Garin Ahƙaf
Wannan maƙala ce game da garin Ahƙaf. Domin samun bayanai game da sura da take da wannan suna, sai ku duba shafin Suratul Ahƙaf.
Garin Ahƙaf wani wuri ne da yake a tsibirin jazirar Larabawa inda Sayyidina Hudu da mutanen Adawa suka rayu. Bisa ayoyin Kur'ani, wannan gari da farko ya kasance wuri mai ni'ima kore shar da yake cike da shuke-shuke, Kur'ani ya ba da labarin irin ci gaba da wayewa da Adawa suka kasance tare da shi,[1] amma bayan saɓawa umarnin ubangiji cikin watsi da kiran da Sayyidina Hudu ya yi musu zuwa ga kaɗaita Allah cikin bauta da kuma azaba da aka saukar musu[2] sai wannan gari ya bushe ya zama sahara. Kur'ani ya kawo labarin Adawa cikin suratul Ahƙaf.[3]
A imanin Allama Ɗabaɗaba'i, garin Ahƙaf yana nan a Kudancin jazirar Larabawa, sai dai cewa babu wata alama da ta wanzu daga wannan gari.[4] Tare da haka cikin ayyana haƙiƙanin inda wannan gari yake an samu saɓani tsakanin malaman tarihi da sanin ƙasa;[5] Oman da ƙasar Mahra ta Yaman, Hamadar da take kallon tekuen shahar Yaman, da kuma wasu yankuna tsakanin Oman da Hadramauti suna daga wuraren da ake tsammanin kasancewarsu Ahƙaf.[6] Masana faɗin ƙasa na ƙarnonin tsakiya, sun tafi kan cewa Ahƙaf shi ne dai saharar Rab'ikhali ko wani sashe daga gare shi.[7] A cewar Abdul-Karim Bi Azar Shirazi mazaunan ƙauyukan kudancin jazirar Larabawa suna kiran wani yanki da yake na tsaunuka daga Azfar zuwa Adan da cibiyarsa take Hadramauti da Ahƙaf.[8] Cikin wannan gari akwai wani wuri da aka san shi da sunan maƙabartar Hudu (A.S).[9]
Bayanin kula
- ↑ Suratul Fajr, aya ta 6-8.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1309 AH, juzu'i. 18, shafi. 210.
- ↑ Daneshname Quran WaQuran Fajuhi, 1998, juzu'i. 2, shafi na 1251-1250.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1309 AH, juzu'i. 18, shafi. 210.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1309 AH, juzu'i. 18, shafi. 210.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1309 AH, juzu'i. 18, shafi. 210; Tabarsi, Majma'ul al-Bayan, 1372 AH, juzu'i. 9, shafi na 135-136.
- ↑ Biazar Shirazi, Abdul Karim, BastanShinasi Wa Jografiyayi Tarikhi Qasas Qur'an, 2001, shafi. 307.
- ↑ Biazar Shirazi, Abdul Karim, BastanShinasi Wa Jografiyayi Tarikhi Qasas Qur'an, 2001, shafi. 308.
- ↑ Biazar Shirazi, Abdul Karim, BastanShinasi Wa Jografiyayi Tarikhi Qasas Qur'an, 2001, shafi. 307. Al-Najjar, Qasasul Annbiya, 1406 Hijiriyya, shafi na. 54.
Nassoshi
- Biazar Shirazi, Abdul Karim, BastanShinasi Wa Jografiyayi Tarikhi Qasas Qur'an, Tehran, Ofishin Buga Al'adun Musulunci da Ilimi, 1380.
- Daneshname Qur'ani Wa Qur'ani Fajuhi, juzu'i. 2, editan Baha'uddin Khoramshahi, Tehran: Dostan-Nahid, 1377.
- Tabatabaei, Sayyid Mohammad Hussein, Al-mizan Fi Tafsir Alqur'an, Beirut, Al-Alami Publishing House, 1390H.
- Tabatabaei, Sayyed Mohammad Hussein, Tarikh Anbiya, wanda Qasim Hashemi, Beirut, Al-Alami Publishing House, ya tattara, 1423H.
- Tabarsi, Fadl bn Hassan, Majma'ul-Bayan Fi Tafsirin Alqur'ani, Tehran, Nasser Khosrow, 1372H.
- Al-Najjar, Abdulwahhab, Qasasul Anbiya, Beirut, Farfaɗo Gadon Larabawa, bugu na 9, 1406 Hijira.