Abdus-Salih (Laƙabi)
Abdus-Salih (arabic: العبد الصالح) ma'ana Bawan Allah nagari, wani isɗilahi ne daga Alƙur'ani da aka yi amfani da shi kan wasu Mutane, Masadir na Shi'a da Ahlus-sunna sun naƙalto cewa ana yi wa Imam Kazim (A.S) laƙabi da Abdus-Salih sakamakon yawan ibadarsa Wannan kalma ta zo cikin Alƙur'ani cikin sigar jam'i (Ibadikas As-salihin) [1] haƙiƙa Alƙur'ani ya kira Nuhu da Luɗu [2] da Bayin Allah Nagargaru [3] haka kuma akwai riwayoyi da suka nakalto cewa ana yi wa Zil-ƙarnaini laƙabi da Abdus-Salih. Kan asasin Masadir na Shi'a da Ahlus-Sunna sakamakon yawana Ibadar Imam Kazim (A.S) shima ana masa laƙabi da Abdus-Salih [4] cikin Sanadin ba'arin wasu riwayoyi da aka nakalto daga gare shi an ambaci sunansa da wannan laƙabi [5] Cikin Ziyarar Hazrat Abbas da aka rawaitota daga Imam Sadiƙ (A.S) an kiraye shi Abdus-Sailh. [6] haka ma cikin Ziyarar Muslim bin Aƙil [7] da Hani bin Urwa [8] duka biyun an musu sallama tare da gaisuwa da laƙabin Bayin Allah nagargaru. [9] haka cikin sallama a sallah ana gaisuwa cikin faɗin (Assalamu Alaina wa Ala Ibadallahis As-Salihi)
Bayanin kula
- ↑ Suratul Namal, aya ta:19
- ↑ Suratul Tahrim, aya ta 10.
- ↑ Majlesi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 12, shafi na 199; Ayashi, Tafsir, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi na 343.
- ↑ Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 AH, juzu'i na 13, shafi na 29; Yagoubi, Tarikh Yakubi, Darsader, juzu'i na 2, shafi na 414.
- ↑ Misali: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 177, 539, Mujalladi na 3, shafi na 59, 109, Mujalladi na 4, shafi na 72, 412.
- ↑ Ibn ƙolawieh, Kamel Al-Ziyarat, 1356, shafi na 257; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 98, shafi na 277.
- ↑ Ibn Mashhadi, Al-Mazar Al-Kabir, 1419 AH, shafi na 178; Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 97, shafi na 428.
- ↑ Ibn Mashhadi, Al-Mazar Al-Kabir, 1419 AH, shafi na 180; Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 97, shafi na 428.
- ↑ Imam Khumaini wa Digaran, Risaleh Tauzihul Al-masa'il (Maraji'u), Daftare Intisharat Islami, juzu’i na 1, shafi na 598.
Nassoshi
- Ibn ƙolawieh, Jafar bin Muhammad, Kamel al-Ziyarat, bugun Abdul Hossein Amini, Najaf, Dar al-Mortazawieh, 1356.
- Ibn Mashhadi, Al-Mazar Al-Kabir, Edited by Jaɓad ƙayyumi Isfahani, ƙum, Islamic Publication Office mai alaka da kungiyar malamai ta ƙum Seminary Society, 1419 AH.
- Imam Khumaini da Ruhollah wa Digaran, Risalaeh Tauzihul masa'il (Maraji'u), wanda Sayyid Mohammad Hasan Bani Hashemi Khomeini da Ehsan Usoli, ƙum, ofishin yada labaran Musulunci, Beta suka hada.
- Baghdadi, Khatib, Tarikh Baghdad, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 1417H.
- Ayashi, Muhammad Bin Mas'ud, Tafsir Al-Ayashi, Seyyed Hashim Rasouli Mahalati ya gyara, Tehran, Al-Mattabah Al-Alamiya, 1380H.
- Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, al-Kafi, Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, suka yi bita, 1407H.
- Majlesi, Mohammad Baƙir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
- Yaƙoubi, Ahmad bin Abi Yaƙoob, Tarikh yaƙoubi, Beirut, Dar Sader, B.T.A.