Jump to content

Auren Imamul Mahadi (A.F)

Daga wikishia
Aƙidun Shi'a
‌Sanin Allah
TauhidiTabbatar Da AllahTauhidi ZatiTauhidi SifatiTauhidi Af'aliTauhidi IbadiSiffofin ZatiSiffofin Fi'ili
RassaTawassuliCetoTabarrukiIstigasa
Adalcin Allah
Husnu Wa ƘubhuBada'uAmrun Bainal Amraini
Annabta
Ismar AnnabawaKhatamiyyatAnnabin MuslunciMu'ujizaAsalantuwar Kur'ani
Imamanci
AƙiduIsmar AnnabawaWilaya TakwiniyyaIlmul GaibiKhalifatullahiGaibar Imam Mahadi (A.F)MahadawiyyaIntizarul FarajBayyanaRaja'aImamanci Na Nassi
ImamanImam AliImam HassanImam HusainiImam SajjadImam BaƙirImam SadiƙImam KazimImam RidaImam JawadImam HadiImam AskariImam Mahadi
Ma'ad
BarzahuMa'ad JismaniHasharSiraɗiTaɗayurul KutubMizan
Fitattun Mas'aloli
Ahlil-BaitiMa'asumai Goma Sha HuɗuKaramaTaƙiyyaMarja'iyyaWilayatul FaƙihiImanin Mai Aikata Manyan Zunubai

Auren Imam Mahadi (A.F) (Larabci: زواج الإمام المهدي (عج)) yana daga cikin batutuwan da Malamai suke da sabani akai, bangaren da suka amintu da cewa ya yi aure sun jingina ne da wasu riwayoyi da a cikin su aka yi ishara kan `ya`yansa, sannan kuma da kasancewar shi aure karfafaffar sunna ce ta Annabi (S.A.W) da wannan dalili ne suke ganin Hazrat Mahadi (A.F) yana da aure, sai dai cewa kuma wadanda suke da sabani da haka suna ganin yin aurensa baya dacewa da falsafar buyansa (Gaiba), akwai wasu da suka tafi kan cewa duk da cewa akwai yiwuwar ace ya yi aure ba zamu iya fitar da tabbataccen ra'ayi kan hakan ba. Sayyid Muhammad Sadar, Babban Malamin Hadisi Nuri wanda ya bar duniya shekara 1320 h, Ali Akbar Nahawandi wanda ya bar duniya a shekara 1369 h suna daga cikin Malaman da suka tafi kan cewa Imam Mahadi (A.F) ya yi aure. Anfara bijiro da wannan bahasi ta hanyar warwara a littafin Tarihkul Al-gaiba A-lkubra wallafar Ssayid Muhammad Sadar wanda ya bar duniya shekara 1420 h.

Gabatuwar Wannan Bahasi

Malaman Shi'a suna da sabanin ra'ayi dangane kasancewa Imam Mahadi (A.F) ya yi aure ne a zamanin Gaiba ko kuma bai yi ba, cikin littafin Kundin Ilimin Imam Mahadi (A.F) wannan bahasi a karni na sha hudu an fara bijira kansa[1] littafi na farko da ya fara kawo bahasi na warwara kan wannan batu shine littafin Tarikhul Al-gaiba Al-kubra wallafar Sayyid Muhammad Sadar wanda ya bar duniya shekara 1420 h[2] na'am gabanin sa an samu kwatankwacin wannan bahasi a litattafan Najamul Assakib[3] wallafar babban Malamin Hadisi Nuri wanda ya bar duniya 1320 h da kuma Al'abkariyul Hisanu,[4] wallafar Ali Akbar Nahawandi wanda ya bar duniya shekara 1369 hijiri kamari haka kuma cikin Bihar-Anwar akwai wani babi mai taken Kulafa'u Mahadi wa Auladihi wa ma yakunu alaihi wa ala aba'ihi salam,babi ne da kunshi bahasi kan aurensa.[5]

Mahanga

Akwai mahanga guda uku dangane da auren Imam Mahadi:

Wadanda Suka Yarda Da Cewa Ya yi Aure

Assayid Muhammad Sadar,[6] Muhaddis Nuri[7] Ali Akbar Nahawandi[8] dukkaninsu sun aminta da cewa Imam Mahadi (A.F) ya yi aure, haka kuma ya zo cikin littafin Daneshnameh Imam Mahadi (A.S) cewa Allama Majlisi shi ma ance yana cikin jerin Malaman da suka aminta da hakan[9] sannan wadannan Malamai sun dogara da dalilai kamar haka:

  • Shi aure sunna ce ta Annabi (S.A.W) ce kuma Imam Mahadi (AF) shine mafi cancantuwar mutumin da ya kamata ya yi aiki da wannan sunna da wannan hujja ce suka tafi kan cewa ya yi aure lokacin Gaiba.[10]
  • Hadisai da kuma ziyarori da suke Magana kan cewa yana da `ya`ya dalili ne kan cewa ya yi aure. Cikin littafin Daneshnameh Imam Mahadi an kawo riwayoyi daidai har guda goma sha hudu[11] daga ciki akwai shahararren hadisin nan wanda aka fi sani da hadis wasiyya, da ya kunshi bayani cewa bayan Imam Mahadi (A.F) akwai wasu Mahadi guda goma sha biyu daga zuriyarsa da za su zo su karbi ragamar hukuma.[12] Na'am Allama Majalisi ya tafi kan cewa wannan riwaya ta sabawa mashhur, akwai tsammanin cewa abin da ake nufi daga Mahadi sha biyu shi ne Manzon Allah (S.A.W) da kuma Imaman shi'a banda shi Mahadi din.[13] Haka kuma daga cikin hadisan da suka kafa hujja da su akwai riwayar daga Imam Sadik (A.S) wanda a cikinsa anyi ishara cewa Imam Mahadi tareda iyalansa ya je Masallacin Sahala da yake garin Kufa.[14] amma a mahangar wanda basu amintu da cewa ya yi aure suna cewa idan ma mun karbi wadancan riwayoyin to suna nuni kan cewa zai yi aure ya haihu bayan bayyanarsa ba lokacin Gaiba ba.[15]
  • Akwai wasu bayanai da suka kunshi batun rayuwar Imam Mahadi (A.F) a Jaziratul Khadra[16] sai dai kuma an samu wasu Malamai da suka bayyana cewa wannan batun Jazirar Kadra ba komai bane face tatsuniya.[17]

Masu Sabani Da Cewa Ya yi Aure

Dalilan Wadanda Basu Yarda Ba:

  • Rashin dacewar hakan da falsafar gaiba: falsafar gaibar Imam Mahadi (A.S) shine buya daga idanun mutane, aurensa baya dacewa da wannan falsafa, domin yin auren zai iya sanyawa mutane su gano shi.[18]
  • Riwayoyin da suke nuni kan cewa Imam Mahadi (A.F) ba shi da `ya`ya.[19]
  • Babu ishara daga Jakadunsa da Wakilansa: idan Imam Mahadi (A.S) ya yi aure sannan kuma yanada `ya`ya da tabbas wakilansa da jakadunsa za su yi ishara kan haka a lokacin gaiba sugra.[20]

Kame Baki Da Yin Shiru

Kamar yanda ya zo cikin Mausa'atu Imam Mahadi (A.F) dalilan wanda suka amintu ya yi aure da wanda basu amintu da hakan ba suna cin karo da juna da karyata da juna to da wannan ba za mu iya jingina da dalilan dukkanin bangarorin biyu kan bayyanar da makomar mas'alar tarihi,[21] Sayyid Jafar Murtada Amili sanannen mai bincike kan mas'alolin tarihi wanda ya bar duniya shekara 1441 h, ya tafi kan cewa batun cewa Imam Mahadi (A.F) yana da `ya`ya batu ne cikinsa akwai shakku da kokwanto, ba zamu iya fitar da tabbataccen ra'ayi a kai ba.[22]Ayatullahi Safi Gulfaigani daya daga cikin Maraji'an Taklidi wanda ya bar duniya 1444 h yana cewa duk da cewa akwai tsammanin yin aurensa a Gaiba Kubra sai dai kuma a wannan batu fa babu wani ingantaccen hadisi.[23] Ibn Mashhadi, Muhammad Ibn Jafar, Al-Mazar al-Kabir, Edited by Javad Qayyumi Esfahani, Qum, Islamic Publication Office wanda ke da alaka da kungiyar malamai ta Qum Seminary

Nazari

Littafin "Tahlil Mas'ale Izdiwaje Imam Mahadi (A.S)" talifin Muhammad Rida Fu'adiyan, littafi ne da ya yi bahasi da bincike kan dalilan maganganu daban-daban game da auren Hazrat Mahadi (A.S) da kasancewar ya haifi `ya`ya, cibiyar bincike mahadawiyya ta dauki nauyin buga wannan littafi a shekara 2021 miladi.[24]

Bayanin kula

  1. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi (AS), 1393, shafi na 56.
  2. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi (AS), 1393, shafi na 45
  3. Muhaddith Nouri, Najm al-Thaqib, 2003, shafi na 402-407.
  4. Muhaddith Nouri, Najm al-Thaqib, 2003, shafi na 402-407.
  5. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403H, juzu'i na 53, shafi na 145 bayan hijira.
  6. Sadr, Tarikh al-Ghaibah al-Kubari, Dar al-Taarif, juzu'i na 2, shafi na 64
  7. Muhaddith Nouri, Najm al-Thaqib, 2003, shafi na 403.
  8. Nahavandi, Al-Abqari al-Hessan, 2006, juzu'i na 6, shafi.537.
  9. Mohammadi Raishahri, Daneshnameh Imam Mahdi (AS), 1393, shafi na 46.
  10. Muhaddith Nouri, Najm al-Thaqib, 2003, shafi na 403.
  11. Duba Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi (AS), 1393, shafi na 51-46.
  12. Sheikh Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 150.
  13. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 148-149.
  14. Ibn Mashhadi, Al-Mazar Al-Kabir, 1409 AH, shafi na 134-135.
  15. Safi Golpayegani, Pasukeh Dah Pursesh, 2013, shafi na 54.
  16. Duba Muhaddith Nouri, Najm al-Thaqib, 2003, shafi na 405.
  17. Kashif al-Gheta, al-Haq al-Mubin, 1319 AH. P. 87.
  18. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 1393, juzu'i na 3, shafi na 52-53.
  19. Sheikh Tusi, Kitab Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 224.
  20. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi (AS), 1393, juzu’i na 3, shafi na 53.
  21. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, mujalladi na 3, 55-56.
  22. Aamili,Dirasatu Alamat Al-Zhoor wa Al-Jazeera Al-Khadera, 1412 A.H., shafi na 257, Mohammadi Rishahri, Imam Mahdi Daneshnameh, 2013, mujalladi na 3, shafi na 55 ya ruwaito.
  23. Safi Golpayegani, Pasukeh Dah Pursesh, 2013, shafi na 54.
  24. «به قلم محمدرضا فؤادیان بررسی شد؛ آیا امام زمان (عج) ازدواج کرده و فرزند دارد؟» Hukumar yada labaran Hauza Ilimiyya.

Nassoshi

  • Ibn Mashhadi, Muhammad Ibn Jafar, Al-Mazar al-Kabir, Edited by Javad Qayyumi Esfahani, Qum, Islamic Publication Office wanda ke da alaka da kungiyar malamai ta Qum Seminary Society, 1409 AH.
  • «به قلم محمدرضا فؤادیان بررسی شد؛ آیا امام زمان (عج) ازدواج کرده و فرزند دارد؟» Kamfanin dillancin labarai na Hauza , wanda aka buga a ranar 27 ga Yuli, 2019, an duba shi a ranar 21 ga Maris, 1400.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ghaibah, Qum, Al-Maarif Islamic Foundation, 1411H.
  • Safi Golpayegani, Lotfollah, Pasukeh Dah Pursesh, Qom, Ofishin Ayatullahi Safi Golpayegani, 1390. ‮
  • Sadr, Seyyed Mohammad, Tarikh Al-Ghaibah Al-Kubra, Dar al-Taraif, B.T.A.
  • Aamili, Jafar Mortaza, Dirasatu Alamta Zahur wa-Al-Jazeera Al-Khadera, Qum, Manajan Jebel Amil al-Islami, Rukunin Buga da Bugawa, 1412 AH/1992 Miladiyya.
  • Kashif al-Ghata, Jafar, Al-Haq Al-Mubin a cikin yardar al-Mujtahidin da kuma kuskuren al-Akhbariyin, Tehran, Ahmad Shirazi, 1319 AH.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Muhaddith Nouri, Mirzahosein, Najm Al-Thaqib, Jamkaran Mosque, Qom, 2003.
  • Mohammadi Rishahri, Mohammad, Daneshnameh Imam Mahdi (Aj), Kum, Darul Hadith, 2013.
  • Nahavandi, Ali Akbar, Al-Abkari al-Hessan fi ahwal Maulana Sahib al-Zaman (Aj), Qom, Masjid Jamkaran Publication, 1386