Hajjaju Bn Masruƙ

Daga wikishia
(an turo daga Hajjaju Bin Masruƙ)
Makwancin Shahidan Karbala

Hajjaju Bin Masruƙ Muzhiji Ju’ufi (Larabci: الحجاج بن مسروق الجعفي) ɗaya daga cikin Sahabban Imam Ali (A.S) da Imam Husaini (A.S) wanda ya yi shahada a ranar Ashura a filin Karbala. Wasu ba’arin masadir sun kira shi Ladanin Imam Husaini (A.S) cikin tafiyarsu daga Makka zuwa Karbala.

Suna Da Nasaba

Hajjaju Bin Masruƙ Malik Bin Kasif Bin Utba Bin Kila’u Ju’ufi, [1] daga ƙabilar Muzhiju, Shaik Mufid [2] ya raubuta cewa sunansa Hajjaju Bin Masrur.

Tarihi A cewar Muhammad ɗahir Samawi haƙiƙa Hajjaju Bin Masruƙ ya kasance daga Shi’a kuma Sahabban Imam Ali (A.S) a garin Kufa, lokacin da Imam Husaini (A.S) ya ta so daga Madina ya nufi Makka sai shima ya ta so daga Kufa ya nufi Makka, a can ne ya shiga cikin ayarin Imam Husani (A.S). [3] A gidan Zu Hasam, a lokacin da ayarin Imam ya gana da sojojin Kufa ƙarkashin jagorancin Hurru Bin Yazid Riyahi, da tsakar rana, sai Imam ya ce wa Hajjaj bin Masruƙ ya yi kiran Sallah. [4] Lokacin da ayarin Imam Husaini (A.S) suka isa gidan ƙasre Bani Maƙatil, sai ya ga wani kafaffen tanti, sai ya yi tambaya shi wannan Tanti Na wanene ? sai suka ce masa na Ubaidullahi Bin Hurrul Ju’ufi, sai ya aika Hajjaju Bin Masruƙ Ju’ufi wajensa domin kiransa ya zo ya taimakawa Imam Husaini (A.S) sai dai cewa bai karɓi gayyatar ba. [5]

Shahada

A ranar Ashura Hajjaju Bin Masruƙ ya karɓi izini daga Imam Husaini (A.S) ya kutsa fafen daga ya gwabza yaƙi da Maƙiya bayan wani lokaci sai ya dawo wurin Imam Husaini (A.S) jikinsa jike da jini ya yi magana da Imam cikin rera waƙa:

فدتک نفسی هادیا مهدیا الیوم ألقی جدّک النبیا

ثمّ أباک ذی الندی علیا ذاک الذی نعرفه الوصیا[۶][یادداشت ۱]

raina fansarka ya shiryayye mai shiryarwa. Ranar da zan haɗu da kakanka Annabi. Sannan babanka ma’abocin karamci Aliyu Shi ne wannan wanda muka sani Wasiyyi. [6] [yadsht 1] Sai Imam yace: na’am wannan magana haka take nima bayanka zan haɗu da su, sannan Hajjaj ya koma fagen yaƙi ya cigaba da gwabza yaƙi har sai da ya yi shahada. [7] Cikin ziyaratu Nahiya Muƙaddasa wacce ta shahara da (Ziyaratu Shuhada) da kuma cikin Ziyaratu rajabiyya Imam Husaini (A.S) nan ma an ambaci sunan Hajjaju Bin Masruƙ:

«السَّلَامُ عَلَی الْحَجَّاجِ بْنِ مَسْرُوقِ الْجُعْف

Amincin Allah ya tabbata kan Hajjaju Bin Masruƙ

Bayanin kula

  1. Balazri, Ansab Al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 3, shafi na 199.
  2. Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 78.
  3. Samawi, Absar Al-Ain, 1419 AH, shafi na 151.
  4. Tabari, Tarikh Al'umam wa Al-Muluk, 1387 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 401
  5. Samavi, Absar Al-Ain, 1419 AH, shafi na 151; Hosseini Haeri Shirazi, ZoKhirat Al-Daraini, Zamzam Hedayat, shafi na 407.
  6. Samawi, Absar Al-Ain, 1419 AH, shafi na 151.
  7. Samawi, Absar Al-Ain, 1419 AH, shafi na 151.

Nassoshi

Belazari, Ahmad bin Yahya, Ansab Al-Ashraf, Beirut, Darul Fikr, bugu na farko, 1* ƙomi, Sheikh Abbas, Nafs Al-Mahmoum fi Misibah Sayyidna al-Hussein al-Mazloum, ƙum, Al-Maktab Al-Haydaria Publications, bugu na farko, 1421H.

  • Hosseini Haeri Shirazi, Abdulmajeed, Zakhiratul Al-Daraini Fima yata'alla ƙu mi Masa'ib Al-Hussain (A.S) wa As'jabihi, ƙum, Zamzam Hedayat, Bita.
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad fi Marafah Hajjullah Ali al-Abad, ƙum, bugun majalissar Shaikh Mofid, bugu na daya, 1413 AH.
  • Samavi, Muhammad bin Taher, Absar Al-Ain fi Ansar Al-Hossein, ƙom, Daneshgahe Shahid Mahalati, bugu na farko, 1419H.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarihin Al'umam wa Al-Muluk, Beirut, Darul Trath, bugu na biyu, 1387H.

417H.