Husaini daga Gareni Yake

Daga wikishia
Hotan ƙofar shiga Haramin Imam Husaini (A.S)

Husaini daga gareni yake ni ma kuma daga Husaini nake, (arabic: حسين مني وأنا من حسين) wani Hadisi ne na Annabi da aka nakalto shii a mafi Tsufan Littafan Hadisi na Shi’a da Ahlusu-sunna cikin Falalolin Imam Husaini (A.S) an nakalto cikin littafin Al-musannaf na Ibn Abi Shaiba Malamin Hadisi daga bangaren Ahlus-sunna wanda ya mutu a shekara ta 235 haka Ibn Kaulawaihi Marubicin Littafin Kamilul Azziyaratwanda ya bar duniya shekara 368 Dukkaninsu suna bayanin Falalolin Imam Husaini (A.S) wasu ba’ari sun tafi kan cewa wannan Hadisi yana nuni da dayantuwar Ruhin Annabi (S.A.W) dana Imam Husaini (A.S) sakamakon soyayyarsa sababin samun soyayyar Allah ce kuma wannan hadisi yana ishara kan mikewa Imam Husaini (A.S) da dorewar tsatson Imaman Shi’a (A.S) haka kuma wasu Masu zurfafa bincike kan tarihi sun tafi kan cewa Jumlar (ni daga Husaini nake tana ishara ne zuwa ga Mikewa da yunkurin Imam Husaini (A.S) wacce da ita addinin Muslunci ya samu wanzuwa An rubuta wannan Hadisi a Kofar shiga Haramin Imam Husaini (A.S)

Gabatarwa da Kuma Matsayi

An rubuta wannan hadisi (Husaini daga gareni yake) a jikin Kabarin Imam Husaini (A.S), a cewar Assayid cikin ambaton Falalolin Imam Hausaini (A.S) hakika Hadisin (Husaini daga gareni yake) yana daga cikin hadisan Annabi (S.A.W), Allama Hashim Bahrani ya bayyana cewa wannan hadisi yana nuni kan irin soyayyar da Annabi (S.A.W) yake yiwa Imam Husani (A.S), an rubuta wannan Hadisi a bakin kofar shiga Haramin Imam Husaini [1] wannan hadisi ya zo a cikin masadir din `Yan Shi’a daga Ahlus-Sunna masu yawa, haka wannan Riwaya an rubuta ta a jikin Kusurwa Shida ta Jikin Hubbaren Imam Husaini (A.S)[2] Husaini daga gareni yake [3] Hazrat Muhammad (S.A.W) a kan hanyar zuwa wani Walima ya ga Husaini (A.S) yana wasa [4] tareda wasa Yara, sai Annabi (S.A.W) ya je ya tarfe shi ya bue Abokansa ya dauko shi sannan yace:

«حُسَیْنٌ مِنِّی وَ أَنَا مِنْ حُسَیْنٍ، أَحَبَّ اَللَّهُ مَنْ أَحَبَّ حُسَیْناً، حُسَیْنٌ سِبْطٌ مِنَ اَلْأَسْبَاطِ؛

Husaini daga gareni yake kuma ni daga Husaini nake, Allah ya so mai son Husaini, Husaini Jikane daga Jikokin Annabawa. [5]

Zanen hadisin "Hussein Minni" akan Haramin Imam Husaini (A.S).

Abin da Hadisin ya tattaru akai

Rubuta wannan Hadisi a jikin Dutse a Masallacin Alkahira da yake kasar Misra. A cewar wasu ba’arin Masu zurfafa binicike, hakika abinda wannan yake tattare da shi ya kunshi wasu abubuwa kamar haka:

  • dayantuwar Ruhin Annabi (S.A.W) dana Husaini (A.S)
  • soyayyar Husaini (A.S) sababi ce ta soyayyar Allah
  • ta hanyar Husaini (A.S) tsatson Imaman Shi’a ya mike ya cigaba [6]

Amnawi wanda ya bar duniya shekara 1031 hijiri Kamari daya daga cikin Malaman Mzahabar Shafi’iya cikin sharhinsa kan wannan hadisi yace me ya rigaya ya sani tsakanin Husaini (A.S) da al’ummarsa, Alkadi Waki’u ya nakalto yana cewa kai kace Annabi (S.A.W) yana Magana kan wani abu mara dadi da zai faru da haka ne ya ambaci sunan Husaini Kadai cikin riwayar wanda ta ke nuna cewa taba mutuncin Husaini da yakarsa daidai yake da taba mutuncin Annabi da yakarsa wannan ya bayyana cikin jumlar Allah ya so wanda yake son Husaini, saboda son Husaini (A.S) Son Manzon Allah (S.A.W) ne kuma Son Manzon Allah, Son Allah ne [7] Bakir Karashi wanda ya mutu a shekara 1433 hijiri Kamari, Mai zurfafa bincike kan tarihi da rayuwar Ahlil-Baiti yace Mikewar Imam Husaini (A.S) ta zama sababin samun kariyar Muslunci addinin Husaini (A.S) kuma yunkurinsa ne ya zama sanadiyar wanzuwar muslunci [8]

Masadir da Ingancin Hadisin

Mafi tsufan Masdarin Hadisi da ya nakalto (Husaini daga gareni yake) shine Littafin Almusannaf na Ibn Abi Shaiba wanna ya kasance Malamin Ahlus-Sunna [9] wanda ya bar duniya shekara 235 ya kuma bayyana cewa [10] dukkanin Rijal din isnadin Muwassakai ne [11] sai kuma littafin Kamilul Ziyarat talifin Ibn Kaulawaihi Malamin Shi’a wanda ya bar duniya shekara 368 Sharh Akbar talifin Kadi Numan [12] wanda ya bar duniya shekara 368 hijiri Kamari shima ya kawo wannan hadisi, da kuma sauran Masadir da suka kawo shi kamar Kitabul Ershad na Shaik Mufid [13] wanda ya bar duniya shekara 413 hijiri Kamari, 24 Allama Majlisi [14] ya tafi kan cewa littafin Kamalul ziyarat yana daga shahararrun ingantattun Asalai a wurin Malaman fikihun Shi’a Wannan Riwaya an nakalto ta kan asasin Kamilul Azziyarat kamar haka: Muhammad Bn Abdullahi Jafar Marawaitan Silsilar Isnadin Himyari, Abi Sa’id Hassan Bn Ali Bn Zakariya Adawi Basari, Abudl A’ala Bn Hammad Bursi, Wahab [15] Bn Abdullahi Bn Usman, Sa’idu BN Abi Rashid da kuma Ya’la Amiri Sunanu Ibn Majaj [16] shima yana cikin Masadir din da suka kawo wannan hadisi, sannan wannan hadisi ya zo cikin Musnad Ahmad Bn Hanbal, [17] da Almustadrak Alal sahihaini [18] talifin Hakima Naishaburi [19]Tirmizi yana ganin wannan Hadisin ya kai mukamin Hasanu [20] Haitami [21]Naishaburi sun bashi matsayin sahihi

rubutunb kan dutse daga Hadith Hossein Minni wa Anna Min Hossein a Masallacin Al-Hussein da ke birnin Alkahira.

Bayanin kula

  1. Bahrani, Hilyatu Al-Abrar, 1411 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 127
  2. Ranjbarhosseini wa Haeri, "Barasi Itibar wa Dalalatu hadisi Nabawi, Hossein Minni wa Anna Min Hossein", shafi na 7.
  3. <a class="external text" href="https://www.farsnews.ir/news/13911215001380">«آیات، روایات و مضامین به کار رفته بر روی ضریح جدید امام حسین»</a>
  4. Ibn Quluweh, Kamel Al-Ziyarat, 1356H, shafi na 53.
  5. Ibn Quluweh, Kamel Al-Ziyarat, 1356H, shafi na 53.
  6. Ranjbarhosseini wa Haeri, "Barasi Itibar wa Dalalatu hadisi Nabawi, Hossein Minni wa Anna Min Hossein", shafi na 8
  7. Manavi, Faiz Al-Qadir, 1356 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 387.
  8. Qurashi, Hayat Al-Imam al-Hussein, 1398 AH, juzu'i na 1, shafi na 94; Mousavi Garmarodi, Farhang Ashura, 1368, shafi na 163.
  9. Ibn Abi Shaibah, Al-Musannaf, 1409H, juzu'i na 6, shafi na 380.
  10. Ranjbarhosseini wa Haeri, "Barasi Itibar wa Dalalatu hadisi Nabawi, Hossein Minni wa Anna Min Hossein", shafi na 9
  11. Ibn Quluyeh, Kamel al-Ziyarat, 1356H, shafi na 53.
  12. Ibn Quluweh, Kamel al-Ziyarat, 1356H, shafi na 53.
  13. Sheikh Mofid, Al-Arshad, 1413 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 127.
  14. Ranjbarhosseini wa Haeri, "Barasi Itibar wa Dalalatu hadisi Nabawi, Hossein Minni wa Anna Min Hossein", shafi na 8
  15. Ibn Quluweh, Kamel al-Ziyarat, 1356H, shafi na 53.
  16. Ibn Hanbal, Musnad, 1421H, juzu'i na 29, shafi na 103.
  17. Ibn Majah, Sunan, 1418 AH, juzu'i na 1, shafi na 101.
  18. Tirmizi, Sunan Tirmizi, 1419 AH, juzu'i na 5, shafi na 658.
  19. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 194.
  20. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 194.
  21. Haytami, Majma Al-Zawaed, 1414 AH, juzu'i na 9, shafi na 185.

Nassoshi

  • <a class="external text" href="https://www.farsnews.ir/news/13911215001380">«آیات، روایات و مضامین به کار رفته بر روی ضریح جدید امام حسین»</a>Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, ranar buga labarin a ranar 15 ga Maris, 2011, ranar ziyarar 1 ga Yuni, 1402.
  • Qazoor Tehrani, Mohammad Mohsen, Al-Dhari'a Ila Tasaneef Al-Shi'a, Beirut, Dar al-Awat, 1403 AH.
  • Ibn Abi Shaiba, Abdullah Ibn Muhammad, al-Musnaf Fi Ahadith and Works, Riyadh, Al-Rashad School, 1409 AH.
  • Ibn Hanbal, Ahmad, Musnad, Beirut, Al Risala Foundation, 1421H.
  • Ibn Qolwieh, Jafar bin Muhammad, Kamel Al-Ziyarat, Najaf, Dar al-Murtazawieh, 1356H.
  • Ibn Majah, Muhammad bin Yazid, Sunan, Bija, Mazhabar Abi al-Maati, 1418H.
  • Bahrani, Seyyed Hashem, Hilyatul-Al-Abrar fi Ahwaal Muhammad wa Alayh al-Athar (amincin Allah ya tabbata a gare su), Qum, Cibiyar Nazarin Musulunci, 1411H.
  • Tirmizi, Muhammad bin Isa, Sunan, Alkahira, Mustafa Al-Babi Al-Halabi Press, 1395 AH.
  • Hakim Neishaburi, Abu Abdullah, Al-Mustadrak Ali al-Sahihin, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1411H.
  • Ranjbarhosseini, Mohammad dan Majdeh Haeri <a class="external text" href="http://www.maarefehosseini.ir/article_93305_d73116f8a414d3230e7c791516f6dfa9.pdf">«بررسی اعتبار و دلالت حدیث نبوی:حسین منی و انا من حسین»</a>
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad bin Nu'man, Al-Arshad fi Mafarah Hajjullah Ali al-Abad, Qum, Sheikh Mofid Congress, 1413 AH.
  • Qurashi, Baqer Sharif, Hayat al-Imam al-Hussein, 1398 AH/1974 AD.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
  • Mashar, Khanbaba, Fihirast Kitabahaye cafe Arabi, Bija, Bina, 1344.
  • Maghribi, Noman bin Muhammad, Sharh al-Akhbar fi dhadael al-Imam al-Athar, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Qom, Jamia Madrasin, 1414 AH.
  • Manawi, Zainul-Din Mohammad, Faiz al-Qadir, Masar, Al-Kubra Al-Tajjariyah School, 1356H.
  • Nawi, Yahya bin Sharaf, Tahhib al-Asmaa wa Al-Laghat, Damascus, Dar Risala Al-Alamiya, 1430H.
  • Haytami, Ali bin Abi Bakr, Majma al-Zawaed kuma tushen fa'ida, Alkahira, Mazhabar Qudsi, 1414H.