Kaffarar Azumi

Daga wikishia
(an turo daga Kaffara ta Azumi)

Kaffarar Azumi (Larabci: كفارة الصوم), nau'i ne na tara da mutum baligi yake yi sakamon karya azumi na Ramadan ko azumi bakance ko na ramuwar wata azumin na ramadan, bayan kiran sallar Azzahar, duk wanda ya karya azuminshi da gangan,to wajibine ya yi wata azumi na wata biyu, kuma dole ne ya yi azumi na kwana goma talatin da ɗaya a jere ko kuma ya ciyar da muskini sitin. Kaffara tana wajabta ne idan mutum ya san cewa abin da yake aikatawa zai kai shi ga karya azuminshi, wasu daga cikin malamai kamar malamin nan mai litattafin Jawahir da Sayyid Khuyi sun tafi kan cewa duk wanda ya karya azumi da gangan bayan wajabcen Kaffara to dole ya rama wannan azumin, amma wasu malaman fiƙihu suna ganin cewa dan mutum ya aikata abin da zai karya azuminshi da gangan, kamar amai, to ba wajibi ba ne su yi kaffara. Bisa fatawa ta malaman shi'a, idan mutum ya karya azuminshi ta hanyar aikata abin da yake haramin ne kamar shan giya ko zina, to wajibi ne ya haɗa dukkan kaffarori guda biyu, (ya yi azumin wata biyu kuma ya ciyar da muskini sittin), amma wasu daga cikin malamai sun tafi kan cewa kaffara ta haɗawa anan ana nufin ya yi Ihtiyaɗi na wajibi ko kuma Ihtiyaɗi na mustahabbi wato ya zaɓi ɗaya a cikin guda biyun.

ƙarin bayani

Kaffara kamar wata tarace ta kuɗi ko ta jiki wanda mutum baligi yake yi, sakamakon aita wasu laifuka. [1] sau dayawa tana kankare zunubi ko kuma rageshi.[2] Malamai sun ambaci guri uku da kaffara take wajibi sakamakon karya azumi;

  • Idan mutum ya karya azumi na watan ramadan.
  • Idan mutum ya karya azumi na ramuwaar watan Ramadan,amma idan bayan azzahar ne.
  • Idan mutum ya karya azumin Bakance na wani lokacin ƙayyadajje.[3]

Kuma tayiyu ayi amfani da kalmar kaffara a cikin al'uma da ma,anar Fidaya, misali ciyar da kwarkwadan Mudu ɗaya [750 na krma] wannan shima ana cemishi kaffara,[4] duk dacewa wannan Fidiya ce, ba kaffara ba. Wannan Fidiyar madadi ce ta azumin watan ramadan ga wanda rashin lafiya tahanashi azumi, da kuma mutuman da ya jinkirta rama azuminshi har wani watan azumin ya kewayo, to irin wannan mutuman dolane ya bada kaffara ta jinkiri.[5]

Kaffara ta azumi tana bin ilimin mutum ko Jahilcishi ne

Malaman fiƙihu sun tafi kan wajabcin kaffara da ramuwar azumin da ya karya a tare ga duk wanda ya karya azumi da gangan batare da wani uzuri ba a shari'a,[6] kazalika sunce sharaɗi ne kan wajabcin kaffara ya zama mutum ya sani cewa abin da yake yi yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke karya azumi,[7] saboda haka wannan hukuncin baya gudana kan jahili [ƙasir shi ne wanda bashi da hanyar da zai san hukunci],[8] da kuma jahilil Muƙassir, [shi ne wanda zai iya sani hukunɓci idan ya bincika,amma yaƙi bincikawa],[8] sai dai akwa waɗanda suke ganin shi jahili Muƙassir dolane ya yi kaffara kuma ya rama azumi, saboda shi kamar wanda yasa hukunci yake, saboda haka dola ne ya yi duka biyun.[7]

Abubuwan da suke karya azumi kuma sunasa kaffara

Mawallafin littafin Jawahiri bisa dogaro kan wasu ruwayoyi da abin da yake bayyana daga garesu, yana ganin cewa duk mutuman da ya aikata abubuwan da suke karya azumi, to dolane ya yi ramuwa kuma ya bada kaffara a tare,[9] Sayyid Ku'i ya tafi kan cewa aikata duk abin da yake karya azumin to yana wajabta kaffara, har ƙarya ga Allah da Manzonshi ko kuma yin amai da gangan.[10] Wasu malaman fiƙihu sun tafi kan cewa karya azumin, ba kodayaushe bane yake wajabta kaffara,[11] kamar yadda imamu Kwamaini yake ganin idan mutum ya yi amai da gangan ko kuma ya yi mafarki da dare kuma ya farka daren sau uku,sannan ya koma bacci, sai bai farkaba har akayi kiran sallar Asuba, to wajibine ya rama azumin wannan ranar kaɗai kuma ba bu kaffara a kanshi.[12]

Banbanci kaffara idan mutum ya karya azumi da haramin ko halal

Wasu daga cikin malamai suna ganin idan mutum ya karya azumin da abin da yake halal, kamar abinci da ruwa, to wajibi ne a kanshi ya rama azumin wannan ranar kuma ya bada ɗaya daga cikin kaffarori nan guda uku.[13] amma idan mutum ya karya azumi da abin da yake haram ne kamar ya yi zina Allah ya kiyayemu ko yasha giya, to dolane ya aikata dukkan kaffara guda uku, wanda ake kiranta da kaffarar haɗawa.[14] amma wasu maraji'a kan kaffarar Ja'm [kaffarar hɗawa] sun ce mutum ya yi Ihtiyaɗi na mustahabi, wasu kuma sukace ya yi ihtiyaɗi na wajib. [16] Bisa ra'ayi sananne a tsakanin malaman fiƙihu na shi'a kaffarar azumi zata zama ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa;

  • Azumin wata biyu ɗaya bayan ɗaya, kuma dolane mutum ya yi kwana talatin da ɗaya a jere.[17]
  • Ciyar da muskini sittin
  • ‘yanta bawa.[18]

Amma haƙiƙa a wannan lokacin ba bu batun ‘yanta bawa. [19]