Huɗuba Mai Lamba 115 A Cikin Nahajul Balaga

Daga wikishia
Ƙasidar huɗuba mai lamba 115 tana da alaƙa da Huɗuba Mai Lamba 143 A Cikin Nahajul Balaga.

Huɗuba mai lamba 115 ko huɗubar istisƙa (Larabci: الخطبة 115 نهج البلاغة أو خطبة الإستسقاء) neman ruwan sama, wata addu'a ce da ake yi domin neman saukar ruwan sama, an yin wannan addu'ar ne bayan idar da sallar roƙon ruwa sama da ta guda a ɗaya daga garuruwan kufa da suka fuskanci fari da yankewar ruwan sama a lokacin halifancin Imam Ali (A.S). an bada rahoto cewa Shaik Saduƙ da Shaik Ɗusi sun rawaito wannan huɗuba tare da bamabcin jumloli. Kan wannan asasi ne ake tsammani da cewa ɗaya daga malaman hadisi yana da kwafi nasa na musamman daga wannan huɗuba, haka nan ana cewa akwai tsammanin Sayyid Radiyu ya naƙalto wani ɓangare da jumlolin Shaik Saduƙ, haƙiƙa wani sashe daga huɗubar istisƙa ya zo cikin madogaran riwaya na ahlus-sunna.

Huɗubar istisƙa ta ƙunshi sashe biyu na asali, sashe na farko, Imam Ali (A.S) ya yi ishara game da irin yadda fari da yankewar ruwan sama yake tasiri ga mutane da ɗabi'a kai har ma da dabbobi, ɗaya daga cikin dalilai da sabubban da suke haifar da afkuwar fari wakai aikata zunubai da saɓo da mutane ke yi. A sashe na biyu nan ma cikin roƙon ruwan sama daga ubangiji, Imam ya yi ambaci wasu hususiyoyi game da ruwan sama, yana roƙon Allah ya saukar da duk wani abu da yake da amfani ga mutane da ɗabi'a ya kuma nesantar duk wani abu da zai zama hijabi ko shinge. An yi umarni da karanta wannan addu'a lokacin sallar roƙon ruwan sama.

Taƙaitaccen Tarihi

Huɗuba mai lamba 115 cikin littafin nahajul balaga ko huɗubar roƙon ruwa, wata addu'a ce da ake yi domin roƙon ruwan sama a lokutan da aka fuskanci fari da yankewar ruwan sama, wace Imam Ali (A.S) ya yi bayaninta bayan idar da sallar roƙon ruwan sama.[1] a cewar Makarim Shirazi yana da kyau sosai a ce an karanta wannan huɗuba yayin sallar roƙon ruwa.[2]

Huɗubar istisƙa an naƙalto ta cikin litattafan Man La Yahdurul Al-faƙihu na Shaik Saduƙ (Rayuwa: 305-381. h. ƙ)[3] Tahzibul Al-ahkam[4] da Misbahul Al-mutahajjid[5] na Shaik Ɗusi (Rayuwa: 385-460. h. ƙ), tare da bambancin kalmomi. A cewar Abdul-zahara Husaini (Rayuwa: 1338-1414. h. ƙ) cikin littafin Masadiru Nahjil Al-balaga, saɓanin da aka samu cikin naƙalin wannan huɗuba yana nuni cewa Shaik Saduƙ, Sayyid Radiyu (Rayuwa: 359-406. h. ƙ) da Shaik ɗusi ko wane ɗaya cikinsu ya dogara ne da keɓantacciyar madogara cikin naƙalto wannan huɗuba.[6] Habibullahi Khuyi (Rayuwa: 1265-1324. h. ƙ), yana ganin cewa Sayyid Radiyu ya ɗauko wannan huɗuba ne daga Shaik Saduƙ.[7] sannan daga cikin madogaran ahlus-sunna da suka kawo wani sahse daga wannan huɗuba akwai misalin Zamakshari (Rayuwa: 467-538. h. ƙ) cikin Rabi'ul Al-abrar[8] da Ibn Asir (Rayuwa: 555-630. h. ƙ) cikin Al-nihaya.[9]

Abin da Yake Cikin Huɗubar

Huɗubar Istisƙa ta fara ne tare da bayanin matsaloli da suka faru sakamakon yankewar ruwan sama, ɗaya daga cikin sabubun ɓullar fari da ƙamfar ruwan sama shi ne aikata zunubi da mutane ke yi, ciki ci gaba an roƙi Allah da ya saukar da ruwan sama tare da keɓanatattun hususiyoyi.[10]

Sunan Kwafi Lambar Huɗuba
Al-mujam Al-mufahras Wa Subhi Salih 115
Faizul Islam 114
Khuyi, Mulla Salih 114
Ibn Abil Al-hadid 114
Muhammad Abduhu 109
Mulla Fatahullahi 136
Fi Zilal 113
Ibn Maisam 112.[11]

Tuba Daga Zunubai Tare da Fatan Rahamar Allah

A sashe na farkon wannan huɗuba Sayyidina Ali (A.S) ya suranta yadda matsananci fari ya kasance a wancan zamani tare da bayanin halin duwatsu da ƙasa da yanayin da wuraren kiwon dabbobi suka zama,[12] faruwar wannan bala'I ya sanya mutane ɗebe fata da kuma shiga wahalhalu, ya roƙi Allah ka da ya yi musu uƙuba da ayyukan zunuban da suka aikata. Waɗannan jumloli suna nuni da cewa da yawan matsaloli da mutane suke samun kansu ciki, sun faru ne sakamakon zunubansu, kuma matuƙar mutane ba su koma zuwa ga Allah ba sun roƙe shi gafara da afuwa ba, babu ranar da zasu fita daga cikin halin d asuke ciki.[13] Ibn Maisam Baharani (Rayuwa: 636-679 ko 699. h. ƙ) a cikin sharhin nahajul balaga da ya rubuta shi ma yana ganin ɗaya daga sabubba da dalilai masu tasiri cikin ɓullar wahalhalu da haramtuwar mutane daga rahamar ubangiji akwai saɓawa umarni Allah.[14] Bayan nan sai Imam Ali (A.S) ya yi bayanin asalin buƙatarsa zuwa ga Allah tare da neman Allah ya saukar da rahamarsa ta hanyar hadari mai ɗauke da ruwan sama tare da kaka mai ni'ima da korayen shuka ɗanyaku masu faɗaɗuwa, Allah ya saukar da ruwan sama mai tsirar da kakkauran ƴaƴan shuka da zai rayar da matacciyar ƙasa ya dawo da abin da aka rasa.[15]

Ruwan Sama Mai ɗauke Da Alheri Wanda Babu Sharri Cikinsa

Imam Ali (A.S) a sashe na biyu daga wannan huɗuba ya roƙi Allah saukar da ruwa ya kuma bayyana wasu siffofi. A cewar Makarim Shirazi ko wane ɗaya daga waɗannan siffofi, wata dandaƙaƙƙiyar ishara ce mai bam mamaki. Wannan siffofi, suna ƙasƙantar da mutum gaban mahaliccinsa kuma tana fahimtar da masu saurare waɗannan ɗigon ruwan sama wace irin albarka da kufaifayi zai iya kasancewa tare da su.[16]

An ce Imam Ali (A.S) don haka ya bayyana wasu halayen ruwan saman da yake neman da Allah ya saukar musu, domin ruwan sama na iya kasance mai kawo ambaliya wanda kuma zai iya lalata komai. Ko kuma yana iya sauka a keɓantaccen wuri wanda amfaninsa ba zai game ko ina da ko ina ba, ko kuma ya kasance tare iska mai tsananin sanyi ya kuma haifar da abubuwa marasa kyau. Ko kuma tare da shinge da hijabi misalin iska mai zafi da matsananci guguwa, cutuwa ga shuka, ɗauke da kwari masu cutarwa da misalinsu, wanda haka na iya tafiyar da albarkokin ruwan da ya sauka. Cikin addu'ar Imam Ali (A.S) duk waɗannan abubuwa an yi la'akari da su, ya kuma roƙi Allah dukkanin alheri tare da tunkuɗe duk wani shinge da hijabi.[17]

Bayanin Kula

  1. Makarem Shirazi, Payame Imam Amir al-Momenin (AS), 1386, juzu'i na 5, shafi na 125 da shafi na 131-13.
  2. Makarem Shirazi, Payame Imam Amir al-Mominin (AS), 1386, juzu'i na 5, shafi na 126.
  3. Sheikh Sadouƙ, Man Lay Hazara Al-Faƙih, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi na 527-535.
  4. Sheikh Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 3, shafi na 151-154.
  5. Sheikh Tusi, Mesbah al-Mutahajjid wa Selah al-Muta'abbid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 227-230
  6. Hosseini, tushen Nahj al-Balaghah da Asanidah, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 252.
  7. Hashemi Khoei, Minhaj al-Bara'a fi Sharh Nahj al-Balaghah, 1400 AH, juzu'i na 8, shafi na 72.
  8. Zamakhshari, Rabi al-Abrar wa Nusus al-Akhbar, 1412 AH, Mujalladi na 1, shafi na 128-129.
  9. Ibn Athir, Al-Nahiya fi Gharib al-Hadith, 1399 AH, Juzu'i na 2, shafi na 448.
  10. Makarem Shirazi, Payame Imam Amir al-Mominin (AS), 1386, juzu'i na 5, shafi na 126.
  11. Dashti wa Mohammadi, Al-Mu'jajm Al-Mufars Lalfaz Nahj al-Balagha, 1375, shafi na 510.
  12. Makarem Shirazi, Payame Imam Amir al-Momenin (AS), 1386, juzu'i na 5, shafi na 129.
  13. Makarem Shirazi, Payame Imam Amir al-Mominin (AS), 1386, juzu'i na 5, shafi na 131.
  14. Ibn Maitham Bahrani, Sharhu Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 3, shafi na 105-106.
  15. Makarem Shirazi, Payame Imam Amir al-Momenin (AS), 1386, juzu'i na 5, shafi na 132.
  16. Makarem Shirazi, Payame Imam Amir al-Mominin (AS), 1386, juzu'i na 5, shafi na 134.
  17. Makarem Shirazi, Payame Imam Amir al-Momenin (AS), 1386, juzu'i na 5, shafi na 135.

Nassoshi

  • Ibn Athir, Mubarak bin Muhammad, Al-Nahiya fi Gharib al-Hadith da Al-Athr, Beirut, Al-Maqabah Al-Elamiya, 1399H.
  • Ibn Maitham Bahrani, Maitham bin Ali, Sharhe Nahj al-Balagha, Tehran, ofishin buga littattafai, 1404H.
  • Dashti, Mohammad wa Kazem Mohammadi, Al-Mu'jajm Al-Mufahras lil Nahj al-Balagheh Words, Qom, Amir al-Mominin Research Institute (AS), 1375.
  • Husseini, Abd al-Zahra, Masadir Nahj al-Balaghah wa Asanidah, Beirut, Dar al-Zahra, 1409H.
  • Zamakhshari, Mahmoud bin Omar, Rabi al-Abrar wa Nasus al-Akhbar, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1412 AH.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man Lai Hazara Al-Faqih, bincike da: Ali Akbar Ghafari, Qum, ofishin da'awar Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Qum, bugu na biyu, 1413 AH.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Tahzeeb al-Ahkam, wanda: Hassan Khorsan, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya ya yi bincike, bugu na 4, 1407H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Misbah al-Mutahajjd wa Selah al-Muta'abbid, Beirut, Cibiyar Fiqh al-Shi'a, bugu na farko, 1411H.
  • Makaram Shirazi, Nasser, Payame Imam Amir al-Mominin (AS), Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1386.
  • Hashemi Khoi, Habibullah, Minhaj al-Baraa' afi sharhe Nahj al-Balaghah, ya yi bincike daga: Ibrahim Mianji, Tehran, Laburaren Musulunci, bugu na 4, 1400H.