Amru Bn Abdi Wuddi
Amru Bn Abdi Wuddi (arabic: عمرو بن عبد ود) wanda aka kashe shekara 5 h kamari; ya kasance daga Jaruman Mayakan Kuraishawa da Imam Ali (A.S) ya kashe su. Ya zo a ba’arin wasu riwayoyi Annabi (S.A.W) ya ce: Saran da Ali ya yi a wannan Yakin ta fifici Ibadar dukkanin Mutane da Aljanu. Ibn Taimiyya Malami daga Ahlus-sunna kuma wanda ya asssasa Salafanci, ya karyata samuwar wani mutum mai suna Amru Bn Wuddi. Wasu ba’arin masu zurfafa bincike suna ganin cewa dalili da ya sanya Ibn Taimiyya karyata samuwar Amru bn Wuddi shi ne Inkarin Falalolin Imam Ali (A.S) Kan asasin wata riwaya daga littafin Al-Manakib Ale Abi Talib, wanda Ibn ShahreAshub ya rubuta, hakika Imam Ali (A.S) cikin gwabzawarsa da Amru Bn Abdi Wuddi bayan Amru Bn Abdi Wuddi ya tofa miyau (Ruwan Baki) a kan fuskar Imam Ali (A.S) sai Imam ya dan dagata da gwabza yaki da shi domin fushin da ya yi ya sauka, bayan fushinsa ya sauka sai ya kashe Amru Bn Abi Wuddi.
Kashe Shi a Yakin Khandak
Litattafan tarihi basu kawo rahoto kan tarihin Rayuwar Amru Bn Abdi Wuddi da kuma ranar da aka Haife shi, in banda batun cewa ya fito daga gidan Banu Amir Bn Lu’ayyi cikin Kuraishawa.[1] kamar yanda ya zo cikin Masadir din `Yan Shi’a da Ahlus-sunna, a lokacin Yakin Khandak a shekara ta 5 h, Amru Bn Abdi Wuddi tare da Ikramatu Bn Abi Jahal,Hubairatu Bn Abi Wahab, Naufal Bn Abdullahi Bn Mugira da Dhiraru Bn Khaddab sun samu da kyar sun tsallake.[2] wawakeken ramin da Musulmai suka haka wanda ya zama shinge tsakanin Rundunoni biyu, Amru Bn Abdi Wuddi wanda ya kasance na uku.[3] cikin jerin Jaruman Mayakan Kuraishawa ana kamanta shi da cewa daidai yake da Mayaka dubu,[4] ya fito yana cika baki yana tayin wanda zai fito ya Gwabza yaki da shi daga cikin Musulmai, ya wulakanta Musulami yana cewa: na daga Murya ina kururuwar neman wanda zai gwabza yaki dani,[5] [Tsokaci 1] kamar yanda ya zo a Masadir din tarihi Ali bn Abi Talib ne kadai ya iya Kalubalantarsa ya tashi domin gwabza yaki da shi, sai dai cewa Annabi (S.A.W) ya nemi ya zauna, sai ya zauna har zuwa lokacin da ya samu izini daga Annabi (S.A.W) Annabi ya daura masa rawaninsa ya bashi takobi domin ya gwabza da Amru bn Abdi Wuddi.[6]
Saran Imam Ali (A.S)
Da farko dai Imam Ali (A.S) ya kira Amru Bn Abdi Wuddi zuwa ga Tauhidi da Muslunta, bayan yaki karbar kira, sai ya nemi ya koma daga inda ya fito, sai yaki yarda, bayan ganin yaki karba dukkanin tayin da ya yi masa, sai ya ce masa ya sauko daga kan Doki ya zo su gwabza, sai ya yarda ya sauko, kan asasin Nakalin Ibn Abil Al-Hadid ya zo cewa Amru Bn Abdi Wuddi bayan ya sauko daga kan Dokin sai ya datsa dokin Gida biyu,[7] ko kuma dai ya Sari Fuskar Dokin sai Dokin Ya ruga ya gudu.[8] kan nakalin Jabir Bn Abdullahi Ansari wanda ya kasance tare da Imam Ali (A.S) ya bayyana cewa Gwabza da kwami ta zafafa tsakanin Imam da Amru Bn Abdi Wuddi, sai kawai aka ji Sautin Imam Allah yana Kabbara, sai Musulmi kawai suka ga ai har Imam ya riga ya kashe Amru Bn Abdi Wuddi.[9] Jabir Bn Abdullahi Ansari yana cikin wadanda a gaban idanunsu wannan gwabzawa ta kasance kuma ya ga sanda Mushrikai suka ranci ta Kare suka arce bayan kashe Amru Bn Abdi Wuddi, ya kamanta kisan Amru da misalin Kisan da Daluta ya yiwa Jaluta.[10] [Tsokaci 2] kan asasin Masadir din Tarihi an bada rahoto cewa Imam Ali (A.S) kari kan Kashe Amru Bn Abdi Wuddi ya kashe dansa da ake kira da Hissal.[11] a ba’arin wasu rahotannin ya zo cewa bayan Imam Ali (A.S) ya kashe Amru Bn Abdi Wuddi ya kamo dansa ya kawo shi gaban Annabi (S.A.W) a lokacin ne Abubakar da Umar suka mike tsaye suka sumbaci fuskar Imam Ali (A.S) shi kuma Annabi (S.A.W) a halin da yake cike da farin ciki fuskarsa nata Annashuwa sai ya ce: wannan nasara ta hakika, a wani nakalin ance ya ce: wannan nasara ce ta farko da aka karya karfi da kwarjinin Mushrikai daga yau ba zasu kara iya yaki damu mu ba mune za mu yake su.[12] Kan asasin abin da ya zo cikin littafin Al-Manakib Ale Abi Talib, talifin Ibn ShahreAshub Mazandarani wanda ya mutu shekara ta 588 h kamari, cikin nakali daga Imam Ali (A.S) ya zo cewa Amru Bn Abdi Wuddi lokacin da yake gwabzawa da Imam Ali (A.S) ya tofa masa Miyau a Fuska, Imam don gudun kada ya zamana ya kashe shi ne saboda ya fusata shi da kuma huce haushi, sai Ya dan dagata kadan har sai da fushinsa ya tafi sannan ya dawo ya kashe Amru Bn Abdi Wuddi saboda Allah,[13] Maulawi wanda ya mutu shekara ta 672 cikin wannan Baiti ya rera waka kamar haka: (daga Ali ake koyan Iklasi/Zakin Allah wanda ya san Gaskiya kuma tsarkakakke daga Damfara), wannan riwaya tana bayanin abin da ya faru tsakanin Imam Ali (A.S) da Amru Bn Abdi Wuddi bayan tofa masa miyau a Fuska. Cikin Masadir Din riwaya an nakalto daga Annabi (S.A.W) ya ce: Saran Imam Ali kan Amru Bn Abdi Wuddi a ranar Yakin Khandak ta fifita kan Ibadar Mutane da Aljanu.[14] cikin ba’arin wasu Masadir na Ahlus-sunna an nakalto cewa Annabi (S.A.W) bayan Saran da Imam Ali (A.S) ya yi kan Amru Bn Abdi Wuddi, ya ce: ya Ali lada ya tabbata a kanka hakika Saran da ka yi yau a kan Amru Bn Abdi Wuddi ta fifici ayyukan Al’umma kuma ta rinjaye su.[15] a wata riwaya da Hakima Naishaburi ya kawo a cikin Al-Mustadarak Alas As-Sahihaini, ya nakalto daga Annabi cewa Saran Ali (A.S) yana tare da fifita kan ayyukan dukkanin Al’umma har zuwa tashin Alkiyama.[16] bayan Imam Ali (A.S) ya kashe Amru Bn Abdi Wuddi bai dauki komai daga kayansa ba, lokacin da a ka tambaye shi me yasa ya yi haka, hatta Sulkensa da babu irinsa a wurin larabawa shima Imam bai dauka ba, sai ya ce: (ina jin kunyar ace in tsaraita al’aurar `Dan Kawuna),[17] [Tsokaci 3] `Yar’uwar Amru ita ma bayan samun wannan labari ta ce: (ba zan taba bakin cikin ba da kashe `dan’uwana, sabida Mutum ne mai kiyaye karamci ya kashe shi, da ace ba shi ne ya kashe shi ba, zan ta yin kuka har zuwa karshen rayuwata).[18]
Shakku Kan Samuwar Amru Bn Abdi Wuddi
Ibn Taimiyya Malamin Ahlus-sunna kuma wanda ya assasa Salafanci ya yi kokwanto a kan samuwar Amru Bn Abdi Wuddi,[19] a imaninsa, ba a taba jin sunansa ko sawunsa ba a cikin Fitattun Yakuna da aka yi misalin; Badar, Uhudu, da sauaran yakoki da aka yi, sannan labarinsa da aka nakalto a lokacin Yakin Khandak babu daya daga Sahihaini (Bukhari da Muslim) da ya kawo labarin.[20] amma tare da haka sauran litattafan tarihi sun nakalto kamar misalin Tarikh Tabari [21] Tarikh Islam na Zahabi,[22] sun kawo hallarar Amru Bn Abdi Wuddi a Yakin Khandak, Hakim Naishaburi Malamin Ahlus-sunna cikin littafin Almustadarak Alas As-Sahihaini, ya kawo wata riwaya ta take hakaito zuwan Amru bn Abdi Wuddi filin Yakin Badar da kuma cewa ma yaji ciwo a wurin.[23] haka kuma cikin litattafan Tarikhi akwai waka da aka nakalto ta Hassanu Bn Sabit Sahabin Annabi (S.A.W) wacce cikinta yake nuna Alfahari kan kashe Amru Bn Abdi Wuddi da Imam Ali (A.S) ya yi.[24] haka zalika akwai wakar Makoki daga Musafi’u Bn Abdul-manaf.[25] Hubairatu Bn Abi Wahab,[26] wadanda suka kasance tare da amaru Bn abdi Wuddi a wurin Yakin Khandak suka tsallake Ramin da Musulmai suka haka,[27] kuma `yar’uwar Amru Bn Abdi Wuddi ta nakalto hakan.[28]
Wasu ba’arin Masu zurfafa bincike sun bayyana cewa dalili da ya sanya Ibn Taimiyya karyata samuwar Amru Bn Abdi Wuddi ba komai bane face son yin Inkarin Falalolin Imam Ali (A.S).[29]
Bayanin kula
- ↑ Misali, duba: Ibn Hisham, Sirah al-Nabi, 1383 AH, juzu'i na 3, shafi na 732; Ibn Asaker, Tarikh Madina Dimashk, 1415 Hijira, juzu'i na 42, shafi na 78; Ibn Athir, Al-kamil fi Al-Tarikh, 1385 AH, juzu'i na 2, shafi na 181.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, 1387 AH, juzu'i na 2, shafi na 573-574; Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 100.
- ↑ Hakim Naishaburi, Al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 34, H4329.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib, 1375 Hijira, Mujalladi na 2, shafi na 324.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 100.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 100.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharhin Nahj Al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 19, shafi na 64.
- ↑ Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi na 100 da na 101.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 102.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 102.
- ↑ Ibn Kathir, Al-Bidaya wa al-Nihaya, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 116; Ameli, Sahih Man Sirat al-Nabi al-Azam, 1426 AH, juzu'i na 11, shafi na 160.
- ↑ Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 19, shafi na 62.
- ↑ Ibn Shahrashob, Manaqib Al Abi Talib, 1375 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 381.
- ↑ Allameh Hilli, Nahj Al-Haq, 1982, shafi na 234.
- ↑ Kundozi, Yanabi'ul Al Mowadda , 1422 AH, Juzu'i na 1, shafi na 284.
- ↑ Sarkin Nishaburi, al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 34.
- ↑ Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 104.
- ↑ Sobhani, Forough Ebedit, 2005, juzu'i na 1, shafi na 628.
- ↑ Ibn Taimiyyah, Minhaj Sunnah Al-Nabawiya, 1406 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 105-110.
- ↑ Ibn Taimiyyah, Minhaj Sunnah al-Nabawiyah, 1406 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 109.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, 1387 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 573.
- ↑ Dhahabi, Tarikhul Islam, 1410H, juzu'i na 2, shafi na 290.
- ↑ Hakim Naishaburi, al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 34, H4329.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabiwiyah, Dar al-Marifa, shafi na 268-269.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabiwiyah, Dar al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 266-267.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabiwiyah, Dar al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 267-268.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, 1387 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 573-574.
- ↑ Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 106-109.
- ↑ Jam'i az Nawisandegan, Imam Ali (AS), Kungiyar Hajji da Hajji, Mujalladi na 2, shafi na 148.
Tsokaci
- ↑ Karfin Amr bin Abdud tare da jajircewarsa ta yadda babu wani musulmi da ya ba da hadin kai ya fito ya gwabza yakida shi. a tarihi cewa a lokacin gwagwarmayar Amru an yi shiru a bangaren Masmana. (Allameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403H, juzu'i na 39, shafi na 4.) Shi ma takobin Amru bin Abdud ana kwatanta shi da harshen wuta, wanda ke nuni da irin hazakarsa da kaifinsa na ban mamaki. (Hakim Nishaburi, al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 34. ↑ Ya yi galaba a kansu da iznin Allah, ya kashe Dawuda da Jaluta, suratu Baqarah, aya ta 251.
- ↑ فَهَزَمُوهُمْ بِاِذْنِ أللّهِ وَقَتَلَ دَاوُدُ جَالُوتَ سوره بقره آیه ۲۵۱
- ↑ A tsarin shari’ar Musulunci, duk wanda ke cikin yaki zai iya daukar ganima kayan yaki na daya bangaren da ya kashe, kamar su sulke da takuba da sauransu, taken wannan shari’a shi ne: (wanda ya kashe abokin gaba yana da hakkin diban kayansa). Farhang Fiqh Farsi, Juzu'i na 4, shafi na 520.
Nassoshi
- Alameh Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, wanda kungiyar malamai ta Beirut, Dar Al-Ahiya al-Tarat al-Arabi, bugu na biyu, 1403H. Kundozi, Suleiman bin Ibrahim, Yanabi Al-Mouda, bincike na Ali Ashraf, Qum, Darul-Aswa na Bugawa da Bugawa, 1422H.
- Allameh Hilli, Hassan bin Youssef, Nahj al-Haq da Kashf al-Saddeq, tare da sharhin Farajullah Hosni da gabatarwar Seyyed Reza Sadr, Beirut, Dar al-Kitab al-Lebanani, 1982.
- Ameli, Jafar Morteza, Sahih Man Sirah al-Nabi al-Azam, Qom, Dar al-Hadith Scientific and Cultural Institute, 1426/1385.
- Bin Abi al-Hadid, Abdul Hamid bin Hibatullah, Sharhin Nahj al-Balaghah, Ibrahim Muhammad Abul Fazl, Qum, Mazhabar Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, ya inganta shi, bugu na farko, 1404H.
- Hakeem Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, bincike na Mustafa Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Katb Al-Elamiya, 1411 AH/1990 AD. Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, Tarihin Musulunci da rasuwar mashahurai da fitattun mutane, bincike na Omar Abd al-Salam Tadmari, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1410H/1990 Miladiyya.
- Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarihin Madina Damascus, Beirut, Darul Fikr, 1415H/1995 Miladiyya.
- Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Al-Kamal fi al-Tarikh, Beirut, Dar Sadhir da Dar Beirut, 1385H/1965 miladiyya.
- Ibn Hisham, Abd al-Malik, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Mustafa al-Saqqah da Ibrahim al-Abiari suka yi bincike da Abd al-Hafiz Shalabi, Beirut, Dar al-Marafa, Beta. Kungiyar marubuta Imam Ali (AS) da kungiyar Hajji da Hajji ta Kum, Bita.
- Ibn Hisham, Abd al-Malik, Sira al-Nabi, Muhammad Muhyiddin Abd al-Hamid, Alkahira, Makaranta Muhammad Ali Sabih, ya yi bincike, 1383/1963 miladiyya.
- Ibn Taimiyyah, Ahmed bn Abdul Halim, Sunnar Annabi a take Kalam na Shi'a Al-Qadriyah, Bincike na Muhammad Rashad Salem, [Riyadh], Imam Muhammad Bin Saud Islamic University, 1406 AH/1986 AD.
- Ibnshahrashoob, Muhammad bin Ali, Manaqib Al Abi Talib, Najaf, al-Matabah al-Haydariyyah, 1375 AH/1956 miladiyya.
- Molavi, Jalaluddin Mohammad Balkhi, Masnavi Manavi, editan Reynold Elaine Nicholson, Holland - Leiden, Bita Hamai, Jalaluddin, Sunan Molavi: Menene Molavi ke cewa?, Tehran, Homa, 2005.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad fi Marafah Hajjullah Ali al-Abad, Bincike na Mu’assasar Al-Baiti don Farfado da Al’adunmu, Qum, taron kasa da kasa na karni na Sheikh Al-Mofid, 1413H.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh al-Tabari: Tarikh al-Rasul al-Maluk: Tarikh al-Tabari, Beirut, Darul-Tarath, 1387H.