Ibrahim Zakzaki
| Cikakken Suna | Ibrahim Yaƙub Zakzaki |
|---|---|
| Laƙabi | Shugaban Shi'a a Najeriya |
| Tarihin haihuwa | 1953m |
| Mahaifa | Zariya |
| Wurin rayuwa | Zariya-Abuja |
| Wurin karatu | Zariya-Kano |
| Sauran abubuwa | Ɗalibi ne da ya kammala karatu a fannin tattalin arziki, kimiyyar siyasa, da ilimin addini. Yana koyar da tafsirin kur'ani, Nahjul Balaga, da... a Husainiyyar Baƙiyyatullahi |
| Siyasa | Shugaba kuma wanda ya kafa Harkar Muslunci Najeriya |
Ibrahim Zakzaki, wanda aka haifa shekarar 1953m, malamin Shi'a kuma jagoran ƴanshi'a a Najeriya. Zakzaki ya zama ɗanshi'a sakamakon tasirantuwa da juyin juya halin Muslunci na Iran da kuma Imam Khomaini, bayan kafa harkar Muslunci Najeriya ya kafa makarantun addinin Muslunci guda 300 a Najeriya da ƙasashe maƙotan Najeriya. Har ila yau, ya samar da mu'assasa da take ba da taimakon kuɗi da magani da ma taimakon karatu ga ƴanshi'a.
Kamar dai yadda aka ji daga bakinsa, ya bayyana cewa daidai lokacin nasarar juyin juya hali a Iran (1979m) ya fara tabligi da kira zuwa ga Muslunci, an samu gomomin mutane sun amsa wannan da'awa da yake yi, tare da wasu adadi daga mabiya Ahlul-Baiti (A.S). zuwa shekarar 2011m, albarkacin ƙoƙarinsa milyoyin mutane ne suka zama ƴanshi'a a Najeriya.
A lokacin jerin gwano na taron ƙudus na shekarar 2014m, jami'an tsaron Najeriya sun kai hari kan wannan taro tare da kashe gomomin mutane ciki kuwa har da ƴaƴan Zakzaki guda uku, haka nan sojojin Najeriya sun kama Zakzaki tare da tsare shi a kurkuku lokacin da suka kai hari kan Husainiyyar Baƙiyatullahi Zariya a shekarar 2015m. sakamakon kama shi musulmi sun shirya taron nuna rashin amincewa a ƙasashen Iran, Amurka, Ostiraliya, Suwed da Turkiya. Haka nan Sayyid Ali Khamna'i, jagoran jamhuriyar Muslunci ta Iran da Husaini Wahid Khurasani daga maraji'an taƙlidi da Isa Ƙasim shugaban ƴanshi'ar Bahrain sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan waƙi'a
Zakzaki tare da matarsa bayan tsare su na tsawon shekaru shida tsakanin tsarewa a gida da kuma zama a kurkuku, a ranar 28 ga watan Yuli ne suka shaƙi iskar ƴanci suka dawo gida daga kurkuku.
Tarihin Rayuwa Da Karatunsa
An haifi Ibrahim Yaƙub Zakzaki a shekarar 1953 a garin Zariya da yake a Arewacin Najeriya.[1] Zuwa shekarar 1975 ƙari kan karatun zamani, ya yi karatun addini a garin Kano.[2] A shekarar 1977m, ya samu shaidar kammala karatu a matakin digiri na ɗaya a fannin kimiyyar tattalin arziƙi daga jami'ar Ahmadu Bello Zariya, bayan wani lokaci, ya kasance limami a ɗaya daga cikin masallatan makarantun addini.[3] A farko dai Zakzaki ya fara gwagwarmaya cikin kasancewa memba a ƙungiyar ɗaliban jami'a musulmi, bayan nan ya zama babban sakataren wannan ƙungiya.[4]
Ibrahim Zakzaki, ya haɗu da Imam Khomaini cikin wata tafiya da ya yi zuwa Faransa a shekarar 1978m, sannan bayan nasarar juyin juya halin Muslunci a Iran ya zo hauzar Ƙum domin karatun addini.[5] Ya bayyana yadda ya yi matuƙar tasirantuwa da Imam Khomaini da juyin juya halin Muslunci na Iran.[6] Da farko Zakzaki ya kasance Ahlus-Sunna mabiyin mazhabar malikiyya, amma bayan ganawarsa da Imam Khomaini sai ya zama ɗanshi'a.[7]
Ayyuka
Bayan juyin juya halin Muslunci na Iran, Zakzaky ya kai ziyara Iran, bayan dawowarsa ne ya samar da harkar Muslunci Najeriya.[8] Har ila yau, malamin ya kafa makarantun Islamiyya kusan guda 300 a Najeriya da maƙotanta.[9] Bugu da ƙari Zakzaki gama garin memba ne na Majma Jahani Ahlul-Baiti(Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya).[10] Ya kuma kafa mu'assasatul shuhada domin kula da ƴaƴan shahidai da kuma marayu, da mu'assasar Azzahra domin hidindimu ga al'umma daga taimakon ilimi da lafiya.[11]
A cewar Nusaiba ƴa ga shehin malamin, bisa ƙoƙarin babanta kusan mutum miliyan goma sha biyu suka shi'ance a Najeriya.[12] Kamar dai yadda Zakzaki ya faɗa da bakinsa, ayyukan tabligi da yake yi a ƙarshe-ƙarshen 1970 zuwa farkon 1980m, daidai lokacin nasarar juyin juya halin Muslunci, ya fara ne da jawo gomomin mutane, bayan shekaru goma sun kai dubunnan ɗaruruwa, sannan zuwa 2011 sun kai miliyoyi daga mabiya Ahlul-Baiti (A.S) a ƙasar Najeriya.[13]
Kamu Da Zaman Kurkuku

Lokacin taron arba'in na shekarar 2015m, da harkar muslunci ta shirya a Najerya, sojojin Najeriya sun kai hari kan masu shirya wannan taro, lamarin da janyo kashe gomomin mutane.[14] Zakzaki da matarsa su ma a farko watan Rabi'ul Awwal shekarar 2015m, a cikin wani hari da sojojin Najeriya suka kai kan Husainiyyar Baƙiyatullahi Zariya, wanda ya haifar da kashe ɗaruruwan ƴanshi'a da jikkata wasu adadi masu yawa, an kama su tare da tsare su a kurkuku.[15] Kafin faruwar wannan waƙi'a, a shekarar 2014m, jami'an tsaron Najeriya sun kashe mutane 33 a lokacin da suke gabatar da muzaharar ranar ƙudus, cikunsu har da ƴaƴan Zakzaki guda uku.[16]
Babban kotun tarayya ta Najeriya, a shekarar 2016m, ta ƙi amincewa da buƙatar sakin Shaikh Zakzaki[17] amma bayan wata guda ta fitar da hukuncin sakin shehin malamin[18] amma tare da haka ba a sake shi ba, a shekarar 2017m, shehin ya hallara gaban ƴanjarida bayan yaɗuwar jita-jitar mutuwarsa a kurkuku.[19] A watan Afrilu 2018m, cikin wayar tarho da ya yi tare da ɗansa Muhammad, ya bayyana cewa an kashe ƴanshi'a a Zariya a shekarar 2015m, sakamakon kuɗaɗe da ƙasar Saudi Arabiyya ta baiwa sojojin Najeriya.[20]Zakzaki a cikin shekarar 1981 zuwa 1989m, gwamnatin Najeriya ta ɗaure shi har kawo uku gaba ɗaya na tsawon shekaru bakwai.[21]
Martanoni
Kai hari kan ƴanshi'a, karkashe su da kama Zakzaki da matarsa a Najeriya, ya haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar Najeriya[22] da wasu yankuna na duniya daga jumlarsu Iran,[23]Amurka, Astiraliya, Seweden da Turkiyya.[24]
Husaini Wahid Khurasani, daga maraji'an taƙlidi na Shi'a, a watan Yuli 2014m, cikin martani kan kashe masu zanga-zangar ranar ƙudus ta duniya a Najeriya da kuma kashe ƴaƴan Zakzaki guda uku da sojojin Najeriya suka yi, cikin magana da ya yi da shehin malamin ta wayar tarho, ya yi masa ta'aziyyar shahadantar da ƴaƴansa guda uku.[25] Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar Muslunci ta Iran, ya kira Zakzaki da mutumin da aka zalunta a wannan duniya.[26]Cikin taron shuwagabannin ƙasar Iran da taron baƙin na taron haɗin kai na Muslunci, cikin ishara zuwa ga abin da ya faru a Najeriya, ya bayyana Zakzaki matsayin mutum mai son kawo gyara kuma Mumini mai son haɗin kai wanda aka kashewa ƴaƴa guda shida cikin shekaru biyu.[27] Haka nan Ayatullahi Khamna'i ya kira harin da jami'an Najeriya suka kai kan ƴanshi'a da bala'i mai girma[28] Shaik Isa Ƙasim, shugaban ƴanshi'a a Bahrain, ya bayyana harin da aka kaiwa ƴanshi'a tare da karkashe su da matsayin babban lefi, kuma haƙƙi ne da yake wuyan gwamnatin Najeriya.[29]

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, Hassan Ruhani, shugaban ƙasar Iran, bayan harin da jami'an tsaron Najeriya suka ƙaddamar kan Husainiyyar Baƙiyatullahi Zariya, cikin tattaunawa ta wayar tarho da ya yi tare da shugaban ƙasar Najeriya Muhammad Buhari, ya buƙaci shi da ya kafa kwamitin bincike don gano haƙiƙanin abin da ya faru.[31] Ma'aikatar harkokin waje ta Iran, cikin martini kan harin da aka kai kan ƴanshi'a a Najeriya, ta gayyaci jakadan Najeriya a Iran ta kuma nemi da a kare rayukan ƴanshi'a a Najeriya.[32]
Rashin zartar da hukuncin sakin Zakzaky, ya haifar da martini mai yawan gaske a cikin Najeriya. A lokacin taron arba'in na shekarar 2018m, wasu jama'a daga ƴanshi'ar Najeriya sun shirya zanga-zanga a babban birnin Abuja domin nuna rashin amincewa da ci gaba da tsare shi. Sai dai cewa sojojin Najeriya sun kai hari kan masu wannan zanga-zanga, bisa rahotan majiyoyin labarai, an kashe fiye da mutane 40.[33] Haka nan a ƙarshe-ƙarshen watan Yuli, lokacin da jikin Zakzaki ya tsananta lafiyarsa ta ksance cikin barazana, wasu jama'a daga ƴanshi'a a babban birnin Najeriya sun yi zanga-zanga tare da neman sakinsa, jami'an tsaron Najeriya sun kai musu hari, bisa rahotan majiyoyin labarai a wannan hari an kashe mutane 11 da jikkatta 30.[34]
Samun Ƴanci
A watan Yuli 2016m, an tsare tsawon shekaru shida tsakanin ɗaurin gida da na kurkuku, a ranar 28 ga Yuli 2021m, babban kotun tarayya ta wanke Zakzaky daga baki ɗayan tuhume-tuhumen da ake yi a kansa..[35]
Faɗaɗa Nazari
- Littafin “Shaikh Ibrahim Yaƙub Zakzaki Wa Naƙshe Bunyadin U Dar Shaklegiri Wa Gustaresh Tashayyu Dar Nijeriye” Na Amir Abraham Arab Ahmadi, Tehran, Kamfanin Negaristane Andishe ya buga a shekarar 2018m.
Bayanin kula
- ↑ Navaian Rudsari, Cehar Dehe Mujahadat Baraye Tablig Andishehaye Imam Dar Nijriye, Jaridar Khorasan, shafi. 12.
- ↑ Navaian Rudsari, Cehar Dehe Mujahadat Baraye Tablig Andishehaye Imam Dar Nijriye, Jaridar Khorasan, shafi. 12.
- ↑ Navaian Rudsari, Cehar Dehe Mujahadat Baraye Tablig Andishehaye Imam Dar Nijriye, Jaridar Khorasan, shafi. 12.
- ↑ Navaian Rudsari, Cehar Dehe Mujahadat Baraye Tablig Andishehaye Imam Dar Nijriye, Jaridar Khorasan, shafi. 12.
- ↑ "Sheikh Ibrahim Zakzaky; Rahbari Keh ba'is Geruyedne Miliyonha Afriqayi Beh Maktabe Ahlil-Baiti Shod, Jaridar Khorasan, shafi. 12.
- ↑ "Sheikh Ibrahim Zakzaky; Rahbari Keh ba'is Geruyedne Miliyonha Afriqayi Beh Maktabe Ahlil-Baiti Shod, Jaridar Khorasan, shafi. 12.
- ↑ «شیخ زکزاکی چگونه شیعه شد.» Kunshe akan gidan yanar gizon Gidauniyar Istifsar ta Duniya
- ↑ "Imam Khomeini, Munadi Haqqe Wa Ihyagere Tafakkur Dini, shafi. 26.
- ↑ Navaian Rudsari, Cehar Dehe Mujahadat Baraye Tablig Andishehaye Imam Dar Nijriye, Jaridar Khorasan, shafi. 12.
- ↑ «ارتحال والده شیخ ابراهیم زکزاکی/ حضور گسترده مسلمانان در مراسم تشییع والده رهبر شیعی نیجریه + تصاویر», Kamfanin Dillancin Labarai na Abna.
- ↑ «جنبش شیعیان نیجریه ، از شکلگیری تا کشتار زاریا»Shafin Yana gzo na Alwaqtu
- ↑ «پدرم ۱۲ میلیون نفر را به مذهب شیعه دعوت کرد»، Fars News.
- ↑ "Sheikh Ibrahim Zakzaky; Rahbari Keh ba'is Geruyedne Miliyonha Afriqayi Beh Maktabe Ahlil-Baiti Shod, Jaridar Khorasan, shafi. 12.
- ↑ «انتقام حماسه اربعین از شیعیان مظلوم نیجریه»، Yanar Gizon Jaridar Kayhan.
- ↑ Gafi، «Leader of Nigerian Shiite Muslims Arrested After Deadly Clashes With Army»،Gidan yanar gizon Newsweek;«بازداشت شیخ زکزاکی و کشتار شیعیان عزادار در نیجریه+تصاویر»،Shafin yanar gizo na Masreq News؛ «رئیس جمهور نیجریه خطاب به حسن روحانی: درباره حادثه زاریا تحقیق میکنیم»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars؛ «دلایل حمله به شیعیان نیجریه چه بود؟»، Nateqan Analytical News Base.
- ↑ «تسلیت تلفنی آیت الله وحید خراسانی به شیخ ابراهیم زکزاکی»Kamfanin dillancin labarai na Abna.،
- ↑ «مخالفت دادگاه عالی نیجریه با آزادی شیخ زكزاكی»،Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA.
- ↑ «دادگاه حکم آزادی فوری شیخ زکزاکی را صادر کرد»،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «افشاگریهای شیخ زکزاکی»، Gidan yanar gizon jaridar Siestas Rooz.
- ↑ «شیخ زکزاکی عربستان را عامل کشتار شیعیان نیجریه دانست»، Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA.
- ↑ "Imam Khomeini, Munadi Haqqe Wa Ihyagere Tafakkur Dini, shafi. 26. Sheikh Ibrahim Zakzaky; Rahbari Keh ba'is Geruyedne Miliyonha Afriqayi Beh Maktabe Ahlil-Baiti Shod, Jaridar Khorasan, shafi. 12.<
- ↑ Idame Kushtare Shi'ayane Dar Nijreye, jaridar Watan Emrooz, shafi. 15.
- ↑ «مراسم گراميداشت چهلم شهداي نيجريه در قم برگزار شد», Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA.
- ↑ «دستگیری روحانی مشهور شیعه و همسرش در آفریقا»،Kamfanin Dillancin Labarai na Rokna.
- ↑ «تسلیت تلفنی آیت الله وحید خراسانی به شیخ ابراهیم زکزاکی»، Kamfanin dillancin labarai na Abna.
- ↑ «دیدار رئیس و مسئولان قوه قضائیه با رهبر انقلاب»،Gidan yanar gizo na bayanai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ «بیانات در دیدار مسئولان نظام و میهمانان کنفرانس وحدت اسلامی»، ،Gidan yanar gizo na bayanai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei
- ↑ «بیانات در دیدار مسئولان نظام و میهمانان کنفرانس وحدت اسلامی»، پایگاه اطلاعرسانی دفتر حفظ و نشر آثار آیتالله خامنهای.
- ↑ «دستگیری روحانی مشهور شیعه و همسرش در آفریقا»، Kamfanin Dillancin Labarai na Rokna.
- ↑ «دیدار شیخ ابراهیم زکزاکی رهبر جنبش اسلامی نیجریه، همسر و فرزندان ایشان»، Shafin yada labarai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ «گزارش نیوزویک از شیخ زکزاکی قدرتمندترین روحانی شیعه در نیجریه»، Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA; «رئیس جمهور نیجریه خطاب به حسن روحانی: درباره حادثه زاریا تحقیق میکنیم»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ «گزارش نیوزویک از شیخ زکزاکی قدرتمندترین روحانی شیعه در نیجریه»،Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA;.
- ↑ «شمار قربانیان حمله ارتش نیجریه به عزاداران حسینی(ع) به 42 نفر رسید»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ «افزایش تعداد تلفات راهپیمایی مسالمتآمیز نیجریه به ۱۱ شهید + تصاویر», Kamfanin Dillancin Labarai na Abna.
- ↑ «گزارشهایی از تبرئه و آزادی شیخ زکزاکی از زندان»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
Nassoshi
- «ادامه کشتار شیعیان در نیجریه»، Jaridar Vatan Emrooz, Disamba 16, 2015.
- «ارتحال والده شیخ ابراهیم زکزاکی/ حضور گسترده مسلمانان در مراسم تشییع والده رهبر شیعی نیجریه + تصاویر»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Abna, ranar shigarwa: Nuwamba 18, 2014, ranar ziyarar: Nuwamba 25, 2018.
- «افزایش تعداد تلفات راهپیمایی مسالمتآمیز نیجریه به ۱۱ شهید + تصاویر»،Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, ranar bugawa: Agusta 1, 2019, kwanan wata: Agusta 2, 2019.
- «افشاگریهای شیخ زکزاکی», Gidan yanar gizon jaridar Siasat Rooz, ranar shigarwa: Janairu 15, 2017, kwanan wata ziyara: Nuwamba 1, 2023.
- «امام خمینی منادی حق و احیاگر تفکر دینی»، A cikin kwata-kwata mujallar "Huzor", No. 8, Fall 1994.
- «انتقام حماسه اربعین از شیعیان مظلوم نیجریه»، Gidan yanar gizon Jaridar Kayhan, ranar shigarwa: Disamba 12, 2015, kwanan wata ziyara: Nuwamba 1, 2023.
- «بازداشت شیخ زکزاکی و کشتار شیعیان عزادار در نیجریه+تصاویر», Shafin yanar gizo na Masreq, kwanan watan shigarwa: Disamba 12, 2015, kwanan wata ziyara: Nuwamba 2, 2018.
- «بیانات در دیدار مسئولان نظام و میهمانان کنفرانس وحدت اسلامی», Yanar Gizo don Kiyayewa da Buga Ayyukan Ayatullah Khamenei, Ranar Shiga: 29 ga Janairu, 2015, Ranar Ziyara: 29 ga Nuwamba, 2018.
- «پدرم ۱۲ میلیون نفر را به مذهب شیعه دعوت کرد», Fars News, Ranar shigarwa: Nuwamba 4, 2016, Ranar ziyarta: Nuwamba 1, 2023.
- «تسلیت تلفنی آیت الله وحید خراسانی به شیخ ابراهیم زکزاکی»، Kamfanin Dillancin Labarai na Abna, ranar bugawa: Agusta 1, 2014, kwanan wata ziyara: Nuwamba 1, 2023.
- "Harkokin Shi'a a Najeriya, tun daga kafuwarta har zuwa kisan kiyashin Zariya", gidan yanar gizon Al-Waqt, ranar shigowa: Fabrairu 12, 2017, ranar ziyarar: 2 ga Nuwamba, 2018.
- «دادگاه حکم آزادی فوری شیخ زکزاکی را صادر کرد», Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, Ranar aikawa: Disamba 1, 2016, Ranar Ziyara: Nuwamba 4, 2018.
- «دستگیری روحانی مشهور شیعه و همسرش در آفریقا»،Kamfanin Dillancin Labarai na Rokna, ranar shigarwa: Disamba 5, 2019, kwanan wata ziyara: Nuwamba 2, 2023.
- «دلایل حمله به شیعیان نیجریه چه بود؟», Natiqan Analytical News Yanar Gizo, Kwanan buga: Disamba 14, 2015, Ranar ziyarta: Nuwamba 1, 2023.
- «دیدار رئیس و مسئولان قوه قضائیه با رهبر انقلاب»،Shafin yanar gizo na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei, ranar shiga: 1 ga Yuli, 2017, ranar ziyarar: 2 ga Nuwamba, 2018.
- «دیدار شیخ ابراهیم زکزاکی رهبر جنبش اسلامی نیجریه، همسر و فرزندان ایشان»،Ofishin kiyayewa da buga ayukkan Jagora Ayatullah Khamenei, ranar shiga: 12 ga Oktoba, 1402, ranar ziyarar: 2 ga Nuwamba, 1402.
- «رئیسجمهور نیجریه خطاب به حسن روحانی: درباره حادثه زاریا تحقیق میکنیم», Gidan yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, ranar shigarwa: Janairu 29, 2015, kwanan wata: Nuwamba 29, 2018.
- «شمار قربانیان حمله ارتش نیجریه به عزاداران حسینی(ع) به 42 نفر رسید», Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, Ranar shigowa: Nuwamba 2, 2018, Ranar ziyarta: Nuwamba 2, 2023.
- «شیخ ابراهیم زکزاکی؛ رهبری که باعث گرویدن میلیونها آفریقایی به مکتب اهل بیت شد»،Jaridar Khorasan, Lamba 18908, 16 ga Fabrairu, 2014, kwanan wata: Nuwamba 1, 2023.
- «شیخ زکزاکی چگونه شیعه شد.» An buga akan gidan yanar gizon Gidauniyar Bincike ta Duniya, kwanan wata ziyara: 8 ga Agusta 1404.
- «شیخ زکزاکی عربستان را عامل کشتار شیعیان نیجریه دانست»،Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA, kwanan watan bugawa: Mayu 27, 2018, kwanan wata ziyara: Nuwamba 2, 2018.
- «گزارش نیوزویک از شیخ زکزاکی قدرتمندترین روحانی شیعه در نیجریه»،Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA, ranar shiga: 17 ga Disamba, 2015, ranar ziyarar: 2 ga Nuwamba, 2018.
- «گزارشهایی از تبرئه و آزادی شیخ زکزاکی از زندان»،Kamfanin Dillancin Labaran Fars, ranar shigarwa: 26 ga Agusta 1401, kwanan wata: 21 Nuwamba 1403.
- گفی، کانر، «Leader of Nigerian Shiite Muslims Arrested After Deadly Clashes With Army»، Gidan yanar gizon Newsweek, ranar shigarwa: Disamba 14, 2015, kwanan wata ziyara: Nuwamba 25, 2018.
- «مخالفت دادگاه عالی نیجریه با آزادی شیخ زكزاكی»، Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA, kwanan watan bugawa: Satumba 29, 2016, kwanan wata ziyara: Nuwamba 1, 2023.
- «مراسم گراميداشت چهلم شهداي نيجريه در قم برگزار شد»، Gidan yanar gizon IRNA, kwanan shigarwa: Fabrairu 1, 2015, kwanan wata ziyara: Nuwamba 2, 2023.
- نوائیان رودسری، جواد، «چهار دهه مجاهدت برای تبلیغ اندیشههای امام در نیجریه»، Jaridar Khorasan, No. 18908, Fabrairu 16, 2014.