Kitmanul Haƙƙi
Kitmanul haƙƙi ko ɓoye gaskiya, (Larabci: كتمان الحق) shi ne ɓoye wani abu da zai sadar da mutum zuwa gaskiya.[1] A cewar manazarta, a cikin Kur'ani akwai ayoyi guda ashirin da suke magana game da ɓoye gaskiya.[2] waɗannan ayoyi suna yin ishara zuwa ga misalai daga ɓoye gaskiya kamar ɓoye ilimin addini, ɓoye shahada, ɓoye imani, ɓoye sirrika da ɓoye ni'imomin Allah.[3] Hassan Musɗafawi, a cikin littafin Tafsir Roshan, ya bayyana cewa shi kitmanul haƙƙi a isɗilahin Kur'ani yana fassara ɓoye ilimummukan addini da aƙidun addini ne[4] Kur'ani a cikin Ayar Kitman da wasu ayoyin daban kamar aya ta 146 da 42 suratul baƙara da aya ta 71 suratul Alu Imran suna bayani ne kan misalsalan kitmanul haƙƙi.[5]
Bisa tafsirin Shi'a, masu ɓoye tabbatattun abubuwa da ilimummukan addini sun kasance malaman Ahlul-Kitabi[6] waɗanda Kur'ani ya bayyana su da masu wulaƙantaccen matsayi ya kuma zarge su tare kuma da tsine musu.[7] Haka nan ba'arin malaman tafsiri sun yi imani cewa a wuraren da mutane suka kasance suna tsananin buƙatuwa da sanin gaskiya, yin shiru ana lissafi shi matsayin ɓoye gaskiya.[8]
Kur'ani mai girma a cikin ayoyi misalin aya ta 106 suratul Ma'ida da aya ta 283 suratul baƙara ya yi ishara kan ɓoye shahada,[9] a aya ta 28 suratul gafir kuma ya yi ishara kan ɓoye imani,[10] haka nan a aya ta 228 suratul baƙara ya yi magana game da ɓoye abin da yake cikin mahaifa[11] sannan kuma a aya ta 37 suratul nisa'i ya yi magana dangane da ɓoye ni'imomin Allah.[12]
A imanin manazarta, shi kitman a kankin kansa ba shi da hukunce-hukuncen shari'a ko na Akhlaƙ, yana samun mabambantan hukunce-hukunce ne sakamakon la'akari da misalsalansa.[13] Alal misali, ɓoye sirrika da aibobin mutane da ɓoye imani a wuraren da ake fuskantar tsoro da barazanar cutuwa, yin taƙiyya abu ne mai kyau a ɗabi'ance[14] a mahangar fiƙihu yana kasancewa wajibi ko mustahabbi[15] sannan kuma ɓoye tabbatattun abubuwa na addini, kamar ɓoye shahada, ta fuskacin akhlaƙ abun zargi ne da ƙyama[16] kuma haramun ne a shari'a.[17]
Bayanin kula
- ↑ Rezaei Isfahani, Tafsir Ƙur'an Mehr, 2008, juzu'i. 2, shafi. 59.
- ↑ Muezzin, Kitmane Haƙƙi
- ↑ Hadi. Kitmane Mamduh Wa Mazmum (Mi'iyarha Wa Calesheha) Shafi na 126; Beigi, Jamal, Jurme Angari Kitmane Shaida Wa Calesheha Dar Huƙuƙ Iran, shafi na 151-152.
- ↑ Mostafavi, Tafsir Roshan, 2001, juzu'i. 4, shafi. 268.
- ↑ Beigi, Jamal, Jurme Angari Kitmane Shaida Wa Calesheha Dar Huƙuƙ Iran, shafi na 151-150.
- ↑ Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1993, juzu'i. 1, shafi. 442.
- ↑ Muezzin, "Kitmane Haƙƙi."
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir-e-Numno, 1992, Juzu'i. 1, shafi. 550.
- ↑ Beigi, Jamal, Jurme Angari Kitmane Shaida Wa Calesheha Dar Huƙuƙ Iran, shafi na 151-151.
- ↑ Muezzin, "Kitmane Haƙƙi."
- ↑ Riosheyabi Made Katam, "shafin Tanzil".
- ↑ Riosheyabi Made Katam, "shafin Tanzil".
- ↑ Hadi. Kitmane Mamduh Wa Mazmum (Mi'iyarha Wa Calesheha) Shafi na 124
- ↑ Hadi. Kitmane Mamduh Wa Mazmum (Mi'iyarha Wa Calesheha) Shafi na 126
- ↑ Tayyib, Atyabul al-Bayan, 1369 AH, juzu'i. 2, shafi. 266; Shahid Awal, Al-Qawa'id Wal Al-Fawa'id, Maktaba al-Mufid, juzu'i. 2, shafi. 157; Farhange Fiqhi Mutabiq Mazhab Ahlul-Baiti (A.S), ta zo a shekara ta 1426H, juzu'i. 1, p. 591.
- ↑ Hadi. Kitmane Mamduh Wa Mazmum (Mi'iyarha Wa Calesheha) Shafi na 138.
- ↑ Shahid Thani, Masalik al-Afham, 1413 AH, juzu'i. 14, shafi. 263.
Nassoshi
- بیگی، جمال، «جرمانگاری کتمان شهادت و چالشهای آن در حقوق ایران»، Jaridar Bi-Quarterly na Rukunan Dokokin Laifuka, Na 14, 2017.
- Rezaei Isfahani, Mohammad Ali, Tafsir Mehr, Qum, Bincike akan Tafsiri da Ilmi na Alqur'ani, bugu na farko, 1999.
- Risheyabi Made Katam,«سایت تنزیل»،Ziyarar kwanan wata: Nuwamba 9, 1402.
- Muassase Da'irate Al-marif Islami Bar Mazhab Ahlul Baiti (A.S),Farhange Fiqhe Mutabiq Mazhab Ahlul-baiti (A.S), Qum, bugu na farko, 1426H.
- Tayyib, Abdul Hussein, Atyab al-Bayan fi tafsir al-Quran, Tehran, Islam Publishing House, bugu na biyu, 1369.
- Shahid Awal, Muhammad, Al-Qawa'id wa al-Fawa'id, Qum, Maktaba al-Mafid, bugun farko, 1400H.
- Shahid Thani, ZaynulDin ibn Ali, Masalik al-AFham ila-Tanqih Shari’ al-Islam, Al-Ma’arif al-Islamiyya Foundation, Qum, bugu na farko, 1413H.
- Tabarsi, Fadl ibn Hassan, Majma’ al-Bayan fi tafsir al-Quran, Tehran, Nasser Khosrow Publishing House, bugu na uku, 1372.
- Mustafavi, Hassan, Tafsir Roshan, Tehran, Markaz al-Kitab Publishing House, bugun farko, 1380.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuno, Tehran, Darul Kutb al-Islamiyya, bugun farko, 1371.
- مؤذنی، محمد، «کتمان حق»، Bank Maƙalat Ulum Insani, 2014.
- هادی، اصغر، «کتمان ممدوح و مذموم (معیارها و چالشها)»،Jaridar Da'a ta Kwata-kwata, Shekara ta 8, Fitowa ta 30, bazara 2018.