Khana Al-Amin
Khana Al-Amin (ma'ana: Amintacce ya yi ha'inci) wata magana ce da wasu daga malaman Ahlus-Sunna suka danganta wa Shi'a.
A cewar wannan da'awa, an ce Shi'a suna ganin cewa Mala'ika Jibrilu an umurce shi da ya kai wahayi ga Imam Ali (A.S), amma sai ya yi kuskure ko ha'inci ya kai shi ga Annabi Muhammad (S.A.W), kuma saboda haka ake cewa Shi'a suna maimaita wannan magana a ƙarshen salla.
Shi'a suna da yaƙinin cewa Imam Ali (A.S) ba annabi ba ne. Haka kuma suna imani cewa Mala'ika Jibrilu ma'asumi ne, wato ba ya yin kuskure ko saɓo. Saboda haka, ba su yarda da zargin cewa Jibrilu ya kai wahayi ga Annabi Muhammad (S.A.W.) maimakon Imam Ali (A.S) ba.
Haka kuma, Shi'a ba sa faɗin "Khana Al-Amin" a ƙarshen salla. Abin da suke yi shi ne yin kabbara sau uku, wato su ce: "Allahu Akbar" sau uku bayan kammala salla.
A ra'ayin malaman Shi'a, wannan zargi ƙarya ce da aka jingina musu domin ɓata sunan mazhabarsu da kuma kamanta ta da wasu ra'ayoyin Yahudawa. An ce wasu daga cikin Yahudawa sun yi imani cewa Jibrilu an aike shi ne da annabta ga wani daga cikin mutanensu, amma ya kai ta ga wani daban. Saboda haka, malaman Shi'a suna ganin cewa an ƙirƙiri wannan zargi ne domin a danganta Shi'a da irin wannan ra'ayi, alhali ba ya cikin aƙidarsu ko littattafansu na asali.
Danganta Kalmar Khana Al-Amin Ga Shi'a
Khana Al-Amin, wato "Amintacce ya yi ha'inci", wani zargi ne da wasu malaman Ahlus-Sunna[1] da Wahabiyawa[2] suka danganta wa Shi'a. Wasu daga cikinsu sun taƙaita wannan aƙida ga wasu ƙungiyoyin masu guluwi (masu wuce gona da iri) daga cikin masu danganta kansu ga Shi'a.[3]
A cewarsu, Shi'a suna da yaƙinin cewa an umurci Mala'ika Jibrilu da ya kai wahayi ga Imam Ali (A.S), amma ya yi ha'inci ya kai shi ga Annabi Muhammad (S.A.W).
Sai dai wannan zargi ba ya wakiltar aƙidar Shi'a Imamiyya, domin Shi'a suna imani cewa Annabi Muhammad (S.A.W) shi ne hatimin annabawa kuma wanda aka saukar wa wahayi, sannan suna ɗaukar Jibrilu a matsayin mala'ika ma'asumi wanda ba ya yin kuskure ko ha'inci.[4]
A cewar Abdullah bin Jibrin (ya rasu 1430H), wani mufti na Wahabiyawa, an nakalto a cikin sharhinsa kan al-Riyadh al-Nadiyyah Ala Sharhi al-Aƙidah al-Ɗahawiyyah cewa an ruwaito masa cewa wasu daga cikin Shi'a suna dukan gwiwowinsu kafin sallama a sallah, suna kuma maimaita kalmar "Khana Al-Amin".[5]
Sai dai kuma su Shi'a ba sa faɗin "Khana Al-Amin" a cikin sallah. A maimakon haka, bayan sallama, suna ɗaga hannuwansu sau uku suna yin kabbara uku.[6] Wannan kuwa saboda a ra'ayin malaman fiƙihun Shi'a, yin takbiri sau uku bayan sallama na daga cikin abubuwan da ake so (mustahabbi).[7]
Dogaro Da Waƙar Ibn Hammad
Wasu daga malaman Ahlus-Sunna sun ɗauki wani baitin waƙa da aka danganta ga Ali bin Hammad Al-Basri, mawaƙin Shi'a na ƙarni na 4 Hijira, a matsayin hujja cewa wasu daga Shi'a suna da aƙidar cewa Jibrilu ya yi ha'inci.[8] Wannan baitin shi ne:
Tarjama: "Amintacce ya ɓace ya hana ta ɗaga (zuwa ga) Haidar Na rantse da Allah, amintaccen bai kasance amintacce ba".[9]
A cewar Ƙazi Nurullah Shushtari da Abu Ali Ha'iri, daga malaman Shi'a, kalmar "Amin" a cikin wannan waƙa tana nufin Abu Ubaida Jarrah, wanda Ahlus-Sunna suke kiran shi "Amin al-Umma". Suna ganin ya taimaka wajen tabbatar da halifancin Abubakar da kuma hana Imam Ali (A.S) samun halifanci.[10]
Haka kuma an nakalto a cikin Sahihul Bukhari, ɗaya daga cikin littattafan hadisi shida na Ahlus-Sunna, cewa Abu Ubaida Jarrah an kira shi amintaccen al'ummar Musulmi.[11]
Dalili Da Manufa
A cewar Jafar Subhani, daga maraji'an Shi'a, ra'ayin cewa Jibrilu ya yi "ha'inci" wajen isar da wahayi asalin aƙidar Yahudawa ce, amma masu adawa da haɗin kan Musulmi ne suka jingina wannan ra'ayi ga Shi'a.[12]
Haka kuma Fakhrud-dini Razi, wani malamin tafsiri na Ahlus-Sunna (ya rasu 606H), ya bayyana a tafsirinsa a ƙarƙashin ayar 97 ta suratul Baƙara cewa Yahudawa sun kasance suna adawa da Jibrilu, kuma suna ganin cewa an umurce shi da ya sanya annabci a cikin wani mutum daga ƙabilarsu, amma ya kai shi ga wanda ba daga cikinsu ba.[13]
Ibn Abd Rabbihi (ya rasu 328H), malami daga Ahlus-Sunna, a cikin littafinsa Al-Iƙdul Farid, bayan ya kawo ra'ayin Yahudawa game da adawarsu da Jibrilu, ya ce "Rafidawa" (Shi'a) ma suna da irin wannan ra'ayi; saboda a cewarsa suna ganin Jibrilu ya yi kuskure wajen isar da wahayi ga Muhammad (S.A.W) kuma ya kamata ya kai shi ga Ali (A.S).[14]
Haka kuma Ibn Jauzi (ya rasu 597H), daga malaman fiƙihun mazhabar Hanbali,[15] da Ibn Taimiyya Harrani (ya rasu 728H), daga masu ra'ayin Salafiyya, sun maimaita wannan magana a cikin bayanansu lokacin da suke kwatanta abin da suke kira kamanceceniyya tsakanin Shi'a da Yahudawa.[16]
Rashin Dacewa Da Aƙidun Shi'a
Malaman Shi'a sun ɗauki danganta zargin "ha'inci ga Jibrilu" ga Shi'a a matsayin zallan tuhuma da kuma ƙage da ƙarya.[17] Sun bayyana cewa babu wani daga Shi'a da ya yi imani cewa Jibrilu ya yi kuskure ko ha'inci, kuma ba sa amfani da kalmar "Khana Al-Amin".[18]
A cewar malamai, wannan aqida ta ha'inci ga Jibrilu ta ci karo da muhimman ginshiƙan aƙidar Shi'a, ciki har da:
- Ismar mala'iku (Tsarkin mala'iku): A ra'ayin Shi'a, Jibrilu da sauran mala'iku ma'asumai ne, ba sa saɓawa umarnin Allah,[19] kuma ba sa yin kuskure ko da gangan ko mantuwa.[20] Allama Ɗabaɗaba'i ya bayyana cewa Jibrilu ba ya canja wahayi ta kowace hanya, ko kuskure ko mantuwa.[21]
- Rashin Annabcin Imam Ali (A.S): Malaman Shi'a suna cewa Imam Ali (A.S) ba annabi ba ne,[22] sai dai shi ya kasance Imami kuma magajin Annabi Muhammad (S.A.W.). Wannan yana bayyana a cikin Hadisin Manzila, wanda ake amfani da shi[23] wajen tabbatar da matsayin Imam Ali (A.S.).[24]
Haka kuma Abdullahi Jawadi Amoli, malamin tafsiri na Shi'a ya bayyana cewa babu wanda ya fi Annabi Muhammad (S.A.W) kamala, domin idan akwai wanda ya fi shi, to ma'anar hatimin annabawa ba za ta cika ba.[25]
Bayanin kula
- ↑ Ibn Abdi Rabbihi, Al-'Iƙdul Farid, juzu'i na 2, shafi na 250; Ibn Jauzi, Al-Maudu'at, juzu'i na 1, shafi na 339; Ibn Taimiyya, Minhajus Sunn An -Nabawiyya, juzu'i na 1, shafuffuka na 27 da 32.
- ↑ Ibn Usaimin, Al-Ƙaulul Mufid, juzu'i na 1, shafi na 321; Adawi, Silsilatul Tafsir li Mustafa Al-Adawi, juzu'i na 23, shafi na 15.
- ↑ Misali, a duba: Sam'ani, Al-Ansab, juzu'i na 10, shafi na 23; Tahanawi, Mausu'at Kashshaf Istilahat Al-Funun wa Al-Ulum, juzu'i na 2, shafi na 1249.
- ↑ Ibn Abdi Rabbihi, Al-'Iƙdul Farid, juzu'i na 2, shafi na 250; Ibn Jauzi, Al-Maudu'at, juzu'i na 1, shafi na 339.
- ↑ Ibn Abil-Izz, Al-Riyadun Nadiyya Ala Sharhi Al-'Aƙida Aɗ-Ɗahawiyya, juzu'i na 4, shafi na 568.
- ↑ Misali, a duba: Safi, Sautul Haƙƙi, shafi na 45; Subhani, Rahnamaye Haƙiƙat, shafi na 363.
- ↑ Misali, a duba: Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 10, shafi na 408; Mufid, Al-Muƙni'a, shafi na 114.
- ↑ Misali, a duba: Dawani, Al-Hujajul Bahira, shafi na 359; Dehlawi, Mukhtasar Al-Tuhfa al-Isna Ashariyya, juzu'i na 1, shafi na 13.
- ↑ Shushtari, Majalis al-Mu'minin, juzu'i na 2, shafi na 566.
- ↑ Shushtari, Majalisul Mu'minin, juzu'i na 2, shafi na 566; Ha'eri, Muntahal Maƙal, juzu'i na 4, shafi na 406; haka kuma a duba Muhaddis Armawi, Ta'liƙate Naƙz, juzu'i na 2, shafi na 1085.
- ↑ Bukhari, Sahihul Bukhari, juzu'i na 9, shafi na 88.
- ↑ Subhani, Rahnamaye Haƙiƙat, shafi na 363.
- ↑ Fakhr Razi, Al-Tafsir Al-Kabir, juzu'i na 3, shafi na 611.
- ↑ Ibn Abdi Rabbihi, Al-'Iƙdul Farid, juzu'i na 2, shafi na 250.
- ↑ Ibn Jawzi, al-Mawdu'at, juzu'i na 1, shafi na 339.
- ↑ Ibn Taimiyya, Minhajus Sunn An -Nabawiyya, juzu'i na 1, shafuffuka na 27 da 32.
- ↑ Misali, a duba: Amini, Al-Ghadir, juzu'i na 3, shafi na 127; Subhani, Zahirat al-Iftra' Alash Shi'a Abra At-Tarikh, shafi na 59; Safi, Sautul Haƙƙi, shafi na 45.
- ↑ Misali, a duba: Safi, Sautul Haƙƙi, shafi na 45; Subhani, Rahnamaye Haƙiƙat, shafi na 363.
- ↑ Soroush, «Shubha Khana Al-Amin,» shafi na 148.
- ↑ Misali, a duba: Shaik Saduƙ, Al-I'itiƙadat, shafi na 96; Mufid, Awa'ilul Maƙalat, shafi na 71.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 15, shafi na 316.
- ↑ Misali, a duba: Sayyid Murtada, Ash-Shafi Fil Imama, juzu'i na 3, shafi na 5.
- ↑ Misali, a duba: Sayyid Murtada, Ash-Shafi Fil Imama, juzu'i na 3, shafi na 5.
- ↑ Barƙi, Al-Mahasin, juzu'i na 1, shafi na 159; Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 8, shafi na 26.
- ↑ Jawadi Amoli, Tafsir Maudu'i Qur'ane Kareem, juzu'i na 8, shafi na 24.
Nassoshi
- Allama Hilli, Hassan Bin Yusuf, Kashful Murad fi Sharhi Tajridil I'tiqad, da gyara da bincike na Hassan Hasan-zadeh Amoli, Qom, Cibiyar Nashre Islami, 1413H.
- Amini, Abdul-Husain, Al-Ghadir Fil Kitab Was Sunna Wal Adab, Qom, Cibiyar Ghadir Lil Dirasatil Islamiyya, 1416H.
- Barƙi, Ahmad Bin Muhammad Bin Khalid, Al-Mahasin, bincike da gyara na Jalal al-Din Muhaddis, Qom, Darul Kutubil Islamiyya, 1371H.
- Bukhari, Muhammad Bin Isma'il, Sahihul Bukhari, binciken Muhammad Fu'ad Abdul Baƙi, Beirut, Dar Tauƙ al-Najat, 1422H.
- Dawani, Jalal al-Din Muhammad Bin As'ad, Al-Hujajul Bahira Fi Ifham Al-Ɗa'ifa Al-Kafira A-Fajira, bincike na Abdullah Hajj Ali Munib, Maktabatab Al-Imam Al-Bukhari, ba wuri, 1420H/2000M.
- Dehlawi, Shah Abdul-Aziz Gulam Hakim, Mukhtasar Al-Tuhfa Al-Isna Ashariyya, fassarar Hafiz Gulam Muhammad Bin Muhyid-Din Bin Umar Al-Aslami, taƙaitawa da gyara na Mahmud Shukri Al-Alusi, bincike na Muhibbid al-Din al-Khaɗib, Alkahira, Gidan bugawa na al-Salafiyya, 1373H.
- Fakhr Razi, Muhammad Bin Umar, Al-Tafsir Al-Kabir, Beirut, Gidan Raya Gadon Tarihi na Larabawa, 1420H.
- Ha'eri, Muhammad Bin Isma'il, Muntahal Maƙal fi Ahwal Ar-Rijal, binciken Cibiyar Alul Bait (A.S.) Li Ihya' Al-Turas, Qom, 1416H/1374Sh.
- Ibn Abdi Rabbihi, Shihab al-Din Ahmad Bin Muhammad, l-'Iƙdul Farid, Beirut, Darul Kutubin Ilmiyya, 1404H.
- Ibn Abil-Izz, Ali Bin Ali, Al-Riyadun Nadiyya Ala Sharhi Al-'Aƙida Aɗ-Ɗahawiyya, sharhi na Abdullah bin Jibrin, gabatarwa na Ɗariƙ Bin Muhammad Khuwaiɗir, Riyad, Darul al-Sumai'i, 1431H.
- Ibn Jauzi, Abdulrahman bin Ali, Al-Maudu'at, gabatarwa da bincike na Abdulrahman Muhammad Usman, Madina, Muhammad Abdul-Muhsin Sahib Al-Maktabatus Salafiyya Bil Madinatil Munawwara, 1388H.
- Ibn Taimiyya, Ahmad Bin Abdul-Halim, Minhajus Sunna An-Nabawiyya Fi Naƙzi Kalam Ash-Shi'a Al-Ƙadariyya, bincike na Muhammad Rashad Salim, Riyad, Jami'atu Imam Muhammad Bin Saud Al-Islamiyya, bugu na farko, 1406H.
- Ibn Usaimin, Muhammad Bin Salih, Al-Ƙaulul Mufid Ala Kitab Al-Tauhid, Al-Mamlatul Arabiyyatis Sa'udiyya, Dar Ibn al-Jauzi, 1424H.
- Jafar Subhani، ظاهرة الإفتراء علی الشیعة عبر التاریخ، (Abin da aka fi sani da ƙirƙira da ƙage a kan Shi'a a tsawon tarihi), Tehran, Mash'ar, ba tare da ranar bugu ba.
- Jawadi Amoli, Abdullah, Tafsir Maudu'i Qur'ane Kareem Sire Rasul Akram (S.A.W) fi Dar Qur'an, Qom, Cibiyar Nashre Isra', 1379Sh.
- Kulaini, Muhammad Bin Yaƙub, Al-Kafi, da gyara da bincike na Ali Akbar Gafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kutubil Islamiyya, 1407H.
- Mufid, Muhammad Bin Muhammad, Awa'ilul Maƙalat, bincike na Ibrahim Ansari, Qom, Al-Mu'tamar al-'Alami li Alfiyyat al-Shaik al-Mufid, 1413H.
- Mufid, Muhammad Bin Muhammad, Al-Muƙni'a, Qom,Jama'atul Mudarrisin Hauzatil Ilmiyya Qom. Cibiyar Al-Nashril Islami, 1410H.
- Muhaddis Armawi, Mir Jalal al-Din, Ta'aliƙate Naƙz, Tehran, Gidan Buga na Anjumane Asare Melli, 1358Sh.
- Mustafa Al-Adawi, سلسلة التفسیر» لمصطفی العدوی»، (Jerin Tafsirin Mustafa Al-Adawi), Darusan sauti da shafin yanar gizo na "Al-Shabaka al-Islamiyya" ya rubuta daga sauti zuwa rubutu, ba tare da shekara ba.
- Najafi, Muhammad Hassan, Jawahirul Kalam fi Sharh Shara'i'il al-Islam, tarawa da bincike na Abbas Quchani, Beirut, Dar Turasil Arabi, 1362Sh.
- Naƙze Bar Kitabe Al-Mawdu'at Abul Faraj Ma'aruf Be Ibn Al-Jauzi," a cikin Kalam al-Islami, lamba 30, shafi na 148–160, bazara 1378Sh.
- Safi, Luɗfullah, Sautul Haƙƙi Wa Da'watus Sidƙi, Beirut, Darul Ta'aruf Lil Maɗbu'at, bugu na uku, ba tare da shekara ba.
- Sam'ani, Abu Sa'd Abdul-Karim Bin Muhammad, Al-Ansab, binciken Abdulrahman Bin Yahaya al-Mu'allimi al-Yamani da wasu, Hyderabad, Majalisar Da'iratil Ma'arif Usmaniyya, 1382H/1962M.
- Sayyid Murtada, Ali Bin Husain, Ash-Shafi Fil Imama, bincike na Sayyid Abduz-Zahra al-Husaini, Tehran, Cibiyar As-Sadiƙ, 1410H.
- Shaik Saduƙ, Muhammad Bin Ali, Al-I'itiƙadat, bincike na Ali Misharifi da Abdus-Sayyid Isam, Qom, Kongire Shaik Mufid, 1371Sh/1413H.
- Shushtari, Nurullah Bin Sharif al-Din, Majalis al-Mu'minin, Tehran, Islamiyya, 1377Sh.
- Soroush, Jamal da Shahrazad Dehghan Jabbarabadi, «Shubha Khana Al-Amin,» (Shubuhar tuhumar Jibrilu da aikata ha'inci), a cikin Hikmat al-Islami, lamba 3, shafi na 131–158, hunturu 1393Sh.
- Subhani, Jafar, Rahnamaye Haƙiƙat, Tehran, Mabugar Mash'ar, 1387Sh.
- Ɗabaɗaba'i, Sayyid Muhammad Husaini, Almizan Fi Tafsiril Kur'an, Beirut, Cibiyar Al'alami Lil Madbu'at, 1393H.
- Tahanawi, Muhammad Bin Ali, Mausu'at Kashshaf Istilahat Al-Funun wa Al-Ulum, gabatarwa da kulawa na Rafiƙ al-'Ajam, binciken Ali Dahruj, fassara daga Farisanci zuwa Larabci na Abdullah al-Khalidi, Beirut, Maktabatu Lubnan Nashirun, 1996M.