Abdullahi Ɗan Misma'a Al-hamdani
| Cikakken Suna | Abdullahi Ɗan Misma'a Al-hamdani |
|---|---|
| Mahallin Rayuwa | Kufa |
| Ayyuka | Kai sakon wasiku farko-farko na `yan shi'ar kufa ga Imam Husaini (A.S) |
Abdullahi ɗan Misma'a Al-Hamdani (Larabci: عبد الله بن مِسمَع الهَمْداني) ya rayu a shekara ta 60 bayan hijira, yana daga cikin ƴan shi'ar Kufa, Abdullahi Ɗan Misma'a shi ne wanda ya kai wasiƙa ta farko tare da Abdullahi Ɗan Wal Al-tamimi, daga mutanan Kufa zuwa ga Imam Husaini (A.S).
Bisa abin da Aɗ-ɗabari ya ruwaito (Wafati: 310 bayan hijira), shahararren marubucin tarihi, a cikin littafinshi mai suna Tarikh Al-umam wa Al-muluk, ya nakalto daga Abu Muknif cewa, `yan Shi'ar Kufa bayan sun sami labarin rasuwar Mu'awiya Ɗan Abi Sufyan.(a ranar 15 ga watan Rajab shekara ta 60 bayan hijira), sun taru a gidan Sulaiman Ɗan Surad Al-Khuza'i, sai Sulaiman ya sanar da su cewa, Hussain (A.S) ya ki yin mubaya'a ga Yazid Ɗan Mu'awiya, sannan ya ce musu: ku ƴan Shi'arshi ne, kuma ƴan Shi'ar mahaifinsi ne, don haka idan kun san cewa ku magoya bayanshi ne kuma mayaƙan makiyinshi, to ku rubuta mashi wasiƙa.[1] Don haka sai suka rubutawa Imam Husaini (A.S) wasiƙa suna kiranshi da ya zo garin kufa, Abdullahi ɗan Saba'a Al-Hamdani ya ɗauki wannan wasiƙa tare da Abdullahi ɗan Wal, suka miƙata zuwa ga Imam Husaini (A.S) a ranar 10 ga watan Ramadan. shekara ta 60 bayan hijira, a lokacin yana cikin garin Makka.[2] Shaikh Mufid ya ruwaito wannan ruwaya a cikin littafinshi mai suna Al-Irshad kuma sunan wanda ya ɗauko wasiƙar Abdullahi ɗan Misma'a Al-hamdani,[3] sai dai cewa Ibn Ƙutaiba ya ambaci sunanshi a cikin Al-Akhbaru Attawil da sunan Ubaidullah ɗan Subai'a.[4]
Ku Duba Masu Alaƙa
Bayanin kula
Nassoshi
- Ibn Qutaybah al-Dinawari, Ahmad ibn Dawud, الأخبار الطوال، Qum, Sharif Radhi Publishing, 1373H.
- Sheikh Al-Mufid, Muhammad ibn Muhammad, الإرشاد في معرفة حجج الله على العباد، Gyara: Mu’assasa Aal al-Bait, Qum, Laburare Sheikh Mufid Hazara, 1413H.
- Al-Tabari, Muhammad ibn Jarir، تاريخ الأمم والملوك، Beirut, Al-Aalami Publications Foundation, 1409 AH.