Abdullahi Ɗan Misma'a Al-hamdani

Daga wikishia

Abdullahi ɗan Misma'a Al-Hamdani (Larabci: عبد الله بن مِسمَع الهَمْداني) ya rayu a shekara ta 60 bayan hijira, yana daga cikin ƴan shi'ar Kufa, kumA Abdullahi ɗan Misma'a shi ne wanda ya kai wasiƙa ta farko tare da Abdullahi ɗan Wal Al-tamimi, daga mutanan Kufa zuwa ga Imam Husaini (A.S).

Bisa abin da Aɗ-ɗabari ya ruwaito (Wafati: 310 bayan hijira), shahararren marubucin tarihi, a cikin littafinshi mai suna Tarikh Al-umam wa Al-muluk, ya nakalto daga Abu Muknif cewa,'yan Shi'an Kufa bayan sun sami labarin rasuwar Mu'awiya ɗan Abi Sufyan. (a ranar 15 ga watan Rajab shekara ta 60 bayan hijira), sun taru a gidan Sulaiman ɗan Surad Al-Khuza'i, sai Sulaiman ya sanar da su cewa, Hussain (A.S) ya ki yin mubaya'a ga Yazid ɗan Mu'awiya, sannan ya ce musu: Ku ƴan Shi'arshi ne, kuma ƴan Shi'ar mahaifinsi ne, don haka idan kun san cewa ku magoya bayanshi ne kuma mayaƙan makiyinshi, to ku rubuta mashi wasiƙa [1]. Don haka sai suka rubutawa Imam Husaini (A.S) wasiƙa suna kiranshi da ya zo Kufa, kuma Abdullahi ɗan Saba'a Al-Hamdani ya ɗauki wannan wasiƙa tare da Abdullahi ɗan Wal, sai suka miƙata zuwa ga Imam Husaini (A.S) a ranar 10 ga watan Ramadan. shekara ta 60 bayan hijira, a lokacin yana cikin garin Makka [2] Shaikh Mufid ya ruwaito wannan ruwaya a cikin littafinshi mai suna Al-Irshad kuma sunan wanda ya ɗauki wasiƙar shi ne Abdullahi ɗan Misma'a Al-hamdani [3], sai dai cewa ɗan ƙutaiba ya ambaci sunanshi a cikin littafinshi Al-Akhbaru Al- ɗawil da sunan Ubaidullah ɗan Subai'a[4].

Bayanin kula

Nassoshi