Daƙiƙa:Du'a'u Ya Man Arjuhu
| Mai Asali/Mara Asali | Ma'asur (Mai Asali) |
|---|---|
| Ya fito daga | Imam Sadiƙ (A.S) |
| Madogaran Shi'a | Usulul Al-Kafi, Misbahul Mutahajid, Iƙbalul Bi A'amalil Hasana Fima Ya'amal Marra Fis Sana (Littafi) |
| Nazari | Tuhufa Rajabiyya |
| Lokaci | Watan Rajab |
Du'a'u ya man arjuhu, (Larabci: دعاء يا من أرجوه) wata addu'a ce daga Imam Sadiƙ (A.S) da aka yi umarni da karanta ta a watan Rajab. Wannan addu'a ta tattaro dukkanin neman alheri na duniya da lahira da neman tsari daga dukkanin sharrin duniya da lahira. Manya-manyan malaman Shi'a daga jumla Kulaini, Muhammad Bin Umar Kasshi, Shaik Ɗusi da Sayyid Ibn Ɗawus sun naƙalto wannan addu'a.
Kan asasin naƙalin Sayyid Ibn Ɗawus, Imam Sadiƙ (A.S) yayin karanta wannan addu'a ya kasance yana riƙe gemunsa da hannunsa na hagu, yana kuma motsa yatsan shahada na hannunsa na dama. Duk da cewa akwai mabambantan maganganu game da lokacin da ake yin wannan aiki yayin wannan addu'a, wasu daga cikin malamai sun ce ana fara wannan aiki tun farkon addu'ar, wasu kuma sun ce ana yi ne yayin da aka isa gaɓa ta ƙarshe a cikin addu'ar. Wasu kuma sun ce motsa yatsa alama ce ta Tadarru'i (Roƙo, Magiya da marairacewa Allah) da nuna shiga halin tsananin larura.
Addu'ar "Ya man arjuhu" an naƙalto cikin litattafai daban-daban tare da samun ɗan bambanci cikin nassin addu'ar da sanadinta, haka kuma an yi wasicci da karanta a mabambantan lokuta misalin bayan sallolin farilla na yau da kullun, ko kuma cikin sallolin nafila a ranar Juma'a.
Nassin Da Tarjama
Sanadi
Ya man arjuhu, wata addu'a ce da ake jingina ta ga Imam Sadiƙ (A.S) wace Sayyid Ibn Ɗawus (Rasuwa: 664 H), ya naƙalto a cikin littafin Iƙbalul A'amal.[1] Allama Majlisi ya yarda da ingancin sanadin wannan addu'a.[2] Muhammad Bin Umar Kasshi masanin mazajen sanadin riwaya a Shi'a a ƙarni na huɗu hijira ƙamari, shima ya rawaito wannan addu'a.[3] Sai dai cewa Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, yana ganin cewa sanadin wannan addu'a yana da rauni,[4] Na'am ba'arin malamai sun yi suka da raddin kan wannan ra'ayi na Ayatullahi Khuyi tare da jaddada ingancin sanadin riwayar wannan addu'a.[5]
Kwafin farko na wannan addu'a, ya kasance ne ba tare da gaɓa ta ƙarshe na jumlar "Ya Zal jalali Wal Ikram", a cikin littafin Al-Kafi wannan kwafi ya zo,[6] Allama Majlisi ya bayyana cewa sanadin wannan kwafi yana da rauni.[7] Dalilin haka shi ne cikin salsalar sanadin akwai wasu mutane majhulai da a ba sansu ba, kamar Husaini Bin Ammara da Abi Jafar.[8]
Wani kwafin daban tare da bambance-bambance cikin jumlolin addu'ar, ya zo a cikin littafin Misbahul Mutahajjid, na Shaik Ɗusi (Rasuwa: 360H).[9] An ce naƙalin wannan addu'a ta hannun manya-manyan malamai misalin Kulaini, Kasshi, Shaik Ɗusi da Sayyid Ibn Ɗawus yana ba da nutsuwa da tabbaci cewar abin da wannan addu'a take tattare da shi ya fito daga Imam Sadiƙ (A.S).[10] Haka kuma baki ɗayan malaman da suke tattaro riwayoyi da suke da alaƙa da addu'a sun naƙalto wannan addu'a.[11]
Lokacin Karanta Wannan Addu'a
Kan asasin naƙalin Sayyid Ibn Ɗawus, ana karanta du'a'u ya man arjuhu a watan Rajab, safiya da dare da bayan idar da ɗaya daga cikin sallolin farilla na yau da kullun.[12] Tare da haka bisa naƙalin Kulaini a cikin littafin Al-Kafi[13] da naƙalin Kasshi[14] ba a ayyana takaimaiman lokacin karanta wannan addu'a ba.
Shaik Ɗusi a cikin littafin Misbahul Mutahajjid a sashen sallolin nafila na ranar Juma'a, ya naƙalto wata sallar nafila ta neman biyan buƙatu cikin ladubbanta, ana karanta du'a'u "Ya man arjuhu".[15] Haka kuma wannan addu'a cikin ladubban neman haihuwa ana karanta ta a ranar Juma'a.[16]
Abin da Yake Cikin Addu'ar
Cikin addu'a ya man arjuhu, mai karatu yana roƙon Allah ya ba shi dukkanin alherin duniya da lahira, kuma yana neman Allah ya nesanta shi daga dukkanin munanan abubuwa na duniya da lahira, a farko da ƙarshen wannan addu'a yana yabon Allah tare da siffofinsa kyauta da karamci, alal misali a cikin ɗaya daga cikin gaɓoɓin wannan addu'a ya zo kamar haka: haƙiƙa Allah sakamakon tausayi da rahamarsa yana kyauta hatta ga wanda bai roƙe shi ba, da wanda ma bai san shi ba.[17] ba'arin malamai sun fassara jumlar “Ya man arjuhu li kulli khairi” da fawwala al'amura zuwa ga Allah.[18]
Motsa Hannu Da Yatsa A Halin Karanta Du'a'u Ya Man Arjuhu

Kan asasin naƙalin littafin Iƙbalul A'amal, Imam Sadiƙ (A.S) tun daga farkon addu'ar ya man arjuhu har zuwa gaɓar «وَ زِدْنِی مِنْ فَضْلِکَ یا کَرِیم» ya karanta ta, bayan nan sai ya ɗora hannun hagunsa kan gemunsa ya kuma dinga motsa yatsan shahada na hannun damansa har zuwa ƙarshen addu'ar.[19][Tsokaci 1] Allama Majlisi babban malamin hadisi na Shi'a, ta hanyar naƙali daga Sayyid Ibn Ɗawus ya kawo rahoton cewa wannan aiki ana fara shi daga gaɓar «یا ذَا الْجَلَالِ وَ الْإِکْرَام» har zuwa ƙarshen addu'ar.[20] Abdullahi Jawadi Amoli malamin tafsiri na Shi'a, kan asasin riwayar littafin Iƙbalul A'amal ya yi amanna da cewa Imam Sadiƙ (A.S) ya fara wannan aiki ne tun daga farkon wannan addu'a.[21] Shaik Abbas Ƙummi shima ya naƙalto.[22] Muhammad Ali Isma'il Fur Ƙomshe'i ya tafi kan cewa mustahabbi ne yin wannan aiki daga farkon addu'ar.[23]
Jawadi Amoli ya fassara ɗora hannun kan haɓar baki ba a gemu matsayin alama ta tsananin buƙata.[24] Ɗuraihi , marubucin littafin Majma'ul Bayan, ya fassara jumlar «یَلوذ بِسَبّابَتِه» (Yana neman mafaka da yatsan shahadarsa). Da ta zo a cikin riwaya[25] kan motsa yatsa ta kasance domin bayyanar da gazawa da tawali'u da marairaicewa gaban Allah.[26] Allama Majlisi ya fassara shi da motsa yatsan shahada hagu da dama.[27] Kishiyar wannan ra'ayi, wasu daga malamai sun jingina wannan jumla da ɗan gajeren motsin yatsan shahada sama zuwa ƙasa.[28]
Ba'arin masana sun yi amanna da cewa motsin da ake halin karatun wannan addu'a wanda aka bada rahotonsa kaɗai yana hakaito halin Imam Sadiƙ (A.S) bai ƙunshi wani ɓangare daga ibada ba.[29] Kan asasin naƙalin Kasshi, Imam yayin da yake karanta wannan addu'a bai ɗora hannu kan gemensa, kuma bai motsa yatsan hannunsa ba, bari dai bayan gama addu'a ne ya ɗora hannunsa kan gemensa.[30] Wani hali da ne da yanayi da aka fassara shi da alama tawali'u, roƙo da kuka.[31]
Bayanin kula
- ↑ Ibn Tawus, Iqbal al-A‘mal, 1409 H., Juzu‘i na 2, shafi na 644.
- ↑ Majlisi, Zad al-Ma‘ad, 1423 H., shafi na 16.
- ↑ Kashi, Ikhtiyar Ma‘rifat al-Rijal, 1404 H., Juzu‘i na 2, shafi na 667
- ↑ - Khuyi, Mu‘jam Rijal al-Hadith, 1372 S., shafi na 230.
- ↑ - Pishgar, “Guneha, Itibar wa Sakhtare Du'a'eh Ya man Arjuhu”, shafi na 70.
- ↑ - Kulaini, al-Kafi, 1429 H., Juzu‘i na 4, shafi na 559.
- ↑ Majlisi, Mir’āt al-‘Uqul, 1404 H., Juzu‘i na 12, shafi na 458.
- ↑ - Pishgar, “Guneha, Itibar wa Sakhtare Du'a'eh Ya man Arjuhu”, shafi na 69.
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 H., Juzu‘i na 1, shafi na 353 da shafi na 356
- ↑ Ghafuuri-Nejad, “Matane Kawe, Itibare Sanji Wa Dalalate Riwayate Du'a'e Ya man Arjuhu li-kulli Khayr”, shafi na 50
- ↑ «شرح دعای ماه رجب»، Shafin yanar gizo na bayanai na ofishin Ayatollah Makarem Shirazi.
- ↑ Ibn Tawus, Iqbal al-A‘mal, 1409 H., Juzu‘i na 2, shafi na 644.
- ↑ - Kulaini, al-Kafi, 1429 H., Juzu‘i na 4, shafi na 559.
- ↑ Kashi, Ikhtiyar Ma‘rifat al-Rijal, 1404 H., Juzu‘i na 2, shafi na 667
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 H., Juzu‘i na 1, shafi na 353 da shafi na 356.
- ↑ Sheikh Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 H., Juzu‘i na 1, shafi na 378.
- ↑ Ibn Tawus, Iqbal al-A‘mal, 1409 H., Juzu‘i na 2, shafi na 644
- ↑ «شرح دعای ماه رجب»، Shafin yanar gizo na bayanai na ofishin Ayatollah Makarem Shirazi.
- ↑ - Ibn Tawus, Iqbal al-A‘mal, 1409 H., Juzu‘i na 2, shafi na 644
- ↑ - Majlisi, Zad al-Ma‘ad, 1423 H., shafi na 16.
- ↑ Jawadi، درس خارج فقه مبحث بیع، ۱۱ خرداد ۱۳۹۰ش، Madraseh Fakahat.
- ↑ - Qummi, Mafatih al-Jinan, 1388 S., shafi na 229. - Isma‘ilpur Qumsha’i, al-Dalā’il al-Zāhirāt, 1394 S., Juzu‘i na 2, shafi na 120.
- ↑ - Isma‘ilpur Qumsha’i, al-Dalā’il al-Zāhirāt, 1394 S., Juzu‘i na 2, shafi na 120.
- ↑ Jawadi، درس خارج فقه مبحث بیع، ۱۱ خرداد ۱۳۹۰ش، Madraseh Fakahat.
- ↑ Ibn Tawus, Iqbal al-A‘mal, 1409 H., Juzu‘i na 2, shafi na 644
- ↑ - Turiihi, Majma‘ al-Bahrayn, 1375 S., Juzu‘i na 3, shafi na 188. - Majlisi, Zad al-Ma‘ad, 1423 H., shafi na 16. - Pishgar, “Nau’o’i, inganci da tsari na addu’ar Ya man Arjuhu”, shafi na 70. - Pishgar, “Nau’o’i, inganci da tsari na addu’ar Ya man Arjuhu”, shafi na 70. - Kashi, Ikhtiyar Ma‘rifat al-Rijal, 1404 H., Juzu‘i na 2, shafi na 667.
- ↑ Majlisi, Zad al-Ma‘ad, 1423 H., shafi na 16
- ↑ - Pishgar, “Guneha, Itibare Wa Sakhtare Dua'aeh , Ya man Arjuhu”, shafi na 70.
- ↑ - Pishgar, “Guneha, Itibare Wa Sakhtare Dua'aeh , Ya man Arjuhu”, shafi na 70.
- ↑ - Kashi, Ikhtiyar Ma‘rifat al-Rijal, 1404 H., Juzu‘i na 2, shafi na 667.
- ↑ Kashi, Ikhtiyar Ma‘rifat al-Rijal, 1404 H., Juzu‘i na 2, shafi na 667.
Tsokaci
- ↑ Daga bayanin Sayyid a cikin Iqbal ana fahimta cewa Imam Ja’afar Sadiq (a.s) a karon farko ya karanta wata addu’a ga mai ruwaya (Muhammad Sajad), sannan ya koya masa, kuma bisa umarnin Imam ya rubuta wannan addu’a. Wannan addu’a ta kare da jumlar nan: "وَ زِدْنِي مِنْ فَضْلِكَ يَا كَرِيمُ" (Ka ƙara mini daga falalarka ya Mai karamci). Bayan haka Imam ya sake karanta wannan addu’a tare da ƙarin jumla a ƙarshen ta: "يَا ذَا الْجَلَالِ وَ الْإِكْرَامِ يَا ذَا النَّعْمَاءِ وَ الْجُودِ يَا ذَا الْمَنِّ وَ الطَّوْلِ حَرِّمْ [شبابي و] شَيْبَتِي عَلَى النَّارِ" (Ya Mai girma da ɗaukaka, Ya Mai ni’ima da karamci, Ya Mai alheri da tsawo, Ka haramta samartakaina da tsufana ga wuta). A lokacin da Imam ya fara karanta addu’ar, hannunsa yana kan gemunsa, kuma yana motsa yatsan shahada na hannun dama.
Nassoshi
- Aqa Buzurg Tehrani, Muhammad Mohsen, al‑Dhari‘a ila Tasānīf al‑Shi‘a, mai tarawa Ahmad bin Muhammad Husayni, Beirut, Dar al‑Adhwa, ba tare da shekara ba.
- Aqiqi Bakhshayishi, Abdul Rahim, Rukunin masu fassarar Shi‘a, Qum, Ofishin Buga Navid al-Islam, 1387 Sh.
- Ibn Tawus, Ali bin Musa, Iqbal al‑A‘mal, Tehran, Dar al‑Kutub al‑Islamiyya, 1409 H.
- Kashi, Muhammad bin Umar, Ikhtiyar Ma‘rifat al-Rijal, da gyaran Muhammad Baqir bin Muhammad Mirdamad, taƙaitawa daga Muhammad bin Hasan Tusi, Qum, Hukumar Āl al-Bayt (A) don farfaɗo da turath, 1404 H.
- Kulaini, Muhammad bin Ya‘qub, al-Kafi, da gyaran Dar al-Hadith, Qum, Dar al-Hadith, 1429 H.
- Majlisi, Muhammad Baqir bin Muhammad Taqi, Mir’āt al-‘Uqul fi Sharh Akhbār Āl al-Rasul, da bincike da gyaran Sayyid Hashim Rasuli Mahallati, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, 1404 H.
- Majlisi, Muhammad Baqir bin Muhammad Taqi, Zad al-Ma‘ad, da bincike da gyaran Alā’uddin A‘lami, Beirut, Hukumar al-A‘lami don bugawa, 1423 H.
- Qummi, Abbas, Mafatih al-Jinan, Fassarar Husaini Ansariyan, Qum, Dar al-‘Irfan, 1388 Sh.
- Sadrayi Khuyi, Ali, Jerin littattafan rubutattun hadisai da ilimin hadis na Shi‘a, Qum, Hukumar Kimiyya da Al’adu Dar al-Hadith, Hukumar Buga da Yaɗa, 1382 S.
- Safrah, Husaini, Tarihin Hadisin Shi‘a a ƙarni na goma sha biyu da goma sha uku hijira, Qum, Hukumar Kimiyya da Al’adu Dar al-Hadith, Hukumar Buga da Yaɗa, 1385 S.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Misbah al-Mutahajjid da Silah al-Muta‘abbid, Beirut, Hukumar Fiqhun Shi‘a, 1411 H.
- Habib‑Abadi, Muhammad Ali, Makarim al‑Athar dar Ahwal Rijal dawra Qajar, Isfahan, Kamal, 1362 Sh.
- Khui, Sayyid Abu al‑Qasim, Mu‘jam Rijal al‑Hadith wa Tafsil Tabaqat al‑Ruwwat, Qom, Markaz Nashr al‑Thaqafa al‑Islamiyya fi al‑Alam, 1372 Sh
- Muhammad Gafur Nejad، «متن کاوی، اعتبارسنجی و دلالت پژوهی روایات دعای یا من ارجوه لکل خیر»،A cikin mujallar kimiyya ta kwata-kwata ta Hadith Sciences, ranar shiga: 1 ga Nuwamba, 2020, ranar ziyara: 23 ga Fabrairu, 2020.
- «کتابشناسی تحفه رجبیه»، Ƙungiyar Taskar Tarihi da Laburare ta Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ranar ziyara: 14 ga Fabrairu, 2020.
- «شرح دعای ماه رجب»، Shafin yanar gizo na bayanai na ofishin Ayatollah Makarem Shirazi, ranar shiga: Maris 7, 2018, ranar ziyara: Fabrairu 17, 2020.
- Abdullahi Jawadi Amoliصادقیه درس خارج فقه مبحث بیع، ۱۱ خرداد ۱۳۹۰ش، Makarantar Fiqhu, ranar ziyara: 23 ga watan Bahman shekara ta 1399 (Shamsi).
- Fishger Omid«گونهها اعتبار و ساختار دعای یا من ارجوه»،A cikin Mujallar Mobalighan, lamba 225, watan Esfand shekara ta 1396 da watan Farvardin shekara ta 1397. hijira shamsi
- Mahadawi Muslihdin، اعلام اصفهان, wanda Gholam Reza Nasrollahi, Isfahan, Ƙungiyar Al'adu da Nishaɗi ta Isfahan Municipality, ta shirya kuma ta yi bincike a kai, 2007.