Addu’ar Ya Aliyu Ya Azimu
| Maudu'i | Sanin Allah, sanin watan Ramadan |
|---|---|
| Mai Asali/Mara Asali | Mai Asali |
| Ya fito daga | Imam Sadiƙ (A.S) da Imam Kazim (A.S) |
| Madogaran Shi'a | Iƙbalul A'amal, Misbahul Kaf'ami. Zadul Ma'ad |
| Lokaci | Bayan idar sallolin farilla a watan Ramadan |
Addu'ar Ya Aliyu Ya Azimu (Larabci: دعاء يا عَلِيُّ يا عَظِيم) wannan addu'ar tana daga cikin addu'o'i na watan ramadan, wanda aka yi umarnin karantata bayan sallar wajib, sabo da haka ƴan shi'a suna karantata a yayin taro bayan sallah ta wajib, kuma an rawaito wannan addu'a a cikin littafi Iƙbalul A'amal da littafin Misbahul Al-kaf'ami da littafin Zadul Ma'ad daga Imam Sadiƙ (A.S) da Imam Kazim (A.S). kuma wannan addu'a tana da tasiri wajan sanin Allah, da watan Ramadan da kur'ani da daran Lailatul ƙadri da kuma tasirin dasa addu'a a zuciyar ɗan adam.
Matsayin wannan Addu'a
Wannan addu'a ta ya Aliyu ya Azimu tana daga cikin addu'o'in da Makarim shirazi ya ce tana ɗauke da babbar ma'ana[1] Allama Majlisi ya rawaito wannan addu'a a cikin littafin shi mai suna Zadul Ma'ad daga Imam Sadiƙ (A.S) da kuma Imam Kazim (A.S), kuma wannan addu'ar mustahabi ne karantata bayan sallolin wajibi a watan Ramadan.[2] Wannan addu'a tana da tasiri wajan sanin Allah da kuma watan Ramadan da kur'ani da daran Lailatul kadri da kuma tasirin dasa addu'a a zuciyar Ɗan adam.[3]
Sanadin Wannan Addu'a
Farkon wanda ya kawo wannan addu'a ta ya Aliyu ya Azim shi ne Sayyid Ibni Ɗawus ya rasu a shekara ta 664 bayan hijira, a cikin littafin shi mai suna Iƙbalul A'amal ya jingina wannan addu'a zuwa Imam Sadiƙ (A.S) da kuma Imam Kazim (A.S).[4] Kazalika Alkaf'ami ya kawo wannan addu'ar a cikin littafin shi mai suna Almisbah.[5] Allama Majlisi a cikin littafin shi mai suna Zadul Ma'ad.[6] amma addu'ar da ta zo a cikin Almisbahu ta sha banban kaɗan da wadda ta zo a cikin littafin Iƙbalul A'amal da kuma Zadul Ma'ad, misali wannan jumlar ta zo a cikin littafin Iƙbal da kuma Zadul Ma'ad a haka,
amma kuma a cikin littafin Misbah.[8] ga yadda ta zo,
Kamar yadda wannan Jumlar «يَا عَلِيُّ يَا عَظِيمُ يَا غَفُورُ يَا رَحِيمُ...»،[9] ta zo ne a tsohon bugu na littafin Al-iƙbal da wanan sigar [10]«يَا
Abin da Addu'a Ta Tattaro
Bisa abin da Ayatullahi Makarim Shirazi ya faɗa kan wannan addu'a mai albarka ya ce, kowanne ɓangare na wannan addu'a yana ɗauke da saƙo na masamma[11] misali An yi amfani da sashin farko na addu'ar don neman ilimin sanin Allah ta'ala da sifofinshi, sai kuma sashi na gaba yana magana ne akan sifofin watan ramadan, kuma yana cewa Allah ta'ala ya saukar da kur'ani a cikin watan ramadan shiriya ga mutane, kuma Lailatul ƙadri ya fi watanni dubu, kuma ladubban addu'a na ɗaya daga cikin koyarwar wannann addu'ar, wanda Sheikh Makarem Al-Shirazi ya ambata.[12]
Nassin Addu'a
يا عَلِيُّ يا عَظِيمُ يا غَفُورُ يا رَحيمُ، انْتَ الرَّبُّ الْعَظِيمُ، الَّذي لَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ وَهُوَ السَّميعُ الْبَصِيرُ، وَهَذا شَهْرٌ عَظَّمْتَهُ وَكَرَّمْتَهُ وَشَرَّفْتَهُ وَفَضَّلْتَهُ عَلَى الشُّهُورِ، وَهُوَ الشَّهْرُ الَّذي فَرَضْتَ صِيامَهُ عَلَيَّ، وَهُوَ شَهْرُ رَمَضانَ، الَّذي انْزَلْتَ فيهِ الْقُرْآنَ، هُدىً لِلنّاسِ وَبَيِّناتٍ مِنَ الْهُدى وَالْفُرْقانِ، وَجَعَلْتَ فيهِ لَيْلَةَ الْقَدْرِ وَجَعَلْتَها خَيْراً مِنْ الْفِ شَهْرٍ. فَيا ذَا الْمَنِّ ولا يُمَنُّ عَلَيْكَ، مُنَّ عَلَيَّ بِفَكاكِ رَقَبَتي مِنَ النّارِ، فيمَنْ تَمُنُّ عَلَيْهِ، وَادْخِلْني الْجَنَّةَ بِرَحْمَتِكَ يا ارْحَمَ الرَّاحِمِينَ
'([13])
Bayanin kula
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Mafatihul Al-jadida, shafi na 470.
- ↑ Al-Majlisi, Zad Al-Maad, shafi na 84.
- ↑ «شرح دعای «یا عَلِی یا عَظِیمُ» از منظر آیت الله العظمی مکارم»،Kamfanin Dillancin Labarai na Ofishin Mai Girma Ayatullah Makarem Shirazi.
- ↑ Ibn Tawus, Iqbal al-A'mal, juzu'i na 1, shafi na 80.
- ↑ Al-Kafami, Al-Misbah, shafi na 630.
- ↑ Al-Majlisi, Zad Al-Maad, shafi na 84.
- ↑ Ibn Tavus, Iqbal al-Iqmaal, vol. 1, p. 80; Al-Majlisi, Zad al-Ma'ad, shafi. 84.
- ↑ Al-Kafami, Al-Misbah, shafi na 630.
- ↑ Ibn Tawus, Iqbal al-A'mal, juzu'i na 1, shafi na 24.
- ↑ Ibn Tawus, Iqbal al-A'mal, juzu'i na 1, shafi na 24
- ↑ «شرح دعای «یا عَلِی یا عَظِیمُ» از منظر آیت الله العظمی مکارم»، Kamfanin dillancin labarai na ofishin Ayatollah Makarem Shirazi.
- ↑ «شرح دعای «یا عَلِی یا عَظِیمُ» از منظر آیت الله العظمی مکارم», Kamfanin Dillancin Labarai na Ofishin Mai Girma Ayatollah Makarem Shirazi.
- ↑ Ibn Tavus, Iqbal al-Iqmaal, vol. 1, p. 80; Al-Majlisi, Zad al-Ma'ad, shafi. 84
Nassoshi
- Ibn Tawus, Ali bin Musa, Iqbal al-Amal, Tehran, Darul Kutub al-Islamiyyah, bugu na biyu, 1409H.
- Ibn Tawus, Ali bin Musa, 'Iqbal al-A'mal (Iqbal al-Amal), edited by: Jawad Qayyumi Isfahani, Qum, Islamic Publishing Foundation, bugu na 1, 1376H.
- Al-Kafami, Ibrahim bin Ali Al-Amili, Misbah Al-Kafami, Qum, Dar Al-Radi, bugu na biyu, 1405H.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Zadul Al-Ma'ad, bugun: Alaa Al-Din Al-Alami, Beirut, Al-alami Publications Foundation, bugun farko, 1423H.
- «شرح دعای «یا عَلِی یا عَظِیمُ» از منظر آیت الله العظمی مکارم»،Kamfanin dillancin labarai na ofishin Ayatullahi Makarem Shirazi, mai lissafin kwanan wata: 02/17/1399, na duba: 02/17/1403.
- Makarem Al-Shirazi, Nasser, Mafatihul Al-jadida, Qum, Madarasatul Imam Ali bin Abi Talib a.s, bugu na daya, 1431H.