Fatima Ƴar Imam Hassan (A.S)

Daga wikishia
Don sauran Qasidu, duba Fatima.

Fatima ƴar Imam Hassan (A.S) (arabic: فاطمة بنت الحسن (ع)) Matar Imam Sajjad (A.S) mahaifiyar Imam Baƙir (A.S), ta kasance ɗaya daga marawaitan hadisai, dangane da ita Imam Sadiƙ (A.S) yana cewa tana daga cikin Mata Muminai, mai tsantseni da kyautata aiki, Allah yana son masu kyautata aiki, Fatima ta halarci filin Karbala an kamata matsayin fusrunan yaƙi. Imam Sadiƙ (A.S) dangane da Kakarsa Ummu Abdullah yana cewa:

کانَت صِدّیقةً لَم تُدرَک فی آلِ الحَسَنِ امرَأَةٌ مِثلُها.

Ummu Abdullah ta kasance mace mai gaskiya da ba a samu irinta ba a ƴaƴan Imam Hassan (A.S). Biharul Al-Anwar, j 46 sh 215; Usulul Alkafi j 2 sh 446.

Gabatarwa

Imam Sadiƙ (A.S) dangane da kakarsa Ummu Abdullah:

کانَت صِدّیقةً لَم تُدرَک فی آلِ الحَسَنِ امرَأَةٌ مِثلُها

ta kasance mai mai gaskiya, ba a taɓa samun mace misalinta ba cikin iyalan Imam Hassan (A.S).

Bihar al-Anwar, juzu'i na 46, shafi na 215; Usul Kafi, Mujalladi na 2, shafi na 446.

Fatima Ummu Abdullah[1] Mahaifinta Imam Hassan (A.S) Mahaifiyarta Ummu Is'haƙ Bint ɗalha Bn Ubaidullahi Altaimi,[2] Ummu Muhammad[3] ko Ummu Abduhu[4] suna daga cikin sauran Alkunyar da ake faɗa mata, cikin wata riwaya Jabir yana cewa ya ga sunan iyayen Imamai cikin Sahifatu Fatima, cikin wannan riwaya ya ga sunan Ummu Abdullah ƴar Hassan Bn Ali Bn Abi ɗalib Mahaifiyar Imam Baƙir (A.S).[5] Ta kasance daga marawaitan hadisi, a cikin litattafan riwaya akwai hadisi da aka naƙalto daga Fatima Bint Alhassan daga Mahaifinta Imam Hassan (A.S),[6] Imam Sadiƙ (A.S) game da muƙaminta yana cewa: ta kasance daga mata Muminai, Mai tsoran Allah mai kyautata aiki kuma Allah yana son masu kyautata aiki.[7]cikin masadir ɗin tarihi ba a kawo tarihin rana da lokacin da ta rasu ba da inda aka binneta.

Aure

Fatima Ummu Abdullah ta auri ɗan baffanta ma'ana Imam Sajjad (A.S) wannan shi ne aure na farko tsakanin jikokin Imam Ali (A.S),[8] cikin naƙalin Nasikhul Tawarikh, Fatima ita ce mata ta farko da Imam Sajjad (A.S) ya aura auren da'imi,[9] aure tsakanin Fatima da Ali Bn Alhusainin (A.S) shi ne sababi danganewar tsatson Imam Baƙir (A.S) ga Imam Hassan (A.S) ta hanyar mahaifiya, sannan yana danganewa da Imam Husaini (A.S) ta hanyar Mahaifinsa, wannan aure ya zama sababin yiwa Imam Baƙir (A.S) laƙabi da Bahashime tsakanin Hashimawa guda biyu, Alawi tsakanin Alawiyyawa biyu, Fatimi tsakanin Fatimawa guda biyu.[10] Daga ribar wannan aure an samu wani ɗa' mai suna Abdullahi,[11] sakamakon kyawunsa da kwarjini da Annurin Fuskara ana masa laƙabi da “Bahir”[12] Abudllah ya girmi ɗan'uwansa Imam Baƙir (A.S) ya kasance wanda ya jiɓanci al'amari Waƙafin Annabi (A.S) da Imam Ali (A.S).[13]

Halartar Filin Karbala

Fatima Bint Hassan, ta halarci filin waƙi'ar karbala an kamata matsayin fursunan yaƙi tare da sauran iyalam Imam Husaini (A.S)[14]

Bayanin kula

  1. Bihar Al-Anwar, juzu'i na 46, shafi na 215.
  2. Shaykh Mofid, Al-Irshad fi Mafarih Hajjullah Alal Al-Ibad, juzu'i na 2, shafi na 20.
  3. Tarikh Madinati Damashƙ, juzu'i na 70, shafi na 261.
  4. A'ayan Al-Shia, juzu'i na 8, shafi na 390.
  5. Bihar Al-Anwar, juzu'i na 36, ​​shafi na 194.
  6. Sayyed Ibn Tawos, Falah al-Sa'il wa Najah Al-Masail, shafi na 138.
  7. Tawarikh Al-Nabi wa Al-Al, Al-Sheikh Mohammad Taƙi Testari, shafi na 90.
  8. Tabari Amoli, Dala'ilul Al-Imamah, shafi na 217
  9. Nasakh Al-Tawarikh Imam Sajjad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, juzu'i na 8, shafi na 40.
  10. A'ayan Al-Shia, juzu'i na 8, shafi na 390; Bihar al-Anwar, juzu'i na 46, shafi na 215; Mentehi Al-Amal, juzu'i na 2, shafi na 173.
  11. Ibn Hajar Asƙalani, Tahzeeb Al-Tahzeeb, Dar Sader, juzu'i na 5, shafi na 325; Khoi, Majam Rijal Al-Hadith, Al Khoi Islamic Foundation, juzu'i na 11, shafi na 283.
  12. Mantehi al-Amal, juzu'i na 2, shafi na 101; Nasakh Al-Tawarikh Imam Sajjad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, juzu'i na 8, shafi na 40
  13. Mantehi al-Amal, juzu'i na 2, shafi na 101; Nasakh al-Tawarikh Imam Sajjad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, juzu'i na 8, shafi na 40
  14. Duba: Ibn Asaker, Tarihin Madina Damashƙ, 1415 Hijira, juzu'i na 70, shafi na 261.

Nassoshi

  • Amin, Mohsen, A'ayan Al-Shi'a, binciken Hassan Amin, Beirut, Dar al-Taarif na manema labarai, Beta.
  • Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarikh Madinati Damashq, Beirut, Bincike na Ali Shiri, Darul Fikr, 1415H.
  • Ibn Hajar Asqlani, Tahzeeb al-Tahzeeb, Beirut, Dar Sader, Bita.
  • Khoi, Abu al-Qasim, Rijal Al-Hadith, Mu'assaseh Al-Khoi Islami.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Usul Kafi, Hasan Hassanzadeh Amoli ya fassara, Kum, Qaim Al Mohammad, 1387.
  • Majlesi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar Al-Jamaeeh shugaban Akhbar al-Aima al-Athar (AS), edita ta ƙungiyar marubuta, Beirut, Dar Ahya al-Tarath al-Arabi.
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Arshad fi Ma'rifah Hajjullah Alal Al-Ibad, Research of Al-Al-Bayt Lahiya Al-Trath Foundation, Qom, International Conference of Lafiya Al-Sheikh Al-Mufid, 1372.
  • Qommi, Abbas, Mentehi al-Amal, Qum, Hijrat Publications Institute.
  • Tabari Amoli, Muhammad bin Jarir, Dala'ilul Al-Imamah, shafi na 217, Qom, Ba'ath, bugun farko, 1413H.