Abdullahi Nasir Jumu'a

Daga wikishia

Abdullah Nasir Jumu'a (Larabci: عبداللهي ناصر جمعة) an haifeshi a shekara ta 1932 - 2022, wanda aka fi sani da Abdullah Nasir, malamin addini na Shi'a a ƙasar Kenya, kuma ya taka rawar gani wajen yaɗa Shi'anci a Kenya da yankunan Afirka. A baya ya kasance malamin Ahlus-sunna, sannan ya zama ɗan Shi'a a wajajen shekara ta 1975 miladiyya.

Daga cikin ayyukanshi na wayar da kan jama'a da addini har ya kafa makarantar addini mai dauke da sunan Imam Ali (A.S), da ɗakin nazarin karatu watau laburare (Library), munazara (Muƙabala) da malaman Wahabiyawa, kuma ya kasance mamba a majalisar Ahlul Baiti (A.S) ta duniya. da kuma gabatar da laccocin addini a ƙasashe daban-daban na Musulunci, ya kuma rubuta littafai sama da 25 a cikin harshen Sawahili kan Musulunci da Shi'anci. A lokacin ƙuruciyarshi, Abdullahi Nasir ya yi gwagwarmayar neman `yancin kai kan Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a ƙasar Kenya, kuma ya kasance memba a taron kundin tsarin mulkin ƙasar Kenya san da suka shirya samun `yancin kai daga turawan Ingila.

Tarihi

Abdullah Nasir Jumu'a malamin shi'a ne daga ƙasar Kenya ya karbi jagorancin wani sashe na `yan shi'a a Kenya a matsayinshi na mai ilimi bayan juyin juya halin musulunci na Iran.[1] An haife shi a shekara ta 1932 miladi birnin Mombasa na ƙasar Kenya daga gidan Ahlus-Sunna.[2]

A shekara ta 1950 miladiyya ya koma Zanzibar a Tanzaniya, sannan ya shiga kwalejin ilimin tarbiya, sannan ya koma Mombasa, sannan aka naɗa shi malami a makarantar firamare ta Larabawa da kuma mu'assar tarbiyyar musulmi ta Mombasa.[3]

A shekarar 1950 miladiyya ya tafi Nairobi babban birnin ƙasar Kenya, inda ya yi aiki a matsayin mai kula da sashen Larabci da Sawahili a tashar BBC, sannan ya zama manajan editan yaɗa labarai na jami'ar Oxford da ke yankin gabashin Afirka, daga shekarar 1974 zuwa 1977. ya yi aiki a matsayin shugaban jarida a Jami'ar Oxford a reshen Afirka ta Gabas, sannan a 1980 ya koma Mombasa.[4]

Rasuwa

Abdullahi Nasir ya rasu a ranar 11 ga watan Junairun shekara ta 2022 miladiyya yana da shekaru 89 a duniya, a birnin Mombasa na kasar Kenya.[5] an binne shi a makabartar Kanjawi a Mambasa.[6]

Shi'ancewa

Shaikh Abdullah Nasir ya karɓi mazhabar Shi'a cikin shekarar 1960 ƙarnin da ya gabata, kuma a shekarun baya ya kasance malamin Ahlus-Sunna.[7] kuma ya bayyana kanshi bayan ya gano Falalolin Imam Ali (A.S) cewa ta yiwu shi Imam Ali (A.S) ya fi sauran Sahabbai. Sannan ya ce, bayan karanta littafin Al-Ghadir na Allama Amini da sauran littafai, sai na gane cewa akidar Shi'a ita ce akidar gaskiya, a shekara ta 1975 miladiyya ya karɓi akidar Shi'a gaba ɗaya.[8]

A farkon shekara 1980 na ƙarnin da ya gabata, bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran, ya shelanta shi'ancinsa,[9] wanda hakan ya rage masa farin jini da matsayinsa a wajen Ahlus-Sunna [10] kuma ya bayyana cewa cibiyoyi masu alaka da Wahabiyawa sun yi kokarinsu Domin hana shi karɓair Shi'anci, amma abin ya faskara.[11]

Ayyukan Wayar Da Kan Al'umma Da Na Siyasa

Gabatar da lambar yabo ta Al-Abbasiya ga Abdullah Nasser, wanda tsohon shugaban kungiyar Al-Khoja Al-Athni Ashariya a Afirka ne a watan Afrilun 2011, saboda yabon ayyukan addini.

Abdullah Nasir ya kafa makarantar hauza ta Imam Ali (A.S) a ƙasar Kenya, ya kuma gudanar da muƙabala tare da Muftin Wahabiyawa,[12] ya kuma gabatar da huɗubobi a ƙasashen Tanzaniya, Indiya, Pakistan, ƙasar Ingila, da Amurka cikin harshen Ingilishi da Swahili.[13] ayyukanshi su na da tasiri wajan yaɗa Shi'anci a Kenya da sauran yankunan Afirka.[14]

Daga cikin sauran ayyukan da ya yi har da kasancewarshi mamba a Majima'a Alami Ahlul Baiti[15] ya kafa ɗakin laburare domin amfanin jama'a[16] A cikin watan Afrilu shekara ta 2011 miladiyya aka ba shi lambar yabo ta Abbasiyawa da wata ƙungiyar 'yan Shi'a mai suna (Isna Ashara Koja) a Afirka a taronsu na Majalisar koli a zamansu na saba'in da biyu, wanda aka gudanar a Mombasa, don ayyukan addini da wa'azi na Abdullahi Nasir.[17]

Kafin ya sanar da sauya sheƙa daga shekara ta 1978 zuwa 1980 miladiyya ya kasance mai wakiltar gabashin Afirka a Majalisar Matasan Musulmi ta Duniya, wace take birnin Jiddah a kasar Saudiyya.[18]

Abdullah ya ba da gudunmawa tin yana cikin kuruciyarshi a tsakanin shekarun 1958 zuwa 1963 miladiyya, a yunkurin da ake yi na yaƙar ƴan mulkin mallaka a ƙasar Kenya Har ila yau mamba ne a taron kundin tsarin mulkin ƙasarshi a Lancaster House da ke birnin Landan wanda aka gudanar domin samun 'yancin kai na ƙasar Kenya daga turawan Ingila. ƴan majalisar ƙasar Kenya sun zaɓe shi a matsayin wakili na garin Mombasa[19]

Ayyuka

Abdullahi Nasir ya rubuta littafai kusan 25 da Rasaloli akan Shi'anci a cikin harshen Sawahili, kuma ya fassara wasu sororin kur'ani, an buga fassarar wasu daga cikin ayyukanshi zuwa Turanci da yaren Ruwanda (wadda ɗaya ne daga cikin harsunan wasu yankuna na Afirka).[20]

Shi'a da Taƙiyya: Abdullah Nasir ya rubuta littafin (Shi'a da Taƙiya, (Majibu na Maelezo Shi'a da Taƙiya) a cikin harshen Sawahili.[21] a matsayin raddi ga littafin Mai suna Kuɗuɗul Arida li Usus allati ƙama alaiha Dinush Shi'a Imamiyya Al'isna Ashariyya wanda Muftin Wahabiyya Mufti Muhib Din Alkaɗib ya rubuta wanda ya rasu 1389 hajira, wanda kuma aka buga da yaran Sawahili, Abdullah Nasir Juma'a ya yi magana a cikin wannan littafi kan takiyya da mas'alolin Shi'a a zamanin Umayyawa da Abbasiyawa. , da takiyya a mahangar Ahlus-Sunna da Shi'a.[22]

Ga ba'arin sunayen litattafai da Abdullahi Nasir ya rubuta:

Bamgon littafin Yazid Was Never Amir Mumin
  • Shia na Qur'ani: Majibu na Maelezo (الشيعة والقرآن)[23]
  • Shia na Sahaba: Majibu na Maelezo (الشيعة والصحابة)[24]
  • Shia na Hadith: Majibu na Maelezo (الشيعة والحديث)[25]
  • Ukweli wa Hadith ya Karatasi (حقيقة حديث القرطاس)[26]
  • Mut'a Ndoa ya Halali (المتعة الزواج الحلال)[27]
  • Malumbano Baina ya Sunni na Shia (الخلاف بين الشيعة والسنة)[28]
  • Sura al-Ahzaab: Tafsiri na Maelezo (تفسير سورة الأحزاب)[29]
  • Tafsiri ya Sura at-Talaaq (تفسير سورة الطلاق)[30]
  • Yazid Hakuwa Amirul-Mu'minin (يزيد لم يكن أمير المؤمنين)[31]
  • Hadith Al-Thaqalayn: Hadith Sahihi (حديث الثقلين)[32]
  • Ahlul Bayt: Ni Nani, Si Nani (أهل البيت)[33]
  • Maulidi: Si Bida, Si Haramu (الميلاد النبوي ليس بدعة ولا حرام)[34]
  • Tafsiri ya Juzuu ya 'Amma (الترجمة السواحيلية لعم جزء)[35]

Bayanin kula

  1. «وضعيت شيعيان كنيا»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  2. «درگذشت عالم بزرگ شیعه در کنیا»، خبرگزاری شبستان.
  3. "Alhaj Sheikh Abdillahi Nassir Juma", Africa fedration، نسخه بایگانی شده؛ تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی با سایت باحساب.
  4. "Alhaj Sheikh Abdillahi Nassir Juma", Africa fedration، نسخه بایگانی شده؛ تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی با سایت باحساب.
  5. "Alhaj Sheikh Abdillahi Nassir Juma", Africa fedration، نسخه بایگانی شده؛ تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی با سایت باحساب.
  6. "DEATH ANNOUNCEMENT (LOCAL)- UPDATE SAD DEMISE OF Sheikh ABDILAHI NASSIR JUMA", KSI Jamaat Mombasa.
  7. Steven Reese, «The Transmission of Learning in Islamic Africa»2004 ,p. 219.
  8. «عالم بزرگ شیعه کنیا درگذشت»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  9. Steven Reese, «The Transmission of Learning in Islamic Africa»2004 ,p. 219.
  10. Steven Reese, «The Transmission of Learning in Islamic Africa»2004, p. 212.
  11. «عالم بزرگ شیعه کنیا درگذشت»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  12. «عالم بزرگ شیعه کنیا درگذشت»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  13. "Alhaj Sheikh Abdillahi Nassir Juma", Africa fedration، نسخه بایگانی شده؛ تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی با سایت باحساب.
  14. «عالم بزرگ شیعه کنیا درگذشت»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  15. "Alhaj Sheikh Abdillahi Nassir Juma", Africa fedration، نسخه بایگانی شده؛ تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی با سایت باحساب.
  16. "Alhaj Sheikh Abdillahi Nassir Juma", Africa fedration، نسخه بایگانی شده؛ تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی با سایت باحساب.
  17. "Alhaj Sheikh Abdillahi Nassir Juma", Africa fedration، نسخه بایگانی شده؛ تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی با سایت باحساب.
  18. «عالم بزرگ شیعه کنیا درگذشت»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  19. «عالم بزرگ شیعه کنیا درگذشت»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  20. «عالم بزرگ شیعه کنیا درگذشت»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  21. Nassir, Shia na Taqiya, 2003.
  22. «عالم بزرگ شیعه کنیا درگذشت»، خبرگزاری اهل بیت (ابنا).
  23. Nassir, Shia na Qur'ani, Bilal Muslim Mission of Tanzania.
  24. Nassir, Shia na Sahaba, Bilal Muslim Mission of Tanzania.
  25. Nassir, Shia na Hadith, Bilal Muslim Mission of Tanzania.
  26. Nassir, Ukweli wa Hadith ya Karatasi, 2003.
  27. Nassir, Mut'a Ndoa ya Halali, Ahlul Bayt Centre .
  28. Nassir, Malumbano Baina ya Sunni na Shia, Ahlul Bayt Centre .
  29. Nassir, Sura al-Ahzaab, 2005.
  30. Nassir, Tafsiri ya Sura at-Talaaq, Shungwaya.
  31. Nassir, Yazid Hakuwa Amirul-Mu'minin, Bilal Muslim Mission of Kenya.
  32. Nassir, Hadith Al-Thaqalayn, Ahlul Bayt Centre .
  33. Nassir, Ahlul Bayt, Ahlul Bayt Centre .
  34. Nassir, Maulidi, Bilal Muslim Mission of Kenya.
  35. Nassir, Tafsiri ya Juzuu ya 'Amma, Bilal Muslim Mission of Kenya.

Nassoshi