Daƙiƙa:Hassan Bin Fadli Ɗabrisi
Don sauran amfani na kalmar Ɗabrisi, duba: Ɗabrisi (Bambancewa). Hassan Bin Fadli Ɗabrisi, yana daga cikin malaman hadisi na Imamiyya a ƙarni na shida bayan hijira, kuma ɗa ne ga Fadlu Bin Hassan Ɗabrisi. Yana daga cikin malamai na gidan Ɗabrisi, kuma littafin Makarimul Akhlaƙ (Daga cikin shahararrun littattafan ɗabi'a a wajen Shi'a) yana daga cikin wallafe-wallafensa.
Tarihin Rayuwa
Hassan Bin Fadli, wanda ake yi wa laƙabi da Abu Nasr, yana daga cikin zuriyar gidan Ɗabrisi,[1] kuma ɗa ne ga Fadlu Bin Hassan Ɗabrisi (wanda ya rasu a shekara ta 548 bayan hijira), marubucin tafsirin Majma'ul Bayan. Ali Bin Hassan Bin Fadli Ɗabrisi, marubucin littafin Mishkatul Anwar, shi ne ɗan Hassan Bin Fadli.[2]
Babu cikakken bayani game da rayuwar Hassan Bin Fadli Ɗabrisi, haka kuma ba a san ainihin ranar haihuwarsa da rasuwarsa ba.[3] An ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin ɗaliban mahaifinsa,.[4] kuma an ruwaito cewa mahaifinsa ya rubuta tafsirin Jawami'ul Jami'i ne bisa buƙatarsa..[5]
Akwai saɓani game da dalilin danganta kalmar Ɗabrisi ga wannan gida. Wasu sun danganta Ɗabrisi da garin Ɗabris (Tabris) wanda ake cewa sauyawar lafazin Larabci ne daga Tafresh,[6] yayin da wasu kuma suka danganta shi da yankin Ɗabristan (Tabaristan).[7]
Rubuce-rubuce
Mafi shahararren aikin Hassan Bin Fadli Ɗabrisi shi ne littafin Makarimul Akhlaƙ, wanda ake ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin muhimman littattafan Akhlaƙ a wajen ƴan Shi'a.[8]
Haka kuma an danganta littafin Jami'ul Akhbar gare shi.[9] Sai dai Sayyid Muhsin Amin da Jafar Subhani sun ƙaryata cewa shi ne marubucin wannan littafi.[10]
Abul-Ƙasim Gorji, a gabatarwar littafin Jawami'ul Jami'i, ya ambaci cewa an danganta littafin Asrarul Imama ga Hassan Bin Fadli Ɗabrisi.[11]
Kamar yadda aka ruwaito daga ɗansa Ali Bin Hassan Ɗabrisi, bayan da mutane suka karɓi littafin Makarimul Akhlaƙ cikin farin ciki, Hassan Bin Fadl ya fara rubuta littafin Jami'un li Sa'iril Aƙwal wa Hawin li Mahasinitl Af'al (Littafin da ya tattara maganganu daban-daban tare da kyawawan ayyuka), amma bai samu damar kammala shi ba kafin rasuwarsa.[12]
Ɗabrisi ya ruwaito ruwayoyi daga mahaifinsa, kuma Muhazzabud-Ddin Husaini Bin Abul Faraj ya ruwaito hadisai daga gare shi.[13]
Batutuwa Masu Alaƙa
- Fadlu Bin Hassan Ɗabrisi
- Ali Bin Hassan Ɗabrisi
Bayanin kula
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami'i, juzu'i na 1, gabatarwar Gorji, shafi na 2.
- ↑ Subhani, Mausu'at Tabaƙatul Fuƙaha, juzu'i na 6, shafi na 77; Husaini Jalali, Fihrisul Turath, juzu'i na 1, shafi na 566.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami'i, juzu'i na 1, gabatarwar Gorji, shafi na 9.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami'i, juzu'i na 1, gabatarwar Gorji, shafi na 2.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami'i, juzu'i na 1, shafi na 2.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami'i, juzu'i na 1, gabatarwar Gorji, shafi na 2; Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 3, shafi na 29.
- ↑ Mudarris Tabrizi, Raihanatul Adab, juzu'i na 4, shafi na 32–33.
- ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 1, shafi na 158.
- ↑ Hurru Amili, Amalul Amil, juzu'i na 2, shafi na 75.
- ↑ Amin, A'ayanush Shi'a, juzu'i na 5, shafi na 225–226; Subhani, Mausu'at Tabaƙatul Fuƙaha, juzu'i na 6, shafi na 77.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami'i, juzu'i na 1, gabatarwar Gorji, shafi na 9.
- ↑ Ɗabrisi, Mishkatul Anwar, shafi na 1.
- ↑ Hurru Amili, Amalul Amil, juzu'i na 2, shafi na 93; Subhani, Mausu'at Tabaƙatul Fuƙaha', juzu'i na 6, shafi na 76.
Nassoshi
- Amin, Sayyid Muhsin, A'ayanush Shi'a, Beirut, Darut Ta'aruf lil Matbu'at, 1406H.
- Hurru Amili, Muhammad Bin Hassan, Amalul Amil, Bagadad, Laburaren Andalus, 1385H.
- Husaini Jalali, Sayyid Muhammad Husaini, Fihrisul Turath, Qum, Mawallafar Dalil Ma, 1422H.
- Mudarris Tabrizi, Muhammad Ali, Raihanatul Adab, Tehran, Kantin Sayar da Littattafan Khayyam, 1369Sh.
- Subhani, Jafar, Mausu'atut Tabaƙatil Fuƙaha, Qum, Cibiyar Imam Sadiƙ, 1418H.
- Ɗabrisi, Fadl Bin Hassan, Tafsiru Jawami'il Jami', gyaran Abul-Ƙasim Gorji, Qum da Tehran, Cibiyar Gudanarwar Hauzar Ilmiyya ta Qum da Bugawar Jami'ar Tehran, 1377Sh.