Kalimullahi (Laƙabi)

Daga wikishia
(an turo daga Kalimullah (laƙabi))

Kalimullah (Larabci:کلیم الله) Ma'anar shi: wanda Allah ya yi magana da shi. laƙabin ya keɓanta ga Annabi Musa (A.S).[1] kuma ana kiransa Kalimullah saboda Allah ya yi magana da shi ba tare da wani a tsakani ba.[2] an ɗauke shi a matsayin suna mai alheri a gare shi.[3] Kamar yadda aya ta 164 a cikin suratun Nisa’i, ta nuna Allah ya yi magana da Musa (A.S).[4] A cikin aya ta 144 a cikin suratu A’araf, an kuma ambaci zancen da Allah ya yi da Musa. (a.s)[5] kamar aynda cikin aya ta 11 suratul ɗaha nan an kiraye shi da wannan siffa da aka ishara kanta, wnanan nau'in tattaunawa an samu wasu ba'arin malaman muslunci[6] da [7] da suke lissafata[8] matsayin abin da ya keɓantu da Musa (A.S) Ana kiran yahudawa “Kalimi” saboda sifar Kalimullah ga Annabi Musa[9]

Wasu malaman musulmi sun yi imani da cewa Allah ya yi magana da Annabin Musulunci a lokacin mi’iraji, kuma hadisai sun yi nuni da wannan magana.[10] Sun yi imani da cewa yin magana da Allah kai tsaye ya keɓanta da Annabin Musulunci (S.A.W) da Musa (a.s).[11] An ɗauki maganar Allah a matsayin magana ba tare da jiki ba; Domin magana da harshe alama ce ta samun jiki, alhali kuwa Allah ba shi da jiki.[12]

Ya zo cikin baiti waka cewa: Duk wata wahala sharar fage ce zuwa ga hutu harshensa ya kasance tare da gaskiya harshen badaɗayin Allah ya ƙone.[13]

Masanin tafsiri na ƙarni na goma sha biyu Burossawi ya yi imani da cewa dalilin da ya sa Allah ya keɓanta Musa (A.S.) ga irin wannan magana shi ne lokacin da Musa (A.S) yake yaro harshensa ya ƙone. Saboda haka baya iya magana yanda ya kamata saboda wannan ƙonewar sai Allah ya yi masa magana kai tsaye sannan ya kirashi da Kalimullah.[14] Wasu malaman tafsiri sun sake yin wani tawili kan dalilin laƙabin Kalimullah, ta yadda Allah a bayyanarsa ta farko ga Musa (A.S) ya ce: “Ni ne Ubangijinka” kuma annabcin Musa (a.s) ya fara da magana da Allah, shi ya sa ake kiransa da “Kalimallah”.[15]

Bayanin kula

  1. Fadlallah, Tafsirin min wahayi Alƙur’ani, 1419 AH, juzu’i na 20, shafi na 202
  2. Tayyab, Atyab Al-Bayan, 1378 AH, juzu'i na 3, shafi na 3. ↑
  3. Zuhayli, Al-Tafsir Al-Munir, 1418H, juzu'i na 6, shafi na 35
  4. Suratul Nisa’i, aya ta:164.
  5. Tayyab, Atyab Al-Bayan, 1378 AH, juzu'i na 5, shafi 453.
  6. Sheikh Tusi, Al-Tibyan, Beirut, juzu'i na 3, shafi na 394; Fakhr Razi, Al-Tafsir Al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 11, shafi na 267.
  7. «لقب حضرت موسی به فارسی چه می‌باشد و نبوت ایشان چگونه بود؟»، انجمن کلیمیان تهران.
  8. ƙureshi, Tafsiri Ahsan al-Hadith, 1377, juzu'i na 1, shafi na 470; Rashid Reza, Al-Manar, 1990, juzu'i na 3, shafi na 4.
  9. «لقب حضرت موسی به فارسی چه می‌باشد و نبوت ایشان چگونه بود؟»، انجمن کلیمیان تهران.
  10. Banu Amin, Makhzan Al-Irfan, 1361, juzu'i na 2, shafi na 379.
  11. Boroujerdi, Tafsir Jame, 1366, juzu'i na 2, shafi.462.
  12. Makarem Shirazi,Yek sado hashtade purseshi wa pasukh, 2006, shafi na 75
  13. Brosui, Tafsir Ruh al-Bayan, Beirut, juzu'i na 5, shafi.372.
  14. Brosui, Tafsir Ruh al-Bayan, Beirut, juzu'i na 5, shafi.372
  15. ƙaraati, Tafsir Noor, 2003, juzu'i na 7, shafi na 328

Nassoshi

Bano Amin, Makhzan al-Irfan in Qur'an Tafsir, Tehran, Muslim Women's Movement, 1361.

  • Boroujerdi, Seyyed Mohammad Ibrahim, Tafsir Jame, Tehran, Sadr Publications, bugu na 6, 1366.
  • Brusowi, Ismail, Tafsir Ruh al-Bayan, Darul Fekr, Beirut, Bita.
  • Rashidreza, Tafsir al-Manar, Misr, Al-Masriyyah al-Katab, 1990.
  • Zaheili, Wahba bin Mustafa, al-Tafseer al-Munir fi al-Aqeedah wa al-Shari'a wa al-Manhaj, Dar al-Fikr al-Mudhamdin, Beirut, Damascus, bugu na biyu, 1418H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsir al-Qur'an, gabatarwa: Sheikh Agha Bazar Tehrani, bincike: Ahmad Qasir Ameli, Beirut, Darahiya al-Trath al-Arabi, Bita.
  • Tayeb, Seyyed Abdul Hossein, Atyeb al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Islam Publications, bugu na biyu, 1378.
  • Fakhr Razi, Muhammad Ibn Umar, Al-Tafsir al-Kabir (Mufatih al-Ghayb), Beirut, Darahiya al-Trath al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
  • Fazlullah, Seyyed Mohammad Hossein, Tafsir Man Wahayi Al-Qur'an, Beirut, Dar al-Mulak Lalprinta da Al-Nashar, bugu na biyu, 1419H.
  • Qaraati, Mohsen, Tafsir Noor, Cibiyar Al'adu ta Kur'ani, Tehran, bugun 11, 2003.
  • لقب حضرت موسی به فارسی چه می‌باشد و نبوت ایشان چگونه بود؟»، وبگاه انجمن کلیمیان تهران، تاریخ بازدید: ۱ اسفند ۱۴۰۲ش.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Yek Sado hashtade purseshi wa pasukh Tehran, Darul-e-Kitab al-Islamiyya, 2006.