Jump to content

Adawar Imam Khomaini Da Dokar Kafitalasiyon

Daga wikishia
Adawar Imam Khomaini Da Dokar Kafitalasiyon
Hotan takardar dokar Kafitalasiyon
Hotan takardar dokar Kafitalasiyon
Bayanin Abin da ya faruَAdawa da kuma nuna rashin amincewar Imam Khomaini da dokar Kafitalasiyon
LokaciZamanin mulkin Shah Pahlawi
DaliliDokar da majalisar ƙasa ta Iran ta amince da ita, wadda ke bawa sojoji ƙasar Amurka da ke zaune a Iran kariya daga tuhuma da hukunci daga kotunan Iran
SaƙonniKama Imam Khomaini da korar sa zuwa Turkiyya
Mai alaƙaKorar Imam Khomaini Zuwa Turkiyya


Adawar Imam Khomaini da dokar Kafitalasiyon, (Larabci: معارضة الإمام الخميني للاستسلام) nuna rashin amincewa da Imam Khomaini ya yi kan rattaba hannun da majalisar ƙasa ta ti kan ƙudurin doka da ta ginu kan togace sojojin Amurka da suke zauna a Iran daga dokokin ƙasar Iran a lokacin gwamnatin Hassan Ali Mansur. Baya ga Imam Khomaini ya samu labarin rattaba hannu kan wannan ƙudurin doka, a ranar 26 Oktoba 1964m, sai ya rubuta wasiƙa ta adawa kan wannan ƙudiri ya kuma aike da ita a taron da mutane suka yi a gidansa, Imam ya bayyana cewa kana sasin ayar nafyis sabil wannan ƙudirin doka ya saɓawa Muslunci da kur'ani, kuma ba komai bane sai ƙuduri na takardar shaidar mulkin mallaka da bautar da al'ummar ƙasar Iran.

Hukuma Pahlawi ta yi la'akari da wannan tonen silili na Imam Khomaini matsayin barazana ga zaman lafiyar al'umma, cin gashi da cikar baki ɗayan ƙasar Iran, kuma a ranar 4 Nuwamba 1964m, suka aika da jami'an tsaro suka kama Imam Khomaini, tare da korarsa zuwa ƙasar Turkiyya.

Gabatarwa Da Kuma Matsayi

Ƙudurin Kafatalasiyon, wata shawara ce domin samarwa sojojin Amurka da suke zaune a Iran rigar kariya daga dokokin ƙasar Iran[1] wace a ranar 25 Yuli 1964m, firaministan Iran Hassan Ali Mansur ya gabatar a majalisar shura ta ƙasar Iran, kuma a ranar 13 Oktoba na wannan shekara dai aka rattaba hannu kan wannan ƙudurin doka.[2]

Imam Khomaini bayan samun labarin wannan ƙudurin doka da aka rattaba hannu kansa, a ranar 26 Oktoba 1964m, wanda ya yi daidai da zagayowar ranar haihuwa Sayyida Faɗima (S), cikin nuna adawa da wannan ƙudurin doka ne ya aike da saƙo[3] tare da gabatar da jawabi cikin taron malaman hauza da sauran mutane a gidansa, ya kuma bayyanar da nuna rashin amincewarSa kan wannan ƙudurin doka.[4]

Cikin wannan jawabi da Imam ya gabatar a gidanSa da yake birnin Ƙum, ya fara da karanta ayar istirja'i da take nuni da faruwar babbar musiba.[5] A cikin wani ɓangare na jawabinSa, ya tsunduma cikin warwara da bayani filla-filla game da abin da ƙudurin wannan doka yake ƙunshe da shi, ya kuma fito da sakamako na siyasa da zamantakewa daga wannan ƙudiri tare da ambaton misalsalai da wannan ƙudurin doka zai haifar a dokance, alal misali da wani ba'amurke zai kashe marja'in taƙlidi ko wani sarki na Iran, daular Iran da kotukan Iran ba su da haƙƙin hukunta shi, amma da wani ba'iraniye zai taka karen Amurka, to da za a kama shi a hukunta shi.[6] Tare da bayyanar da adawarsa da Imam Khomaini ya yi, sauran malamai da ma'abota addini da ma sauran ƴan ƙasa su ma sun nuna adawarsu da wannan ƙudurin doka tare da neman a soke ta.[7]Ayatullahi Mar'ashi ya yaba da wannan motsi na Imam Khomaini, sannan ya yi amfani da Kalmar "Izzar Muslunci" kan Imam Khomaini.[8]

Kafitalasiyon (A harshen Faransanci:Capitulation) wani haƙƙi ne da a wata ƙasa ake keɓance ƴan ƙasar waje, wanda ya ginu kan cewa da za su aikata lefi cikin wannan ƙasa to ba za a hukunta su a kotukan wannan ƙasar ba; bari dai za mayar da su ainahin kotukan ƙasashensu a hukunta su a can.[9]

Jawabin Imam Khomaini game da dokar Kafitalasiyon:
Bismillahir Rahmaninr Rahim Inna Lillahi Wa inna Ilaihi Raji'un, lallai ni ba zan iya bayyana yadda nake jin baƙin ciki a zuciyata ba... `yan kwanakin nan da suka wuce ne labari ya isa gare ni game da abin da yake faruwa a Iran, baccina ya ƙaranta, ina cikin damuwa sosai, zucita na cikin halin takura. Da tsananin raɗaɗin zuciyata, ina kirga kwanaki ina jiran ranar mutuwa. Iran ba ta da bukukuwan farin ciki; an mayar da bukukuwan Iran makoki. ... Sun sayar da mu, sun sayar da ‘yancinmu. An kasƙantar da martabarmu. Girman Iran ya salwanta.

[10]

Madogara Ta Fiƙihu Kan Adawa Da Kafitalasiyon

Cikin saƙon adawa da rattaba hannun kan ƙudurin dokar Kafitalasiyon da Imam Khomaini ya fitar, ya bayyana cewa haƙiƙa ƙudurin wannan doka ya yi hannun riga da Muslunci da kuma Kur'ani[11] kuma tare da jingina da ayar nafyis sabil,[12] a saƙonsa وَلَنْ يَجْعَلَ اللهُ لِلْكَافِرِينَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ سَبِيلًا Kuma Allah ba zai taɓa ɗora kafirai a kan muminai ba.[13] ya fara da karanta wannan aya.[14]

Malaman fiƙihu kana sasin wannan aya da ƙa'idar nafyis sabil, sun tafi kan cewa duk wani hukunci da duk wata doka da za ta ɗora kafirai a kan muminai, ba ta wuri ba ta da ƙima a Muslunci.[15] Imam Khomaini ya bayyana rattaba hannu kan ƙudurin dokar Kafitalasiyon a matsayin takardar shaidar mulkin mallaka da bautar da al'ummar Iran da kuma sababin ɗora baƙin haure kan ƴan ƙasa, kuma yin shiru kan haka lefi ne babba a muslunci.[16] Tare da buƙatar mutane da kuma sojojin ƙasar Iran su yi fatali da wannan doka ka da su taɓa yarda da ita.[17]

Ku duba: Ayar Nafyis Sabil da Ƙa'idar Nafyis Sabil

Martanin Hukumar Pahlawi Kan Matakan Imam Khomaini

Cikin martani kan jawabin Imam Khomaini, Hassan Ali Mansur, firaministan Iran na wancan lokaci, a ranar 31 Oktoba 1964m, yayin da yake ba dalili da hujja kan amincewa da ƙudurin dokar Kafitalasiyon, ya bayyana cewa wannan ba wani sabon abu ba ne da za a tada hankali kansa, tunda dai hatta a ƙasashen makwabta sun rigaya sun karɓa sun kuma rattaba hannu kan wannan doka. Ya kuma bayyana baƙin cikinsa kan yin adawa da wannan doka, tare da la'akari da yin hakan matsayin ƙasƙantar da sha'anin daular Iran, ya kuma siffanta masu adawar da ginshiƙan biyar na maƙiyan daular Iran.[18] Gwamnatin Pahlawi sakamakon yaɗuwar da wannan tonen silili da Imam Khomaini ya yi musu, sun yanke shawarar kama shi da kuma korarsa daga ƙasar Iran zuwa Turkiyya.[19] A daren 4 Nuwamba 1964m, wasu gayyar kwamando na jami'an tsaro sun kutsa cikin gidan Imam Khomaini, sun kama shi bayan nan sai suka kore shi zuwa ƙasar Turkiyya.[20]

Sawak (Hukumar leƙen asiri ta gwamnatin Pahlawi) a safiyar ranar 4 Nuwamba ne cikin wani bayanan sirri, sun yi bayyana matakan da Imam Khomaini yake ɗauka gaban hukuma a matsayin barazana kan tsaro, cin gashin kai da tabbatuwar cikar baki ɗayan Ira, kuma wannan ne babban dalilin korarSa daga Iran.[21]Wani adadi daga malaman addini da masu huɗuba, daga jumlarsu Sayyid Kazim Ƙarshi su ma sakamakon tuhumarsu da lefin bore kan ƙudurin wannan doka ta Kafitalasiyon, da kuma wayar da kan mutane kan saƙon da wannan doka ke ƙunshe da shi, an kama su an kuma azabtar da su.[22]

Bayan samun nasarar juyin juya halin Muslunci A Iran, cikin wata shawara da sabuwar gwamnatin wuci gadi da ta gabatar ga majalisar shura ta juyin juya halin Muslunci, a ranar 13 Mayu 1979m, an soke dokar Kafitalasiyon.[23]

Kuma Ku Duba: Korar Imam Khomaini Zuwa Turkiyya

Bayanin kula

  1. Mahdavi, Siyasat Kahriji Iran, 1994, shafuka 309 zuwa 313
  2. Mahdavi, Siyasat Kahriji Iran, 1994, shafi na313
  3. Imam Khomeini, Sahifat Imam, bugu na 1389 Hijira Shamsiyya, juzu’i na 1, shafi na 409.
  4. Imam Khomeini, Sahifat Imam, bugu na 1389 Hijira Shamsiyya, juzu’i na 1, shafi na 415.
  5. Aghaei, "Daurane Tab'id Imam Khumaini dar Turkiyye," shafi na 46-47.
  6. Imam Khomeini, Sahifat Imam, bugu na 1389 Hijira Shamsiyya, juzu’i na 1, shafi na 416.
  7. Tabatabai, Faqihan Wa Inqilabe Iran, bugu na 1396 Hijira Shamsiyya, shafi na 15
  8. Tabatabai, Faqihan Wa Inqilabe Iran, bugu na 1396 Hijira Shamsiyya, shafi na 15
  9. Dehkhoda, Lugatnameh Dehkhoda, 1998, juzu'i. 11, shafi. 15762.
  10. Imam Khomeini, Sahifat Imam, bugu na 1389 Hijira Shamsiyya, juzu’i na 1, shafi na 416.
  11. Imam Khomeini, Sahifat Imam, bugu na 1389 Hijira Shamsiyya, juzu’i na 1, shafi na 411.
  12. "Kamran da Amiri-Fard, 'Ka'idar Nafyi al-Sabil da Aiwatarta,' shafuka 110 zuwa 111."
  13. Fassarar Suratu Nisa’i, Aya ta 141
  14. Imam Khomeini, Sahifat Imam, bugu na 1389 Hijira Shamsiyya, juzu’i na 1, shafi na 409.
  15. Bajnordi, Al-Qawāʿid al-Fiqhiyyah, bugu na 1419 Hijira Qamariyya, juzu’i na 1, shafuka 187 zuwa 188; Fadhil Lankarani, Al-Qawāʿid al-Fiqhiyyah, bugu na 1383 Hijira Shamsiyya, shafi na 233.
  16. Imam Khomeini, Sahifat Imam, bugu na 1389 Hijira Shamsiyya, juzu’i na 1, shafi na 420.
  17. Imam Khomeini, Sahifat Imam, bugu na 1389 Hijira Shamsiyya, juzu’i na 1, shafi na 409-412
  18. Mas’ud Asadullahi, Ihya Kapitulasiyon wa Payamadhaye An, bugu na farko, 1373 Hijira Shamsiyya (daidai da 1994), shafuka 99 zuwa 100
  19. Mas’ud Asadullahi, Ihya Kapitulasiyon wa Payamadhaye An, bugu na farko, 1373 Hijira Shamsiyya (daidai da 1994), shafuka 99 zuwa 96-98
  20. "Tolu'i, Bazigaran Asre Pahlavi Az Furūghī Ta Fardust, bugu na 1376 Hijira Shamsiyya (daidai da 1997 Miladiyya), juzu’i na 1, shafi na 495."
  21. "Tolu'i, Bazigaran Asre Pahlavi Az Furūghī Ta Fardust, bugu na 1376 Hijira Shamsiyya (daidai da 1997 Miladiyya), juzu’i na 1, shafi na 495."
  22. Ruhani, Nehzat Imam Khomeini, bugu na 1381 Hijira Shamsiyya (daidai da 2002 Miladiyya), juzu’i na 1, shafi na 1047.
  23. Jaridar Etelat, Mayu 14, 1979, p. 4.

Nassoshi

  • Aghaei, Abdolreza, "Daurane Tab'id Imam Khumaini Dar Turkiyya", a cikin Mujallar Roshd Ilimin Tarihi, No. 35, Summer 2009.
  • Asadollahi,Masoud, Ihya Kafotalasiyun Wa Payamadhaye An,Tehran,Ungiyar yada farfagandar Musulunci,Bugu na Farko,1994.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Sahifeh Imam, Tehran, Cibiyar Tattaunawa da Buga Ayyukan Imam Khumaini, Bugu na Biyar, 2009.
  • Bojanvardi, Seyyed Hassan, Al-Qawwa'id al-Fiqhiyyah, Bincike na Mehdi Mehrizi da Mohammad Hassan Derayati, Kum, Al-Hadi, Bugu na Farko, 1419 Hijira.
  • Dehkhoda, Ali Akbar, Lugathnameh Dehkhoda , Tehran, Tehran University Press, 1998.
  • Rouhani, Sayyid Hamid, Nehzate Imam Khumaini, Tehran, Oruj, bugu na 15, 2002.
  • Jaridar Etlatla, 14 ga Mayu, 1979.
  • Tabatabai, Sayyid Hadi, FaqqihaneInqilabe Iran, Tehran, Kavir, bugu na uku, 2017.
  • Tolo'i, Mahmoud, Bazigaren Asre Pahlavi Az Foroughi Ta Ferdoust, Tehran, Alam, bugu na 4, 2017.
  • Fazil Lankarani, Mohammad, Al-Qawa'id al-Fiqhiyyah, Kum, Cibiyar Fiqhu ta Imamai Tsarkaka, 2004.
  • کامران، حسن و امیری‌فرد، زهرا، «قاعده نفی سبیل و تطبیقات آن»،A cikin mujallar Fikh da Ijtihād da ake bugawa sau biyu a shekara, lamba ta 3, lokacin bazara da rani na shekarar 1394 Hijira Shamsiyya (daidai da 2015 Miladiyya).
  • Mahdavi, Abdolreza (Hooshang), Siyasat Khariji Iran Daurane Pahlawi, 1931-1978, Tehran, Alborz, bugu na farko, 1994.