Isra'il (Laƙabi)
- Ka da ku kuskure da gwamnatin Isra'ila
Isra'il (Larabci: إسرائيل) laƙabi ne na annabi Yaƙub, kamar yadda littafin Tafsir Majma'ul Bayan ya yi bayani, a harshen Abraniyanci Isra'il yana nufin zaɓaɓɓen Allah ko bawan Allah.[1] Shaik Ɗusi yana ganin wannan kalma ta Isra'il ta harhaɗu ne daga kalmomi guda biyu “Isra” wace take nufin bawa da kuma "Il" da take da ma'anar Allah, da haka ta ba ba ma'anar bawan Allah.[2] Malaman tafsiri na Shi'a suna ganin cewa abin nufi daga kalmar Isra'il da ta zo a aya ta 93 suratul alu imran da aya ta 58 suratul an'am shi ne Yaƙub.[3] Da wannan dalili ne ne ake kira ƴaƴa da zuriyar Yaƙub da sunan Bani Isr'ail.[4]
A cikin Attaura ya zo cewa bayan Allah ya yi kokawa tare da Yaƙub ya ji irin ƙarfin da yake da shi da galaba da ya yi kan Allah da ɗan'adam, sai Allah ya kira shi da Isra'il.[5]
Bayanin kula
- ↑ Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1415 AH, juzu'i. 1, shafi. 182.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Tebyan, Dar Ihya Al-Turahat Al-Arab, juzu'i. 1, shafi. 180.
- ↑ Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i. 2, shafi. 344; Sobhani, Manshru al-Javid, 1391 AH, juzu'i. 11, shafi. 325.
- ↑ Rouhi, Simaye Bani Isra’il DarQur’an Wa Ahdaini, 2005, shafi. 58.
- ↑ Ahde Atiƙ, 1393, juzu'i. 1, shafi na 234-236.
Nassoshi
- Rouhi, Abul-Fadl, Simaye Bani Isra'il Dar Qur'ai Wa Ahdaini, a cikin Mujallar Marafat, No. 95, Nuwamba 2005.
- Sabhani, Jafar, Manshor Javid, Qum, Imam Sadiq (AS) Foundation, 2011.
- Sheikh Tusi, Muhammad ibn Hassan, Al-Tebyan fi Tafsirin Quran, Beirut, Dar Ihya al-Turat al-Arab, Beta.
- Tabarsi, Fadl ibn Hassan, Majmu’ul al-Bayan fi Tafsir al-Quran, Beirut, Al-Alamy Publications Foundation, 2015.
- Ahadu al-Atiq (Juzu'i na 1: Littattafan Sharia ko Attaura), wanda Pirouz Sayar ya fassara, Tehran, Hermes Publications, 2014.