (A.S)", dar Mjmu'ej Maƙalat Hamayeshe Bainal Milali Sibɗil An-Nabiyi (kj 3) ƙum Majma Jahani Ahlul- Bayt, 2014.