Hammalatul Haɗabi
Hammalatul Haɗabi, (arabic: حمالة الحطب)(wacce take ɗaukar ɗaurin ƙirare a kafaɗa) haka Alkur’ani ya siffanta matar Abu Lahabi [1] Matar Abu Lahabi `yar uwar Abu Sufyan kuma gwaggon Mu’awiya, [2] ana mata Alkunya da Ummu Jamil kuma ana kiranta da Aruye Jamila. [3] da Sakhara [4] An yi amfani da wannan jumla a suratul Masad, [5] dangane da cewa me yasa Alkur’ani ya yi amfani da wannan siffa a kanta, akwai maganganu da aka kawo: Ummu Jamil tana zuwa da ɗebo ƙayoyi a daji ta ɗauko su a kafaɗarta lokacin da Annabi (S.A.W) zai tafi sallar sai ta dinga zuba wannan ƙaya a kan hanyar da yake bi domin ya taƙa yaji ciwo. [6] Ummu Jamil sakamakon aikin da ta aikata ta tanadarwa kanta da kanta wuta da ƙirare a Jahannama. [7] Ta kasance tana yiwa Annabi (S.A.W) isgilanci sakamakon kasancewarsa talaka, da wannan dalili Allah ya wulaƙantata cikin wannan siffantawa. [8] Wannan jumla kinaya ce daga Annamimancinta. [9] Ya zo cikin tafsir Namuneh cewa bakiɗayan waɗannan wurare da aka ambata basa cin karo da juna kuma za su iya kasancewa ma’anar abin da ake nufi daga yar kenan. [10]
Bayanin kula
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 27, shafi na 420
- ↑ Ibn Abd Al-Barr, Al-Istiy'ab, 1412H, juzu'i na 3, shafi na 1430
- ↑ Sheikh Tusi, Al-AMali, 1414 AH, shafi na 265.
- ↑ Meybodi, Diwan Amir Al-Mu’minin (AS), 1411 AH, shafi na 92.
- ↑ Suratul Masad, aya ta 4.
- ↑ Ɗabarasi, Majma Al Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi.852.
- ↑ Motahari, Majmu'eh Asar, Beta, juzu'i na 28, shafi na 825>
- ↑ Fakhr Razi, Mufatih al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 32, shafi na 353.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Tabyan, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 10, shafi na 428.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 27, shafi na 421.
Nassoshi
- Ibn Abd Al-Barr, Yusuf bin Abd Allah, Al-Istiy'ab fi Marifah Al-As'hab, bincike na Ali Muhammad al-Bajawi* Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatih al-Ghaib, Beirut, Dar Ihya al-Tarat al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, bugun farko, 1374.
- Meibdi, Hossein bin Moinuddin, Diwan Amir Al-Mu’minin, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, wanda Mustafa Zamani ya fassara, ƙom, Dar Nada al-Islam Llanshar, bugu na farko, 1411H.
- Motahari, Morteza, Majmu'eh Asar, ƙom, Sadra Publications, bugu na farko, 2009.
- Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, gabatarwar Mohammad Javad Balaghi, Tehran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
- Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Amali, Kum, Darul Taƙfa, bugun farko, 1414H.
- Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsir al-ƙur'an, bincike da Ahmad ƙusayr Aamili, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, Beirut, Bita, Beirut, Dar al-Jeel, bugun farko, 1412 Hijira.