Jump to content

Daƙiƙa:Sayyid Muhammad Kazim Ɗabaɗaba'i

Daga wikishia

Don sauran amfani, duba Ɗabaɗaba'i (Domin Bambancewwa)

Sayyid Muhammad Kazim Ɗabaɗaba'i
Daga cikin Maraji'an Taƙilidi
Cikakken SunaSayyid Muhammad Kazim
NasabaSharifai Gidan Ɗabaɗaba'i
Tarihin haihuwa1248H
MahaifaƘauyen Kesnawiyya, Yazdi.
Tarihin rasuwa28 Rajab 1337H
Mahallin kabariMasallacin Imran Bin Shahin a cikin Haramin Imam Ali (A.S)
Fitattun dangiSayyid Muhammad (Ɗa) Jagoran ƙabilu a yaƙi da Ingila• Sayyid Abdul-aziz Ɗabaɗaba'i Yazdi
MalamaiMuhammad Baƙir Agha Najafi Isfahani•Sayyid Muhammad Baƙir Khunsari•Sayyid Muhammad Hashim Khunsari•Sayyid Muhammad Hassan Shirazi
Wurin karatuIsfahan•Najaf
Wallafe-wallafeAl'urwatul Wusƙa
SiyasaFatawa kan mulkin mallaka na Italiya, Rasha da Ingila• adawa da tsarin mashruɗiyya (Constitutionalism).


Muhammad Kazim Ɗabaɗaba'i Yazdi (1248H–1337H) ya kasance daga cikin manyan malaman fiƙihu na Shi'a kuma marubucin littafin Al-Urwatul Wusƙa, wanda yake daga shahararrun littattafan makarantun hauza. Bayan rasuwar Sayyid Muhammad Hassan Shirazi, ya zama marja'i (shugaban riƙo a al'amuran addini).

Ya kasance daga masu adawa da yuƙurin mashruɗiyya (tsarin kundin tsarin mulki). a lokacin mamayar Italiya a Libya, Ingila a Iraƙ, da Rasha a Iran, ya fitar da fatawa cewa ya zama wajibi ga Musulmi su kare ƙasarsu da addininsu.

Daga cikin malamansa akwai Muhammad Baƙir Agha Najafi Isfahani da Sayyid Muhammad Hassan Shirazi. Daga cikin shahararrun ɗalibansa kuwa akwai: Muhammad Husaini Kashiful Giɗa, Agha Ziya Iraƙi, Sayyid Abdul-Husaini Sharafud-Din, Hassan Ali Nakhudki Isfahani, Sayyid Muhammad Taƙi Khunsari, Sayyid Muhsin Amin, da Agha Buzurg Tehrani.

Littafinsa Al-Urwatul Wusƙa yana daga cikin shahararrun littattafan fiƙihu a hauzar ilimi, kuma an rubuta masa sharhi da hashiya da yawa. littafin Faƙihi Dur Andishi ya kasance game da rayuwarsa, an kuma rubuta littattafai da nazarce-nazarce kan rayuwarsa da tsarin tunaninsa.

Tarihin Rayuwa

Sayyid Yazdi tare da ƴaƴansa

Sayyid Muhammad Kazim Yazdi an haife shi a ƙauyen Kesnawaihi na Yazdi.[1] Mahaifinsa shi ne Sayyid Abdul-Azim, manomi ne. asalinsa yana komawa ga zuriyar Ahlul-Baiti ta sharifai gidan Ɗabaɗaba'i, har zuwa Imam Hassan Mujtaba (A.S).[2]

Game da shekarar haihuwarsa akwai saɓani: a cikin littafin A'ayanush Shi'a an ambaci shekarar 1247H,[3] yayin da Ali Dawani a cikin Nahzate Ruhaniyyun Iran ya naƙalto daga iyalansa cewa 1248H, ne.[4]

Sayyid Muhammad Kazim ya rasu a ranar 28 Rajab 1337H (1298Sh) sakamakon cutar ciwon huhu, kuma an binne shi a Masallacin Imran Bin Shahin a cikin haramin Imam Ali (A.S).[5] a lokacin rasuwarsa, Musulmi Shi'a da Ahlus-Sunna duk sun yi makoki a Iraƙi, kuma a Iran har ma Sarki Ahmad Shah ya halarci taron ta'aziyyarsa.[6]

Ɗaya daga cikin zuriyarsa shi ne Sayyid Abdul-Aziz Ɗabaɗaba'i Yazdi (1308–1374Sh), wanda ya kasance mashahurin masani a fannin rubuce-rubuce da binciken littattafai.[7]

Sayyid Muhammad Kazim Yazdi ya yi aure a Najaf. Ƴaƴansa sun haɗa da: Sayyid Ali, Sayyida Zahra, Sayyid Hassan, Sayyid Mahmud,[8] Sayyid Asadullah,[9] Sayyid Muhammad. (ɗansa) shi ne marubucin littattafai kamar Saha'iful abrar Bi Waza'ifil as'har da Risala fi Fadli al-Kutub wa Iƙtina'iha.[10]

Ya kuma taka muhimmiyar rawa a Ahwaz wajen jagorantar ƙabilu a gwagwarmaya da sojojin Ingila.[11]

Wasu masana sun ɗauki cewa mutuwar Sayyid Muhammad ta kasance shahada, yayin da wasu kamar Agha Buzurg Tehrani (marubucin Az-Zari'a) suka rubuta cewa mutuwa ta kasance ta ɗabi'a. an ambaci ranar rasuwarsa a matsayin 13 Jumadal-Ula 1334H.[12]

MAghabartar Sayyid Muhammad Kazim Ɗabaɗaba'i Yazdi da ɗansa Sayyid Muhammad a Haramin Imam Ali (A.S).

Haka kuma Sayyid Ali Khamna'i ya bayyana cewa Sayyid Muhammad ya tafi yaƙi da Ingila bisa umarnin mahaifinsa, ya kasance muhimmin jagora a fagen fama, amma bai mutu a matsayin shahidi a yaƙin ba; daga baya ne ya rasu.[13]

Rayuwar Ilimi

Karatu Da Ilimi

Sayyid Muhammad Kazim ya fara rayuwa ne yana aikin noma, amma daga baya ya juya zuwa neman ilimi.[14] Ya fara koyon muhimman darusan hauza tun daga shekarar 1256H, a makarantar Mahsaniyya (ko Zu Manar) a Yazdi.[15]

Bayan shekaru huɗu, ya tafi Mashhad domin ci gaba da karatu, inda ya koyi darusan matakin "Suɗuhu" na hauza, tare da ilimin falaki (Astronomy), ilimin taurari, da lissafi. a shekara ta 1265H, ya koma Isfahan,[16] inda ya zauna a Makarantar Sadra, ya halarci darasin Shaik Muhammad Baƙir Najafi, har ya samu izinin ijtihadi daga gare shi.[17]

Makabartar Muhammad Kazim Yazdi a Haramin Imam Ali (A.S) a shekarar 1445H.

a shekarar 1281H, da shawara da gabatarwar Muhammad Baƙir Agha Najafi Isfahani, ya tafi Najaf.[18] Ya zauna a Makarantar Sadr ta Najaf, kuma zuwansa ya zo daidai da rasuwar Shaik Murtada Ansari da kuma canjin jagorancin marja'iyya zuwa Mirzayi Shirazi.

Bayan ɗan lokaci, ya zama limami na sallah a farfajiyar Haramin Imam Ali (A.S).[19]

Bayan tafiyar Mirzayi Shirazi zuwa Samarra, Sayyid Kazim ya ci gaba da zama a Najaf, yana koyar da ilimin hauza, har zuwa lokacin da ya kai matsayin marja'iyya (shugabancin addini).[20]

Matsayin Ilimi

a cewar A'ayanush Shi'a, a darasin Sayyid Kazim Yazdi ana samun kusan mutane 200 suna halarta.[21]

Sayyid Muhsin Amin ya bayyana shi a matsayin faƙihi mai zurfin ilimin lugga da adabi, kuma ya ce littafinsa Al-Urwatul Wusƙa ya kai matakin da duk wanda yake son zama marja'i, yana rubuta hashiya (ta'Aliƙi) a kansa.[22]

Muhammad Garawi a cikin littafinsa Ma'a Ulama'il Najaf al-ashraf ya siffanta Sayyid Kazim Yazdi a matsayin "Tekun ilimi da bincike", kuma masani a ilimin hankAli (Ma'aƙul) da na ruwaya (Manƙul). Ya kuma ce yana da ƙarfin tunawa da fahimta kan dukkan rassan fiƙihu da hadisai.[23]

Sayyid Musa Shubairi Zanjani ya naƙalto daga Agha Ziya Iraƙi cewa Sayyid Muhammad Kazim Yazdi ya fi Akhund Khurasani ilimi (A'lam), saboda tsananin ƙoƙari da zurfin bincikensa a fiƙihu.[24]

a wajen marigayi Sayyid Muhammad Kazim Yazdi, akwai abubuwa uku masu muhimmanci da ke tattare da shi, waɗanda ba kasafai ake samun su a haɗe a irin wannan mataki a wurin malamai ba:

Na farko, zurfin ilimi da ƙwarewa a fiƙihu da cikakken iko kan ƙa'idojin shari'a. Na biyu, tsantsar taƙawa da tsarkin zuciya da kulawa da lamuran kai da ruhi. Na uku kuma, shirin jihadi da tsayuwa wajen kare Musulunci.

a gaskiya, lamuran gwagwarmaya da Ingila masu mamaya da kuma yaƙin da ya faru a Iraki, sun ta'allaka ne da matsayin Sayyid Muhammad Kazim Yazdi, wanda ya kasance a tsakiyar waɗannan abubuwan.

[25]

Jagorancin addini (Marja'iyya)

Sayyid Muhammad Kazim Ɗabaɗaba'i Yazdi ya kai matsayin marja'iyya a shekara ta 1312H, bayan rasuwar Mirzayi Shirazi. a wancan lokaci, akhund Khurasani da Shaik Muhammad Ɗaha Najaf suma suna cikin manyan marja'an Shi'a masu rai. Bayan rasuwarsu, Sayyid Muhammad Kazim Yazdi ya zama marja'i na kaɗai a zamaninsa.[26]

Bayan rasuwarsa, jagorancin marja'iyya ya koma ga Mirza Muhammad Taƙiyyu Shirazi da Sayyid Isma'il Sadar.[27]

Malaman Da Ya Yi Karatu a Wurinsu (Ustazai)

Daga cikin malamansa akwai:

Almajiransa

an kiyasta cewa ɗAlibansa sun kai 350 kamar yadda aka ruwaito a taron tunawa da shi,[37] amma wani bincike ya nuna cewa sun kai aƙalla 750.[38] Daga cikin shahararrun ɗAlibansa akwai:

Wasu sun ɗauka cewa Abdul-Karim Ha'iri Yazdi da Sayyid Husaini Ɗabaɗaba'i Burujerdi ɗAlibansa ne, amma a ra'ayin Sayyid Musa Shubairi Zanjani, wannan ba daidai ba ne; domin su ɗAliban Akhund Khurasani ne.[40]

Ayyukan Rubuce-rubuce

Abul Hasani ya rubuta a cikin littafinsa Faratar az Rush-e Imtihan wa Khatta, cewa Sayyid Muhammad Kazim Yazdi yana da kusan ayyuka 25 na fiƙihu da usul.[41]

Daga cikin waɗannan ayyuka, mafi shahara kuma mafi muhimmanci shi ne littafin Al-Urwatul Wusƙa.[42] Wannan littafi ya samu matsayi mai girma a cikin muhawarar fiƙihu tsakanin malamai, marja'ai da faƙihai, har ma ya zama tushen sharhi da bincike.

Saboda muhimmancinsa, an rubuta masa sharhi da hashiya da yawa[43] Wannan matsayi ya kai har ana kiran marubucin littafin da lakabin "Sahibul Urwa" (Ma'abocin Urwa).[44]

Matsaya Ta Siyasa

Ana cewa Sayyid Muhammad Kazim Yazdi, idan aka kwatanta da sauran manyan maraji'ai na zamaninsa kamar Akhund Khurasani, yana da ƙarancin kai tsaye shiga harkokin siyasa. Yawancin ayyukansa na siyasa sun kasance ta hanyar tura saƙonni (Telgram) da kuma rubuta bayanan matsaya (bayani/declara­tion). Duk da haka, saboda matsayinsa na babban marja'i, wannan ƙaramin aiki nasa ma yana da muhimmanci sosai.[45]

Wasu muhimman matakan siyasarsa

Tallafawa Kamfanin Musulunci

A shekarar 1316H, wasu masu addini suka kafa Kamfanin Musulunci a Isfahan domin yaƙi da tasirin tattAlin arziƙin ƙasashen waje.[46] Sayyid Muhammad Kazim Yazdi, tare da wasu malamai kamar Akhund Khurasani, Mirzayi Husaini Nuri, Shari'at Isfahani, da Sayyid Isma'il Sadar, ya goyi bayan wannan kamfani ta hanyar rubuta yabo (Endorsement) ga littafin Libas al-Taƙwa, wanda ke ƙarfafa sayen kayayyakin cikin gida.[47]

Fatawa Kan Mulkin Mallaka Na Italiya, Rasha Da Ingila

Bayan mamayar Italiya a Libya, da kuma kai hare-haren Rasha da Ingila a Iran, Sayyid Kazim Yazdi ya fitar da fatawa a shekara ta 1329H, a cikin wannan fatawa, ya wajabta shirin tunkarar kafirai daga dukkan Musulmi-Larabawa da Iraniyawa domin korar su daga ƙasashen Musulunci.[48]

Malaman addini na Najaf a lokacin fuskantar rundunar sojin Ingila.

Sanarwar Jihadi A Kan Ingila

A lokacin yaƙin Duniya na Farko da kuma mamayar Ingila a Iraki, Sayyid Muhammad Kazim Yazdi tare da malamai kamar Muhammad Taƙiyyu Shirazi da Shaikush Shari'a Isfahani, sun fitar da sanarwar jihadi a kan Ingila.[49]

A wannan jihadi, ɗansa Sayyid Muhammad ma ya samu shahada.[50]

Matsayin Mashrutiyya (Tsarin Kundin Tsarin Mulki)

a cikin yunƙurin mashruɗiyya, Sayyid Yazdi ya kasance mai ra'ayi daidai da Shaik Fadlullah Nuri, inda ya ke ganin cewa goyon bayan majAlisa (Parliament) dole ne ya kasance idan ya dace da shari'a gaba ɗaya.

Lokacin da Shaik Fadlullah ya je ya yi zaman neman mafaka a Haramin Abdul-Azim Hasani, Sayyid Yazdi ya ba shi goyon baya sosai.[51]

Malaman addini na Najaf a Kazimaini yayin fuskantar rundunar sojojin Ingila.

Bayan harbin majAlisar dokoki ta Iran da manyan bindigogi, kuma lokacin da Akhund Khurasani ke ƙoƙarin dawo da tsarin mashruɗiyya, Sayyid Yazdi ya fitar da fatawa kan haramcin mashruɗiyya domin hana dawowarta.[52]

Bayanin kula

  1. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  2. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  3. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  4. ↑ Bazrafshan, Sayyid Muhammad Kazim Yazdi: Faƙihi Dur Andishi, shafi na 23.
  5. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 48.
  6. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  7. ↑ Sharif Razi, Ganjina-yi Daneshmandan, juzu'i na 9, shafi na 231.
  8. ↑ Musawi Durudi, «Zendegi-name-ye Mokhtasar wa Sal-shomare Fa'aliyyatha-ye Ilmi-ye Ayatullah al-Uzma Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sahibe Al-Urwatul Wusƙa,» shafi na 198.
  9. ↑ Sharafud-Din,, Ma'a Mausu'at Rijal al-Shi'a, juzu'i na 3, shafi na 360.
  10. ↑ َAgha Buzurg Tehrani, Az-Zari'a ila Tasanifish Shi'a," juzu'i na 15, shafi na 8.
  11. ↑ Sharafud-Din, Ma'a Mausu'at Rijal al-Shi'a, juzu'i na 3, shafi na 360.
  12. ↑ Agha Buzurg Tehrani, Az-Zari'a ila Tasanifish Shi'a, juzu'i na 15, shafi na 8.
  13. ↑ https://farsi.khamenei.ir/speech-content?id=22185
  14. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  15. ↑ Musawi Durudi, «Zendegi-name-ye Mokhtasar wa Sal-shomare Fa'aliyyatha-ye Ilmi-ye Ayatullah al-Uzma Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sahibe Al-Urwatul Wusƙa,» shafi na 197.
  16. ↑ Musawi Durudi, «Zendegi-name-ye Mokhtasar wa Sal-shomare Fa'aliyyatha-ye Ilmi-ye Ayatullah al-Uzma Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sahibe Al-Urwatul Wusƙa,» shafi na 197.
  17. ↑ Sadr, Takmilatul Amalil Amil, juzu'i na 5, shafi na 474.
  18. ↑ Musawi Durudi, «Zendegi-name-ye Mokhtasar wa Sal-shomare Fa'aliyyatha-ye Ilmi-ye Ayatullah al-Uzma Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sahibe Al-Urwatul Wusƙa,» shafi na 197.
  19. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  20. ↑ Agha Buzurg Tehrani, Ɗabaƙatul A'lamush Shi'a, juzu'i na 17, shafi na 71.
  21. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  22. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  23. ↑ Gharawi, Ma'a Ulama'il Najafil Ashraf, juzu'i na 2, shafi na 458.
  24. ↑ Shubairi Zanjani, Jur'a-i az Darya, juzu'i na 2, shafi na 455.
  25. ↑ « آیت‌الله خامنه‌ای در دیدار اعضای ستاد برگزاری همایش سید محمد کاظم طباطبایی یزدی», Khamenei.ir.
  26. ↑ Musawi Durudi, «Zendegi-name-ye Mokhtasar wa Sal-shomare Fa'aliyyatha-ye Ilmi-ye Ayatullah al-Uzma Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sahibe Al-Urwatul Wusƙa,» shafi na 193.
  27. ↑ Shubairi Zanjani, Jur'a-i az Darya, juzu'i na 3, shafi na 386.
  28. ↑ Sadr, Takmilatul Amalil Amil, juzu'i na 5, shafi na 474.
  29. ↑ Habib Abadi, Makarimul Asar, Juzu'i 3 shafi 804-806.
  30. ↑ Tabrizi Khiyabani, Ulamaye Mu'asir, shafuffuka na 68–69.
  31. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a,, juzu'i na 10, shafi na 43.
  32. ↑ Agha Buzurg Tehrani, Az-Zari'a ila Tasanifish Shi'a, juzu'i na 14, shafi na 10.
  33. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  34. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 43.
  35. ↑ Sadr, Takmilatul Amalil Amil, juzu'i na 5, shafi na 474.
  36. ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 10, shafi na 154.
  37. ↑ Sulaimani Burujerdi, «Fehresti az Shagerdane Sahibe Urwa,» shafi na 241.
  38. ↑ Duba: Sulaimani Burujerdi, «Fehresti az Shagerdane Sahibe Urwa,» shafi na 241.
  39. ↑ Sulaimani Burujerdi, «Fehresti az Shagerdane Sahibe Urwa,» shafuffuka na 243–264.
  40. ↑ Shubairi Zanjani, Jur'a-i az Darya, juzu'i na 3, shafi na 387.
  41. ↑ Abul Hasani, Faratar az Rawashe «Azmuno Wa Khata,» shafuffuka na 95–96.
  42. ↑ Abul Hasani,Abul Hasani, Faratar az Rawashe «Azmuno Wa Khata,» shafi na 102.
  43. ↑ Duba: Yazdi, al-Al-Urwatul Wusƙa fima Ta'ummu Bihi al-Balwa (al-Muḥashsha), juzu'i na 1, shafuffuka na 3–4.
  44. ↑ Abul Hasani, Abul Hasani, Faratar az Rawashe «Azmuno Wa Khata,» shafi na 105.
  45. ↑ Hatami da Bihishti-Sarisht, «Taƙabul wa Ta'amule Akhund Mulla Muhammad Kazim Khurasani wa Sayyid Muhammad Kazim Yazdi dar Jarayane Inƙilabe Mashruteh,» shafi na 7.
  46. ↑ Ha'eri, Tashayyu' wa Mashrutiyyat dar Iran, shafi na 131.
  47. ↑ Ha'eri, Tashayyu' wa Mashrutiyyat dar Iran, shafi na 131.
  48. ↑ Hatami da Bihishti-Sarisht, «Taƙabul wa Ta'amule Akhund Mulla Muhammad Kazim Khurasani wa Sayyid Muhammad Kazim Yazdi dar Jarayane Inƙilabe Mashruteh,» shafuffuka na 15–16.
  49. ↑ Abul Hasani, Faratar az Rawashe «Azmuno Wa Khata,» shafi na 627.
  50. ↑ Hatami da Bihishti-Sarisht, «Taƙabul wa Ta'amule Akhund Mulla Muhammad Kazim Khurasani wa Sayyid Muhammad Kazim Yazdi dar Jarayane Inƙilabe Mashruteh,» shafi na 18.
  51. ↑ Ha'eri, Tashayyu' wa Mashrutiyyat dar Iran, shafi na 201.
  52. ↑ Hatami da Bihishti-Sarisht, «Taƙabul wa Ta'amule Akhund Mulla Muhammad Kazim Khurasani wa Sayyid Muhammad Kazim Yazdi dar Jarayane Inƙilabe Mashruteh,» shafi na 13.

Nassoshi

  • Agha Buzurg Tehrani, Muhammad Muhsin, Az-Zari'a ila tasanifish Shi'a, Beirut, Mawallafar Darul al-adwa, bugu na biyu, 1403H.
  • Agha Buzurg Tehrani, Muhammad Muhsin, Ɗabaƙatul A'lamush Shi'a, Beirut, Dar Ihya'il Turasil Arab, 1430H/2009M.
  • Amin, Sayyid Muhsin, A'yanush Shi'a, Beirut, Darul Taaruf Lil Maɗbu'at, 1406H/1986M.
  • Gharawi, Muhammad, Ma'a Ulama'il Najafil Ashraf, Beirut, Darul As-Saƙalain, bugu na farko, 1420H.
  • Ha'eri, Abdul-Hadi, ashayyu' wa Mashrutiyyat dar Iran,, Tehran, Amir Kabir, 1364Sh.
  • Habib Abadi, Muhammad Ali, Makarimul Asar fi ahwal Rijal Al-ƙarnain 13 wa 14 Hijira, Isfahan, 1351Sh.
  • Hatami, Husain da Hassan Bihishti-Sarisht.«تقابل و تعامل آخوند ملا محمد کاظم خراسانی و سید محمد کاظم یزدی در جریان انقلاب مشروطه»، (Muƙabala da mu'amalar akhund Mulla Muhammad Kazim Khurasani da Sayyid Muhammad Kazim Yazdi a lokacin Juyin Mashrutiyya.) a cikin Mujallar wata uku-uku ta Ilmi Pajuheshi Ulum Insani Daneshgahe Az-Zahra (S), lamba ta 71, shekara ta 2008M.
  • Mudarris Tabrizi, Muhammad Ali, Raihanatul Adab, Tehran, Mawallafar kantin littattafai Khayyam, 1369Sh.
  • Musawi Durudi, Zahra Sadat, «Zendegi-name-ye Mokhtasar wa Sal-shomare Fa'aliyyatha-ye Ilmi-ye Ayatullah al-Uzma Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sahibe Al-Urwatul Wusƙa,» (Taƙaitaccen tarihin rayuwa da jadawalin ayyukan ilimi), a cikin Majallar Naƙd Kitab Fiƙh wa Huƙuƙ, lamba 9 da 10, bazara da bazarar 1396Sh/2017M.
  • Sadr, Hassan, Takmilatul Amalil Amil, Beirut, Darul Mu'arrikhil Arabi, bugu na farko, 1429H.
  • Sharafud-Din, Abdullah, Ma'a Mausu'at Rijal al-Shi'a, London, Al-Irshad, bugu na farko, 1411H.
  • Sharif Razi, Muhammad, Ganjina-yi Daneshmandan, Qum, 1370Hsh.
  • Sharif Razi, Muhammad, Ganjina-yi Daneshmandan, Qum, 1370Sh.
  • Shubairi Zanjani, Sayyid Musa,Jur'a-i az Darya, Qum, Cibiyar Kitab-Shinasi, 1389Sh.
  • Sulaimani Burujerdi, Mirza 'Ali, «Fehresti az Shagerdane Sahibe Urwa ,» dar Naƙde Kitabe Fiƙh wa Huƙuƙ, (Jerin ɗaliban Sahibil-Urwa”, a cikin Naƙidin Littafin Fiƙihu da Haƙƙoƙi), lamba 9 da 10, bazara da bazarar 1396Sh/2017M.
  • Tabrizi Khiyabani, Ali, Ulamaye Mu'asir, Tehran, bugun dutse (lithograph), 1366Sh.
  • Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-Urwatul Wusƙa (Muhashi), Qum, Ƙungiyar Malamai ta Hauzar Ilmiyya ta Qum, Gidan Buga Littattafan Musulunci, 1421H.
  • Abul Hasani, Ali, Faratar az Rawashe «Azmuno Wa Khata,» Zamaneh Wa Karnameh Ayatullah al-Uzma Agha Sayyid Muhammad Kazim Ɗabaɗaba'i Yazdi "Sahib al-Urwa," (Fiye da hanyar "gwaji da kuskure": Zamaninsa da tarihin ayyukan Ayatullahil Uzma Agha Sayyid Muhammad Kazim Ɗabaɗaba'i Yazdi), Tehran, Cibiyar Mutala'at Tarikh Mu'asir, 1389Sh.