Daƙiƙa:Umarar Tamattu'i
Umarar Tamattu'i na ɗaya daga cikin nau'o'in umara, wadda ake yi tare da Hajjin Tamattu'i. Umarar Tamattu'i ta bambanta da Umara Mufrada, wadda ake yi dabam da aikin hajji.
Umarar Tamattu'i tana ƙunshe da ayyuka biyar, kamar haka: Ihrami. Ɗawafi. Sallar Ɗawafi. Sa'ayi da Taƙsir.
Umara
Umara ita ce jerin wasu ayyukan ibada na shari'a, kamar ihrami, ɗawafi, da sa'ayi tsakanin Safa da Marwa,[1] waɗanda ake yi yayin ziyarar Ɗakin Allah.[2] Umara ta kasu kashi biyu: Umarar Tamattu'i da Umara Mufrada.[3] Umarar Tamattu'i wani ɓangare ne na Hajjin Tamattu'i kuma ana gudanar da ita tare da shi.[4] Amma Umara Mufrada ibada ce mai zaman kanta, wadda ba ta da alaƙa da Hajjin Tamattu'i.[5]
Bisa ga fatawar malaman fikihu, yin umara, kamar yadda yake ga aikin hajji, wajibi ne sau ɗaya a rayuwar Musulmi idan ya cika sharuɗɗanta.[6] Bayan wannan sau ɗaya, duk ƙarin umarar da za a yi mustahabbi ne.[7]
Ayyukan Umarar Tamattu'i
Umarar Tamattu'i tana ƙunshe da ayyuka biyar, kamar haka:
- Ɗaura ihrami a ɗaya daga cikin miƙatai biyar,[8] kuma a cikin watannin Hajji,[9]ta yadda za a gama ayyukan umara kafin azahar ta ranar Arfa.[10]
- Ɗawafi.
- Sallar Ɗawafi.
- Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa.
- Taƙsir (rage wani ɓangare na gashi ko farce).[11]
Bambanci Da Umara Mufrada
Ayyukan Umarar Tamattu'i sun bambanta da na Umara Mufrada ta wasu fannoni, daga cikinsu akwai:
- Umarar Tamattu'i ba ta da Ɗawafin Mata da Sallar Ɗawafin Mata, saɓanin Umara Mufrada.
- A Umarar Tamattu'i dole ne a ɗaura ihrami a watannin Hajji (Shawwal, Zul-Ƙa'ada da Zul-Hijja), amma Umara Mufrada ba ta da wannan sharadi.
- A Umarar Tamattu'i bayan Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa dole ne a yi Taƙsir (Rage wani ɓangare na gashi ko farce), amma a Umara Mufrada mutum na da zaɓi tsakanin Taksir da Halƙi (Aske kai).[12]
- A Umarar Tamattu'i dole ne a ɗaura ihrami daga ɗaya daga cikin miƙatai biyar. Amma a Umara Mufrada wannan ba wajibi ba ne; ana iya ɗaura ihrami daga Adnal Hill, wato mafi kusa da yankin Harami daga wajensa.[13]
Batutuwa Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Muhaƙƙiƙ Hilli, Shara'i'ul Islam, juzu'i na 1, shafi na 275.
- ↑ Shaik Ɗusi, Al-Mabsuɗ, juzu'i na 1, shafi na 296; Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 20, shafi na 441.
- ↑ Mu'assase Da'iratul Ma'arif Fiƙh Islami, Farhange Fiƙh, juzu'i na 5, shafi na 479.
- ↑ Mu'assase Da'iratul Ma'arif Fiƙh Islami, Farhange Fiƙh, juzu'i na 5, shafi na 481.
- ↑ Mu'assase Da'iratul Ma'arif Fiƙh Islami, Farhange Fiƙh, juzu'i na 5, shafi na 485.
- ↑ Don duba misali: Muhaƙƙiƙ Hilli, Shara'i'ul Islam, juzu'i na 1, shafi na 274; Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 20, shafi na 441.
- ↑ Shaik Ɗusi, Al-Mabsuɗ, juzu'i na 1, shafi na 297; Kungiyar Bincike ta Bi'isar Jagoran Juyin Juya Hali, Muntakhab Manasik Hajj, shafi na 59.
- ↑ Imam Khomaini, Tahrirul Wasila, Mu'assase Matbu'at Dar al-'Ilm, juzu'i na 1, shafi na 411.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 18, shafi na 3.
- ↑ Fallahzadeh, Manasik Hajj Wizheye Banowan, shafi na 32.
- ↑ Muhaƙƙiƙ Hilli, Shara'i'ul Islam, juzu'i na 1, shafi na 275.
- ↑ Muhaƙƙiƙ Hilli, Shara'i'ul Islam, juzu'i na 1, shafi na 275 da 276.
- ↑ Mu'assase Da'iratul Ma'arif Fiƙh Islami, Farhange Fiƙh, juzu'i na 5, shafi na 488.
Nassoshi
- Fallahzadeh, Muhammad Husain, Manasik Hajj Wizheye Banowan, Qom, Mawallafar Mash'ar, bugu na goma sha biyu, 1428H.
- Imam Khomaini, Sayyid Ruhullah, Tahrirul Wasila, Qom, Cibiyar Matbu'at Darul Ilmi, bugu na farko, ba tare da kwanan wata ba.
- Kungiyar Bincike ta Bi'isar Jagoran Juyin Juya Hali, Muntakhab Manasik Hajj, Tehran, Mawallafar Mash'ar, bugu na biyu, 1426H.
- Mu'assase Da'iratul Ma'arif Fiƙh Islami Farhange Fiƙh Mutabiƙ Mazhab Ahle al-Bait (A.S), Qom, Cibiyar Mu'assase Da'iratul Ma'arif Fiƙh Islami,, bugu na farko, 1392Sh.
- Muhaƙƙiƙ Hilli, Jafar Bin Hasasn, Shara'i'ul Islam fi Masa'il al-Halal wa al-Haram, bincike da gyara na Abdul-Husain Muhammad Ali Baƙƙal, Qom, Mawallafar Isma'iliyan, bugu na biyu, 1408H.
- Najafi, Muhammad Hassan, Jawahirul Kalam fi Sharhi Shara'i'ul Islam, Beirut, Dar Ihya'il Turasil Arabi, bugu na bakwai, 1404H.
- Shaik Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, Al-Mabsuɗ fi al-Fiƙh al-Imamiyya, bincike da gyara na Sayyid Muhammad Taƙi Kashfi, Tehran, Al-Maktabat Al-Murtadawiyya Li Ihya'i Asaril Jafariyya, bugu na uku, 1387H.